Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 61

93K to 96K   out of 180.1K words

tofa a wannan maganar ba. Abba dan Allah na fa'da maka ina da damuwa da shi?"
Ya girgiza kai ya ce "Baki fa'da mini ba. Sau biyu kunnena na jiyo mini sadda kake fa'din na cuce ka. Kuma indai ina da hakkin akan ka, ba zata koma ba".

Hawaye ya balle mini, na rasa inda zan saka raina.
Yayin da Yaya Sadik ya shiga wani irin yanayi mai wahalar wa.

Cikin tsawa Abba ya ce mini "Tashi ki bani waje shasha da baki san ciwon kanki ba. Me zaki yi da namijin da zai kushe ki. Yana fa'da miki zaman alfarma yake yi da ke.
Matu'kar ni din ubanku ne, na raba auren kenan".
Jikina na rawa na tashi ina ha'da hanya, ina jin rabani da Gudale tamkar rabani da farin-ciki ne gaba'daya.
A gado na kwanta ina wani irin kuka, mai cin rai.
Ban dan yadda suka 'kare ba. Washagari dai ya kira ni a waya, yana mini sababin na ha'da masa munafurci, sai na yi murna tunda na shiga tsakaninsa da ubansa.
Murya na rawa nake kare kaina.
"Wallahi ban fa'da wa Abba komai ba, ka yarda da ni, ka ga fishin da kake yi da ni, ya jefa ni damuwa, jiya sai da likita ya ce jinina ya dan hau na rage damuwa. Dan Allah ka daina tayar mini da hankali, akan abin da kasan ba zan yi ba".
Jikinsa ya dan yi sanyi ya ce "Ga ni nake yi baki damu da ni bane. Ni kawai na damu ki dawo gare ni".
"Na damu fah Yaya Gudale! Ji nake yi kamar idan an kwanta na tsallako ta katanga".
Ya ce "ko yar sirirya ce ke ai cikin jikinki ba zai bamu wannan damar ba. Kar ki fara tsallakowa, ban son ku ji ciwo.
Amma idan kina son na yarda ba sa hannun ki, to ki shammace su ki taho zan bar kofar gadern a bu'de."
Zuciya 'daya na ce "To".
Wani abin almara. Abba sai ya fahimci kudirina. Sai ya rufe kofar garden da 'kwado.
Sannan ya ja kunnen maigadi kar a bari na fita.
Hakan ya sake firgita ni, mussaman yadda Yaya Sadik ya tsananta tayar mini da hankali.
Rannan unexpected Abba ya karbe wayoyina.
Kwanaki biyu baya samun wayata.


* Wajen Baban Yara*
Tun daga masallacim sallar asuba ya bi Baba ya ce "zasu yi magana. Sun zauna a falonsa tsawon lokaci, ya kasa cewa koami.
"Sadik ka ce zamu yi magana! Kuma ka yi shiru".
"Baba ka je ka samu Abba ya dawo mini da matata yau fiye da sati biyu yana ri'ke da ita. Ya ce sai na saketa"
"Ashha amma ban sani ba! aka ce hutawa take yi sai jikinta ya yi 'kwari."
"Ba wani hutawa Baba! Kawai yana son ya tozarta ni ne, an taba yin hakan? Ana zaune lafiya ace sai ka saki mace?
Idan kuma da nine na yi hakan sai ace na yi wula'kanci, amma ni an rufe ido ana wula'kanta ni".
"To kai ba abin da ka yi ya yanke wannan hukuncin, na sani Alhaji bashi da son zuciya".
"Haba Baba! Saboda Allah ka bi bayana mana kawai, ina zaka tsaya bin ba'asin me na yi? Yo mi sai na yi laifi ne yake hukunta ni?
Bansan me suke 'kullawa shi da ita ba, tunda ya zugeta ko wayarta ma bata shiga".
Jikin Baba ya sanyi ya ce "To kwantar da hankalinka. Zan same shi zamu tattauna".
"Yaushe zaka je?"
Sadik ya tambaya a hanzarce.
"Zuwa anjima"
"A a Baba ni ba zan iya ha'kuri ba! Kawai ka je yanzu. Ni wallahi ban ta'ba shiga rudani irin haka ba. Bana iya barci, komai ya tsaya mini cak, hatta aikin office ban da Anti Rabi mai fahimta ce ai da komai ya cakalkale mini. Gaskiya a bani matata kawai".
A take Baban ya mike ya ce "kwantar da hankalinka! Bari na je na dawo".
Duk yadda Baban ya so su yi magana da Abba fir abin ya faskara domin Abban ya kafe sai Sadik ya kawo masa takardar Halimatu tunda cutarsa ya yi da ya bashi auren ta.
Baba ya ce "Haba Alhaji! Ya za'a yi ka shiga sha'anin aure? Yara suna son junansu, ka rabu da su".
"Oh Ibrahim fa'da mini yadda zan yi! Ina ce dana ha'da auren ban shawarce ka ba? Yanzu kuma da zan raba ne zan shawarce ka saboda kana ganin ka fini tsinkaye?"
Nan da nan Baba ya dinga fa'din"Ba haka bane wallahi! Ka yi ha'kuri."
Cikin fishi ya ce "ka fitar mini daga wannan maganar idan ba so kake na ci mutuncinka ba".
Ya dinga bawa Yayan nasa ha'kuri. Ya tafi guiwa a sace".

