Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 61

63K to 66K   out of 180.1K words

kama shi.
Ya kwantar da Aman akan kujerar, ya yi dakinsa ya yi wanka ya canja kaya ya fito.
Ya sake zama ya yi gyaran murya ya ce "Kawo mini abincin".
Ban kalle shi ba na ce "Ban yi ba".
Ransa ya baci ya ce "Duk hakurin da na baki?
Duk yadda iyaye da yayu suka baki ha'kuri, amma kin kafe sai ka ce mai zuciyar dutse! A ina Kika samo wannan taurin kai da na zuciyar?"
Na 'ki tankawa.
Ya gaji ya ce "Nima dafa mini indomi, idan kuma kin yi snacks din ki soya mini ya ishe ni"
A lalace na ce "Ban yi ba, babu nama".
Ya dan tuzura ya ce "shekaranjiya na siyo nikakken naman na kawo, baki yi amafani da shi ba, ki ce ya kare?"
Ba fargaba na ce "Abida ce na ji tana nema shine na bata".
Ransa ya sake baci ya nuna kansa ya ce "wato yanzu ba ruwan ki da duk abin da zai bata mini rai ko?
Har bu'katar Abida ce ta fi tawa?"
Na murguda baki na ce "ina ce dai yar uwarka ce ba tawa ba".
Ransa ya baci ha'kurinsa ya fara 'kwacewa ya ce "Kar ki fara yi mini rashin kunya, ranki zai baci, ki shiga hankalinki Halah"
Cikin son na sake fusata shi na ce "Guduyo na ke ba wata *Halah* ba".
Ya harzuka ya ce "Halima ki tashi ki dafa mini indomi ko abin da ya faru a 2020 ya sake faruwa a yanzu".
Na tintsire da dariyar iyashege na ce "Ya faru sau uku dan Allah".
Ya mike ya yi kicin yana fa'din "Billahillazi sai Baban Gusau ya zo gidan nan.
Sai na 'kira miki Alaramma Malam mai jalalaini ya fahimtar da ke girman hakkina da yake kanki tunda kin mance".
Na baki ha'kuri, har kuka na yi akan ki amma kin 'ki yafe mini.
Sai ki fa'di me zan yi, a bar wannan maganar haka na gaji da ita matu'ka da gaske".
Jim kadan ya dawo da lemo a hannunsa ha'di da biskit din pure Bliss.
Ya zauna yana ci cikin bacin rai, da alamu yunwa yake ji ba 'yar ka'dan ba.
Ya zauna yana tura biskit din nan, na lura a dole yake ci, shi yafi son abu mai gishiri akan mai za'ki akan dole yake cin wannan din, da alamu ko karyawa bai yi ba.
Na sake kallonsa ta gefen idona, ina tuna ko sau nawa nake yin girki yana 'kin ci?
Ko sau nawa na yi ta ro'konsa ya ci abincin da na 'bata lokaci na yi domin sa yana 'kunsa mini ba'kin ciki ta hanyar 'kin bude wa bare ya ci.
Na nisa na ce "Duniya mai juyi juyi"
Cikin rarrashi ya ce "Dan Allah Guduyo ki ji tausayina mu zauna lafiya, dan Allah let gone be by gone".
Hawaye ya balle mini na ce "wato duk yadda ka wulakantani ta hanyar cewa Ni din tamkar 'kofar Dan-agundi haka ka ke jina. Hakan bai isheka ba, ka sake cewa zaman alfarma kake yi da ni, ka tabbatar mini bolar jakara ta fini a wajen ka.
Sannan ka dauki kwanana ka kaiwa wacce kake so, ka tsaya gaban Mahaifina ka zage shi son ranka sannan yanzu ka yi tunanin zan yafe maka cikin sau'ki!
Wata'kila dai kwayar da kake sha ta shafi wani bangare na tunaninka".
Ya mi'ke ya ce "Ni ban zagi Baba ba! Allah shine shaidar ban zage shi ba, sannan idan ma na zage shi ai kaina na zaga, tunda a yanzun nima bani da uban da ya wuce shi. Kuma akan me zai zuba ido ya bari Sakina da Al'amin su shigo mini gida su cinye ni da yaki bai tsawatar ba?"
Idonsa ya ka'da sosai ya ce "Me yasa kuke mini haka Guduyo?
