Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 47

81K to 84K   out of 139.6K words

""A'a na manta kayi hakuri yaya,"

"ba zan kuma fadin haka ba"""

"Jikinshi yayi lakwas, gaba daya sai abincin ya fita daga ranshi, yayi shiru tsawon lokaci kafin ya yunkura"

"ya mike tsaye, ta bushi da kallo tana fadin ""yaya har ka koshi kenan? Cabdijan WALLAHI sai ma cinye ta duka, ni daman yunwa nake ji ban ci komai ba tum da rana"""

Bai ce komai ba ya fice. Kai tsaye dak in baccinsu ya nufa ya haye gado yayi rigingine ya kurawa silin ido

yana kallo. Tattaunawarsu da ma'u ta dinga dawo masa daki-daki. Shin ko akwai wanda ma'u take so ba shi ba? Ko kuma dan yayar umma (shu'aibu) shine a cikin ranta?

"Ya mike zaune da sauri domin jin wani abu ya soki makoshinsa, ya dafe kansa kamar ya fasa ihu. Yaushe"

"damuwa zata bar shi ya huta ne? Tabbas ummi ce abar son sa, amman tun randa aka daura aurensa da ma'u haji gaba daya hankalinsa da rayuwarsa ya koma kanta."

Ya san ma'u yarinya ce amman yana fatan samun kwanciyar hankali a gurinta wata rana. Sai dai yau

"maganganunta sun daga mass hankali. Yana tsoron kada wata rana a wayi gari ita ma tace bata son shi. Ba ta kaunarshi, da kuwa ya shiga ukunshi."

"Ihun ma'u ya farkar da shi daga tunanin da ya luluka, ya mike tsaye a firgice ya nufi falon yana tambayar"

"abinda ya faru. Ganinta yayi a tsaye tana tsalle. ""Yaya Ahmad ba ka ga wutar NEPA ba? Ai ba manta kwan dakin ya mutu zan ci gaba da kallon debate din 'yan makarantarmu yanzu"""

"Yayi ajiyar zuciya ya bita da kallo tana ta kokarin jogana kayan kallon, kamar ya koma sai kuma ya ga yafi"

"dacewa ya zauna yayi kallon, wata kila ya dan samu sauki a cikin ranshi, don haka ya isa ya zauna har ta kammala jonawa, sai dai har suka kwashe awa guda babu wani abu da gidan talabijin din na N.T.A ke"

"sakowa bayan talla da labarai, har ta fara zobaro baki gaba tana mita."

"Yayi murmushi yace ""kin ga ma'u daman ba kullum ake yi ba, sanya mana receiver ki kunna mana MBC"

ACTION muyi kallo.

"""Gaskiya yaya sai dai mu ga ZEE AFLAM"""

"""Na ji kunna mana ZEE AFLAM din mu gani' ya fadi yana dariya don ya kula ta cika. Ta kunna daidai"

"lokacin da suke wani fin, suka yi shiru suna kallo."

Ma'u da kanta tace fim din ba shi DA kyau. Ta sauya zuwa MBC ACTION a hankali wani fim ya fara fitowa

"THE DIRTY TEACHER, kasancewar ma'u na jin turanci ya sanya fim din ya shiga burge ta, sai dai ga Ahmad wani irin abu ya dinga ji a jikinsa yana yawo. Hankalinsa ya fara kasuwa gida biyu, ya dinga satar kallon ma'u babu wani abu a jikinta da zai iya gamsar da shi, sakar da azuciyarsa ta fara yi masa dama ummi ce"

"matarshida tayi masa abinda yake so a yanzu, ya mike da nufin ya bar gurin."

"Ma'u ta kwalla masa kira. ""Don ALLAH yaya ka tsaya mu gama gani mana, ni wannan shegiyar malamar"

"ta babu haushi haka kawai ya raba masoya, ta kuma koya nasa iskanci, shikenan yanzu ya zama dan iska"""

"Bai kula ta ba ya fice yana fadin ""ina zuwa ma'u"" ta cigaba da kallon ko a jikinta."

"Haka rayuwar tasu ta ci gaba da gudanuwa, kullum ma'u sai kara girma take halittun jikinta na kara"

bayyana.

Shi kuma Ahmad sonta da sha'awarta na kara karuwa cikin ransa. Sai dai tsananin tausayinta ya hana shi

"aikata komai a kanta, hasalima ko gado daya bai bari su kwanta da ita ba. Ita tana gado shi yana kasa kan leda da filo ya wurgar haka ake baccin kullum."

