Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   1 / 61

1 to 3K   out of 180.1K words

 *SABO DA KAZA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*


```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?

*Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).*


*SADAUKAWA GA IYAYENA GUDA HUDU*
*ALHAJI MUHD TUKUR*
*HAJ FATIMA LADI ALI*
*ALHAJI DAHIRU ALI*
*HAJ MARYAM HAMISU KANO*
*ALLAH YA JI'KANKU DA RAHMA YA BAKU ALJANNAR FIRDAUSI*.

*FATAN ALHERI GA MIJINA*
*(M.I. NASHE)*.

*JINJINA GA SHUGABAN KUNGIYAR LAFAZI WRITERS*
*SADIK ABUBAKAR*
*Na gode da kokarinka akan rubutuna*.

*Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.*
*Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*.
*Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.*
*Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*.

*JAN HANKALI*
*GABA'DAYA WANNAN LABARIN 'KIR'KIRARRE NE (FICTION) BAI FARU BA. HAKAN NAN SUNA DA GARURUWAN DA SUKE CIKI BANA KOWA BANE, NA ZABE SU NE TA YADDA ZASU 'KAWATA LABARIN.*
*IDAN KIN CI KARO DA ABIN DA YA YI KAMANCECENIYA DA RAYUWAR KI TO AKASI NE. MANUFAR LABARIN JAN KUNNE DA HANNUNKA MAI SANDA AKAN WANNAN RAYUWAR MAI CIKE DA RU'DANI. BA WAI SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA BA*.




1&2.
*Free page.*


*Tushe*

Asalin kakanmu Alhaji Zubairu Lawal Moriki, 'dan asalin 'kauyen Moriki ta cikin 'karamar hukumar Zurmin
jahar Zamfara ne. Bahaushe ne, kuma Bafulatani, domin mahaifiyarsa Bafulatanar daji ce, kyakkawan dattijo fari tas. Ya taso cikin tsari da 'ka'idar tarbiyar Bahaushen Arewa mai tsananin ri'ko da dokokin shari'ar Islama.
Fataucin dabbobi ne ya kawo shi garin Kano har ta zame masa tamkar gida. Domin kuwa sannu a hankali ya kwaso iyalinsa suka dawo kano gaba'daya. 'Ya'ya biyar mai dakinsa Maimuna (Adda) ta haifa masa, duk da sun binne wasu da dama a dalilin tana wabi.
Hajiya Hafsatu ita ce babba (Yaya ta 'Kwalli) ba ta ta'ba haihuwa ba, sai dai kuma yan'uwan nata ba su ta'ba bari ta ga gurbin rashin haihuwa ba. Sai dai kawai motsawar da zuciya za ta yi idan sha'awar ganin jininka ta motsa. amma ba don kukan wani abu ba, domin 'ya'ya biyu 'yan uwanta suka bata ta goya, ta kuma aurar. Dukkan abin da ya shafi yaran kuwa yana hannunta. Ramla da Ashir. Mace mai zafi idan aka tabo ta, mai son dinke barakar zumunci, duk inda ta ga zumunci zai samu tawaya yanzunan za ta yi dukkan mai yiwuwa ta 'dinke shi.

Sai Alhaji Abubakar Moriki (Abba) shi ne na biyu, dattijon arziki mai tsananin ri'ko da ka'idojin shari'a, masoyin zumunci da kyautata shi. Dukkan karatunsa ya yi ne a bangaren addini, a 'kasar Sudan ya yi digirinsa na farko a fannin sanin ilimin Hadisai. (Hadith Science) Daga nan ya wucewa 'kasar Masar ya sake zurfafa iliminsa a kan sanin a fannin Shari'a da rabon gado. Dukkan karatun tallafi ne na gwamnatin tarayyar Najeriya.
Daga nan kuma sai ya fa'da harkar kasuwaancin safarar zobo da 'karo a tsakanin 'kasashen Africa. Sosai ya samu daukaka a harkar, ba 'karamin nasibi yake samu ba, domin idan ana lissafa attajirai, babu shakka za a saka Alhaji Abubakar Moriki.
Matarsa 'daya Hajiya Saude (Umma). 'Yar asalin garin Yola ta jahar Adamawa ce.
Kyakkawar mace fara 'kal mai cikakken diri, mai yalwataccen gashi, sai dai gajeriya ce.