Yanayin Baba ka'dai ya tabbatar wa Sadik abin yafi karfinsa sannan al'amarin babba ne. Domin Baban cewa ya yi "ka je wajen Yayar 'Kwalli. Ni ba zai saurare ni ba".
Da ga wajen Baba, ya doshi Kwalli ya je ya kinkimo Yayar takanas domin gaba'daya ya birkice.
Dake gaba take da Abba sai bai bude mata wuta ba. Kamar yadda ya yiwa mahaifin Halimatu.
Ta kuma bada umarnin ya bawa yaro matarsa bata son haka.
Cikin ladabi ya ce "saurare ni Yaya! Cikin girma na bashi aure, kuma a gabana ya amsa zai ri'ke ta da amana. Amma kinsan kullum a cikin fa'din na cuce shi yake saboda na yi masa auren dole. Sannan Bayan auren ya wula'kanta ni, ya gudu ya barta tsawon wata biyu ba'a san inda yake ba, ba waya ba aike.
Sannan bai gane gata na yi masa ba, sai yake nunawa alfarma yake yi mana ni da ita.
Sai dai ki yi hakuri! Wallahi ba zan bashi ita ba, alhalin baya sonta a dole yake zaune da ita".
Rantsuwar Abba ta kidima Gudale. Wani irin firgici ya shige shi. 'Kirjinsa ya yi nauyi dama ya sani guduwar nan da Umma ta ingiza shi ya sai ta zame masa sanadin baci rai mai tsananin gaske a wajen Abba.











# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*SUNA RENTING KAYAN AMARE*
*SUNA SAYAR DA SUTTURUN MATA ZABBABU, NA ALFARMA, DA KAYAN KICIN*.
*SUNA SIYAN KAYAN FURNITURES KO ELECTRONICS NA HANNU*
*SUNA KUMA SAYARWA*.
*SUNA SAYAR DA FILI DA GIDA*.
*SUNA BADA HAYAR GIDA*.
*KOMAI DA RUWANKA NE AMYAS GASU DA SANIN DARAJAR CUSTOMER. KAYANSU KUMA MASU INGANCI NE KUMA MASU RAHUSA NE*.
*08083909947*.



*SDK*
*59-60*.

Sai dai bai yi zaton kashe masa aure ne hukuncinsa ba.
Zufa ta dinga karyo masa, duk da yanayin bana zafi bane.
Murya na rawa ya ce "Indai akan rashin sonta ne ka rantse ba zaka dawo mini da ita ba, sai na ce Alhamdulillah.
Domin kaffara bata hau kanka ba Abba. Na rantse da Ubangiji ina son ta, kuma wallahi 'karya na fa'da tsagwaronta da na ce ka cuce ni, gata ka yi mini na sani".
Ya fa'da a hankali.
Zuciyar mace mai rauni, nan da nan sai tausayin sa ya kama Yaya. Ta ce "Alhaji! Yi ha'kuri ka bashi matarsa, ai yanzu ya gane komai, gaba kuma ba zai sake ba".
Abba ya numfasa ya ce "Ba zan bashi ba Yaya! Na gaji da auren ne fa gaba'daya. Wannan yaron bashi da mutunci ko ka'dan ya tisa yarinya da tijara iri iri, tsoronsa take ji kamar me".

