Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   36 / 47

105K to 108K   out of 139.6K words

sannan ta fashe da kuka mai karfi. Malam jibril ya fusata ya kai mata hauri da

kafarsa. Ta ja ciki tana kuka.

"Malam Sulaiman ya yi sauri yace ""baka da hankali jibrilu ko baka kula da abinda take dauke da shi bane?"

Hawaye ya zubo daga idon malam jibril ya juya a fusace yana goge idonsa yana kada kai da tsananin takaici a tattare da shi.

Raliya ta cigaba da kuka zuciyarta na tafarfasa kamar zata kone. Lami kuwa kamar ta sanyawa gidan

"fetur da wuta su kone gaba daya kowa ya huta take ji, sai huci take yi kamar wata kububuwa."

"Malam Sulaiman ya dubeta yace ""kin ga abinda ake gaya miki ko lami? Ka ki naka duniya ta so shi, ka so"

"naka duniya su tattara shi su watsar a kwandon shara. Sannan kuma gori ba shi da amfani, bashi da rana, domin MANZON ALLAH (S.A.W.) ya hane mu da shi. Sannan dukkan abinda ka girantawa wani, kai ma"

"wata rana sai ka wayi gari ALLAH ya jarrabeka da shi..."""

Lami ta tashi fuuu kamar an zabga mata bulala ta nufi gidansu. Suka bita da kallo da mamaki. Malam

"Sulaiman ya yi murmushi kawai don lami ba zata sauya ba. Raliya kam ta kasa yunkuri balle ta mike, domin kafafuwanta sun yi sanyi kwarai da gaske."

"""Ya kamata ku tashi ku wuce gidajenku haka ku kuma"" umma ce ta fadi haka tana kallon yaran nasu,"

daya bayan daya aka fara mikewa domin tafiya.

"Raliya da ma'u kam suna jabe a wajen da suke zaune, kowacce daga cikinsu ta kasa motsi. Sai da Raliya"

ta jiyo ihun kiran lami daga cikin gidansu tana kwala mata kira sannan ta mike a sanyaye kanta a kasa cike da tsananin kunya da takaici ta wuce. 'Yan uwan nata suka bita da kallon tausayawa.

Ma'u kam tun daga sanda taji irin sharrin da taso kullawa mijinta taji ta kara tsanarta bata ko jin

tausayinta. Sai da umma ta kara yin magana sannan ma'u ta mike dakyar. Malam Sulaiman yana ta sanya musu albarka suka yi sallama suka fice.

"Akan babur suke tafe amma a tsakaninsu babu mai cewa da wani kala, kowa da abinda yake sakawa a"

cikin ransa. Ahmad yana kara kallon iko da buwaya ta UBANGIJI yana masa godiya. Mutanen da suka sanya shi a gaba da gori yau an wayi gari ga yadda ALLAH ya nuna musu. Tun a duniya ma kenan.

Ita kam ma'un tuananinta akan ace raliya ya cigaba da kasancewa matar ahmad ne da yaya zata yi da

"rayuwarta? A haka suka isa gidansu ba tare da wani yayi wa dan uwansa magana ba a tsakaninsu, sai tunane-tunanen zuci kawai suke yi. Sai da suka watsa ruwa tare sannan suka fara shirin kwanciya."

Ahamd ya jima akan gado yana yin game a wayarshi amma Ma'u bata shigo dakin ba. Ya mike tsaye

"sanda ya ankara da jimawarta bata shigo ba, ya fito falo yana kiran sunanta da karfi. ""Ma'u! Ma'u!! Ma'u!!!"" Daga can cikin falon ya jiyo muryarta tana amsawa dakyar muryata kasa-kasa. Ya shiga falon da"

"sauri. ""Ma'u kina ina ne?"

"Can bayan kujera ya jiyo ta tana fadin ""gani nan yaya... Cikina da bayana zasu cire...!"

"Ya isa gurin da take da sauri yana salati. ""Cikinki da bayanki me ya faru? Ya tarar da ita ta kankame jikin"

kujera ta hada uban gumi sai kada kai take yi kamar mai hadiyar kunama.

"Cikin fargaba yace ""yaya dai Ma'u lafiya, me ya faru me ya shigo dake nan? Cikin karfin hali tace ""tun a"

"gidan su umma naji cikina yana ciwo, shine da muka dawo ya dan yi shiru yanzu kuma ya dawo na shigo daukar magani sai kafata ta rike na kasa tashi"""

"Ahamd ya matsa gabanta sosai yana kokarin tayar da ita zaune. ""Bari na tayar dake ko kuma mota zan"

nemo muje asibiti?

