Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 47

18K to 21K   out of 139.6K words

mutane suna wucewa suna kallonta babu wanda yayi zaton matar gidance domin komakota basusan ankawo amaryaba sunyi zaton Raliya ce itakuwa daga yanayin kawayenta da gantalin datake fita kullum yasanya suka gano bamatar arzikiceba donhaka babu wani wanda yarabeta tsawon lokaci tananan zaune tana cike da nishadi shikam Ahmad gidansu yanufa kaitsaye yatadda yan uwansa sunzo dayake ranar assabar din karshe sati ce anata cafta saiyazauna anatayi dashi Umma saishige dafice takeyi wurin ganin takammala kirkin rana kunya da nauyi sunhana ta tambayi ma'u takula shima Ahmad kunyar yimata maganar ma'u yake amman daga yanayinsa talura babu wata matsala anan sukaci abinci lokacin da inna tazuba abincinne ma yatuna da ma'u da abinda zataci saidai Allah yataimakeshi umma tacika flask din da dambu datayi tadire tace gana yar gidanka Ahmadu yaji dadin hakan danyana kammala cin abincin yadauki flask yahaye babur dinsa yanufi gidanshi abinda ybashi mamaki da tsoro baiwuce hangon ma'un shi zaune akofar gida daramba tana hirarta da wasu yara da alama yayan makota tasamu tabiye musu yanacigaba da karatowa mamakinsa nakara linkuwa harzuwa sanda ya iso indatake da babur dinsa tadaga kai takalleshi saitadan firgita masamman yanda yanayinsa yacanza lokaci guda takalli yaran dake gabanta tayi duru duru sai tamike ta shige cikin gida dagudu batayi birki ko inaba saibayan gado tana huci talabe cankurya tana maida numfashi yashigo gidan ransa yana suya ya iso harbayan gadon yajawo kunnenta tafasa ihu jikinta naci gaba da bari dan Allah yaya Ahmad kayi hakuri Uban wa yace kifita waje kizauna komunkoya miji wannan tarbiyar agidane? Cikin sheshshekar kuka tace A ah gidan ne shiru ga tsoro shine naleka waje don Allah kayi hakuri tafashe dakuka yadunkule hannu ya rankwasheta yana fadin koda zanhakura saikinji ajikinki kifita kofar gida kizauna kamar wata sokuwa inakikakai aurenki yakoma rankwashemata kai kwas akanta takuma sanya ihu saida yajeramata guda hudu sannan yasakarmata kunne takuma fashewa dai kuka lokacin yafice daga cikin dakin yanufi shago domin yasanya uniform dinshi yatafi wurin aiki saidai yanashirin kukan ma'u yana dukan zuciyarshi tuncan baya bayason bacin ranta yakanyi komai dankar abatamata rai balle dayaji sunan mahaifiyarsa ne akasanya mata hakan yakara soyayyarta acikin zuciyarsa yanzu kuma gashi tazama matarsa wato yanzu soyayyarta agareshi hawa ukku ce don haka dole intana kuka yarikaji harcikin bargonsa da kyar yakammala shirinsa yanufi soro da zummar yafice saikuma yaga rashin dacewar hakan dan haka yajuya cikin gidan yanufi dakinta tana rakube a inda yabarta abayan gado tana kuka ya isa inda take tahada kai da gwiwa tana sharbe yakira sunana tadago takalleshi dafaduwar gaba don batasan yadawo dakinba tayi zaton kara dukanta zaiyi donhaka tafara ja dabaya tana sharbe majinarta tana kuka



24 April 2015 at 08:03 · Public

Save · More

Like

React

Comment

Share

Like51

Write a comment...



·

Aminu M Sirajo

Tnx

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Omar Uba Abbaskk

tnx

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Bakoji Lamara Misau

Gud

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Bilkisu Mukhtar

Tnx..

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Zainab Yahaya Bappah

mungode muna jira

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Hassan S Saddiq

tnx

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Usman Mustapha

Yayi Kyau

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Faisal Sa'ad Isma'il

Mungode

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Afra Ahmad

Please ayi posting kallon kitse

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Fatima Yaquub

tnx

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

View more comments&

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Sirrin zuciya

DAME AKE ADO part 11.