"Ta saki jikinta da gidan domin ya bar yaran suna shigo mata su taya ta hira, su yi ya wasansu irin na yara."

"Sannan yana koyar da ita girki har ta soma iyawa. Sai dai abinda yake damun ta bai wuce rashin zuwan umma gidan ba. Gashi tayi kusan watanni goma sha uku, kuma shi yayan nata ya ki barinta taje, bayan shi kullum sai yaje, yana lallabata dai akan ta yi hakuri."

*

*

*

Zaman aure kenan ma'u mai raba uwa da diyarta na tsawon lokaci.

DA ME AKE ADO?

29

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Yau tun safe ya fice aiki ya bata damar ta dafa shinkafa da miya, domin ta iya yanzu, amman kada ta bari"

kowanne yaro ya fara shigar mata kicin.

"Zuwa yanzu ma nutsuwa ta fara shigar ta, duk wannan shiriritar ta 'yar auta ta fara dainawa, ta iya gyara"

"gidanta tsaf kamar ba shi ba. Ta share ta goge ko ina, girma in dai ba mai wahala bane tana kokarin yinsa, iyakacinta da yaran aike kawai, ko su yi mata wanke-wanke da shara."

"Wajen karfe bakwai ya iso gidan, abunda ya bashi mamaki bai wuce yin horn da yayi sama da sau uku"

"amman ma'u bata zo ta bude masa gidan ba, domin da yayi horn daya biyu a na ukun zata fallo ko ya jiyo muryarta tana fadin ""yaya ina zuwa"""

"Amman yau yayi yafi sau shida bai jiyo motsinta ba, sai ya matsa jikin kofar gidan sosai ya tura da"

"hannunsa sai yaji kofar ta bude, ya shigar da mashin din ya sami guri ya ajiye shi, ga mamakinsa sai yaga gidan kaca-kaca babu gyara kamar yadda ya saba gani."

"Ransa ya dan baci da ya jiyo karara talabijin, da alama kallo ne ya dauke mata hankali, ta manta da gyara"

har da bude masa kofar ma.

"Yayi nufin isa dakin ya jiyo kauri daga kicin, don haka ya nufi kicin din da sauri, shinkafa ce akan risho ta"

"kama har ta kusa konewa gaba daya, miyar kuma gata can gefe murfin a bude hangam."

"Takaici ya kara kama shi, me ma'u ke yi yau na shiririta ne a gidan? Ya sauke shinkafar ya kashe rishon ya"

"nufi dan falon nasu, ko bai daki ma'un ba zata sha fada."

"Ya daga labulen yana kwalla mata kira, ga mamakinsa sai ya ga babu kowa cikin dakin sai TV dake ta"

"faman babatu ita daya, daga sannan hankalinsa ya fara tashi, da wutar nepa babu ma'u a gaban TV tana kallo, lallai akwai matsala."

Me ke faruwa ne?

"Sai ya saki labulen da sauri ya nufi dakin gado yana ci gaba da kiran sunanta. ""Ma'u! Ma'u!! "" ya daga"

"labulen yana wara ido ko zai hango ta, amman babu ita ma acikin dakin babu alamunta. Hantar cikinsa ta kada, a fili yace ""na shiga uku, ina ma'u ta shiga ne? """

"""Ma'u!!!"" Ya sake kwalla mata kira da karfi. Sai ya jiyo kamar shisshikar kukan mutum daga bayan gado."

Ya shiga cikin dakin da sauri yana ci gaba da kiranta. Ga mamakinsa sai ya hango ta rakube a bayan gado ta tattare jikinta kamar wacce aka sanya a haka dole.

"Mamaki ya bayyana akan fuskarsa ganin yadda take ta hada gumi idanta jajur alamun taci kuka ta koshi,"

sai ajiyar zuciya da shisshikar kuka take ta yi.

"Ya isa gabanta yana tambayarta ""ma'u lafiya, me ya faru, me ya same ki?"" Sai kawai ta kara fashewa da"

"kuka tana ja da baya tana fadin ""don ALLAH yaya Ahmad kada ka dake ni, kaine kace ba zaka kara dukana ba, ko me nayi maka. Na rantse da ALLAH ban yi ban yi iskanci da kowa ba, ban yi irin abinda raliya tayi da sisco ba, ka kawo Qur'ani na dafa"""

"Mamaki ya kara kama shi DA tsoro ganin yana kara nufarta tana kara ja da baya jikin lungu, ya dan"

"dakata ya kwantar da hankali yace ""tsaya ma'u, gaya min me ya faru ba zan dake ki ba na rantse da ALLAH ko me kika yi ba zan dake ki ba, ko baki san kin girma ba yanzu, ko umma ma ba za ta dake ki ba balle ni, me ya faru gaya min mene ne?"