Ke da su Al'amin sam sam baku da kara ko kawaici, Yaya Abdallah ne kawai yake kwatanta yi mini alkunya.
Amma ke da sauran brothers 'dinki ba kwa koyi da rayuwar Abba da su Sakina.
Duk abin nan da muke ciki mafi yawan sisters 'dina a bayan ki suke, Amma ni kiri kiri su Al'amin suka nuna mini ke ce tasu".
"A tunzure na ce "Maimuna da Juwairiya menene basu nuna mini ba su?
Sannan ai cin mutuncin da kake yi ne ya wuce iyaka da ka'ida.
Ni Wallahi ba abin da nake so irin ka 'karasa igiyar da ta yi saura a tsakaninmu. Kana zaman alfarma da ni ai kawai ka sauwake wa kanka zaman takura da alkunya. Dama ai ka sha fa'din Abba ya cuce ka da ya ha'da aurenmu".
Na fara kuka sosai na ce " Ban san hirar saurayi da budurwa a tsakanin mu ba, bansan 'da'din hirar mata da miji ba, saboda kullum hantara da kyara ka fi amfani da su a kaina".
Kuka nake har da shessheka na zarce da fa'din "Zamana da kai cutarwa ce, tunda indai ka 'kyalla ka ganni da cikin da yake naka ne, shikenan ni kuma watan shigata bala'i ya kama kenan.
Kullum ina zaune da kai cikin zullumi da fargaba mai yawa.
Ka sauwake mini ka auro taste 'dinka, wacce bata bu'de kamar kofar 'Dan-agundi ba. Wacce zaka dinga shillawa kana cafewa, wacce zata haifa maka yara maza reras a jere, Yar attajiri ba wacce ta shiga rigar arzikin Uban wasu ba".
Hankalinsa ya yi koluluwar tashi, jiri ya debi shi ya zauna kan kujerar da karfi tabbacin bai shirya zama ba, fad'owa ya yi.
Ido jawur, murya ba amo ya ce "Fear God Guduyo! Maganar da na ce Abba ya cuce ni, ai tsohuwar magana ce, tun farkon aurenmu ban sake katobarar fa'da ba, hukuncin da Abba ya dauka sai da na kusan salwanta wani sashen na jikina saboda kawai ma karyata kirarin da na yi, har yau kuma ban sake cewa an cuce ni ba. Amma dan son ki sake jefa ni cikin tasku shine kika dawo da maganar yanzu?"
Na yi masa banza don na sani gaskiya ya fa'da. Ya numfasa ya ce
"Na baki hakuri yafi cikin buhu.
Ina miki albishir matu'kar kika yafe mini Ni kuwa duk abin da kike tunanin ban yi miiki ba, Wallahi sai na yi miki fiye da hakan, sau nawa zan fa'da tun kafin na aure ki nake jin ki cikin zuciyata, nake kishin ki?"
Ido cike da hawaye na watsa masa harara na ce "Sau nawa zan ce maka ba gaskiya kake fa'da ba. Me yasa ka kasa nuna farin ciki da auren?
Me yasa baka ta'ba zuwa zance ko sau 'daya dan ra'din kanka ba?
Me yasa bayan auren ka kasa nuna mini kulawa a farkon kwanakina a gidanka?
Me yasa ka gudu ka bar Ni?
Amsar ita ce *Baka Sona*."
Kuka sosai ya kwace mini na dinga yinsa sosai saboda yadda nake jin bacin rai na taso mini ba ka'dan ba.
Amma a hakan na ce "Wanne zaka dawo da baya ka yi mini shi?"
Da sauri ya matso gabana ya durkusa ya ce "Duka! Har zancen da ban zo ba yanzu zan zo miki. Zan baki kulawa sosai, yanzu ma farkon aure muke, yanzu nake fatan mu yi rayuwa mai cike da nutsuwa, ta baya cike take da kuruciya da wauta, ki bani dama kawai na tabbatar da sannu zan wanke duk ba'kin tambarin da na yiwa kaina a zuciyar ki".
Na kalleshi ido cikin ido na ce to ai ni yanzu bana son ka".
Maganar ta shige shi ainun ya ce "Ni ina son ki, son da nake miki ya isa mu zauna lafiya matu'kar dai zaki yiwa sharia biyayya".
