Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   40 / 47

117K to 120K   out of 139.6K words

ba sai yau."

"Sai da suka yi 'yar rigima kafin ya yarda ya zauna a kusa da shi, cewa yayi dole sai dai ta koma baya, ita"

kuma tace bata yarda ba ai shi ba direbanta bane.

"Hankalinta ya kai kan wani hoto dake sakale a jikin madubin dake cikin motar yana dan lilo, bayan sun"

"shiga. Dan karami ne hoton an sanya shi cikin wata 'yar kwalba tana lilo. 'Ya'yansa ne a jiki sun yi kyau dukkansu a tsaye suke. Rike da kugu Sayyada kenan, an raba mata gashinta gida biyu, hajiya tana gefe ita ma taci kwalliya ga malam a tsakiyarsu shi ma cikin kananun kaya har da hular sojoji akan sa, yaran"

sun yi matukar kyau a hoton.

"Nana ta kalle shi DA sauri sanda ya tada motar suka nufi fita daga kamfanin tace ""wadannan yaran fa"

"ahmad?"" Ya kalli hoton yayi murmushi, daidai lokacin DA suka fita daga cikin kamfanin yace ""yarana ne"""

Yaranka? Nana ta tambaya da mamaki. Iyakacin ganin da take wa ahmad da saninsa bata taba zaton

"yana da aure ba ma balle har da yara uku. Mamakinta ya kasa boyuwa har ya gane yace ""sun yi kadan ko?"

"Da sauri tace ""yara ukun ne sun yi kadan? Ban taba zaton kana da aure ba ma balle yara, don baka yi"

"kama da mai aure ba sam"""

"Yayi dariya da jin dadi yace ""akwai wani da yake nuna mutum yana da aure ko bai da shi daman?"

"Ta kwanta jikin kujerar motar jikinta yayi dan sanyi tace ""no, ba haka ba ne. Amma wani lokacin zaka ga"

"masu aure kamar suna cikin damuwa DA matsala ne, amman kai ban tana ganin ko daya tattare da kai ba"""

"Ya sha kwana yana murmushi yace ""dukkan mai halin da kika ganshi cikin irin halin da kika bayyana to ya"

"jahilci auren ko sam bai yi sa'a da mace ya gari ba, ni kam ina alfahari da matata, duk da kasancewar Ma'u yarinya ce amma bata rage ni da komai ba, ina samun dukkan abun DA nake bukata daga gurinta, bani da damuwa ko matsala sam cikin aurena"""

"Tayi shiru tana tunani har sai da ya kalle ta yace ""yaya dai hajiya, ban san inda muka dosa ba fa"" tayi"

"ajiyar zuciya ""kana so dai muyi rigima da kai in dai baka daina ce min hajiyar nan ba, ka Kai ni shoprite ina so zan yi siyayya"" duk da hankalinsa yana gun zuwa gida amma ba zai ki yin abun da nana ta sanya"

"shi ba, ya juya kan motarshi suka wuce can. Suna tafiya suna yin hira jefi-jefi tana tambayarshi yaran"

nasa. Abin da yafi komai yi mada dadi kenan don haka ya saki jiki suka dinga hirarsu har suka isa shoprite din.

"Irin siyayyar da nana ta dinga yi ta baiwa ahmad mamaki kwarai, yarinyar bata jin kudi, hankalinsa bai"

"tashi ba sai da aka je biyan kudi ya gama rikicewa, siyayyar ba wata mai yawa bace amma sai makudan"

"kudi, babu wani ko dar ta fito da ATM card dinta ta mika aka sanya cikin P.O.S. aka fara diban kudin har aka gama aka ciro mata ATM card dinta aka mika mata."

"Ta kalli Ahmad tace ""Ina ta rokomka ka dauku wani Abu ka ki ko? Ina fatan zaka amshi agogon da na siya"

"maka?"" Yayi murmushi bai ce komai ba suka nufi hanyar fita, masu daukar kaya na biye da su da manyan jakankuna."

Bai gama tsinkewa da lamarin alhaji nura kwangila da iyalansa ba sai da ya isa gidansa. Ya san alhaji nura

"kwangila yana da kudi, amma bai yi tsammanin ya mallaki gida kamar wannan cikin GRA unguwar masu kudi haka ba. Sai da suka yi doguwar tafiya sannan suka iso ainahin gidan. Motarsa tana tsayuwa"

ma'aikata kamar guda uku suka fito daga cikin gidan mata don Nana tayi musu waya dama.