"""Wash! Yaya! Ba zan iya tashi ba, wani abu ne ya rike min kafa. Wash! Innalillah... Wayyo yaya...!!!"""

"Ahmad duk ya rikice ya saketa ya ma rude ya rasa me zai yi. Ya nufi kofar fita yana fadin ""bari na kirawo"

"babar A'ilo..."""

"""Kar ka fita... Kazo na mutu a gabanka yaya... Ka zo don ALLAH...!!! """

"Ya dawo da sauri da tsananin tashin hankali rungume ta gaba daya ya fita daga cikin hayyacinsa, labarin"

"yanda mahaifiyarsa ta haifeshi kawai ke yawo a ransa, yanzu idan Ma'u ta mutu yaya zai yi da rayuwarsa?"

*

*

*

DA ME AKE ADO?

42

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Ma'u kam tana durkushe kankame da kujera sai gyada kai take yi tana nishi. Shi kuma ahmad ya rasa mai

"ya kamata yayi mata. Cikin ikon UBANGIJI ya zabga wani irin nishi hade da doguwar kabbara, sai ga yarinya ta fado facal. Ihun yarinyar ne ya ankarar da ahmad, ya zura hannu ya janye yarinyar gefe a"

"hankali don yaga kamar zata zaune ta, sai ga mahaifa ta fito itama gaba daya."

Ma'u ta kwantar da kanta jikin kujera tana mayar da numfashi. Ahmad kam ya rasa me zai yi saboda sai

"ihu yarinyar take yi, ga mahaifa a jikinta. Ya Kalli Ma'u yace 'Ma'u me zan yi mata ne?"" Ta dan kalli yarinyar tace ""nima ban sani ba yaya, ka kirawo babar A'ilo"""

"Da sauri ya fice daga falon ya nufi gidansu A'ilo ya tarar DA kofar gidan a rufe, don haka ya fara bugawa."

"Bai jima da fara bugawar ba suka bude. Mahaifin A'ilo ne ya fito yana tambayar ""wane ne?"" Yana budewa yayi arba da ahmad hankalinsa a tashe. Nan take ahmad yayi masa bayani, ya juya gida ya sanar da babar a'ilo, suka fito da hanzari suka garzayo gidan. ALLAH ya sa bai jima da yin siyayyar kayan"

haihuwar ba har da reza a cikin kayan.

"Kafin karfe dayan dare babar a'ilo ta kammala komai, ta gyara maijego da jaririya da kuma dakin. Ahamd"

"kam shi ya wanke dukkan kayan da suka baci, cikin ransa yana jin son Ma'u da tausayinta na kuma shigarsa."

"Cikin daren su umma suka ji labari, don haka ana idar da sallar asuba umma ta gidan tun gari bai gama"

"sha ba. Ta tarar da diyarta fes! Ranta yayi fari tas! Shi kuwa ahmad kwana yayi idonsa akan diyarsa, komai dake jikinsa shine a jikin wannan yarinyar. Ya rungume ta a jikinsa kamar zai mai da ta ciki. Yayi tayi mata addu'a duk wacce tazo bakinsa."

"Ma'u dariya kawai take yi masa, da yake su kadai suka kwana a cikin dakin nasu, suna ta sambatu akan"

"diyar tasu. Umma ta dora mata ruwan wanka, tayi wa Ma'u da jaririyar wanka, duk inda suka shiga ahmad ma biye da su, sai da ta hada shi da rikon diyar tasa ta shiga yiwa Ma'u wanka sannan ta sami lafiya, domin zama yayi ya kurawa diyar ido kamar ya lasheta, amma yana jin abu biyu a cikin ransa farin"

ciki da bakin ciki.

"Tun yanzu har ya fara tausayawa diyar tasa, domin 'yar zata tashi cikin gori DA tsangwamar cewa"

"babanta shege ne, har su umma suka fito bai sani ba sai DA umma tace ""Ahmadu wai me kake kallo ne haka? Sannan ya wayance ya goge hawayen dake zubo masa ba tare da ta gani ba, ya mike ya ajiye yarinyar ya fice. Tun safen umma tace masa ya kamata su wuce da ma'un asibiti a duba ya sosai da kuma jaririyar tata, domin haihuwar gida hatsari ce, musamman ga masu karancin shekaru irin ma'u. Sannan"

daga can asibitin sai ta wuce da ita gida ta zauna a can.