Mace ce mai izza da jin 'kai, ta tsani wani ya rabe su, kasancewar mijinta shi ne garkuwa a danginsa.

'Ya'ya shida Ubangiji ya azurta su, biyar 'din farko dukkansu mata ne kyawawan gaske domin dukkansu ita suka biyo, suka sami tsayin mahaifinsu duk da mijin nata ba baya ba ne wurin kyakkawar sifa, sai dai ko kusa ba a hada kyaun mace da namiji, sannan farinta da dogon gashinta baki sidik sun shahara, sai ta zamo tamkar Balarabiya. Haka 'ya'yanta suke farare dogaye, masu gashi, duk irin yadda Ubangiji Ya azurta ta da samun wa'dannan kyawawan yaran kuma masu lafiya, ita ba ta gode ba, domin ba abin da take so irin ta haifi namiji. Hafsat ce babba, wacce ya yi wa yayarsu magajiya, sai Maimuna (Ummu) mai sunan kakarmu, sai Juwairiya, Ramla, Sakina, sai autanta da ya ci sunan sahabin Ma'aiki Abubakar ake ce masa Sadik kasancewar sunan Abbban ke nan, ita kuma ta ce Gudale.

Sai Hajiya Binta Moriki (Maman Kebbi) da take aure a Kebbi tana da 'ya'ya uku Shafa'atu, Adnan da Ashir.

Sai Alhaji Ssni Moriki (Baban Gusau) da ya kasance dan kasauwa mai sayar da suturu, a cikin babbar kasuwar Gusau, a can kuma yake zaune da iyalinsa. Mutum mai tsauri da fe'de gaskiya, komai 'dacinta, marar daukar wargi. Matarsa 'daya da yara biyar, Fatima, Abubakar, Maimunatu (Ummj), Abbas, da Farisa. Abbas kuma yana tare da mu, tun daga karatun sakandire da ya yi a Science Dawakin Kudu da su Ya Sadik shike nan ya zama dan Kano, duk sa'anni ne da su Ya Al'amin, Kuma duk Gudale ne 'karaminsu.

Mahaifina Alh Ibrahim Moriki (Baban Yara) shi ne autansu, kusan Alhaji Abubakar shi ya yi masa komai tunda ga kan hidimar makaranta, har ya zuwa aure. Ma'aikaci ne a hukumar ilimin bai 'Daya. Mahaifiyata Safiyya (Mama) 'yar Kano ce, ta fito daga unguwar Magashi, cikin babbar zuri'a, ina nufin masu haula da yawa ba wai ku'di ba. Matsakaicin kyau ne da ita, sannan tana da dan jiki, da manyan idanuwa dara-dara, sannan wankan tarwada ce, yayin da Baba ya kasance fari tas! Lokacin da aka auro Mamanmu, Umma tana goyon Ramla ne, sosai suke zaman lafiya, domin Mama tana gama gyara bangarenta, matu'kar mijinta ya fita to kuwa za ta rufe ta tafi wurin Umma saboda a gidansu na gado suke zaune wanda Abba ya fadada shi, ya zamanantar da shi, a cikin unguwar Hausawa 'Yan-Babura.

Sosai Umma take jin da'din zama da Mama, saboda biyayyar da take yi mata, musamman yadda take hidima da 'ya'yanta, barin Ramla da barci ne kawai yake raba su.

Mamanmu ba ta cika shekara a gidan ba ta haifi Abdallah, lamarin da bai yi wa Umma Da'di ba, ta ji babu dadi sai dai ba a samu canjin mua'amala ba. Kafin Mama ta cika shekaru hudu ta hada yara Uku duk maza Abdallah, Azzubair (Babangida) da kuma Ammar.

A wannan lokacin kuma Umma ta fito da dukkan munanan dabi'unta, sosai ta dora karan tsana a kan Mama da ya'yanta, babban ba'kin cikinta yadda haihuwa ta tsaya mata cak ga kuma wata ta zo tana haifar maza duk shekara, nan gaba hasken da yake kofarsu zai koma kofar Safiya da Ibrahim. Ta fara hana 'ya'yanta zuwa bangaren kanin mahaifinsu, sannan kuma idan Maman ta zo, ba za ta ga fuska ba, 'dan abu 'kank'anin zai faru za ta fara habaicin har gobe mijinta shi ne garkuwarsu.