"Cikin shisshikar kuka tana kara tattare jikinta tana kudundunewa tace ""amma dai ka san ni ba 'yar iska"

"bace ko yaya? Ya daga kai cikin rawar jiki. ""Na sani ma'una saliha ce, ba 'yar iska ba, me ya faru, wani ne ya shigo gidan yayi miki fyade ne ma'u? Ki gaya min zan iya daukar dukkan abinda ya faru a kanki, na san kaddara ce"""

"""Ka ji har ka fara fada tun ban gaya maka ba. WALLAHI ban yi iskanci da kowa ba yaya, ban yi komai ba."

"Ya fara fusata. ""Haba ma'u ki sanar da ni me ya faru? Ki gaya mini meye ne? Cikin karaji da ihu yayi"

maganar.

Maimakon ta dawo cikin nutsuwarta sai ma ta kara gigicewa kamar zata shiga cikin gadon ta fashe da

"kuka mai karfi, jikinsa yayi sanyi ya gano ya tafka wauta. Ya dube ta yace ""ok, calm down ma'u yi hakuri gaya min mene ne?"""

"Ganin bata da niyyar magana ya sanya ya faki numfashinta ya cafke hannunta ya daga ya cak, sai ta sake"

"fashewa da ihu ta kankame jikinta kamar zata suma, fadi take ""WALLAHI ban yi iskanci da kowa ba yaya, na rantse da ALLAH"""

"Gabansa ya dinga faduwa ganin jini guda-guda a jikin zaninta da gurin, ya bata gurin gaba daya,"

"hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske, ta kasa ci gaba da kukan."

"Cikin karaji yace ""ma'u meye wannan, me zan gani haka, ba jinin al'ada bane irin naku na mata ba..."""

"Cikin kuka tace ""ni ma da farko na zata irin abinda wasu kawayena keyi ne MISTRATION idan suka sanya"

"audiga da ake goge hanci da shi kenan sai ya tsaya, ni kuma ba sanya sai ta jike na kara sanyawa ta kuma jikewa, sai kuma jini ya dinga zubowa bayan ban yi komai ba, WALLAHI ban yi komai ba"""

"Abun ma sai ya ba shi dariya, duk da jinin ya zuba da yawa, ya saki hannunta domin ta dan sami nutsuwa"

"sannan ya fara magana. ""Ba komai bane ma'u, kowacce mace da yanda take fara yin al'adarta, amma zo ki cire kayanki ki yi wanka sai muje chemist mu ji ko wata matsalar ce"""

"Ta yi doguwar ajiyar zuciya da jin dadi, ta ma manta da yayan nata yana gabanta ta fara kokarin cire"

"rigarta da sauri, bai yi zaton ganin abinda ya gani ba. Yaushe ma'u ta zama haka? Ashe ta zama mace cikakkiya bai sani ba."

"Bugun kirjinsa ya fara sauyawa, sai ya Kau da kansa da sauri yana kokarin nemo nutsuwa, ya sanya cikin"

"ranshi sai ma ya fice da sauri ya bar dakin domin ya kula bata cikin nutsuwarta, cire kayan take son yi gaba daya, yau babu 'yar kunyar da take nunawa a gabansa saboda bata cikin nutsuwarta."

"Ta dauko wani zanin ta daure, kafin ta fito ya zuba mata ruwa cikin bokiti ya sanya mata a bandaki, tana"

"fitowa yace ""maza shiga bandaki kiyi wanka"" ba tare DA ya kalleta ba ita ma bata kula da komai ba kawai ta nufi bandakin."

"Yana shiga ya shige cikin dakin da bokiti a hannunsa ya fara kwashe kayan nata da suka baci, yayo waje"

"da su, sannan ya fice domin siyo mata audigar mata (pad)"

"Har ya dawo tana cikin bandakin bata gama wankan ba, hakanya ba shi damar gyara dakin. Yana tsaka"

"da gyaran ta shigo da sallama, ya daga kai da sauri ya kalleta yana amsawa."