"Duk da bai ji dadin karshen maganarta ba, amma ya danne yayi ta maza, domin umman tashi tafi shi iko"

"da su baki daya. Sarai ta kula da yanda ya dan sauya, amman sai ta basar da shi domin idan ta biye masa ba zata je da ma'un gidan ba."

"Tunda cikin Ma'u ya cika wata bakwai taso Ma'u ta koma can gidan ta zauna, amma yanda ahmad ke"

"nunawa da an tayar da maganar ya sanya ta rabu da su. Domin ta kula akwai wata soyayya mai karfi da shakuwa a tsakaninsu, sai taji tausayinsu, amman a yau dai babu wannan maganar. Ta katse shi ganin yanda yayi soror yana kallonsu tace ""yaya dai, yau ba zaka je aikin bane? Da sauri yace ""umma nayi"

"musu waya na sanar da su matata ta haihu, bari naje na dauko motar taxi sai mu tafi asibitin"""

"Umma tayi murmushi ""Ahmadu babu dama, sai kace kaine ka haihu din?"

"Mintuna kalilan ya dawo DA mota taxi. Umma tace masa ""ba tare da kai zamu tafi ba fa manya"" ya kalle"

"ta DA mamaki ""umma saboda me, ai ko diyar na rike muku ko?"

"""Diyar gidanku mara kunya."""

"Kunya ta kama shi ya kau da yana dariya, Ma'u ma dariya ta saka."

"Umma tace ""goyata zan yi, kai ka hada kayan ma'un kayi gaba sai ka wuce da su gida sai mu tadda ka"

"acan"""

"""Amma dai umma har nawa kayan zan hada ko? Don WALLAHI ba zan iya kwana a wannan gidan ni kadai"

"ba"" ya marairaice kamar zai fasa kuka. Umma tayi dariya tana fadin ""idan dai zaka iya kwanan shago ai shikenan"" gaba daya sika fashe da dariya."

***

"Duk wani duba an yiwa Ma'u bata sami matsalar komai ba, su kansu likitocin sun yi mamaki, domin"

"ganin ma'un tana da karancin shekaru, amman dai sun san kowacce mace da irin jikinta, musamman ita da ta haihu a durkushe. Daga karshe dai sun bata magunguna ita da diyar suka wuce gida."

Matan yayyenta da su yayyen dukansu suna gida suna jiran dawowarsu. Ahmad sai basu labarin

"kamannin diyar yake yi ana dariya, kowa ya kagu su dawo din. Sanda suka iso gida ya cika da hayaniya, aka dinga shigowa barka."

"Hayaniyar ce ta sanya lami da 'ya'yanta suka gano wani abu yana faruwa a gidan, ta kira amina ta turata"

domin ta gano mata abin dake faruwa a gidan.

"Amina ta dawo ranta a bace ta kasa yin koda magana. Lami ta dubeta tace ""malama ki gaya mana abin"

"dake faruwa mana kin shigo sumsum sai kace tunkiya"""

"""To me zan gaya miki, wai wannan banzar ce ta haihu"" lami ta tashi a gigice cikin firgici tace ""ba dai Ma'u"

"ba"""

"""Ita mana, sun cikawa mutane gida da ihu banzaye kawai"""

Lami ta koma ta zauna tana huci kamar zata fashe da kuka.

"Raliya kam ta kasa cewa komai sai kallonsu kawai take yi, ita kadai ta san me take ji a cikin ranta. Lami"

"tsinuwa da baki babu irin wanda bata yiwa diyar nan da aka haifa ba, amman da ikon ALLAH ya cika babu yanda za a yi."

"Ma'u taga karamci daga gurin 'yan uwanta da mijinta, don duk kudin hannunsa da wanda yake tarawa"

"akan diyar nan ya karar dasu. Ita ma Hajiya Amina ta dauki soyayya ta dora akan diyar nan, kullum sai tazo ta ganta, sai take tuna mata da ahmad sanda yana jariri."

"Rashin shigowar lami da 'ya'yanta bara ya daurewa umma kai kwarai da gaske, amman ta danne abun a"

cikin ranta.

Ma'un ce ma mai yi mata korafi har sai da umman ta kwabe ta.

