Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
yi karatunsa na (Mass Communication).
Dukkansu kuma Abba ne ya yi dawainiyarsu, hakan ba 'karamin damun Umma yake yi ba, sai dai kuma ba yadda za ta yi, tunda duk wani shigi da ficinta bai yi tasirin da ya hana Abba yi wa 'ya'yan 'dan uwansa hidima da zumunci ba.
Babban abin da ya sake dagula lamarin Umma a kan mu, a lokacin da su Yaya Sadik suka kammala sakandire, sun riga sun sakankance America ko England za a kai shi karatu, tunda suna ganin ya kai wasu bare kuma tilon 'dansa.
Sai dai fir Abba ya tire a kan ba inda zai tura Ya Sadik, a yanzu ma yake yin fitina kala-kala bare kuma ya sake tura shi kasashen da suke da 'yanci, don haka Ya Al'amin da Ya Sadik a Jami'ar Ahamad Bello suka samu gurbin karatu, inda Al'amin ya karanci Halayyar 'Dan Adam (Sociology). Shi kuma Sadik yake karantar Urban And Rural Development. (Tsara Cigaban Birane da Karkara). Yaya Abbas kuma ya samu (Geography).
Ba irin rikicin da bai yi ba a kan ba zai yi karatun ba ga'badaya. Ya samu daurin gindin Umma, Abba kuwa ya ja ya kafe ba zai sauya ra'ayinsa ba, tunda ba ya so sai ya yi ta zama, haka ya dauki su Yaya Al'amin ya kai su Zariya, ya damka su a hannun mijin Anty Hafsatu, wacce muke 'kiran ta da Antin Zariya, shi ne Vice Chancellor na makarantar a lokacin.
Kan dole Yaya Sadik ya tattara ya tafi Zariya shi ka'dai, ya fara karatunsa,da su Yaya Al'amin a gidan Anti suke da yake cikin kwatsas din makarantar.
Yayin da Antin Zaria babbar Ma'aikaciya ce a ma'aikatar E.F.C.C.
A lokacin da nake shirin shiga aji hudu na sakandire inda zan tafi makaranta a Kaduna, a wannan shekarar su Ya Sadik suka kammala digirinsu na farko, suka fito da sakamako mai kyau.
Ganin a lokacin shekarunsu ba wani yawa suka yi ba, bayan sun kammala bautar kasa, Abba ya tura su digiri na biyu (Masters) a wannan karon ne suka rabu domin Yaya Al'amin a Jami'ar Bayero ya samu, yayin da Sadik da Abbas za su sake komawa Zariya.
Yayin da Yaya Ashiru yake karantar pharmacy a B U K.
Ba'kin ciki a zuciyar Umma tamkar ta halaka, sai neman tsari da zama tare da dangin miji gida 'daya take yi, domin gani take yi ai don Gudale ya taso a sa'anninsa da yawa yasa Abba bai kai shi karatu waje ba. Tunda Ashir ma a shekara 'daya suka kammala.
A haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa, tunda na fara boarding ban sake ganin Ya Sadik ba, domin lokacin zan zo hutu, shi kuma ya tafi, ba mu hadu ba sai da ya kammala, a lokacin ni kuma ina shirin kammala sakandire.
# One Love
# Ana tare
# Surayya Dee ✍️.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).*
*Sadaukawa ga iyayena guda hudu*
*Alhaji Muhd Tukur*
*Haj Fatima ladi Ali*
*Alhaji Dahiru Ali*
*Haj Maryam Hamisu Kano*
*Allah ya ji'kanku da Rahma ya baku aljannar firdausi*.
*Fatan alheri ga Mijina*
*(M.I. Nashe)*.
*Jinjina ga shugaban kungiyar Lafazi writers*
*Sadik Abubakar*
*Na gode da kokarinka akan rubutuna*.
*Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.*
*Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*.
*Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.*
*Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*.