2ã 4ã DAME AKE ADO 2 Dan Allah kayi

hakuri wlh bazan kara fitaba

nadaina..........yakada kai yana karemata

kallo wlh da Abba yayi shawara dashi

dazaice abar ma'u takammala karatunta

tazama cikakkiyar mace kafin ayimata

wannan auren yarinya ce tsaba yanzu

tafara kirgen dangi irin namata baikallonta

da komai haryanzu sai kanwarsa ihunta

yadawoda shi hayyacinsa yace kinga

badukanki zanyiba cewa zanyi kidaina fita

waje idan nafita zanturo miki yaran

sudinga tayaki hira kinjiko? Tadaga kai

dagamsuwa tanacew to tuni kukun nata

yakoma ciki tafara dariya gawannan idan

kinason cin wani Abu kisaya gakuma abinci

can aflask Umma tace akawomiki ta amsa

hannu biyu tana godiya yakada kai yafice

tabishi dasaikadawo yaya kamar yadda

tasaba yimasa agida ya amsa da Allah yasa

yafice takalli dari nan tadaka tsalle cike da

murna waiyau itace keda dari duk tatace

lallai Allah yasanya yara sushigo su

siyomata agwalima yayi sa akuwa yan

yaran dayatadda azaune dasu har lokacin

sunanan zaune suna wasansu don haka

yace maza suje sutayata hira dahanzari

suka shige gidan suna murna sallamarsu

tatsinkayo acikin gidan tayi waje dagudu

cike da murna sai alokacin tahango flask

din abinci tashiga kicin tadauko faranti

tadebi nata suma tazuba masu nasu suka

zauna sunaci suna hira itakuma tana

kwasar dariya tundaga wannan rana gidan

nata yazama gidan yara domin ance laifi

yaro kiwa laifin babba rowa Asma'u kam

hannunta asake yake akwaita da kyauta

Ahmad hankalinsa yakwanta shike

hadamusu abinci dazasuci dasafe darana

da dare saidai idan yasan yanada aikin

safe tun asuba zaidora kirkin rana yazuba

aflask ya ajiyemata da daddare kuwa

yazomata da ( take away ) domin yace

batayi wayon dazatayi girkiba harta kunna

risho ba aikinta kawai wanke wanke da

shara ko wanki shine kemusu sanda

yakeda lokaci saidai yanashan fama da

kurciyar ma'u da shirmenta yautunda safe

yakammala girkin yazubamata aflask

yarufe harya kammala shirinsa tana gindin

Tv tana kallon NTA muhawarace akeyi da

daliban makarantarsu dana wata

makaranta cikin harshen turanci tanajin

kamar tatsallake tafada cikin tv idan anyi

tambayar dayan makarantar suka kasa

amsawa tasani saitayi karaf tace dan Allah

kazane kuce kaza ahaka ya isketa tsahon

zamani yana kallonta batasan yazoba

tausayinta yakamashi ma'u tanason karatu

kwarai shima yanason tayi karatun saidai

yanada tsananin kishi bazaitaba yadda ace

matarsa tanazuwa makaranta kullumba

dama dai ace takammala karatunta akayi

aurensu dayaga batada niyyar dawowa

hankalinta yakira sunanta tawaiga dasauri

tace la yaya harka gama shiri zo dan Allah

kaga wadannan sokayen sunkasa amsa

tambayoyo nafi sauki kumafa sinio

dinmune a school yayi murmushi yace

nana nidake sauri zantafi aiki inanakeda

lokacin kallo amshi Nan yamikamata kudin

tasanya hannu ta amsa yaci gaba da

magana zanwuce sainadawo akwai abinci

aflask banason barna dawarkai kada

kilalata komai kinjiko idankuma andauke

wuta kikashe kayan kallo duka dan kada

akawo wuta sulalace ta amsa dato tana

cigaba da kallonta haryakai bakin kofa baiji

tace saikadawo ba yawaiga yakalleta yace

yauba babu adawo lfy kanwata dasauri

tace lah yaya namanta adawo lfy tana

fadin haka tamaida kanta wurin kallonta

yayi dariya yafice baijima dafitaba kuma

nepa suka dauke wuta bakinciki kamar

yakasheta domin taso taga karshen wasan

takoma kan kujera takwanta tafara tunane

tunanen duniya kwatsam yayarta kuma

kishiyarta tafadomata saitaji gaba daya

ranta yabaci saidai abinda kedauremata

kai baiwuce rashin zuwa gurinta da yaya

Ahmad keyiba ko maganarta ma bayayi

sam tanason tatambayeshi amman kishi

da haushi raliya yahanata don haka tabar

abin cikin ranta tana kwance tana sakawa

da kwancewa har kawayenta suka fara

shigowa tamike tafita suka fara lido A'ilo

daya daga cikin yaran ta kalleta tace waike

ma'u bakyayin sabon girkine kullum saidai

naga kindebo acikin flask ma'u tatabe baki

da damuwa ban iya girkinba yayana ne