"Ahmad ya bude motar da sauri ya fice ya bude bayan motar ya fara fito da kayan. Nana tace""tsaya ai ba"

"duka ne kayana ba"""

Ta dauki leda guda uku ta mikawa masu aikin sannan ledojin wajen guda hudu cikin motar suka rage a

"cikin but din motar. Ahmad ya kalleta da sauri cikin mamaki yace""wadannan kuma fa?"""

"Tayi murmushi ""na yarana ne, leda biyu na takwarata Sayyada, daya na malam daya na Hajiya.""kafin yayi"

"magana ta fito da agogo cikin jakarta tace ""wannan kuma na baban yaran ne"""

"Ya kura mata ido da mamaki, domin ya ga yawan kudin da ta sayi agogon."

"Ya kada kai yace ""Nana wannan bai dace da ni ba, yafi dacewa da mutane masu kudi, ki barshi na gode"

"zan kaiwa yaran naki..."""

"Ta bata fuska kwarai da gaske. ""Bana son nayiwa mutum kyauta ya ki karba, shine abinda yafi bata min"

"rai. Kafi karfin komai a gurina Ahmad, kuma ba rokona kayi ba."""

"Ya mika hannu ya amsa ganin yadda ranta ya baci yace ""na gode ALLAH ya saka da alheri, bari na wuce"

"naga magariba ta kawo jiki"""

"Ya juya ya nufi motarsa. Ita kuma ta wuce cikin gidan da sauri tana murmushi, duk da akwai faduwar"

gaba a tattare da ita.

***

"Ahmad yana isa unguwarsu aka fara kiran sallar magriba, don haka ya tsaya a wani masallaci yayi sallah"

sannan ya karasa gida.

Ma'u tana falo tayi wanka tayi kwalliya cikin wata atamfa da tayiwa dinkin doguwar riga amman ya kama

jikinta daurin ma ya kama jikinta.

"Ma'u ba tayi ilimi mai zurfi ba sannan bata yi mu'amala da mutane ba, amman yawan karance-karance"

"da kallo ya sanya ta waye da yawa, babu irin littafin da bata karantawa daga Hausa har zuwa novels na turanci."

"Sannan tana kokarin tafiya da zamani, musamman yanzu da mijinta ya samu rufin asiri, shima da yake"

ma'abocin siyo mata dukkan wani abu na bukata da zai amshi jikinta ko ya burge shi ne.

"Ya shigo da sallama dauke da kaya a hannunsa, ta dora kafa daya kan daya ta amsa ba tare da ta kalle shi"

ba. Ya isa gabanta ya ajiye kayan sannan ya kama Kunnuwansa irin yanda yara suke yi idan sun yi laifi. Ta

"kalle shi dariya ta kubce mata ta sanya hannu ta tureshi ya fadi da bayansa ya kwanta, amman sai da ya janyota da hannunsa ta fada kansa ta fara kokarin kwacewa."

"""Ka sake ni ka iya yiwa mutum laifi sannan ka komo kana yi masa wayo. Yanzu ka tafi ofis tun safe sai"

"Yanzu ka dawo bayan ranar da ya dace ka zauna tare da nice."""

"""Kin san ba zan yi dukkan abunda zai bata miki rai da gangan ba ma'u, aiki ne ya rike ni kiyi hakuri, kin"

"hakura?"""

"Ta kwanta kawai a kirjinsa tace ""Ina son na hakura amman bana son baka damar maimaita irin hakan"

"nan gaba"""

"""Na zan kara ba, kin yarda?"

"Ta daga kai alamar eh, har lokacin tana kwance a jikinsa. ""Wai me ka siyo ne?"

"Ta zame daga jikinsa ta mike ta nufi ledojin, gabansa ya fara faduwa ya mike zaune da sauri, don bai san"

"me zai biyo bayan ganin da zatayi ba, sai dai ya kudurce a ransa zai yi mata karya yau sau daya, don neman zaman lafiya a gidansa."

"Ta fara duba kayan, da farko ta dan fara murna, sai da ta nutsa cikin kallon kayan mamaki ya fara"

"bayyana akan fuskarta, domin kowanne akwai kudinshi a jikinshi, a ranta tana lissafin kudaden sai ta fara sakin baki."

"""Yaya ina ka samu kudin siyan wadannan kaya masu yawa haka?"""

"Gabansa ya kara faduwa ya isa gabanta da sauri yana yake yace ""Wai kina nufin bani da kudin da zan iya"

"siyan wadannan kayan?"""