*BISMILLA HIR RAHMANIR RAHIM*
*Shimfi'da*
*Farko*
Harabar falo ya biyo ni yana fa'din "zo ki ji Halah! Saurare ni mana, sai yaushe za ki yarda da ni? Ai na dauka mun wuce wannan tashin hankalin? na riga na fahimta, na kuma gane bankaura nake yi, ke 'din ce farincikina, ke ce duniyata!"
Ya tsahirta da nufin ko zan tanka masa, amma sai na tsuke bakina tamkar gini yake ba yi wa magana.
Ya nisa tare da fesar da iska sannan ya ci gaba da cewa, "Ki kalli irin yadda Allah Ya juya al'amarinsa mana komai ya kubuce mini, da kaina na dinga 'karyata kalamaina. Bai kamata ki ci gaba da nuna 'bacin rai ba, tunda Ubangijinki ya yi kishinki, kar fa ki bari ni ma Ya yi kishina, tunda ba a miki sassauci wurin yi mini 'kwangen biyayya ba."
Na yi 'kasa da kaina ina jin hawayen takaici na neman kwace mini.
Ba komai ke sani jin takaici ba, sai irin yadda ba ni da yar'uwa shakikiya mace. Wacce duk runtsi ba za ta 'ki yi mini adalci ba, wacce na rik'e tamkar cikinmu guda ta nuna mini wata kusar ta fi wata, ta hanyar fifita farincikin 'dan uwanta a kan nawa, duk kuwa da tana sane da irin zaman da na yi da shi, asalima ita ce kan gaba wurin fa'din ha'kurina ya yi yawa, son da nake yi masa ya wuce hankali, ita ba za ta dauki wulakanci namiji irin yadda nake dauka ba.
Amma da ya fasa kwalbar ha'kurina! Sai t ta shure dukkan ba'kin cikin da na hadiya a hannunsa, ta bari idonta ya rufe, ta 'ki yi mini kara, duk da ta san ita ce 'yar uwa mafi kusanci a gare ni.
Ya sake nanu'kata, yana cewa, "Ni na san ke mai yawan yi mini afuwa ce, wannan taurin zuciyar ba taki ba ce, ba kuma ta dace da ke ba. Kin yi hakuri da ni, na zalunce ki, na shayar da ke gubar ba'kin ciki, na azabtar da ke, na wulakanta ki. Amma don Allah ki ba ni damar da zan gyara na yarda na yi laifi, ina kuma son na gyara, amma kin rufe mini 'kofofofin afuwa.
Hawayen idona ya 'balle mini, cikin rishin kuka na ce, "Sau nawa kana yin irin wannan tuban na muzuru? sau nawa ake danne ni saboda kai?
Shin laifi ne don na zo a jinsin mata masu 'kiba, na kuma zama uwar 'ya'ya mata?"
Kuka ya 'kwace mini kwarai da gaske.
Cikin rarrashi tamkar ba ta'kadiri irin Gudale ba, Ya ce, "Kowa ya shaida wannan nadamar tawa har zuciyata ce, sannan ai yanzu bisa sharadin da aka gindaya mini za mu zauna, ni na sani sakayya ce Ubangiji ya yi a tsakaninmu, aka juyar da al'amarinmu ta yadda ban yi zato ba, ina sake rokon ki kar ki bari rashin kirkina, yasa ki yi watsi da kyawawan dabi'unki na ha'kuri da sassauci, Ubangiji da kansa ya ce, "Fa sabir sabaran Jamila." Wato ku yi hakuri, hakuri mai kyau. Ya sake cewa, "A yi wa masu hakuri bushara."
Na zuba masa ido tar ina mamakin ashe ya san hakuri dabi'a ce mai kyau? A duk tsayin zamana da shi, kullum na bashi ha'kuri yana ba ni amsa da cewa bai san shi ba, domin shi ba zai yi wani ha'kuri ya cutu ba, ba kuma zai sassauta ba, sai ya yi mini hukuncin da ya yi nufin yi koda kuwa ban yi komai ba. Sai don kawai ya jefa ni cikin 'kunci da bacin rai.