yakeyi yazuba acikin flask A'ilo tace

cabdijan to idan bakya gwalgwalawa yaza

ayi ki iya kinganni bankai girmankiba har

wake dashinkafa nake dafawa babanmu

arisho bama da murhuba mamaki yakama

ma'u tace ke A'ilo koni danagirmeki

ummana bata bani girkina saitace

kazantane saidai kawai na izamata wuta

amman kice harwani girki akebaki A'ilo ta

tafa hannu tadoki cinya shekarata shabiyu

amman wlh ina girki tambayi kanena ma

sale idan yashigo saiga sale yashigo da

gudu tamkar yasan nemansa ake A'ilo

tace yauwa sale zo dan Allah banayiwa

ummanmu girki sale yatsaya yana haki

kinayi mana ranar har danwake

kikayimana ma'u tafe kirji danwake lallai

kin iya girki daman inason na iya don allah

ya akeyi A'ilo tayi murmushi dadai akwai

fulawa ne dasai nanuna miki yanda akeyi

ma'u tace bari naduba inada yake ajiye

kayan abincin nasa Allah yasanya da

fulawar daman nagaji dacin shinkafa da

miya ko dafaduka shikenan fa abinda ya

iya tanufi dakin taduba ga rashin sa arta

bata tadda fulawaba amman saitace ga

kudi asiyo gwangwani ukku nafulawa su

kwaba dadi ya cika yaran suna murna

yauzasuci girkin amarya ihu suke yi tamkar

ranar sallah nandai sale yafalle dagudu

yasiyo fulawa aka kwada aka kunna risho

aka fara kokarin saka danwake gabadaya

akaduru akicin din sugoma A'ilo ce agan

risho tun ruwan bai tafasaba akafara saka

danwake duk sanya daya sai anyi ihu tafi

ahaka akammala sakawa aka koma gefe

anajiran yatafasa gabadaya danwake ruwa

yahadu ya cakude ahaka akafara kokarin

saukewa anduba babu tsumman da za

asauke ma'u tace bari tasauke bakin

zanenta takama tana kokarin saukewa

ashe zanin yalaso wuta zafin wutar

dayatabota yasanya tafasa ihu tasaki

tukunya da zaninta dayakama da wuta

nanfa akayi waje ana ihu domin ruwan

danwake yafadi akasa yafallasawa kowa

zanen ma'u yacigaba daci dawuta sukuma

suna ihu gobara! Gobara!gobara haryafara

laso kayan kicin kamar Anjefo shi Ahmad

yashigo agigice jin ihunsu yahango abinda

kefaruwa yakalli ma'u dake ihu daga ita

sai siket duk saiya dimauce yama rasa

mezaiyi candabara tafadomasa yadauki

wani omo da ruwa yanufi kicin dagudu

yafara watsawa dakyar yasamu tamutu

yadawo dabaya yatsaya yana haki saikuma

suka kama ihu wai wutar tamutu takaici

ya isheshi yanufesu afusace yafara dukan

yaran suka sukayi waje aguje afirgice

domin abin yabasu mamaki domin sunsan

duk ihun dasuke baya ce musu kala

amman yau saigashi harda duka yakoma

kan ma'u yazabgamata mari yakoma

zabgamata tafasa ihu tarike kunce

maimakon tabashi tausayi saima kuluwa

yayi yahauta da bala I sai da yayi iyakacin

son ransa sannan yanufi kicin din yafara

gyarawa ranar dai har dare yana bala'i da

masifar dabatasanshi da itaba tayi kum

adaki saikuka washe gari baije ko inaba

yakuma hana kowashigowa gidan duk

yaron dayazo saiya fatattakeshi yafita

dagudu dan haka adaki tawuni tawuni

tanakuka saidai tagama saka abinda zatayi

lokacin daya fita sallar isha'i tadauko

kayanta data kulle adankwali tanufi

hanyar soro tanatafe afirgice cike da tsoro

domin batason kowa yasan inda zata gudu

tagaji dazaman gidan tunda aiba birsina

baceba tafito tajanyo kofar gidan ahankali

tabi gefen duhuwar dake kofar gidan

tafara sauri tana waige don batason wani

yaganta HMMM MUHADU AKASHI NA UKK

U

DAME AKE ADO BOOK 3

1ã DAME AKE ADO 3 Ma'u tanatafe cikin

duhuwa tanata sauri burinta tayi nisa

dagidan cikin ranta tana saka bazataje

gidan yayyentaba kogidan umma bazata

ba domin zasu iyadawo da ita gidan yaya

Ahmad shikuma yacigaba da dukanta yana

kulleta cikin gidan kamar mayya bata

Ankaraba tayi karo Dawani mutum

kayanta suka zube yayi taga taga kamar

zata fadi Allah daiyasanya bata fadinba

mutumin yazabga salati yana kokarin bata

hakuri saigabanta yahau bugabawa domin

muryan yayan natane hakan yasanya

tagintse bakinta batace komaiba tasuri

kullin kayanta tawuceshi dasauri cikin ikon

Allah aka kawo wuta daidai lokacin da

Ahmad kebata hakuri yadan bita da kallo