Ba shakkar komai na ce "idan ba zan yi biyayyar ba fa?"
Ya zuba mini ido sosai nima na zuba masa, ina son na ji ko makauniyar soyayyar da nake yi masa zata ta so mini.
Amma ban ji komai ba, tabbacin na riga na dahu da ba'kin cikinsa.
Na janye idanuwana ina jan majina hadi da goge hawayen da ya ki yanke wa.
A raunane ya ce "Sai na ha'du da jinya sannan zaki fahimci halin da nake ciki Guduyo?"
Da kara'di na ce"sau nawa nake jinya sanadin ka? Amma sannu ma tana yi maka nauyin ka yi mini!
Ka mutu ma 'karewar jinya bani da asara."
A hankali ya ce "Tabbas ba ki da asara! Umma da su Amna ne zasu tafka asara, sai kuma su Sakina da zasu rasa tilon 'dan-uwansu tunda yanzu zumunci idan ba cikinku 'daya ba to babu wani kawaici ko kara".
Ya mike yana tangadi tamkar wanda ya sha abar, nan kuwa tsabar ba'kin cikin yadda na bijire masa ne.
Da wani zai zo gidan wanda bai san mu ba, bai san halin da na shiga a hannun sa ba, sai ya ga laifina, ya ce ina wula'kanta mijin aurena.
Wanda kuma ya san mu sai ya ce "Mayya ce ni da na yarda nake zaune da shi.
Shigar da ya yi ashe zazzabi ne ya rufe shi ina zaune ban sani ba.
Har aka yi la'asar bai fito ba. Sai na yi kamar na leko shi, na ga dalilin da ya hana shi fita sallah sai na basar.
Amma abin na mintsini na tunda Ubangiji ya sanya shi cikin bayi masu mutuntata sallah a jam'i.
Na idar da tawa sallar ba jimawa Aman ya tashi, sanin da na yi Gudale ba lallai ya fito ba, ya sanya na rungume yaron, yayin da shima ya kwanta a jikina ya yi lamo tamkar dai ba daga barci ya tashi ba.
Ban san ya aka yi ba, soyayyar yaron da na 'boye a cikin zuciyata ta dinga taso mini, na dinga jin tausayinsa na kama ni ta yadda na bari zuciya ta rinjaye ni, nake hukunta shi da laifin da ba nasa ba.
Duk yadda bana daukar sa, duk yadda na tsige shi daga nono lokacinsa bai yi ba.
Bai sanya ya guje ni, ko ya yi mini 'kiwa ba.
Na mi'ke sabe da shi a kafa'da, na shiga kicin na dauko masa *Fan yoghurt* na saka stro na bu'de masa, ai kuwa nan da nan ya zuke.
Na soya masa 'kwai, a kicin din na bashi ya cinye tas.
Ya sha ruwa ya yi gyatsa.
Na dauke shi, da nufin shiga dakin Gudale dan na kai masa 'dan sa! Sai kawai ganin shigowar Sakina na yi, a gigice ta nufi dakinsa ba tare da ce mini kanzil ba.










# Tean Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.

*SDK*
*43-44*


Hakan da Sakina ta yi mini sai na zama very guilty. Domin kafatalin makusantan sa ba wacce nake jin nauyin ta irin Sakina.
Shudewar mintina goma suka fito tana ri'ke da shi sosai.
Na kallesu ina jinjina girman soyayyar dake tsakaninsu.
Na tuna irin tijarar da yake yi mata.
Na tuna irin rantsuwar da ta yi akan babu ita, babu shi.
Har cewa ya yi idan ta sake zuwa masa gida sai yasa Yan ta'addah sun dauke ta kowa ya huta da wuyar zaman ta.
Ita kuma ta kafe matu'kar ni ce matar gidan kuwa zata zo a duk sadda ta so.
Amma idan wata daban yake aure, idan ya ganta a gidan sa ya tabbatar ba Sakina Abbansu ya ra'da mata ba.
Amma a yau sai na gane soyayyar da ke tsakaninsu ta daban ce, duk wani cin alwashin da suke yi na babu su, babu juna iya lebensu ne, ko kan harshe bai hau ba, bare kuma zuciyoyinsu.