Amma yanzu saboda rashin ta ido ya karkace baki yana fa'din falalar ha'kuri, domin shi yake so a yi wa uzurin ha'kurin.
Na hasaso irin tsananin da nake fuskanta ta bangaren mahaifiyarsa, take na fashe da kuka mai sauti domin na sani ba abin da zan yi wa Umma ta yi mini adalci. Kishin da take yi da mahaifiyata ne ta tattare ta dawo da shi kaina.
Na dinga jin wani irin tashin hankali na shiga ta, tabbas guduwa zan yi domin ba zai yiyu na tabbata cikin 'kunci ba, sanin kowa ne na yi iyakacin hakurin. Zuwa yanzu kuma na riga da na gama dahuwa da 'kunsar ba'kin cikinsu, tura ta kai bango.
Shi yasa nake takaicin yadda Sakina ta sake dawo da ni gidan nan, gidan da zan iya kididdige adadin farincikin da na yi a cikinsa, saboda gaba'daya ina rayuwa ne tamkar ta baiwa da mugun maigida.
Ya sake 'kaimi wurin rarrashi yana cewa, "Ki yi hakuri ki bari yaranmu su girma a gabanmu, saboda su samu cikakkiyar tarbiya da nutsuwa."
Na sassauta kukan na ce "Yaranmu ko kuwa yarana? Shin da ma kana lissafin kana da yara ne?"
"Um um Guduyo! Komai girman laifukana ai ban ta'ba barranta kaina da su ba, na sani 'yayana ne, jinina ne, kada ki bari fishi ya rinjaye ki."
Kaina ya sara adalilin ba'kin cikin da na sake tunowa na hadiye shi a goyon ciki da kuma haihuwar Afrah! Na zuba masa ido ina kallon sa ina sake hakaito wancan lokacin da ya shu'de, idan da wani ne ya ce mini rashin arzikin Gudale ya kai ya mini abubuwan da ya yi 'din zan 'karyata shi.
Sai dai ba na ganin laifin kowa tabbas son zuciyata ne ya mini sanadin wahalar da nake ciki, ba irin hannunka-mai-sanda da Abba da Sakina har ma Al'amin ba su mini a kan bai kamata na auri SADIK ba.
Tabbas na gaskata azancin maganar nan duk da ke cewa, sabon da kaza ba zai hana a yanka ta ba.
Na goge fuskata wadda ta sake kumubura adalilin kukan da na yini ina yinsa, ido cikin ido na kalle shi, duk wani tsoronsa a yau ban ji shi ba, don haka na sake bude dukkan idanuwana ina fuskantarsa cike da jarumta na ce, "Ka yi mini adalci irin wadda za ka yi wa Sakina.
A yau ba na son ka kalle ni a matsayin matarka, ina son ka mini kallon 'kanwarka wadda jini ya hada ku, ma'ana nasabarku ta hadu ne ta wajen uba, gidanmu daya, ko ba ka sona ai za ka yi kishina tunda dai jininmu guda.
A ko'ina kai mai wakilta ta ne, mai kare ni daga kowanne irin tozarcin rayuwa.
Don haka zan fa'da maka cewa mijina mugu ne, azzalumi ne, bai san komai ba sai son kansa, saboda na haifa masa 'ya'ya mata guda biyu, Allah ka'dai Ya san bala'in da na tsallake wurin cire mini cikin da yake na halal kuma mallakinsa. Yana da arziki, amma ba ya ya wadata ni, ya hana ni aiki, ba sassauci ko kadan a tsakaninmu, asalima yana ganin tamkar alfarma ce tasa yake zaune da ni."
Kuka ya so 'kwace mini, amma na hadiye shi.