da mamakin jin wacce yabuge din batace

komaiba har ya ayyana cikin ranshi ko

kurma ce sai kuma ya hango kamar ma'un

sace mamakinsa yakara karuwa ganin

tanata sauri tayi gaba yafara kwalla mata

kira ma'u ma'u jikinta yadauki rawa

saboda yagama shigarta tatsaya cak takasa

matsawa daga inda take takuma kasa

cigaba da tafiya har ya isa inda take tsaye

yaleka fuskarta don kara tabbatarwa itace

hankalinsa yatashi da yatabbatar itace

cikin fargaba yace ma'u inazaki har lokacin

taka magana sai idonta dake zubda

hawayen tsoro kamar yakara yin magana

saikuma yafasa ya kama hannuta kawai

yafara tafiya Asma'u tafara binsa tana

hawaye SHIKENAN TASHIGA UKKU TASAN

YAU MAIRABATA DA YAYA AHMAD SAI

ALLAH GASHI GIDAN BABU KOWA BABU

MAIKWATAR TA Hakatayita binsa zaro

zaro tanarungume dakayanta harsuka

shiga gidan suna shiga yamaida gidan

dasakta yadatse hakan yakuma

yakadamata ciki tafashe dakuka sosai

yakalleta harlokacin hannunta yana rike

cikin nasa baice komaiba saida suka

dangana cikin dakinsu yazaunarda ita

gefen kujera yana fadin inazuwa bari nazo

yafice yanufi dayan dakin dasauri tamike

tafara zagaya dakin tana kuka hannunta

bisa kanta tafara magiya don Allah kayi

hakuri yaya nadaina wlh bazankara daidai

lokacin yazo da zabgegiyar belt saita kuma

zabura tafara ihu dakarfi yasanya hannu

bisa lebensa yana fadin shishshi kidaina

kuka ma'u badukanki zanyiba nadauko ne

domin kidakeni kirama dukan danayimiki

yanzu nagano illar abinda na aikata Amshi

kirama ma'u yamike mata belt din

mamaki yacikata tafara ja dabaya domin

bata yarda domin batayarda harzuciyarshi

abinda yake nufiba kenan tafi yarda

yanayin hakan ne domin yasami damar

kamata kawai ganin tanaja dabaya yasanya

yacabko hannunta gam cikin nasa saitafasa

kara jikinta narawa yadamkata belt din

yana fadin dagaske nake ma'u badukanki

zanyiba kirama dukanda nayimaki indai

har zakidaina yunkuri gudowa kibarni

ma'u kalamansa suka sata yin sororo tana

kallonsa rike da belt ahannunta duk da

karamcin shekarunta maganar yayan nata

tagirgizata yasakarmata hannu da belt

yajuya yazauna akan kujera yana

maicigaba da kallonta ki dakeni ma'u

kirama don Allah gani nazauna yanda zaki

iya dukan nawa bana fatan kikara yunkurin

gudowa idan kika gudu nashiga ukku

bansan indazan sanya rayuwataba

kobakisan Raliya ma guduwa tayi tabarni

da aure naba? Tadan zare ido tana

mamakin jin abinda yace tadaure tace

dagaske Raliya tagudu? Itama dukanta kayi

tagudu yaya?yanda tayi tambayar abin

yaso yabashi dariya amman yadake yace

bandaketaba kinsan halin Raliya ban isama

natabataba balle duka banso kema kigudu

idan kika gudu kowa bazai yafeminba

harda INNATA MAISONA Kirama don

natabbatar kinhuce kinji ma'u Tayi

murmushi zuwa yanzu hankalinta yadan

kwanta ta isa gabansa tadurkusa

tamikamasa belt din tanafadin yaya bazan

iya dukankaba nasan nice nayi laifin ma

kayi hakuri bazan karaba ranshi yayi haske

yace shikenan nahakura amman kimin

alkawarin bazaki kara yunkuri guduwa

kibarniba Allah bazan karaba nadaina

bazanyimaka irin abinda raliya tayimakaba

Alkawari abune maigirma ma'u kiyi

kokarin rikeshi tadaga kai alamar to tana

murmushi ya mike tsaye shikenan kinhuce

yanzu mikikeson nadafamiki kici ki kwanta

ta turo baki gaba da shagwaba yaya kaine

kace nadinga yin abu irin na matan aure

amman kakibari nakoyi girki daman umma

ma batakoya miniba saitace jagwalgwalo

nakeyi kuma ai matan aure sune sukeyin

girkinsu dakansu nagani yayi murmushi

ma'u ko buhun shiririta yakamo hannuta....



25 April 2015 at 08:47 · Public

Like Page · Save · More

Like

React

Comment

Share

Like7

Write a comment...



·

Maryam Balarabe

nyc stry wlh

Like · React · Reply · More · 25 Apr 2015

Jamilubello Bello

Nxt pls

Like · React · Reply · More · 25 Apr 2015

Tajudeen Aminullah Abubakar

Tnx

1 · Like · React · Reply · More · 25 Apr 2015

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

DAME AKE ADO part 12.