"Gurin yiwa diyar huduba ma sai da aka sami sa'insa, domin shi Ahamd sunan umma yake son a sa mata,"

"ita kuma umma ta dage sunan mahaifiyarsa za a sanya, domin ita sunayenta da tawa. Auwal ya saka, sani shima ya saka. Ita kuwa bayan Ma'u babu mai sunanta."

"Dakyar ya amince da hakan aka sanyawa diyar suna ASMA'U, sai yake ji kamar mahaifiyarsa ce ta dawo"

masa son diyar ya rinka shigarsa.

"Ranar suna anyi suna main kayatarwa irinna masu rufin asiri, an ci ansha daidai Misali. Wannan abu ya"

"kuma komawa lami rai. Raliya kam har kuka tayi, ta kunshe cikin daki ta kasa ko lekowa waje, da tuni itace zata haifi wannan diyar ta halak, ta yiwa kanta, tabbas ta shiga tsananin da ta sani, wacce Hausawa ke cewa keya ce."

"A daren ranar suna ciwo ya kuma raliya cikin daki, tun tana abin ita daya har ta fara kiran mahaifiyqrta."

Lami ta shigo cikin dakin suka ci gaba amma shiru babu haihuwa sai azaba. Tun lami tana ganin abin kamar wasa ne har ta fara tsorata.

Shi kam malam jibril tunda ya fuskanci abun dake faruwa ya shige cikin daki ya rufo kofa. Lami taga haza

"taje ta buga masa tana kuka. Ya bude kofar ransa a bace yana fadin ""yaya aka yi lafiya dai ko?"

"Cikin kuka tace ""raliya zata mutu jibril ka taimaka min"" ya galla mata harara ""rayuwar raliya da"

"mutuwarta duka daya ne a gurin lami, don gwara ma ta mutu ko na huta da abin gori"" ya juya ya shige cikin dakinsa ya ja kofa."

"Lami ta fashe DA kuka gami da juyawa dakin da gudu saboda jiyo ihun diyar tata da take yi, suka ci gaba"

"da fama amma har tsakiyar dare shiru. Shi kansa malam jibril sai da ya karaya ya leka dakin, halin da yaga diyar tashi ya daga masa hankali kwarai da gaske, ya gogice yana tambayar yaya za su yi? Lami tana kuka tace ""asibiti za a kai ta kawai"" ya dan waro ido waje. ""Asibiti kuma! Gashi ban da ko kwandala, shi"

"kuma asibiti sai da kudi kin sani"""

"""Kaje gurin yayanka mana ai ba zai hana ka ba ka sani, ka taimaka don ALLAH jibril"""

"Ya juya a kidime ya nufi gidan yayan nasa, ya jima yana buga kofar da zata sada shi da gidan yayan nasa,"

can jimawa malam Sulaiman ya ISO yana tambayar waye?

"Malam jibril yace ""nine jibril"" malam Sulaiman ya bude kofar cikin mamakin dalilin zuwansa cikin"

wannan dare. A kidime malam jibril yayi masa bayanin abin dake faruwa.

"Malam Sulaiman ya ce ""ai samun mota cikin wannan daren shine aiki, amma bari"""

Ya shiga yayiwa umma magana ko akwai wani abu da zata iya yi a kai.

"Sanda malam Sulaiman ya sanar da umma abib dake faruwa tayi tsalle ta dire tace ""babu inda zani, nima"

"diyata ta haihu har kwana bakwai yau amma daga lami har 'ya'yanta babu wanda ya leko, don haka babu inda zani"""

Tun yana mata fadan har ya fara yi mata magiya da kawo mata hadisai wadanda suka sanyayar mata DA

gwiwa ta nufi gidansu lami.

"Tana zuwa taga halin da Raliya ke ciki ta san lallai ta jigata, ta kwanta sharbe-sharbe ga kan da na"

"yunkurowa yana komawa, ta kasa nishi, lami sai kuka take yi ita da amina."

"Umma ta kalli lami tace ""kuna da koko ko kunu?"

"Da sauri lami tace ""akwai"""

"Ta fice ta dauko umma ta amsa tayi addu'a fa tofa mata a ciki sannan tace a dago mata raliya zaune,"

suka kama raliyar dakyar suka zaunar da ita.

Umma tace ta dafa kujera ta tokare kafafuwanta a kasa ta kafa mata wannan kunu cikin katon sha ta

"dinga sha har sai da shanye shi tas. Cikin ikon ALLAH sai ga karfi ya zowa raliya ta fara wani irin nishi da karfi, umma ta rike ta. Sai ga diya ta fado, Cikin ikon ALLAH kuma har da mahaifar baki daya."

