Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   53 / 61

156K to 159K   out of 180.1K words

ta kwashi kayan Afrah ta ce a ha'da da ita. Domin tana ganin idan yarinyar bata tare da ni wata'kila na fi fahimtar jikina ma yana da hakki a kaina.
Ina ji, ina gani aka tafi da su, na sani zasu fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali a Abuja. Domin sanda aka yi case din Munu sai da Sakina ta tafi dasu asibiti ta duba su ta tabbatar ba'a b'ata su ba. Amma kullum cikin k'orafin makarantar da suke zuwa take yi.
A farkon tafiyar Gudale ya turje akan ba inda zasu je. Sai da Antin Zaria ta bud'e masa wuta ta tuna masa ai ya riga ya bata Amnah, Afrah kuwa hutu zata yi, ta taya Amnah zama kafin ta warware.
Ya hakikance da fa'din "Tunda baki dauketa a farkon ba, to sai ki bari a haifo wata". Ta lallaba shi da fa'din "Shikenan bar su su zo hutun yanzu."
Shikenan suka tafi.
Kwana biyu ciwon nono ya sanya ni a gaba ga zazzabi a dalilin yayen da na yi babu shiri.
Ga kuma rashin Afrah sai komai ya tsaya mini cak. Duk na rafke na zube.
Kukan Aman ya karu, idan Uban ya matsa na bashi nono a gabansa, yaro da ya ga yadda suka sake aune wa ga powder na shafa musu sai ya tsorota.
Ya ki kama wa.
Ya dauke shi suka fice.
Sai gashi ya dawo a matu'kar tunzure ya ce Halimatu da izinin uwar wa kika yaye mini yaro d'an shekara guda tak?"
Raina ya fara baci irin wanda bai ta'ba yi ba.
Na zuba masa ido sosai karon farko da na ji tsanarsa tana nema samun muhalli a gefen zuciyata.
Ido ya ciko da 'kwallah baki na rawa na ce "Kada ka yi kuskuren sake zagar mini uwa Sadik! Kasan waccan zagin ma ba wai na manta bane".
"Na zage ki Makaryaciya mashararranciya. Ni da kika mayar wa uwata magana akan idona kuma a gabanta fa?
Shine kike son sai kin ha'da ni gaba da Mama ko?.
To duk mugun Halina da kuke fa'da ai ban ta'ba zaginta a gabanta ba."
Na girgiza kai na ce "Ato dai na fa'da maka na rantse maka Na gaji, ba kuma zan sake yi maka uzziri ba."
"Kar ki yi din dan uwarki".
Na dago na kalle shi ido cikin ido na ce "ba dai uwata ba Wallahi."
Ya ce "Sai tawa?"
Na make kafa'da "ta wacce ya tsargu".
Ya ajiye Aman ya ru'ko ni da nufin duka.
Sai kawai na shammace shi na rungume shi na dartsa masa cizo a kunne da karfi na sosai.
Ya yi iyakacin kokarinsa ya kwace ya kasa.
Ban yarda na sake shi ba, sai da na tabbatar ya ji jiki, jini ya ya cika mini baki yayin da ya bata masa jikin rigarsa.
Na koma gefe ina haki.
Azaba ta kidima shi ya ce "Ashe ke mayyace da gaske Guduyo ni kika cinyewa kunne?"
Ya rasa inda zai yi dan tsananin azaba.
Ya jima bai dawo daidai ba.
Bare ya iya yin magana.
Sai da azabar ta yi sauki sannan ya ce "Zaki ga k'aryar iskanci Guduyo yau."
Na zum'bura baki na ce "shege ka fasa."
Ya ce "Na rantse miki da girman Ubangiji yaron nan bai yayu ba. Kafin na kirga uku kije ki wanko wannan abin da kika shafa yake firgita shi, ki zo ki shayar mini da shi".
Yana rufe baki na ce "Na rantse da Allah matu'kar ni ce na haife shi, shi da shan nono sai dai na matarsa ko na saniya. Ko kuma ka kaiwa wacce ta ankarar da kai yaye shi na yi ta shayar da shi. Tunda ka mare ni akansa ka yi ka'dan na sake shayar da shi daga jikina".
Ya mi'ke da nufin yin kaina sai kuma ya shafo kunnensa ya tsaya cak ya ce "ko ki zo ki dauke shi, ko na sake ki".
