Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 47

66K to 69K   out of 139.6K words

tadda shi a gidan yana"

"aikin danne danne a computer da alamar aikin ofis yake yi, da yake shi ya samu aiki tun bayan da suka"

"kammala bautar kasa, koda yake shi dan gata ne tun kafin ya kammala aka dinga nemar masa masauki kasancewar ubansa tsohon sakataren jaha."

"jagwab ya fada kan katifar dake yashe a tsakar dakin yana nishi, tabbas idan za a auna jininsa ayanzu za"

atadda shi ya hau.

"ishaq bai san komai game da shi ba, tun zuwan da ya taba yi na farko gurinsa yayi kwanaki hudu bai gaya"

"masa komai ba, yace kawai dan sabani ya samu da babansa, don haka lokacin da ummi tace ta fasa aurensa ma bai sanar da ishaq gaskiyar magana ba, don yana tsoron furta kalmar ga wani, domin bai san yadda za adinga kallonsa ba, yace da ishaq yayyansa ne suka dage lallai sai ya auri raliya auren gida za ayi masa, ishaq ya taya shi bakin ciki, duk da ba unguwa daya suke ba yasan halin raliya daga dan zaman da yake yi gurin ahmad ya fuskanci wacece ita, don haka don haka da yaga ahmad yanzu ya shigo a"

wahalce ya san itace.

"ya kalli ahmad da tausayawa yace 'abokina yaya dai, kai da ka angwance jiya bai kamata aganka a cikin"

"wannan yanayin na damuwa ba' yayi lakwas kamar ba zai yi magana ba, can ya daure ya tashi zaune ya dubi ishaq yana fadin 'iyayenmu basu san wacece raliya ba, sun haife tane amman halayenta sun yiwa tarbiyyarsu nisa, bata da wani na burgewa baya ga jahilci da yayi mata katutu, ba zance sun cuce ni ba"

"domin sun fi kowa sona, saidai sun min zaben tumun dare'"

ishaq ya dafa kafadarshi ko bai yi magana ba daga yanayin da fuskarsa ta nuna yasan yana cikin hali mai

"daci. don haka cikin murmushi yace 'kowanne bawa akwai kaddararsa mai kyau da maras kyau, kai kam da alama auren raliya shi ne mummunar maddararka. idan kuma ka dage zaka cinye dukka jarrabawarka, inda naji dadi ma da kai namiji ne da kake da damar auren mata hudu. don haka kayi hakuri ka cigaba da zama da raliya da dukkan halayenta. watarana idan ka sami faraga sai ka auri irin matan da kake so. kayiwa mahaifanka biyayya na tabbatar ba zaka tabe ba. tun jiya gurin daurin aure na kula da yanayinka"

kana cikin damuwa'

yayi shiru yana sauraron shawaran ishaq saidai a ransa bai hango wata mafita ba domin banda raliya

"babu wata mace da zata iya yadda ta aure shi shege maras uba. mara kowa dan mahaukaciya, amman ya dinga gyada kai alamar yana daukar shawarar ishaq din. anan ya wuni har suka ci abincin rana, sai wajen karfe 4 na yamma sannan yayi shirin tafiya, kai tsaye gidansu ya wuce. a yanzu zai iya haduwa da"

iyayenshi ba tare da sun gano akwai damuwa atattare dashi ba.

"yayi sa'a kuwa babansa ma yana gida a yanayin da suka ganshi sun ji dadi kwarai da gaske, shima ya saki"

"fuskarsa sun gaisa. basu tambaye shi komai agame da gidansa ba shima bai basu labarin komai ba, har suka kammala hirarsu ya wuce. a kofar gida yaci karo da yayansa auwal cikin chemist dinsa ya karasa suka gaisa, auwalun yace 'yaya dai raliya babu matsala ko, domin nasan yarinyar sai kayi hakuri ka kau"

da kai'

"yayi murmushi kawai bai ce komai ba, sun dan taba hira har sai da yaji an fara kiraye-kirayen sallar"

"magariba sannan yayi alwala anan suka wuce masallaci, gurin dawowa suka ci karo da malam jibril ya dan rankwafa yana gaishe shi."