Bansan me ya saka harshena ya yi mini nauyi ainun ba. Na kasa bu'de baki na yi musu magana, ko da kuwa iya sannu ne.
Na koma na zauna a sanyaye! Aman ya kwanta a jikina tabbacin dai yana samun nutsuwa a jikin nawa.
Mama na yiwa waya idan tuwo ta yi ta aikowa Aman! Kai tsaye ta ce bata yi girki ba, na san kuma dalilin da ya sanya ta hana ni.
Har wajen takwas na dare ba su, babu labarin su.
Ina zaune, ina ta faman tubka da warwara.
Sai ga su sun dawo, ya 'dan ji sau'ki ba kamar lokacin da suka fita ba, tabbacin ruwa aka 'kara masa.
A falo ya zauna.
Yayin da Sakina ba ta zauna ba, ta ajiye masa ledar magungunansa, tare da cewa "Ka 'karantawa kanka damuwa, ka dai ji abin da likita ya fa'da maka".
Ta juyo ta kalle ni ba walwala ta ce "jininsa ne ya yi 'kasa a dalilin baya samun barci da kuma wadataccen abinci.
Shiyasa ulcer ta sake bada gudunmawa.
Ki kula da abincinsa da maganinsa".
Na ce "To" a hankali.
Cikin rauni ya ce "Sakina kin ce zaki bata ha'kuri a madadina! Dan Allah kar ki tafi baki kawo 'karshen wannan dambarwar ba.
Da gaske na ke yi bazan iya daukar abin da Guduyo ta dauka ba. Ta fini karfin zuciya, ki huce Sakina dan Allah".
A hankali ta ce "Amma na ce ka kwantar da hankalinka ko?"
"Ta ya ya hankalina zai kwanta kin zuba ido kina kallon yadda na zama a gidana, alhalin kina da damar da zaki kashe mini wannan wutar! Anti Sakina dan Allah ba zan iya ba".
Ya fa'da cikin rauni sosai.
Ta nisa ta ce "yanzu baka gamsu komai ya wuce ba?"
Ya sake shagwabe mata ya ce "ki fa'da mata ta dinga dafa mana abinci, ta daina yi mini rashin kunya, sannan ta dinga zuwa 'dakina, ko kuma ta daina rufe mini 'kofar 'dakinta".
Nauyin maganganunsa suka kama Sakina ta ce "To zan fa'da, za kuma ta gyara".
Ya lumshe ido ya ce "Na gode Anti".
A fili ta ce wannan "Antin dai ba har zuci bane".
Ya sake cewa "Da gaske nake Antina ce ina da yar'uwar da ta zarce ki ne?"
Ta murmusa ta ce "Sai Guduyo".
Ya langwabe kai ya ce "Ita ai yanzu ta ture ni akan matsayina, ta 'ki yarda da dimbin soyayyar da nake yi mata.
Shin an ta'ba yiwa wani 'dan-adam rashin uzziri iri na kuwa Sakina?".
Ta ce "Ai kuwa uzzirin da ta yi maka ba kowa ake yi wa irinsa ba".
Ya girgiza kansa ya ce "Na gamsu ta yi mini, amma yanzu ina rokon a sake yi mini.
Pls Sakina! Ki yafe mini, na tabbatar idan kika huce gaba'daya Guduyo zata yafe mini. Ke ce ita, na sani".
Ya fa'da yana ru'ko dukkan hannuwanta.
Ta zuba masa ido sosai sannan ta ce "Tunda har na dawo maka da ita, ai kuwa ka san na yi ha'kuri".
Ya sassauta murya ya ce "wannan na dole ne Sakina! Ki goge komai a zuciyar ki.
Wallahi na canja, zan yi mata adalci, zama na Fisabidillahi zamu yi".
Na lura jikin Sakina ya yi laushi tubus.
Yayin da ni kuwa ban ji komai ba.
Ta kalle ni fuskarta ba walwala ta ce "Tashi ki samo masa abin da zai ci kafin ya sha magani".
A hankali na ce "Ban dafa komai ba".
Ta zuba mini ido sosai ta ce "cewa na yi ai ki samo masa ba wai ki kawo ba".
Girman Sakina ya sanya na mi'ke na doshi kicin din. A raina kuwa ba karamin takaici nake ji ba, domin na riga na ci alwashin ba zan sake 'dora tukunya saboda shi ba, ba zan sake dafa abinci na bashi dan ra'din kaina ba.