"Ta kalle shi da mamaki tace ""Yaya an sauya ma albashi ne ko kuma wata sana'ar ka samu, don a yanda"

"naga kudin nan na jikin rigunan nan sun fi karfin albashinka na wata uku ma"""

"Yayi yake yace ""Nana ce ta siya musu fa..."""

Bai san sanda bakinsa ya furta wannan kalmat ba.

"Ma'u ta kalle shi da tarin fargaba, daidai lokacin da ta janye hannunta daga kan kayan bakinta na rawa,"

wani irin tashin hankali ya dinga shigarta.

"Ya kula da yanayin da ta shiga, amma ya dake yana son basar da bacin ran nata yace ""ni kaina nayi"

"mamakin siyayyar da ta bada, daga ganin hotunan yara jikin mota suka bata sha'awa sai ga siyayya wai tasu ce'"

Ma'u ta mike tsam daga gurin kayan bata kuma cewa komai ba nufi hanyar dakin baccinta. Ya bita da

kallo da mamaki kafin ya fara kiran sunanta.

"""Ma'u! Ma'u!! Meye haka, meke faruwa ne?"""

"Ya isa da sauri ya sha gabanta da tsananin mamaki yana fadin ""wai meye haka ne ma'u, kayan ne ya bata"

"miki rai? To kin ga dakata bana son damuwarki sai na dauki kayanta na mai da mata faqat!"""

"Ta ja ta tsaya. ""Aikin banza kenan, kuma ta baya ta rago! Meye kuma matsayinta a gurinka ka jima kana"

"raina min hankali akan wannan matar yaya, yau dai ALLAH ya toni asirinka, ko baka san naji lokacin da"

"tayi ma waya tunda safe bane, ka fita gurinta kuka yi ta yawo har wannan lokacin sannan ka dawo ka gaya min maganar banza... Na gaji da wannan yaudarar taka, na gaji..."""

"Ta fashe da kuka, hankalin Ahmad ya tashi ransa ya baci, ya kalleta da muzurai yana fadin ""ni nake"

"yaudarar ki ma'u me zan boye miki? WALLAHI babu wani abu tsakanina da Nana, kalle ni da kyau ban yi kama da mai karya ba"""

"Bata ce komai ba ta fara kokarin tafiya, amman bai bata damar hakan ba, ya riko hannunta ya rike gam"

"da karfi, tayi kokarin kwacewa amma ta kasa ko motsawa. Cikin kuka ta cigaba da magana ""ka sake ni ba zan yarda da duk abinda zaka ce ba yaya"""

"Ya janyota jikinsa ya matse ta tsam tankar zata koma cikinsa tana cigaba da kuka da cewar ya saketa,"

amman ya ki matsawa duk da dukan da take kai masa bai ji ko dar ba. Sai da ya tabbatar ta sare ba zata

"iya kwacewa ba sannan yace ""ma'u ki yarda da ni, babu kowa a cikin raina bayan ke, kece zabin iyayena kece kuma abar sona"" ya dinga surutai da ban hakuri"""

"Ta fara rage kukan don yanayinsa da yanda kalamansa me fitowa ya fara kashe mata jiki, ya sanya"

"harshe ya fara lashe hawayenta dake zuba ya sassauta rikon da yayi mata ta daddage ta ture shi tana dariya saboda cakulkuli da yake mata, ya fadi wanwar a kasa ya dafe keya ta fashe da dariya, shi kam dadi ya ji don ya kula ta fara saukowa, ta juya ta nufi cikin dakin bacci."

"Dukkan abunda ta ajiye masa wanda ta girka sai da ya cinye, kasancewar bai ci komai ba tunda ya fita"

"bayan dan kunu da cincin a ofis, kasancewar Nana ba mai cin abinci bace sosai shiyasa bata damuwa ko ta wuni bata ci abinci ba."

"Wannan ya sanya zuciyar ta dan ji sanyi, ta kara yarda mijin nata ba shan ice cream suka fita ba."

Shi kam kallonta kawai yake yi tana ta wani kwarkwasa jikinta ya kara cika da kyau kasancewar tayi yaye

"cikin satin, sha'awar matarsa da begenta sun cikashi."

***

Sanda ya fito daga wanka sai ya tadda ta sanye da sabuwar shiga cikin kayan bacci wadanda ya san tayi

ne don tsokana.

"Komai na ma'u burge shi yake yi, sai dai a ransa yana mamakin irin wayewar ma'u da yanda ta iya tsara"

"kwalliya. Kodayake yasan tana yawan kalle-kalle da karance-karance, wata kila ta hakan take kara samun wayewa."