Murya na rawa na ce, "Ya sani ina son sa, ya san ni ina yawan begensa, amma zai iya shafe kwanaki masu yawa bai sauke hakkin auren da ke kansa ba, ba don ba ya so ko sha'awa ba, sai don ya nuna mini ni din ce bai da bu'katar hakan daga gare ni, ba tare da tunanin ni ina cutuwa ba, a hakan kuma yake tsananin azabtar da ni ta hanyar hana ni fita koda kofar gida ne, saboda bai gaskata ni ba. Ya tsananta zargi a kaina, dare da rana, a cikin zullumin sa nake, sannan ban huta a hannun mahaifiyarsa ba. Don Allah fa'da mini wane adalci za ka tsaya ka yi mini a wajen wannan azzalumin mijin da yake neman kashe ni a tsaye? Tunda har yau ban wuce ya doke ni ba, ko da kuwa a gaban 'ya'yana ne."
Idonsa ya ka'da sosai tashin hankali ya bayyana karara a dukkan jikinsa, ya rasa kalmomin da zai yi magana su gamsar da ni.
Ya sake tsananta matsata, cikin murya marar amo ya ce, "A farko hakuri zan baki Guduyo! Na kuma fa'da miki irin falalar ha'kuri, da irin matsayin da mai yin sa yake rabauta da shi. Sannan na yi wa mijin naki gargadi, idan ya daina shike nan haka muke so, domin duk gatan mace, duk matsayinta aure shi ne rufin asirinta. Na sani duk tsiyar da yake miki, akwai kuma abubuwan da zai miki wanda ni a matsayin 'dan uwanki ba ni da damar yi miki su, ba mahalu'kin da yake son ya ga yar uwarsa a gida da sunan mutuwar aure sai dole, idan kuma ya'ki canjawa to dole ba yadda za mu yi sai a raba ku musamman tunda da zalunci a cikin zamantakewar."
Hawaye na zuba na ce, "Ka gaskata ni, ba zan yi wa mijina 'kazafi ba? Ka kuma gamsu akwai cutarwa a zamana da shi?"
Da sauri ya ce, "Wallahi Halima na gaskata ki, na kuma yarda ke din adala ce, ba abin da zai fito a bakinki sai gaskiya. Abu 'daya nake so ki yi a yanzu dai dukkanmu 'yan-uwanki kowa ya gamsu ba wacce take ha'kurin da kike yi a gidan aure. To ki 'kara ha'kuri Ubangiji ne ya yi nufin kawo miki mafita shi yasa ya haska lamarinki kowa ya gane halin da kike ciki.
Ki 'kara hakuri ki ba wa mijin naki damar da zai gyara kurakuransa, ai yana son ki."
Zuciya a dake na ce, "To ai ni ba zan iya ci gaba da zaman ba, domin na riga da na gaji, a yanzu na gamsu, na kuma gane ba abin da nake bu'kata a aure irin kwanciyar hankali, da mutuntunta juna.
Na yafe soyayya, na yafe kyau, na yafe dukkan burin zuciya, domin su na biyewa na fa'da cikin halin da nake ciki.
Na gane mutuntata juna da tausayi da adalci irin na shari'a su ne tubalin da yafi kowanne tubali 'karko a wurin ri'ke aure cikin salama.
Amma ni nawa auren tubalin toka ne, domin so, sha'awa, da kyau su ne suka fi rinjaya ta, shi yasa nake 'dandanar kudata. Na ha'kura! Ba zan iya zaman ba, na gaji matu'ka."
Na fa'da cikin kukan da ya kasa 'boyuwa.
Hankalinsa ya tashi domin bai ta'ba ganin rikici tsantsa a idona irin haka ba, bai ta'ba ganin jarumta a tare da ni irin hakan ba.
Ya sassauta murya sosai ya ce, "Ni na sani mai laifi ne, na kuma yarda da hakan, me yasa ba za ki ba ni damar da zan gyara ba? Me yasa za ki kafe? alhalin Annabi ya ce, "ku yi wa 'yan uwanku uzuri sau sabain."
Da sauri na ce, "Na tabbatar na yi maka uzuri saba'in sau biyar, amma a wannan karon ina tabbatar maka wallahi na gaji da hakurin da babu riba ko kawaici a cikinsa, idan kuma ka kafe sai ka ci gaba da ri'ke ni, to kuwa daga yau zan fara addu'ar Ubangiji ya gajarta mini kwana, ba don na san hukuncin wanda ya kashe kansa ba, da sai dai ku wayi gari ku ga na ci abin da zai kubutar da ni da rayuwa tare da kai a kan dole."