2ã DAME AKE ADO 3 Zanfara koya miki girki dagayau amman bazaki fatara yin girkiba harsai kin iya sosai eh nayarda saranda na iya zanyi bazan kara sabamakaba tafada cikin hanzari shikenan muje kicin din mezamu dafa yanzu tanabiye dashi saida suka nufi kicin din tace danmalele da wainar fulawa Mai manja wannan duk abinci bane kayan kwadayine kuma ni ban iyasuba yanzu dare yayi indomie zamudafa da Albasa muci yabata Amsa Ai itama tanadadi yaya amma ni na iya itabafa sai ansanya awutaba idan akasanyata aruwa tadade saikaga tayi laushi sai aci yakalleta dasauri da mamaki yace waye yace miki haka akedafa indomie ma'u tasami kujera tazauna tana dariya ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace amakaranta bording haka mukeyi tunda ba abarinmu mukunna risho kuma akicin ma ba abarinmu sai siniyoyi kawai suke bari tobahaka akeyi bari yanzu nakoyamiki yanda akeyi yafara kokarin bude indomie din yana zubawa acikin tukunya yadauko albasa ya yanka yazuba akai haka rayuwarsu taci gabada gudana kullum ma'u saikara girma take halittun jikinta nakara bayyana shikuma Ahmad sonta da sha'awarta nakara karuwa acikin ransa saidai tsananin tausayinta yahanashi aikata komai akanta hasalima kogado daya baibari sunkwanta da itaba itatana gado shiyana kasa akan leda dafilo yawurgar haka ake baccin kullum tasaki jikinta da gidan domin yabar yaran suna shigomata sutayata hira suyita wasansu irin na yara sannan yana koyarda ita girki hartasoma iyawa saidai abinda yake damunta baiwuce rashin zuwan Ummanta gidan ba gashi tayi kusan wattanni goma sha ukku kuma shi yayan nata yakibarinta taje bayanshi kullum saiyaje yanata lallabata dai akan tayi hakuri yau tunsafe yafice aiki yabata damar tadafa shikafa da miya domin ta iya yanzu amman kadatabari kowane yaro yafara shigarmata kichin zuwa yanzu ma natsuwa tafara shigarta duk wannan shiriritar ta YAR AUTA tafara dainawa ta iya gyara gidanta tsaf kamar bashiba tashare tagoge ko ina girki ma indai bamai wahala bane tana kokarin yinsa iyakacinta dayaran aike kawai kosuyimata wanke wanke dashara wajen karfe bakwai yashigo gidan abunda yabashi mamaki baiwuce yin horn dayayi sama da sau ukku amman ma'u batazo tazo tabudemasa gidanba domin dayayi horn daya biyu ana ukkun zata fallo koyajiyo muryanta tana fadin yaya inazuwa amman yau yayi yafi sau shidda amman baijiyo matsinta ba saiya matsa jikin kofar gidan sosai yatura da hannunsa saiyaji kofar tabude yashigar da mashin dinsa yasami guri ya ajiyeshi ga mamakinsa saiyaga gidan kaca kaca babu gyara kamar yanda yasaba gani Ransa yabaci dayajiyo karar talabijin da alama kallone yadauke mata hankali tamanta da gyara harda budemasa kofarma yayi nufin shiga dakin yajiyo kauri daga kicin danhaka yanufi kicin din dasauri shinkaface