Take na fusata irin fishin da ban ta'ba jin irinsa ba.
Na ce "Har abada ni sakakkiyar ce domin na haramta wa kaina daukarsa bare na shayar da shi".
Nan da nan ya ce "Amma ai ban kai ga sakin ba ko?"
Ido cikin ido na ce "Wallahi na saku, idan juninka dabbanci ne Wallahi zaka ga aikin jakai. Tunda muka yi aure ban samu kwanciyar hankali ba. Ba nau'in wula'kanci da baka yi mini ba.
Ba kalar tozarta ni da baka yi. Amma yau magana ta kare. Idan kana ganin ba zan iya rayuwa ba sai da kai to ka zuba ido ka yi kallo. A yau na yarda kaddara ce ta hada aurenmu. Na kuma kudiri aniyar sai na janyo kaddarar data ha'damu a ko'ina take na fatatattake ta. Yau ko ni ko kai a gidan nan".
Ransa ya kai koluluwar baci mussaman da ya kasa dukana.
Na yi tsaki na doshi kicin a dalilin kauri da nake jiyo wa ashe na dora indomie na manta.
Na kashe gas din. Na dauke wuka a k'asa, ban kai ga ajiye wa ba kawai na ga wata katuwar tsaka ta fado mini ai kawai na kwasa a guje na yi falo.
Shi kuma gani na a guje da wuka na doso shi, ai kawai sai ya suri Aman ya fice a guje tamkar mai gudun fanfalaki.
Ganin yadda ya tsorata ainun sai na yasar da wukar nima na rufa musu baya a tunanina maciji shi kuma ya ga ni.
"Ai muna fitowa harabar gidan muka ga Anti Maimuna da diyarta, ganin mu a guje gaba'dayanmu sai suma suka juya a guje.
Anti Maimuna sai kabarbari da hailala take yi tana cewa "Wuta wuta". Ba kuma ta fasa gudun ba.
Ban yarda na shiga sashin Umma ba. A harabar gate din namu gaba'daya na tsaya ina haki. Yayin da su Al'amin da Sakina suka iso suna cewa "Menene hakan?"
Dake asabar din karshen wata ne duk a gidan ake yini.
Yaya Gudale sai tsuma yake yana fa'din "Ban ta'ba shan maganin tauri ba Billahillazi! Wuka ta dauko zata caka mini".
Yayin da Al'amin ya ja gefe ya na'de hannu a kirjinsa yana kallonmu sosai.
Yaya Abbas ya ce "Me ka yi mata haka har ta iya jarumtar dauko wuka?"
Ya kasa magana.
Yayin da Sakina ta ce "Me ya ha'daku haka?
Sai lokacin hawaye ya b'alle mini na ce "Akuya ya mayar da ni, ya sake ni ne kuma ya bini da duka".
Yaya Al'amin ya fit ya ce "Again?".
Sakina ma ta girgiza kai ta ce "Shine kuma kika za'bi ki saka kanki a uku?
Saboda autan maza ya sake ki?"
Ya tunzura ya nuna Sakina da hannu ya ce "To tozarta ni, ai kin ga yadda dan-uwanta ya koma gefe yana shirin kai mini duka, amma ke baki yi niyyar taimkona ba.
Kuma ni ban saketa ba, ta sani, Allah ma ya sani".
Tun a wajen rikici ya fara tsananta domin dai Al'amin da Sakina sun kafe ya sake ni, suna ta kokarin juya maganar ma akan ai biyu yayi. Ga wanccan dayan aure ya kare kenan.
Yayin da ragowan jama'ar tun daga kan Abbas suka bi bayan Gudale bai sake ni ba, tunda ya musa.
Kowa ya yi masa shaidar baya k'arya ya hakikan ce, barshi dai a zolaya ko son ya burma mutum idan ya ga abu zai kubuce masa ba.
Yaya Abdallah ya mini wutah wuta na koma dakina.
Amma ni nasan me na kudire a raina.
Gaba'daya ya fice mini a kai. Tunda abin nan na Munubiya da ya faru fiye da wata bai saurare ni ba, wani irin zaman gaba yake da ni mai tsananin gaske.
Yanzu kuma akan d'an cikina ya nemi ya wula'kanta ni ya tozarta ni.
Ganin mun dawo gida sai kawai ya karkace ya cigaba da tijararsa har da fa'din tunda bana son Aman shima baya sona, dama shi tuni na fita akansa tunda har na iya cin amanarsa a cikin gidansa.