"malam jibril din sai murmishi yake yi cike da farin ciki, don ko babu komai ahmad ya rufa masa asiri sai a"

yanzu ya kara ya tabbatar da hakan domin ya raba shi da raliya mai dauko masa magana da zagin jama'a. cikin farin ciki yace 'babu wata matsala dai ko? ya kara dukar da kai yace 'babu komai baba' da haka suka yi sallama ya wuce ya dau babur dinsa ya nufi gidansa ganansa yana faduwa. sai da ya tsaya ya sayi

doya da kwai soyayya domin yasan ba zai tadda abinci ba.

"yau kam abin yafi na jiya domin tun daga kofar gida ake jin sautin kidan, ya shiga da sallama ba don"

"yasan zata ji ba, sai domin mutanen boye. abin mamaki sai ya hango takalma barkatai na mata da kuma hayaniyarsu ana ta shewa, ga tukwane nan da kwanika an yi girki an bata gidan faca-faca, har da gara abbanshi ya kawo ta akwai komai na bukata, wato shiga kicin tayi suka yi bidirinsu da kawayenta, ya"

sami guri ya ajiye babur dinsa ya dauki doyarsa ya nufi dakinsa na soro ko nace shago yana kanga kofar

dakinta hayaniyar tana cigaba da yawa.

har aka kirayi sallar isha'i ya tafi yayo sallah ya dawo kawayen suna nan yaji kamar ya karasa yaga su

"waye wadannan marasa hankalin sai kuma yayi tunanin kada ta bashi kunya a gabansu, don haka ya koma daki yayi zamansa sai lazimi ma da ya fara yi."

sai wajen karfe goma na dare sannan ya ji alamun fitowarsu da alama kuma batirin rediyon da suke jin

"kidan yayi sanyi, domin an kashe rediyon gaba daya tunda ba wuyar nepa bace."

a tsakar gida ya jiyo muryar wata tana fadin 'wannan babur din acabar kuma na waye ne? ko makotanku

"ne suka kawo muku ajiya? gabansa ya fadi domin yasan raliya sai tayi cin zarafi agare shi sai ya jiyo muryata ta fashe da dariya tana fadin 'nashi me fa' shi wa? wata ta kuma tambaya 'shi mijin nawa' ta basu amsa. suka bushe da dariya a tare daya daga cikinsu tace 'yo ashe dan acaba ne kina cewa baki san sana'arsa ba,tabdijan gaskiya tsofaffinki.sun mimi ba daidai ba, kamar da su alhaji gwani ke rububi a hadaki da tsohon dan acaba, don wannan da gani ya jima yana acabar kalli yanda babur din duk ya kuje"

saboda azaba' suka kuma bushewa da dariya.

"'shi ya sanya nace ai wannan auren sunanshi ballalle domin ba a yi shi daman don na zauna ba, ku dai"

kada ku tsare min gurina ina nan tafe'

suka bushe da dariya 'waye zai tsare miki? gibinki babu mai iya cike shi babbar yarinya' suka yi dariya da

shewa sannan suka nufi soron gidan.

"ta nuna shagon da yake 'kun ga nan ne fa turakar miji, kuna sha'ani garada na jiyo ku daga waje' suka"

kuma sanya dariya. 'ALLAH SARKI ashe ma yana ciki domin na hango hasken tocilan dinsa. ko yayi bacci

wa ya sani ma? farry ta fadi tana dariya. jamcy tace 'ato ko za a kira shi ne ma mu gaisa? ta harare su 'da alama dai kuna son nemo mini raini ne. don ALLAH ku muje na raka ku'

"suka fice suna dariya da shewa ya hasala iya hasala, saidai kiran sunan ALLAH da yake yi ya sanya"

"zuciyarsa ke dan sanyi, abinda ya bashi mamaki yanda ta fice ba tare da ta sanar dashi ba anya raliya tana da tunani ma balle hankali? ya mike ya leka domin ya tabbatar ko ta bi su din. sai ya hango fitilun motoci guda uku akunne, suka karasa gurin wasu maza suka firfito daga motocin suka yi 'yar hira sannan kawayen nata suka shiga motocin suka tafi. yana kallo sanda wani ya mikawa raliya damin kudi cikin bandir dinsu zuciyarshi ta dinga tafasa, shi mutum ne mai tsananin kishi, a ra'ayinshi kl kofar gida"

"matarsa ba zata fita ba sai da shi, amma ga raliya ta fice ita daya babu izininshi na."

yana nan tsaye har suka tafi sannan ta juyo gidan tana juya kudin da aka bata a daya hannun cike da