Yaya ta ce "To indai ba zaluntarta ya ke yi ba ina ruwanka? Ita ba ta ce ta gaji ba, sai kai ne zaka ce ta gaji? To tsakanin mace da miji sai Allah ba abin mamaki bane Halimatu ta yi maka tustu akan wannan maganar.
Bashi matarsa kawai, ha'kuri zamu yi da Sadik ai, mu ci gaba da yi masa addu'a. Na kuma tabbatar karfin addu'ar ce ta sanya ya tsaya a iya hakan ma".
Abba ya yi shiru alamun bai gamsu ba.
Yayin da Gudale yake jin salama na shigarsa tunda Yaya bata zafafa ba dole Abba ya ha'kura.

Sanin halin Abba da Yaya ta yi na kaifi daya ne ya sanya ta ce "Alhaji yi hakuri na sani ranka ya baci sosai, amma tunda har ya je ya dauko ni, ya gamsu na isa da kai, to yi masa afuwa ya shiga rigata".
Sai lokacin Abba ya ce "Rabu da shi! Yanzun ma na sani ina bashi ita zai tisa ta a gaba da tijarar ta kawo kararsa, sannan nifa tunda cutarsa na yi na bashi ita, to lah shakka sai na janye cutarwar nan".
Da azama Gudale ya ce "Na rantse Abba ba zan tada maganar ba. Ko uffan ba zan cewa Guduyo akan wannan maganar ba".
Yaya ta nisa ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Bana son na matsaka maka ne Alhaji! Saboda na sani duk abin da zaka yi babu son zuciya a ciki. Amma zan so ace ka ha'kura ni ce shaida idan ya kuma fa'din hakan ko ya yi abind da ya saba ka'ida ba zan shiga cikin hukuncinka ba. Amma yanzu ka bashi matarsa tunda yana son ta".

Wata irin ajiyar zuciya ta kwacewa Gudale ta farin ciki.
Amma sai ya ji Abba yana cewa "Ba zata koma ba, sai ya biya ni, komai da na yi masa a harkar auren, zan zauna na yi lissafi. Gida dai da mota na bar masa halak malak.
Amma tunda ga kan lefe har hidimar abinci da sallamar amarya da kawayenta , da duk wata hidimar da na yi sai ya dawo mini da ku'dina.
Idan ya dawo mini da su zan gamsu ba dole na yi masa ba, yana son ta.
Sannan ba maganar na cuce shi.

Yaya ta ce "Shikenan zai kawo abin da zai iya, amma kaima kasan irin kudin da ka narkar bai isa samunsu ba."

Cikin fishi Abba ya ce "ai kuwa sai ya nemo su, ko zai shekara goma ne. Sannan na harmata masa ya yi bashi, ko ya je ya yi ro'ko, ko ya tisa Yan uwansa a gaba su bashi."
Ya zuba masa ido sosai. Ya ce " Wallahi matu'kar wata ta tallafa maka a cikin su, ko ka yi bashi ba zan saurareka ba, idan kuma ka yi mini karya ko zamba Ubangiji zai ganar da ni".
Tashin hankali sosai a tare da Gudalen Ummah. Ko iya ku'din lefe aka ce ya dawo da su ina zai iya samo wadannan milyoyin?
Sannan uban shanu da raguna da aka dinga gasawa a aurensa kadai ina zai iya biyan ku'dinsu da albashinsa, bare a ha'do da sauran hidimomi?
Zufar da ta daina keto masa, ta dawo tana yanko masa fiye da ta farko.
Murya babu amo sosai ya ce "Abba ina zan samo wadannan kudaden saboda Allah?
Gashi ka ce kada na tambayi kowa, ban da haka da ba za'a dauki lokaci mai yawa ba, zan kawo maka tunda 'kararrawa zan ka'da musu kowacce dole ta fito da ku'di da gwalagwalai ta bani".
A lalace Abba ya ce "saboda kai ne Gudalensu ko? Matan dai sune madogararku daga kai har uwar taka. To Billahillazi duk wacce ka je ta baka ku'di ban yafe ba".