Sakina ce mijina da zan ce na fa'da mata, kuma a yadda yasan munafuncinta ai ba zata fadi gaskiya ba.
Gashi kuma yanzu kowa ya gane ita da Al'amin basa nufinsa da alheri, to Wallahi idan basu yi sa'a ba sai ya saka an dauke su an b'atar masa da su kowa ya huta da wuyar zamansu.
Idan ina zaune sai nayi ta tuna sadda ya ce mini Dan uwarki.
Ko kuma ki dauke shi ko na sake ki. Wato har na yi lalacewar da zai dinga yi mini barazana da saki?"
Na shige dakina na shirya yar jakata tsab.
Na ji a raina na ha'kura da shi, na ha'kura da duk abin da yake rikitani akansa. A yanzu na fahimci ba wai soyayya nake bu'kata ba.
Mutuntawa da kwanciyar hankali nafi bu'kata.
Washagari lahadi na tashi tamkar babu komai a raina, na yi yan hudimomina.
Ganin hakan sai ya saki ransa.
Washagari ya shirya, ya tafi wajen Aiki.
Sai da na tabbatar ya kai awa guda da tafiya na kinkimi yar jakata na fice a dalilin ya fita da Aman nasan kuma wajen Umma ya kai shi.
Kai tsaye asibitin Malam na nufa na samu Sakina na fa'da mata zan tafi Calabar wajen Anti Kulsum tunda yanzu tana can.
Nan da nan ta ce "Kin shirya zama mace ne Halimatu?
Idona ya ciko da k'wallah na ce "Eh".
Ta ce "To ba Calabar zaki tafi ba. Jira ni na dauko excuse na fito."
Na sallami mai adaidaita sahun da na yi niyyar ya kai ni har tasha.
Sakina ta dauke ni a mota muka biya ta dauki Al'amin, mun jima muna tafiya .
Sai da muka yi nisa sosai sannan ta samu waje.
Suka bu'kaci na fa'da musu gaskiya shin ya sake saki na ko kuwa?"
Kai-tsaye na fa'da musu gaskiyar abin da ya faru.
Dukkansu sun gamsu bai sake ni ba.
Amma zasu yi amfani da hakan su kawo mafita a cikin murdadden zamanmu da kowa yake cikin zulluminsa.
Kuka ya goce mini ina cewa "Ni dai na gama. Na kuma gaji ba zan koma ba.
Basu matsa mini ba, illah Sakina data mayar da abin tamkar wasa domin dariya ta yi mai yawa tana cewa "Yanzu Yaya Gudalen kike gudu Guduyo?"
Yaya Alamin ya murmusa ya ce "Wata'kila da za'a jima sai ki ga ta lalubo wayarsa".
Na fashe da kuka sosai har jijtinsu ya yi sanyi.
A Ranar suka samo mini wani daki a cikin wani gida da wasu suka karba hayarsa amma mai gidan ya ce ban da wannan dakin.
Ta hannun *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* muka samu wannan d'akin.
Daki ne madaidaici ya ji tayals da bandakinsa a ciki.
Cikin unguwar Mariri kusa da gidan talabijin din da Yaya Al'amin yake aiki.
Komai da zan bu'kata sai da suka zuba mini, hatta medium size din katifa.
Ga shopping din kayan girki da karamin gas dina.
Sai da suka tabbatar komai ya yi musu irin yadda suke so.
Sannan suka bar ni cikin kwanciyar hankali tunda gidan da mutane duk da dai kabilu ne da basa ma jin hausa.
Sakina ta karbi wayoyina.
Ta bani wata karama mai sabon layi.
Suka tafi, suka bar ni.

*Gudale*.
Ya dawo da yamma yana gaban Umma tana ta mitar idan ba Sa'a ta yi ba Halimatu ce ajalinsa. Tana kallona dinkin da aka yi masa a kunne duk kuwa da bai fa'di ita ta cije shi ba.
Ya yi shiru.
Ta zuciya ta ce "Matar da zata yaye maka d'a babu izininka kake zaune da ita, matar da zan fada ta fa'da, bayan sun shiga sun fita sun wargaza lamarin matarka. Oh ni Saude ina kallo".
Ya mike yana cewa ki tsananta yi mini Addu'a.
Ya sunkuya da nufin daukar Aman da yake ta barci.