akan risho takama harta kusa konewa gaba daya miyar kuma gatacan gefe marfi yabude hangam takaici yakara kamashi me ma'u keyine nashiririta yau agidan? Yasauke shinkafar yakashe risho dasauri sannan yanufi dan falon nasu kobai daki ma'u ba zatasha fada yadaga labulen yana kwalla mata kira ga mamakinsa saiyaga babu kawa dakin sai TV dakefaman babatu itadaya daga sannan hankalinsa yafara tashi da wutar nepa babu ma'u gaban Tv tana kallo lallai akwai matsala MEKEFARUWANE? saiya saki labule dasauri yanufi dakin gado yanacigaba dakiran sunanta ma'u ma'u yadaga labule yanaware ido kozaihangota amman babu ita acikin dakin babu alamunta hantar cikinsa takada afili yace na shiga ukku ina ma'u tashigane ma'u yasake kwalamata kira dakarfi saiyaji kamar sheshshekar kukan mutum abayan gado yashiga cikin dakin dasauri yana cigaba da kiranta gamamakinsa saiya hangota rakube bayan gado ta tattare jikinta kamar wacce akasanya zama ahaka dole mamaki yabaiyana akan fuskarsa ganin yanda take ta hada gumi idonta yayi jajir alamar tayi kuka takoshi sai ajiyar zuciya take ya isa gabanta yana tanbamyarta ma'u lfy meyafaru meyasameki? Saikawai takara fashewa da kuka tanaja dabaya tanafadin don Allah yaya Ahmad kada kadakeni kaine kace bazaka kara dukanaba kome nayi maka narantse da Allah banyi iskanci dakowaba banyi abinda Raliya tayi da sisco ba kakawo kur'ani nadafa mamaki yakara kamashi datsoro ganin yanakara nufarta tana karaja baya jikin lungu yadan dakata da kwantarda hankali yace tsaya ma'u gayamin meya faru bazan dakekina nako rantse da Allah kome kikayi bazan dakekiba kobakisan kingirmaba yanzu ko umma bazata dakekiba balleni gayamin meyafaru? Cikin sheshshekar kuka tana kara tsatstsare jikinta tana kudundunewa tace Amman dai kasan niba yar iskabace ko yaya yadaga kai cikin rawar jiki nasani ma'una salihace ba yar iska bace ba meyafaru wanine yashigo gidan yayi miki fyade ne ma'u kigayamini zan iya zandaukan dukan abinda yafaru akanki nasan kaddara ce kaji harkafara fada tun bangayamaka ba wlh banyi iskanci dakowaba yaya banyi komaiba yafara fusata haba ma'u kisanarda ni meyafaru kigayamini meye menene cikin karaji da ihu yayi maganar maimakon tadawo natsuwarta saima takara gigicewa kamar zatashiga cikin gadon tafashe da kuka maikarfi jikinsa yayi sanyi yagamo yatafka wauta yadubeta yace ok calm down ma'u yi hakuri gayamin tell me menene ? Ganin batada niyyar magana yasanya yafaki numfashinta ya cafke hannunata yadaga cak saita kara fashewa da kuka da ihu takankame jikinta kamar zata suma fadi take wlh banyi iskanci dakowaba yaya narantse da Allah gabansa yadinga faduwa ganin jini guda guda ajikin zaninta da gurin gabadaya hankalinsa yatashi kwarai da gaske takasa cigaba dakuka cikin karaji yace

7 / 47