Gudale ya fara fusata domin ya tsani ace Yan uwansa mata sun fi shi amfani. Ya kalli Yaya da ta yi sukuri ya ce "Yi hakuri Yaya! Ni na janyo miki wannan 'bacin ran. Ni nasan zafin da ake ji idan ka bawa na 'kasanka umarni ya bijire. Na kuma rayu a gidan nan ne cikin ba'kin cikin fikon da kowa ya yi mini.
Guduyo kawai na girma! Komai za'a yi mini, duk gaskiyata Abba ya kan ce na yi ha'kuri ai ni ne 'karamin su. Hatta Ashiru na ki, zai zo har gidan nan ya ci mutuncina, amma 'koluluwar abin da Abba zai ce Yayanka ne ai. Dan haka dole ka yi hakuri da su tunda sun girme ka. Haka idan muna rikici da Sakina ita zai bawa gaskiya ya ce ita ce Babba dole na yi mata biyayya. Har na dauka wajibi ne na 'kasa ya yiwa na samansa biyayya".
Abba ya ka'du da kalaman Sadik da 'karara yana yi ne dan ya tunzura Yaya ta ga bekensa, ta yi fishi da shi. Kafin ya yi magana ya ji Sadik din Ya sake cewa "zan ha'do iya abin da zan iya samu, tunda ni ban ce a yi mini biki irin na 'yan gata ba, alhalin ni ba gatan ne da ni ba."
Ya mi'ke tare da sanya hannunsa ya 'daga Yaya cak. Ya ce "mu je na mayar da ke, ki yi ha'kuri, da wannan iyakar da aka nuna miki".
Ai kuwa nan da nan Yaya ta fara share 'kwallah.
Yayin da Abba ya harzuka ya mi'ke da nufin maka masa wani abin. Gudale ya fice da sauri ya na cewa "A to ai gaskiya ne, kullum sai ka ce ita din ba yayarku ba ce kawai, Uwace ta saosai. Amma an kasa bari na shiga rigarta."
Abba ya dinga bawa Yaya ha'kuri yana cewa "Kar ki bari maganarsa ta shige ki, domin so yake ya hada mini rikici, ya mini sanadin rashin walwala tunda ya sani, ba abin da yake hana ni sukuni irin ace kina cikin damuwa ko matsala. Ba sai na ce miki komai ba akan fitinarsa. Idan ban dauki mataki ba. Zai cutar da yarinyar ne sosai, kin sani kuma ko kullum dukanta yake yi ubanta ba zai nuna ya sani ba, bare ya tanka. Amma yau da gobe ba abin da ba zata zo da shi ba. Ina jin tsoron kada ya hargitsa mana zumuncinmu da babu rikita rikitar zamani a cikinsa."
Yaya ta gamsu sosai amma sai ta ce "To amma idan aka dan tura ka'dan ka bashi matarsa. Ba zai iya kawo wadannan kudaden ba."
Abba ya ce "Na sani! So nake na fahimtar da shi irin alfarmomin da muka yi masa Ni da Halimatu. Ina son ya gane ba shi yake yi mana alfarma ba. Mune muka yi masa."
Ya saka hannu ya mayar da ita ta zauna ya ce "zauna a kawo abin kari mu karya sai na kai ki da kaina".
Sai da suka karya cikin nutsuwa da farin-cikin, suna ta hirarsu da ta shafe su, cikin hikimar mace kuma sai hannunka mai sanda take yiwa Abba akan yara masu dabi'ar Sadik ba abin da yake tasiri akan su irin addu'a.
Abba yana tafiya kai Yaya gidanta. Gudale ya shigo gidan. Wajen Umma ya zauna, ya ce "Umma! Abba ya ce na biya shi duk ku'di da ya kashe a aurena. Ya kuma gindaya mini sharadin bai yarda na yi bashi, ko ro'ko ba. Ba kuma zai bani matata ba har sai na ha'do masa kudinsa."
A lalace ta kalle shi ta ce "To ka sakar masa ita mana ka huta wa ranka."
Ya bata rai ya ce "Ba yanzu ba Umma! Bana so idan na saketa na yi nadama.
Ta yi tsuka ta ce "Na rasa gane wannan jarabar! Idan na ce kana sonta ka musa mini, banda haka, auren da muke neman sanadinsa me zai hana ba zaka sallama shi ba, tunda ga dalili an samu mai 'karfi.

Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "Umma so nake sai ta haihu tukun, bai kamata a saketa da 'karamin ciki ba, ko bana sonta ya kamata na yi mata adalci.
Tsaki mai tsananin gaske ta ja tana jin takaicin Halimatu da uwarta na sake tsananta a zuciyarta, domin ta gane Gudalenta yana son Halima da gaske, wanda ta yi imanin ba soyayyar gaskiya ba ce.
Tausayin kanta da Gudalenta ya yi matu'kar kamata. Tabbas wannan gayya Safiya ta yi mata da tilon danta.
A hankali ta mike ta yi cikin bedroom dinta dan ta yi walaha, ta kuma bashi damar shiga dakin Halimatu tunda ta lura hankalinsa na can.
Ai kuwa tamkar jira yake ta kauce ya nufi dakin da take da hanzarinsa.

***�?
*Kina fama da infection mai naci?*
*Kina fama da bushewsr rashin ni'ima?*
*Kina fama da rikicin al'ada?*
*Kuna fama da ulcer?*
*Shin kin ta'ba jarraba maganin GHT?*
*Shin kinsan suna da jakadu da yawa?*
*Bari na fa'da miki jakadiyarsu da zata fa'da miki aikin kowanne magani, ba kuma zata baki Wanda ba zai karbe ki ba*
*Sannan tana da saukakawa wajen farashi*
*Tuntu'bi Faseelat a wannan lambar 07039269902 dan samun naki nau'in supplement din, Kinga dai yadda Iya Basiru ta yi tsaye a zuciyar Mk*
*Idan kina da kyau ki Kara da wanka Haijya*


Ina zaune a 'kasa, na jingina da gadon, Kamar jifa ya shigo.
Farin ciki ya mamaye ni. Na debi rawar jiki da murya na ce "Sa sa sannu da zuwa Yaya Gudale! Kasan da 'kyar na iya hakuri har ka shigo, tamkar na fito na same ka".
Ya watso mini wani lalataccen kallo.
Ya ce "Makaryaciya kawai. Ai zaki san kin yaudare ni. Zan yi komai dan ki dawo gareni. Zaki san kin 'ki bin umarnina, zaki san kin amince da zaman nan, domin lissafin kwanakinki nake yi anan, wlh duk bashin da kike ci mini sai na fanshe su".
Na tsinci kaina da yin murmushi da kuma murguda masa baki.
Ai nan da nan ya iso gareni ya zauna a kasan shima, ya janyo ni jikinsa ya rungume sosai ya dinga sakin ajiyar zuciya. Ina kuma jin yadda zuciyarsa take harba wa.
Tsawon lokaci muna hakan, muna samun nutsuwa a gangar jikinmu gaba'daya.
Murya a dashe ya ce "I really need you Guduyo".
Da'di ya kama ni, amma sai na waske da cewa "Nima hakan sai dai kuma dokar likita".
Haka kawai na fa'da ya zabura ya sake ni ya ce "likita Allah ne?
Ke dai kawai ki ce mini an hure miki kunne. Banda haka har zan ce ga yadda nake so ki kawo mini zance marar tushe?
Ina ce dai likitan ba shi da ikon cewa ga abin da zai faru, domin sanin gaibu sai Allah.".
Na kasa cewa komai. A dalilin al'amarin da Gudale yake neman yi a cikin gidansu ya firgita ni.
Na ri'ke rigata na hana shi cire wa. Ya gallah mini harara.
Ya ce "Zaki bijire mini ne? Ba ki ga 'ko'karina ba?
Kin fi son na fita na nema a waje ko?
Na girgiza kai domin idan har na bu'de baki kuka zan saka masa.
Bai kula da kukana ba, bare ya fasa. Ya dinga ya mutsani, a ki'dime, yadda yake yi din ya tabbatar mini a matu'kar matse yake, sai dai ba zan bari ayi wannan rashin kunyar da ni ba. A gidan Abba da Umma bs.
Ai kuwa cikin sa'a muka ji dawowar Abba.
Nan da nan Gudale ya sake ni ya fara saisaita tunaninsa da rigar jikinsa. Yayin da ni kuma na janyo hijabi na saka, a dalilin na sani zai shigo ya gan ni.
Murya a dakushe ya ce "Ina wayar ki?"
Ba boye boye na ce "Tana wajen Abba"
Ya girgiza kai ya ce "Zan siyo miki

32 / 61