Ta ce "je ka abinka ka huta gajiya tunda ta riga ta washe shi, kuma k'arya take yi fuffuka kawai take yi saboda tasan yanzu ta gama da kai, yau da wata ce ta haifi wannan yaron da tuni ba'a zauna lafiya ba."
Ya wuce ya barta tana faman yi masa addu'ar kada Allah ya sanya Halima da uwatata su kai shi k'asa.
A kasalance ya shiga gidan. Dake a cikin fishi mai tsananin gaske yake bai ko nemi inda take ba.
Tunda ya shige dakinsa bai fito ba, Sai sallar magahriba.
Bai koma ba kuma sai da aka yi Isha.
Sai lokacin shurun gidan ya masa yawa.
Ya leka ko ina bata nan.
Ya sauke girman kansa y shiga har dakinta nan ma shiru.
Zuciyarsa ta fara harbawa da sauri da sauri.
Ya dawo falo yana jin tashin hankali na ratsa shi.
Kamar an tsikare shi ya mike ya yi bangaren Baban Yara. Ya tarar da su a falo.
Suka gaisa Baban yana tambayar yasu Halimatu da dan-uwansa tunda amaren nasa sun yi masa nisa.
Kan Gudale ya sake daure wa tabbas basu san bata nan ba, ba kuma ta gidan.
Ya fice a gaggace babu ko sallama.
Wajensa ya koma ya dauki mukullin mota. Ya nufi gidan Sakina.
Yana ganinta a kicin ya shige cikin gidan yana ayyana ko ta karfin tsiya sai ta bar gidan.
Ya gama dube dubensa bata nan.
Ya hau tambayar su Nana ko Anti Halimatu tana ina?"
Nana ta ce "Mun jima fa bamu ganta ba.
Ya fice ba tare da ya cewa Sakina kanzil ba.
Wasa-wasa an doshi sati biyu yana gararanbar nemanta.
Har Abuja ya yi dirar mikiya a kokarinsa na gano ind take.
Gidan Al'amin da Sakina ya je yafi sau cikin carbi.
Haka gidan Abbas domin cousin dinta ce matarsa Azizan Umman Danladi Nasidi ce.
Gidan Ashir ne a dangi kawai bai je ba.
Wataran sai ya yi tamkar ya je, sai kuma ya fasa.
A sati na uku ne da tura ta fara kai masa bango, ya je har gidan.
Ashir da Farisa suka karbe shi cikin karamci. Jikinsa ya yi sanyi ganin yadda Ashir yake girmama Farisa ita kuma take masa biyayya kan jiki kan karfi.
Ya tabbatar shi bai samar wa Guduyonsa irin wannan nutsuwar ba.
Hankalinsa ya sake tashi ya tabbatar idan ta yi nasarar murkushe aurensa idan ta auri wani namijin da iya biyar da mace tsab zata manta da shi.
Ga dai Ashir da ya karbi Farisa ba dan yana so ba ta wanke masa son kowacce mace a zuciyarsa.

**
Hankalina a kwance nake zaune, domin kullum sai Yaya Al'amin ya zo ya duba ni safe da yamma.
Sakina ce ba kullum ba, amma bata wuce kwanaki biyu.
Sannan kullum sai mun yi waya da ita.
Ba abin da ya dame ni. Sai tunanin mahaifana. Ko ya ya suke ciki a yanzu?.
Kwanci tashi na kusa shafe kwanaki arba'in ba wanda yasan inda nake.

*Gudale*.
Zuwa wanann lokacin gaba'daya ya fita a hayyacinsa hatta uwarsa ta koma Jin tausayinsa duk da dai tana yawan ce masa "Yarinyar da ta biyo ka da wuka zata burma maka amma kake wannan tashin hankalin akan ta?"
Da sauri ya ce "Duk wacce ta ce miki an ganta da wuka karya take yi miki".

*Mama*
Kanta ta kasa sukuni tun tana ganin cewar fishi Halimatu ta yi ta tafi inda zata samu sukunin zuciya, tunda tasan Baban Yara ba zai bata goyon bayan ta zauna a wajensu ba.
Har ta fara sarewa. Gigitar da take ganin Sadik a ciki sai take ganin tamkar Umma ce ta kada mata yarinya uwa duniya.
Hankula suka fara tashi. Kowa ya shiga damuwar rashin Halimatu.