"Lami ta fashe DA ihun murna, umma ta dalla mata harara ""ke da zaki godewa ALLAH sai kuma ki kama"

"guda? To sai ki kawo reza"""

"Lami ta juya da gudu ya fara nemo reza da zare, umma ta amsa ta yanke ta kulle cibiyar bayan ta yanke."

"Raliya tayi zaune ta kasa motsawa saboda abu biyu ke yawo a ranta, murna da rabuwa da abun dake"

"cikin cikinta da kuma takaicin abin kunyar da zai fara bibiyarta har karshen rayuwarta. Malam jibril yana tsaye a bakin kofar dakin da damuwa akan fuskarsa yana jiyo sautin kukan jaririyar ya zame ya zauna yana sallallami da damuwa, shikenan ta tabbata shege ya bayyana a gidansa, diyarsa ce ta haifa masa"

shege ya shiga uku.

"Umma dai tana gama abin da zata yi ya kalli lami tayi wuki-wuki da ido tace ""to lami ga dai raliya ta"

"sauka ta sami irin abinda kika dade kina gorintawa ahmad a kai, sai nace ALLAH ya raya amin"" lami ta"

bude baki da bakin ciki amma bata da abin cewa da zai daidai da irin maganar DA umma ta fada mata har ta fice daga dakin.

"Lami ta kalli raliya dake zaune kamar ta shake ta don bakin ciki, ta kalli diyar wacce ke ta kuka tana"

"wutsil-wutsil da kafafuwa, sai tayi tsaki ta juya ya fice daga dakin da sauri. Raliya ta bi yarinyar da kallo ta mika hannu ta dauketa ta kura mata ido, fatanta bai wuce ta gano da wa diyar take kama wanda zata ce shine ubanta, domin maneman nata na DA yawa. Amman iyakacin kallon da tayiwa yarinyar ta kasa gano"

da wanda tayi kama. Hawaye ya dinga fitowa daga idanunta soyayyar tana shigarta a hankali.

Me ya sanya bata zauna a gidan ahmad ta haifi wannan yarinyar ba ko bayan hakan ne ta bar gidan? Da

ta huta da gori da dukkan abibda zai biyo bayan rayuwar wannan yarinyar da ta haifa yanzu.

Dakyar lami ta iya dora ruwan dumi domin ta kaiwa raliya bandaki sannan ta dauki jaririyar tayi mata

wanka. Ba su sami kwanciya ba sai wajen karfe hudu na dare sannan suka kwanta.

Kiran sallar farko raliya ta mike tsam ta dauko jakar kayanta ta fara zuzzuba dukkan abun da tasan nata

"ne, daman sun gama shiryawa da ruky cikin dare, sun gama shirya abin da zasu yi. Bayan gama kammala shiryawar ta juya ta kalli jaririyar DA take bacci, hawaye ya zubo mata taji kamar kada ta gudu ta bar diyar nan, amma ba zata iya cigaba da harka yadda take so ba matukar tana tare da wannan yarinyar, ta"

goge idonta da sauri ta dauki jakarta ta fice.

"Har gari ya waye rana ta fara fitowa lami bata leka dakin da Raliya take ba, daman amina ta raba daki da"

"Raliya tuntuni. Can yarinya ta fara kuka daga cikin dakin, daga lami har amina babu wanda ya kula da kukan da take yi, domin suna tunanin mahaifiyarta na kusa da ita. Shi kam malam jibril dama tunda ya fita sallar asuba bai dawo gidan ba. Musa kuma tunda aka yi rikicin nan bai kuma dawowa gidan ba, sai"

ya tare a can dakin wani abokinsa don bai san abinda zai faru da shi ba idan suka ci karo da lami.

"Kukan ya ishe su, lami ta mike a fusace ta nufi dakin tana fadin ""raliya wai uban me kike yi ne kika bar"

"yarinyar nan tana kuka haka?"" Ta daga labulen dakin a fusace, sai dai ya mamakinta sai taga dakin wayam babu kowa sai jaririyar dake ta tsala kuka. Ta shiga dakin da sauri ta fara bincike. ""Raliya! Raliya!! Raliya!!!"" Amma taji shiru babu ita balle alamunta. Ta fito da sauri ta kalli amina

36 / 47