Sosai Umma ta takura wa Mama har ta kai fargabar ta yi ba'ki take yi, saboda yadda take fuskantar tozarci.
Hakurin Mama yasa ko Baba bai fahimci halin da suke ciki da Umma ba, sai da tafiya ta yi nisa. Shi ma rashin ganin su Ramla a gidansa ne, ya kuma lura Mama ta rage shiga wajen Umma. Kasancewar shi ma mai son zumuncin ne, sai ya yi kamar bai fahimci matsalar a wurin matar yayan nasa take ba, yana yi wa tasa matar wayo da dabara ta hanyar cewa ita ce 'karama, sannan ai ya lura ita ta janye daga jikinta, ya lura ba ta zuwa 'kofarta kamar da.

Ana cikin haka Umma ta haihu, again dai mace ce, ko ka'dan ba ta yi farinciki a zuciyarta ba balle ta yi godiya.
Aka yi sunan Sakina babu wani armashi, saboda ta riga ta dora rai a kan boy ne a dalilin ta yi scanning an tabbatar mata namiji ne, sai kuma ga kyawawar budurwa ta iso. Watan Sakina goma Mama ta sake haihuwar Al'amin, Wohoho! Ina wuta Umma ta jefa ta, a lokacin mahaifiyarmu ta fuskanci wani irin tashin hankali da matsatsi, domin an kai jallin da ko tsakar gidanta ya gagare ta fitowa, kullum tana 'daki, haka 'ya'yanta, sannan duk shedantar Umma ba ta yinta idan maigidanta Abba yana gida, musamman da yake mai yawan tafiye-tafiye ne sai abin nata ya sake bun'kasa.

Tashin hankalinta yadda duk tafiya ba ya banbance tsakanin 'ya'yansa da na 'kaninsa, hatta keke da ya ce ba ya son 'ya'yansa mata su hau, duk ya saya wa su Abdallah kowa da nasa, haka indai yana gari to da Abdallah yake yawo ko'ina, daurin aure ne, ko ta'aziyya ko yawo haka, duk dinkin da zai yi tare yake yi da shi. Haka makaranta 'daya suke zuwa da 'yayansa shi ne kuma yake biya gaba'daya.

Wannan ya sake ki'dima Umma tana ganin tamkar gazawarta ne yasa ta kasa haifar namiji duk kuwa da ko a fuska mijinta bai ta'ba nuna mata cewar 'ya'ya matan da take haifa masa ya gaji ko baya so ba, duk haihuwa sosai yake murna da hidima ya kuma zaba musu kyawawan suna.

Cikin ikon ubangiji watan Al'amin goma.

Umma ta haifi 'danta lafiyayye sak ita ya biyo shima, fari kal, mai gashi domin gashin har idonsa yake, tun yana jaririnsa dan tsurut ne babu nauyi, ma'ana ba jiki. Ga mamakin Umma Abba bai yi wani zumudinsa fiye da su Sakina ba, domin har zuciyarsa bai ji yaron ya 'dara Abdallah a wajensa ba, ke nan shi ba yanzu ya yi 'da ba.

Wannan al'amarin ya sake tsananta kiyayyar Mamana a zuciyarta, ta gaskata asiri take yi don ta mallake su ga'badaya.

Rainon Abubakar ya banbanta da duk 'ya'yan da Umma ta haifa, wani irin gata take nuna masa tamkar dai ba ta samu haihuwa gaba'daya ba sai da ta shekara talatin a dakin miji. Komai na yaron a wajenta mai girma ne, ba ta ha'da shi da komai, tun mijinta na yi mata fa'dan kar ta lalata shi, har ya ha'kura ya koma yi mata addu'a.

Shekarar Sadik wanda Umma take'kiransa Gudale biyu aka aurar da Hafsatu 'yar wajen Umma ta farko aka kaita Zariya, saboda nan ne garin mijinta, kuma malami a Jami'ar Ahamadu Bello, daan boko na gaske, tun kafin auren ya sama mata gurbin karatu a Jami'ar inda za ta karanta Tsumi da Tanadi (Economics).
Hakan yasa Umma ta 'ki haihuwa tuburan ta dakatar da ita da 'karfin tuwo a cewarta ta barwa Yara.