Na sani bai son jollof din taliya tsurarta, wacce babu vegetables a ciki.
Dan haka na dafa a hakan.
Na zubo masa plate na Kai gabansa na ajiye.
Na koma na dauko kifi a fride wanda na Riga na soya, na yi pepper fish.
Na yi warming dinsa, na zuba mana taliyar a plate daya na dora kifin a kai saboda na sani Sakina masoyiyar kifi ce fiye da nama.
Na saka fork guda biyu, na kai gabanta tare da cewa "ga abinci Maman Nana".
Ta ce "Ya baki saka masa kifin ba shi?
Na ce "Bai dame shi ba ne".
Ina kallonsa yana ta juya abincin nan. Amma ga mamakina sai na ga yana ci a gaggauce tamkar dai ya samu abin da yake tsananin so.
A zuciyata na ce "Ashe dama wulakanci ne, ba ci ne baka yi ba.
Muka ci abincin mu da Sakina tana yi tana bawa Aman a baki.
Muka kammala ta yi haramar tafiya, na rakata har harabar gate.
Ta kalle ni ta sassauta murya ta ce "Ki dinga bashi abinci, sannan ki daina jan doguwar magana a tsakanin ku, komai ya ce kawai ki ce "To".
Nan da nan na fara kuka na ce "Na gane dai yanzu so kike kawai ki koma bayan sa".
Cikin rarrashi ta ce "Ai na sha fa'da miki ke da shi 'daya kuke a waje na, ba wanda ya fi wani. Kin sani a koyaushe ina bayan ki ne. Ba dan kin fi shi ba, sai dan kin fi shi gaskiya da ha'kuri. Sannan ba zai yiwu na zuba ido na bari ki wula'kanta ba, a ko'ina zan baki kariya.
Hakan kuma ba shine dalilin da zan 'ki fa'da miki gaskiya ba."
Ta yi shiru tana kallon yadda nake kuka 'kasa 'kasa.
Ta sake sassauta murya ta ce "ki yi shiru! Ki ji me zance miki Sadiya".
Na dan nutsu ka'dan. Ta yi waiwaye dan ta tabbatar babu kowa a kusa da mu.
Ta numfasa ta ce "Ulcer ke damunsa. Ki kula da lafiyarsa ta hanyar bashi abinci mai kyau kuma marar yaji.
Shin idan bai koshi ba, ta ina ma zai dinga kwadayin ki bare ki ja shi a kasa?
Idan ba kya kwalliya ta ina zaki ki'dima shi ya rasa nutsuwa?
Shin idan ba kya ta'kaita magana a tsakaninku yaushe zai damu da sai kin yi masa magana?
Idan ya fita ki shiga ki gyara masa dakinsa.
Na sani yanzu ya gane yana sonbki, amma so nake sai ya gane ke ce duniyarsa! kuma dole ne ya zauna dake cikin mutuntunta wa.
Amma hakan ba zai faru ba sai kin iya takun ki."
Hawaye ya 'balle mini na ce "kina nufin na dinga zuwa 'dakinsa kenan?"
Da sauri ta ce "Idan ba ya gidan ki shiga ki gyara masa, amma ban ce ki je masa kwana ba. Ai na yi miki al'kawarin sai ya gane kuren sa akan furucinsa, sai ya 'karyata kansa da kansa."
Bakina na rawa na ce "Na gode sosai".
Mun jima a wajen sannan ta tafi.
Na dawo na tarar basa falon.
'Dakina na shiga, ga mamakina sai ganinsa na yi, har ya yi wanka yana sanye da wata cotton 'din jallabiya marar nauyi maroon kala.
Yana kwance akan gadona ya saka Aman a gabansa da yake barcinsa cikin nutsuwa, shima ya yi masa wankan.
Ban ce masa 'kala ba, na shiga na yi wanka na kuma yi alwallah.
Na shirya cikin lallausan kayan barci, riga mai dogon wando. Wanda order ne na mussaman cikin tarin odar *Umm Muhd collection* 08063358662.

Har yanzu ban daina amfani da kayan Oriflame ba, tunda na yi sa'a na hadu da jakadiyar su

22 / 61