"Ganin irin kallon da take yi masa ya sanye ya nufe ta kai tsaye da dariyar mugunta, tana hango shi ta"

"tashi ta zura da gudu tana dariya, ya rufa mata baya da yake ba ta da wani jiki ta iya gudu kamar 'yar barewa, don haka ya kasa cimmata sai da ta nufi kicin ya sanya kafa ya sharbe ta, saura kiris ta zube kasa amma ya tare ta, ta fara mai da numfashi da tsoro tana fadin ""amma yaya baka da kirki da na fadi fa?"""

"""Ba ma zaki fadi ba"" ya bata amsa kafin ya fara aika mata wasu sakwanni da suka fara rikita mata lissafi."

"Ahmad namiji ne da ya iya mallake dukkan zuciyar mace, musamman da yake kakkarfa mai kirar zaki."

Dakyar ma'u ta lallaba shi suka nufi daki don taga karatun nasa ya fara wuce saninta.

"Cak ya dauke ta tamkar wata 'yar tsana, sai da ya tabbatar ya wanke mata zuciya fes ta ta yarda babu"

wata mace a cikin ransa bayan ita.

Daren wannan rana sai ya zamto musu kamar daren amarcin da ba zai gogu a cikin rayuwarsu ba.

***

"Ga Ahmad yana yin iyaka kokarinsa wajen ganin bai kara yin wani abu da ya shafi Nana a gaban ma'u ba,"

ko sunanta bai iya ambata balle wani abu da ya shafe ta.

"Yana kallon kayan da ta baiwa yaran ma'u bata taba sanya musu shi ba, ta ma ajiye su guri dabam,"

"amma bai taba nuna damuwarsa ba don bai son rikici, sai da ita da kanta taga dacewar ta sanya musu din ta saka musu da kanta."

"A ranshi ya yaba da kayan, amman bai iya fitowa ba don ganin irin kallon da take masa na tuhuma, sai ya"

"bar abin a cikin ransa ya nuna kamar bai gane kayan ba ma, hakan ya dan sassauta mata damuwarta."

*

*

*

Hm kishi kenan kumallon mata

DA ME AKE ADO?

47

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Ranar wata lahadi ta farkon wata lokacin Ahmad aljihunsa akwai nauyi, ya tattara iyalanshi da matarshi"

"don fita yin siyayya a kanti. Yaran suna cikin kwalliya gwanin sha'awa kamar 'ya'yan turawa. Yayin da mahaifiyarsu ke sanye da atamfa ta amshi jikinta riga da siket, gyalen da kayan kamar tare suka zo. Haka nan takalmi da jakar hannunta, idan baka sani ba ba zaka yi zaton ma'u uwar yaran bace, don bata yi"

kama DA wacce ta haihu ba sam.

"Sun siyo abubuwan da suke bukata, masu tsaron gurin suka rako su aka zuba a mota, suna shirin shiga"

"mota suka jiyo muryar mace daga can bayansu yana fadin ""Ahmad"" gaba dayansu su daga kansu ga kinda sunan yake fitowa. Muryar nan ba bakuwa bace a gurinsu, ko bayan shekaru dari suka ji ta sai sun"

"gane ta, mamaki ya kama su gaba daya."

"Ummi ce tsohuwar budurwar Ahmad, bata cikin kazamar shiga amma babu alamun jin dadi a tattare da"

"ita, kayan dake jikinta sun nuna haka."

"Ta karasa kusa da su da farin ciki tana fadin ""Ahmad kayi mamakin ganina ko?"""

"Yayi saurin wayancewa tana kallon ma'u don ta hade rai nan da nan yace ""ban yi zaton ganinki ba ma, ya"

"kike?"""

"Da sauri tace ""lafiya lau Ahmad, shikenan sai ka buya'"

"Ta kalli yaran dake gabansa tace ""Woo! Wadannan kyawawan yaran fa?"""

"Cikin sauri yace ""yarana ne"""

"Mamaki ya kama ta tace ""yaranka fa kace? Yanzu har kayi aure ka haifi wadannan yaran lallai ka cika mai"

"sa'a"""

"Ta kalli ma'u tana kokarin tunota. ""Wai wannan ba ma'u ba ce ba?"""

"Ma'u ta dan yi yake amman ta kasa magana Ahmad ne yace ""ita ce mahaifiyar wadannan yaran da kika"

"gani"""

"Ummi ta dan ja da baya da fargaba da mamaki tana fadin ""wai kana nufin ma'u ka aura Ahmad? Ma'u"

"kece matar Ahmad?"""