"Cikin shagwaba tace ""yaya na gama amma har yanzu yana zubowa kadan-kadan"" dariya ta kwace masa"

ya daga kai yana kallonta.

"""Wai ke wacce irin sakarya ce ma'u? Amshi nan ki sanya da pant dinki, ai kin san yadda ake yi ko? Ta"

daga masa kai alamar eh ta sani.

"""Yauwa shirya kafin ni ma na watso ruwa yanzu na dawo, na dan gaji"""

"Ya amsa ya fice. Shi ma ya juya domin shiga wankan, amma zuciyarsa tana cigaba da sakawa da"

kwancewa.

A haka dai don wautar ma'u ta dage wai sai sun je chemist din yaya auwal. Saboda burinta kawai ta shiga

gidansu don ta ha ummanta.

"Ahmad ya gyada mata kai yana fadin ""sannan ba abun damuwa bane amma ki tabbatar idan mun je ke"

"da bakinki zaki yiwa yaya auwal din bayanin komai ba ni ba, kin yarda da hakan?"

"Sai a lokacin ta gano wauyar da take shirin yi ya fashe da dariya tace ""kai na fasa, WALLAHI yaya kunya"

"nake ji, sai dai muje wani chemist din. Amma don ALLAH idan mun je wani chemist din zaka kai ni naga"

"umma da baba? Don ALLAH yayana ka taimaka min na dade ban gan su ba"" tana maganar ne cikin shagwaba."

"Ya kada kai yana kwaikwayon maganarta ""sai abinda hali tayi, wuce kawai muje"" ta fashe da dariya tabi"

bayansa suka fice daga gidan.

A haka suka je chemist din wata ma'aikaciyar jinya da take dan taimakawa a cikin unguwa idan dare yayi.

"Duk karadin ma'u kasa yi mata bayani tayi, sai rufe fuska da dariya kawai ta iya."

Aunty Deejah ma'aikaciyar jinyar ta dinga dariya tana zolayar ma'u. Daga karshe ta yiwa Ahmad bayanin

"babu wata matsala daman wasu matan sukan yi haka a farkon fara al'adarsu, amma da sun yi sau daya shi kenan, idan zasu kara yi jinin baya zuwa kaman farko."

Ta ba su magunguna da shawarwari sannan suka bar gurinta.

"A hanya ma'u ta yi shiru taga inda yayan nata zai kai su, domin taga ba hanyar gidansu suka yi ba."

"Ga mamakinta sai taga kamar hanyar gidan su ummanta aka nufa, tayi shiru dai ta shanye murnarta,"

saidai sanda taga sun shiga layin dadi ya cikata har ta gaza boyewa sai da ta rukunkumeshi tana zabga ihun dadi.

"Da fari ya dan tsorata da yanda yaji ta makalkale shi har suka kusa faduwa, amma da ya gano murnar jin"

"dadi ce sai ya saki ranshi, amma rikon da tayi masa ya kara tsinka jijiyoyin jikinsa, cikin ranshi ya fara korafin abinda yarinyar ke masa cikin wannan lokaci, ya gaza jurewa yana ganin zai iya karya alakwarin da ya daukarwa zuciyarshi na barin ma'u ta zama cikakkiyar mace, ta san kanta kafin ya tunkare ta da"

wasu al'amura na aure. Haka dai ya daure ya karasa kofar gidan ya tsaida babur dinsa.

Yana tsayawa tana dira tun bai karasa tsayawar ba. Caraf ya cafko hannunta ganin tana shirin zurawa da

"gudu tayi cikin gida. ""Ma'u baki da hankali gudu zaki sanya a tsakiyar titi? Ko baki san ke matar aure ba ce yanzu? Sai ki sanya mu koma WALLAHI ki fasa shiga gidan"""

Ta kwantar da kai cike da fargaba domin ta san kadan ne daga abinda yayan nata zai iya aikatawa ne.

"""Yi hakuri yaya Ahmad ba zan kuma ba"""

"Ya saki hannun nata yana girgiza kai. ""To ki tsaya mu shiga tare, bana son zumudi na gaya miki"""

"Ta kada kai kawai ta kasa cewa komai, amman murna da zumudi sun cikata ta dan daure ya tsaya ya"

gyara tsayuwar babur din ya kulle shi sannan suka nufi cikin gidan.

"Yaya auwal yana cikin chemist dinshi a zaune ya hango su, tun daga nesa ya fara wangale baki da fara'a"

don ganin yadda ma'unsa ta zama bukekiya.