Wani abin da ya damu Umma yadda Sadik ya bijire mata daga hana shi zuwa sashinmu, duk juyin da za ta yi sai ya zo wajen Al'amin, kullum cikin saya masa kayan wasan da za su dauke masa hankali take. Amma da zarar gari ya waye tofa zai tafi, ba zai yarda ya dawo ba, sai ya yi barci sannan Abdallah zai kawo shi.

Watarana yana ta kukan zai tafi ta ri'ke shi ta hana, Abba ya gane dalilin kukansa aikuwa cin mutuncinta da ya yi ba ka'dan ba ne, ya ce matu'kar dansa ne to dole kuwa ya so jinin Ibrahim.
Shike nan sai ya zama rabi-rabi, har ya fi zama wurin Mamanmu.

Mama kuwa tun haihuwar Al'amin ta dinga 'bari, duk cikin da za ta samu sai ya bare, a haka har aka shafe shekaru tara da haihuwar Al'amin yayin da Sadik yake da takwas, shakuwa ce mai tsananin gaske a tsakaninsu, hakan nan sosai Ya Sadik ya shaku da Mamanmu.

Na iso duniya ne cikin cire tsammanin haihuwa daga iyayena, sannan ba 'karamin wahalar gaske Mama ta sha wajen haihuwar ba, hakan ya zama sanadin da aka juya mata mahaifa gaba'daya.

Idan mai karatu na biye da kyau, zai gane mu biyar ne 'ya'yan Ibarahim Moriki, ni ce kuma 'ya mace tilo da na biyo maza hudu, kamar yadda Ya Sadik ya biyo mata biyar ya zama namiji tilo.

Na taso cikin gata iri-iri, ba daga iyayena ba, ba daga yayye ba, haka nan ba daga Abba da iyalinsa ba, kawai Umma ce ba ta sona, take adawa da duk abin da mijinta ko 'ya'yanta za su yi mini. Ta yi juyin duniya Sakina da Sadik su daina kula ni amma ina, domin duk miskililancin Gudale zai dauke ni, shi yasa mafi yawan hotunan muna yara ina hannunsa, ko ina kan cinyarsa, muna da hotuna ni da shi muna yara kala-kala.

Wani ikon Allah yadda Ya Sadik ya fi zaman sashinmu, ni kuma na fi zaman sashinsu saboda Sakina, tunda aka yaye ni, na yi wayo kullum ina gurinta, duk zare idon Umma da muzurunta ba na fasa zuwa ko fasa zama, sai idan Sakina tana makaranta, domin duk inda za ta je tare da ni take zuwa.

A lokacin an aurar da duka 'ya'yan Umma Sakina ce kawai ta rage.

Sakina ita ka'dai ce mace domin tsararrakinta duk maza ne, Al'amin da Sadik. Don hakan shakuwa ce a tsakaninsu ba ka'dan ba. Sai dai ba zai yiwu ta dinga yawo tare da su ko kwana ba, sai ya zamana ta ja ni a jiki duk da karancin shekaruna, tunda shekaru goma ta ba ni cif, tare muke kwana, ita take mini wanka ta shirya ni.
Wata irin shakuwa ce ta musamman a tsakaninmu, hakan ba 'karamin da'di yake yiwa Abba ba shi yasa ma ya dawo da ni bangaren gaba'daya. Umma ce take kyashi da hakan, take yawan hantarar Sakina a dalilin ita ta janyo ni. Da wayona da hankalina aka yi bikin Sakina, domin na shekara sha uku a duniya, saboda sai da ta yi karatun Nursing ta gama, a lokacin tana da shekaru ashirin da uku.

Tunda aka yi bikin Sakina na kasa jin da'din zaman, saboda ka'daici da rashin samun fuskar yin walwala, na fara a-sha-ruwan-tsuntsaye, idan ba Abba ne a gari ba, ba na kaunar kwanan wurin Umma.

A hakan dai rayuwar ta ci gaba da gudana ina kallon irin yadda mahaifiyata take rayuwa cikin zullumi da kaffa-kaffa, saboda takurar da Umma ta yi mata. Musamman da Abban ya sayi wani katon kango da yake jikin gidanmu, ya fasa kofa ta cikin gidan aka yi shuke-shuken su alaiyahu, shuwaka, lemon tsami, zogale da sauran tsirrai. To fa Mama ba ta isa zuwa ta tsinka ko ta aika a ciro mata ba.