"Ma'u tayi murmushi ""WALLAHI kuwa, haka ALLAH ya kaddara. Yaya mu wuce ko?"" Tana kallonshi take"

"magana, don ganin irin yanda fuskarsa take."

"Bai ko kalli inda Ummin take ba yace ""OK sai an jima Ummi."""

"Ya suri malam suka nufi motarsu, Ummi ta bisu da kallo da tsananin mamaki ta kasa furta komai. Ahmad"

ne ya zama haka?

Wani irin sonshi da sha'awarshi suka bijiro mata. Da tuni itace mai wadannan kyawawan yaran. Gaskiya

mahaifanta sun cuce ta. Sai hawaye ya fara biyo kuncinta.

"Tana tsaye tana kallonsu har suka ta da mortar suka yi nisa. Sai ta ji ta fasa siyan hodar da ta zo siya, ta"

"juya da sauri tana tsai da adaidaita sahu, daman ta zo siyan hoda da kuma rage yamma ne kamar yanda 'yan mata da zawarawa keyi."

***

Ga ma'u kam hade rai tayi katamau zuciyarta kawai ke tafasa. Irin kallon da Ummi ta rinka yiwa Ahmad

ne ke bijiro mata.

"Wai Ummi tana da aure ne ma ko bata da shi? Ko tana da aure ko bata da shi ba damuwarta bane,"

"damuwarta daya kallon da Ummi ke yiwa mijinta kamar zata lashe shi danye. Ma'u tana tsananin kishin mijinta, bata son kowacce mace ta ko kalle shi ma."

"Ahmad ya kula da halin da ma'u ta shiga, ko kadan baya ganin laifinta akan kishin da take yi, sai ma jin"

"dadi da hakan ke sanya shi, don burinshi a duniya bai wuce ace matarshi na matukar kaunarshi ba, irin abunda ya so samu kenan ga Ummi kasancewar tana tsananin son shi, ashe ba ita ce matarshi ba."

"Ya sanya hannu ya zunguro ma'u daidai inda ke sanyata dariya, ta noke amma taki dariya sai ma cewa"

"tayi ""don ALLAH yaya ka bari"""

"Yace ""na ki na bari sai kin bani labarin da kika ce zaki bani na Amina"""

"Ma'u ta dan yi yake tana fadin ""Yanzu kuma na fasa sai wani lokacin, bana jin dadi"""

"Dariya taso kwace masa amman ya dake yace ""yarinya waye ko yake jin dadi a wannan lokacin?"""

"Haka ya dinga janta da Hira tana basarwa har suka isa gida, shi kuma bai nuna mata ya damu ba sam."

Sai da aka yi kwanaki biyu babu wata magana ko wani abu da ya shafi Ummi da ya fito daga bakin mijinta

"sannan hankalin ma'u ya kwanta, ta tabbatar lallai mijinta ya manta da rayuwar Ummi gaba daya."

***

"Ga Ahmad ba haka abun yake ba, tunda yaga Ummi yake tunanin rayuwarsu ta baya, idan yace baya son"

Ummi a zahiri yayi karya.

"Yau yana zaune a ofis ayyuka sun sha gabansa, wayarsa tayi kara. Ya duba yaga bakuwar lamba ce kamar"

"bai zai dauka ba, haka ya daure dai ya dauka. Yana dagawa yaji an ce ""Ahmad"" sai yayi saroro da mamaki saboda jin muryar Ummi da duk rintsi duk tsawon shekaru ba zata bace masa ba. Da mamaki yace ""Ummi ina kika samu lambar wayata?"""

"Ummi tayi yake tace ""Ai mai son dan tsuntsu shi yake binsa da jifa. To kafin komai dai ya kake ya aiki ya"

"yaranaka?"""

"Ya jingina da kujera yace ""duk suna lafiya. Hajiya da sayyada suna school, malam kuma yana tare da"

"ummansa a gida"". Tayi doguwar ajiyar zuciya tana yake kamar tana gabansa tace ""Ahmad da ma'u 'yan gata, domin kowa ya samu sa'a da iyaye irin naku ya more"""

"Ya bata fuska don ya soma gano inda ta dosa yace ""haka ne ko?."

"Tace ""babu tantama, ba zan ja ka da nisa ba Ahmad na jiyo dukkan abunda ya faru da rayuwarka bayan"

"rabuwarmu da kai, da yake har gobe kaine zabina, sai dai na jima

40 / 47