Ina rufe baki na ga ya zabura ya mike da azama sosai, yana ambaton, "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun!''
Ya fice, ni kuma na ci gaba da kuka sosai ina ta tunanin na shirya faruwar komai, ko da kuwa zan rasa wanda zai taimake ni.
Na dinga hawaye ina tunano matayen da kullum suke cikin fitinar miji, suna kuma da iyaye amma ba za a kai musu dauki ba, sai a bar mace tana ta kwankwadar ba'kin cikin da yake zama ajalinta, duk asibiti idan ka je bangaren masu ciwon hawan jini da ciwon zuciya, mafi yawa matane suke cika wurin ba kuma komai ba ne yake sababa musu wadannan muggan ciwon ba face ba'kin cikin miji ko na rashin kintsuwar 'ya'yansu.
Lokaci ya yi da za mu fahimci gaskiya, aure ibadar Allah ne, shi da kansa ya tsara yadda zaman zai kasance cikin tausayi, girmamawa da kuma adalci. Shi yasa Ya kewaye shi da tarin dokoki iri-iri, hatta saki ma sai da Ubangiji Ya kawo matakai hudu kafin a yi shi, amma a yau muna cikin wani irin zamani a kan dan kankanin abu sai ka ji an cewa mace je ki na sake ki, saboda yadda kullum darajar aure take sake karyewa, tamkar ba ilimi ne yake fadada ba.
Iyaye mussaman iyayen 'kasar Hausa ba sa ta'ba tsayawa su fahimci matsalar da 'ya'yansu mata suke fuskanta a gidajen aurensu, ko zuwa ta yi da matsala da zarar an tambaye ta shin akwai abinci? Indai ta amsa da e, sai ka ji an ce tashi ki koma, domin kuwa wata ba abincin ma take zaune.
Wai shin abinci ne ka'dai hakkin da idan ba a sauke shi ba za a tuhumi miji?
A ko'ina mace take za ta samu abinci matu'kar ba zabe za ta yi ba, domin bakin da Allah Ya tsaga ba Ya hana shi abinci. Don akwai wasu hakkokin da shari'a ta tsara ba wanda yake da hakkin sauke su sai miji, ba inda aka yi wa mace halaccin ta same su sai wajen mijinta kawai. Amma abin kaico, a yau mata da yawa suna nan babu wannan hakkin, kunya da kawaici ya hana su yi 'korafi.
Da kuma mace za ta bude baki ta koka wannan gingimemiyar matsalar, ba za a yi mata adalci ba, sai ka ji ana fadin wance ai jarababbiya ce, harija ce, marar kunya ce, da sauran sunayen da za ta muzanta ta yi ba'kin ciki. Kuma abin mamakin har da yan'uwa mata wurin irin wadannan kalaman.
A yau kowa ya san wannan matsalar ta damu mata da yawa, domin kuwa ta zama ruwan dare ba a tsakanin yara matan ba, ba kuma matasa ba, bare kuma wadanda suka fara manyanta.
Ba abin da yake tayar mini da hankali irin yadda maza suke buda 'kofofin da matayensu suka hallaka a dalilin su din ba sa sauke wannan hakkin, wanda rashin kyatatuwar wannan al'amarin manufar auren ma gaba'daya ta lalace.
Ina zaune a wajen kawai na ga ya dawo, Sakina na biye da shi da kuma antin Zariya.
Suna zama Yaya Abdallah ya shigo. Abin mamaki ban ji 'dar ba, na ganin ya dauko mini antin Zariya da Ya Abdallah, domin ai ba su ne suke mini zaman auren ba, ba da su nake raba bacin ran da nake kwana nake tashi a cikinsa ba. 'Karkari dai su ce ba za su taimake ni ba, idan na kashe aure to na riga da na shirya wa faruwar komai, idan har