Na kammala aji uku na sakandire ba dadewa da bikin Sakina, kwatsam sai ga Abba da takardar makarantar kwana ta Sojin Sama ta garin Kaduna, (Air force Staff School Kaduna). Ko ka'dan ban yi murna ba, domin ban ta'ba sha'awar boarding ba, Aunty Ramla ce kawai ta yi boarding a gidanmu, sai su Ya Sadik.

'Karin 'bacin raina Kaduna ta yi mini nisa, da ma a cikin Kano ne da sauki. Hankalina ya tashi, na dinga kuka. Baba ko ya ce ba zai yiwu Abba ya yanke hukunci ya yi masa musu ba. Ya Sadik da ke tsakaninmu da tsakuwa sai murna yake yi yana fa'din, "Na gode wa Abba da ya samo miki boarding wata'kila idan aka yi sa'a kya zazzage wannan tebar da kika ajiye tamkar wata uwar mata, ke kam da wuri za ki tsufa."

Wadannan kalaman su ne kullum a bakin Ya Sadik har ya sa na zama very guilty. Ina tunanin laifi ne don na kasance mai jiki.

A tsaye nake cak ma'ana ina da tsayi, sannan ina da jiki sai na zama irin giant din nan da suke tafe da tsayinsu da jikinsu, ni din fara ce tas, sannan na yi sa'a ina da manyan idanu dara-dara, hanci ba wani dogo ba ne, amma kuma dai ba laifi akwai, sai dimples a dukkan kumatuna, ko abinci nake ci, suna lotsawa bare na yi murmushi ko dariya.

Ina da gashi sosai, sai dai yawa ne da shi ba tsayi, har gaban goshina yake, har wani kamar saje ya yi mini, 'kirjina a cike suke kwarai da gaske, hakan ya janyo ana mini kallon na zarce shekaruna, haka 'kasana a bude yake, kusan ma kibar ta fi shahara daga kuguna.

Bangaren halayya kuwa na kasance mai nacin kan abin da na saka a raina, sannan ina da kafiya, sai dai kuma ina da hakuri, da wahalar gaske aji ana fa'da da ni. Ni ko irin fitinar yarinta ban yi ba, ba ni da abokin fa'da sai Yaya Sadik shi ma shi ne mai tsokanar ta hanyar ce mini Yar sukuta, ko Sady bon bon, ko Guduyo, duk cikin sunayen na fi tsanar Guduyo, ban san manufar sunan ba, amma dai na fi zaton saboda ina da jiki ne.

Ba yadda ban yi ya daina ba amma ya 'ki, sai na tsiri ce masa Gudale. A farkon abin ba kurarin da bai mini a kan na kiyayi ce masa wannan sunan domin ba sa'ana ba ne.
Ban ji ba, don kuwa ban daina ba, tun yana kawo mini duka, har ya hakura.

Ni dai tun tashina ban ga fitanannen a gidanmu irinsa ba, domin Umma ta riga ta sangarta shi, komai yake so sai ta yi masa koda kuwa ba daidai ba ne, yanzun nan zai gama yin iyashege amma da zarar ya bukaci abu to ba ta tuna laifukansa za ta yi masa son ransa jikinta na rawa.

Kowa nan nan yake da shi, ba ga su Mama da Baba da yafi zaman wurinmu ba, ba ga Ummansa ba, ba ga su Ya Abdallah ba, barin ma Ya Al'amin da komai zai yi a duniya sai da Gudale, wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninsu tamkar tagwaye, kammaninsu daya sai bannacin shi Al'amin baki ne, sannan mai sanyin hali ne, yayin da Sadik ya zama siriri fari tas, yanayinsa 'daya da Ramadan Both hatta gashin kansu kusan iri 'daya ne saboda ya dauko jinin fulanin Yola.

Abba ne kawai ba ya ta Sadik saboda bai son giggiwar da yake yi, ba ya banbanta shi da yayyuna, kusan ma ya fi fifita Ya Abdallah domin ni dai ban taso na same shi a gidan ba, Abba ya kai shi 'kasar Oman yana karantar Law.

Haka Yaya Babangida a Sudan ya yi digirinsa akan Arabiya, Ya Ammar kuwa a Jami'ar Nigeria (Nsukka) ya

1 / 61