Suna gab da shagon ma'u ta kufce ya fella da gudu tayi cikin gidan domin ba zata iya jure wannan jan ran

da Ahmad din ke yi mata ba.

Ahmad ya bita da kallo DA tsananin mamaki kafin ya fashe da dariya.

"Yaya auwal ma ya fito daga cikin chemist din yana babbaka dariya yace ""hoo ma'u autar mama wai haka"

take daman har yanzu bata yi hankali ba Ahmad?

"Ahmad yayi dariya ""da sauki dai har yanzu yaya"" ya mikawa yayan nasa hannu suka gaisa suna cigaba da"

dariyar duk su biyun.

"Yaya auwal ya cigaba da magana ""rufe chemist ya kama ni domin ya zama dole naje naga autar umma"

"don kada umma tayi fushi da ni"""

"Suka sake yin dariya, sannan suka rankaya suka yi cikin gidan gaba dayansu bayan yaya auwal ya rufe"

chemist din nasa.

*

*

*

Hajiya ma'u yau an zo ganin gida ai ko dole ki zumudi

DA ME AKE ADO?

30

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

A can cikin gida umma da malam suna zaune suna kallo kasancewar akwai wutar nepa. Labaran karfe

Tara suke kallo. Ma'u ta shigo a guje ta manta babu ko sallama ta fada dakin tana kwallawa umma kira. Da sauri suka juyo suna kallonta don fargaba.

"Umma kam kasa magana tanata, sai malam ne yayi karfin halin daka mata tsawa lokacin da ta iso ta fada"

cinyar umma tana dariya.

"""Ke ma'u lafiyarki kuwa! Hala kina yin hauka ne ko?"

"Cikin dariyar farim ciki tace ""yi hakuri baba, WALLAHI dadi ne ya cika ni na dade ban gan ku ba, ina yini?"

Umma dai kallon autar tata take yi bakinta ya ki rufuwa domin ta koma wata babbar budurwa. Malam ya

"daure ya hadiye fadan domin yayi murna da ganin autar tasa yace ""har kullum dai ba zaki daina sakarci ba, ina mijin naki yake kuma?"

"Ta rike baki tana dariya. ""Umma kinji abinda baba yace wai mijina maimakon yace yayana"" abun ya ba su"

"dariya gaba dayansu, suka bushe da dariya umma na shafa kan ma'un tace ""ho autata na ga ran da zaki daina shiririta WALLAHI"""

"Daidai lokacin auwal da Ahmad suka shigo. Ma'u ta kalli yaya Ahmad tana yar dariya tace ""yaya ba zan"

"kara gudu ba, ALLAH yanzu ma na kagu na ga ummata ne"" ya kada kai yana murmushi bai ce komai ba."

"Yaya auwal yayi hararan wasa yana fadin ""ni kuma meye laifina da aka ki tsayawa a gaishe ni? Ta rufe"

"fuska tana dariya ""yaya ina yini"" bana cin kwantai"" ya bata amsa."

"Umma tana dariya tace ""duk kin cika mu DA surutu kin hana ni gaisawa da dana. Manya yaya aka yi ne"

"sai ga ku da dare kuma, lafiya?"""

"Ahmad ya sami guri ya zauna yana dan yake yana satar kallon ma'u da ta fara raba ido yace ""lafiya lau"

"mun zo kawai gaishe ku ne, baba ina yini"" malam Sulaiman ya amsa da sakin fuska sannan ya gai da umman tashi. Daga nan aka balle da hira ana ta dariya."

Ma'u dadi ya cika ta tana ji kamar kada ta koma gidan mijinta.

"Shi kansa Ahmad hirara tayi masa dadi, ji yake kamar kada ya bar gidan iyayensa, domin hira cikin"

iyayensa da danginsa yafi komai dadi.

"Malam ne ya fara ankara yace ""kai sai yaushe zaku tafi ne, naga kun tsare su sai hira kuke sharba dije'"

"Umma tayi dariya tana fadin ""ni babu ruwana, su tafi mana ai ban hana su ba"" ma'u ta turo baki gaba"

"kamar zata fashe da kuja. ""Ni dai mu kwana a nan don ALLAH baba"""

"""Kwana kuma? Malam ya tambaya. Ahmad yace ""eh gobe said mu wuce da safe"""

"Auwal ya fashe DA dariya

28 / 47