Yayin da Sakina da Al'amin suka yi kememe basu san inda take ba.
Sau uku Gudale yana cewa Baban Yara ya matsa wa Sakina da Al'amin sun san inda take.
Amma Baban bai dauki maganar serious ba.
Cewa yake yi "Ba yadda za'a yi suyi hakan.
Suma baka ga hankalinsu a tashe yake ba.
Addu'a kawai zamu yi Àllah ya bayyana ta, Allah ya sa kada bacin ran da tafi da shi ya yi tasiri akan ta."
Wannan maganar ta Baba ta hassala Gudale kwarai da gaske, ya zargi yabi bayan yarsa ne.
Ban da haka yana kallon bala'in da ya shiga amma ya nuna masa ya zalunceta ne shiyasa ta barsu cikin bacin rai.
Ya kwana yana nazarin hukuncin da zai dauka, domin ko sama da kasa zata ha'de ba zai rabu da ita ba.
Sannan yanzu ya gano inda matsalar take.
Sakina wa Al'amin sune a farko sai kuma samun daurin gindi a wajen Babansu.
Ya girgiza kai a fili kuma ya ce "Zan yi maganinku gaba'daya".
Sassafe dukkan sisters dinsa inka cire Antin Zaria da Sakina.
A waya ya kira su ya fa'da musu Baban Yara ya ki tsawatarwa Al'amin da Sakina. Alhalin suna da saka hannu a batan matarsa
Su taimake shi su yi masa kara su bashi gudunmawa kar su bar shi shi ka'dai.
Ya sake rokansu su zo a hadu a gida ayi shawara. Ya riga kuma ya shata layi da Sakina banshi babu ita har a kiyama kuwa.
Ai kuwa da yamma duk suka zo Kamar yadda ya so. Ya dinga ro'konsu su taya shi k'in gaida Baban Yara ko da na iya yau ne. Yasan hakan zai tayar masa da hankali sosai".
Cikin sa'a kuwa sun fito sai ga Yayar Kwalli da Baban Yara sun fito da alamun damuwa a fuskokinsu.
Duk suka risina suna fa'din "Yaya ina yini?"
Kawai Ramla ce ta ce "Baba ina yini a gajar ce..
Hakan ya tayar da hakankalin Baba matu'ka da gaske.
Yayin da Gudale ya yi fuska ko yayar ma bai gaishe ta ba.
Yaya ta yiwa Juwairiya da'kuwa tana fa'din baku ga Babanku bane?"
Suka dauke kai suna fa'din "Ya nuna mana banbanci ai. Ya nuna Halimatu ce mai uba, ya bar Sadik a maraya".
Yaya ta yi kan Juwairiya da ke a hannunta ta girma.
Yayin da Baba ya ce "Sadik zo mana ko kai ma ka gamsu baka da uban ne?"
Fes ya ce "Kwarai kuwa domin ka nuna mini hubbul ra'as da ace Abba ne yake raye ba zai ta'ba nuna wa Halima banbanci ba, amma kai akan kununena ka nuna mini ita ce taka ina zaluntarta.
Kiri kiri ka zuba ido ana mini wula'kanci ko ban ci arzikin komai ba, ai sai na ci na ubana da ya wanzar da rayuwarsa akan ka da iyalinka. Menene bai yi maka ba na gata? Shine yanzu zaka juya wa iyalinsa baya.
Sai kawai ya fashe da kuka sosai.
Yaya ta hauro ta ce "Ka ci uwarka Sadik!.
Nan da nan ya ha'diye kukan ya ce "Daina zagin Umma" zagi Abba kawai".
Ta dauki salati tana kuka tana cewa "Iyalin Alhaji ne suka saka mu a gaba haka da cin mutunci?"
Ya kuwa zabura tamkar ya afa k'waya ya ce "Me zaki ce mini, me zaki fa'da mini Yaya?
Kin riga kin nuna mini ke ido kike duba wa ba k'eya ba. Ban da hakan ina ce sadda Abba ya ri'ke mini Guduyo har kuka kika dinga yi da bai baki biko ba. Saboda yana da rai amma yanzu fa? Saboda ita Halima ubanta da ransa sai kika bi bayansu to ki je kwa hadu da Abba ranar k'iyama.
Al'amin da bai jima da iso wa ba, shi da Yaya Abdallah ya yi kan Gudale yana cewa "Bari dai na

53 / 61