"farin ciki, yasha gabanta a soro ransa a bace yana huci yace 'uban waye ya baki wannan kudin? me kuma kika fita yi gurin wadancan 'yan iskan ba tare da izinina ba?"

ta kalle shi ta kyalkyale da dariya cikin rashin kunya tace 'ALLAH sarki masu aure ashe fa ni matar aure ko?

na manta sam ko don ban shirya zaman auren bane oho! wadancan da ka gani samarin kawayena ne

"suka bani kudi, wai na dan kashe kafin lokacin da zaka sallame ni domin sun sanba zaka iya ciyar da ni ba albashinka na wata guda shi ne kudin shan ice cream dina'"

ya kalle ta a raine abar bai fi yayi mata shaqa daya ta sume ba amman ta tsaya tana gaya masa abinda

"take so, banda darajar aure ko a hanya bai da lokacin kula raliya ya kankance ido yace 'kina da damar fadin duk abinda kika ga dama, saidai ki sani albashin da kike rainawa yafi dukkan abinda kike samu albarka, shi guminane halak dina: don haka ba zan damu ba amman dole ki bi dokata a matsayina na wanda ya bada sadakin da ya aure ki, idan kuma kika saba hakan komai zai iya faruwa' yana kaiwa nan ya"

juya ya shige cikin dakinsa.

"tayi shewa ta tafa cinya tana fadin 'kace an zo gurin da nake bukatar a zo, wallahi kayi kadan don zan fita"

"sai ka ba ni izini ko iyayena da suka kawo ni duniya ba su sanya min irin wannan dokar ta tauye hakki ba balle kai wanda cikin mutane ma baka da daraja, limancin sallama haramun ne a gare ka'"

"ya runtse idanu zuciyarsa tana cigaba da zabalbala, kalaman raliya tamkar zubar ruwan dalma ne a"

"zuciyarsa, ya tsane ta ya tsani kalamanta mara alkhairi baya son cigana da sauraronta don haka ya sanya"

hannuwa ya toshe kunnuwa ya kuma fara ambaton sunan ALLAH domin cigaba da sauraranta zai iya haifar da komai a gare shi.

"sai da tayi rashin mutuncinta iyakacin iyawarta sannan ta wuce ta nufi cikin daki, ta yi sabon zubin"

"sabbin batira a rediyonta ta kureta ta mike tana taka rawarta, duniya tayi mata yanda take so kenan."

*

*

*

to raliya a taka rawa dai a sannu saboda kowa ya debo da zafi bakinsa.

DA ME AKE ADO?

20

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Tsahon sati guda ana zaman 'yan marina a gidan, babu wani abu raliya take yi da ya zama na aure ne,"

"hatta shara shi ke yin ta wanke-wanke kawai take yi shi ma don ita ce ke bata kwanikan da kawayenta dake wuni a gidan kullum, da ya fita aiki su kuma zasu dira basu barin gidan sai dare, matuka abin ya ishe shi saidai yayi alkawarin ba zai kai karar ta ba. zai yi hakuri da juriya har zuwa sanda zai ga karshen abin"

domin ya san ba komaine ke dauwama ba.

zaman da yayi cikin hutun karshen mako wanda aka bashi don angwanci ne ya sanya ya fahimci ashe har

"fita yawonta take yi, tabbas da gaske raliya take yi bata shirya zaman aure da shi ba, ba kuma zata hankalta ba domin bata amfani da komai nashi, ko kudin cefanensa da yake ajiye mata tace tafi karfinsu, don haka yanda ya ajiye haka yake dawowa ya taddasu. don haka ya daina ajiyewar, saidai fa ko a sharar da yake yi ya kula da irin dadin da raliya ke ci, domin kasusuwan kaji da kwlaaben lemo kullum sai ya"

"share su, hakan ya tabbatar masa da yawonta take yi, shi kam ya maida hankalinsa gurin aikinsa kawai."

zuwan lami na farko kuma na karshe gidan shi ya karasa dagula komai. suna daki ita da diyarta suna ta

"kulle-kullensu ya iso gidan, a gajiye yake tubus, domin yau bai tsaya hutawa ba kamar yadda ya saba yana tashi daga aikin yayo gid kawai, kai tsaye ya shigo da babur dinsa gidan. daidai lokacin da lami ta"

"fito daga dakin raliya tana biye da ita, furucinta na karshe ne ya doki dodon kunnensa."

ta waiga ta kalli diyar tata cikin zafin rai tana fadin 'kin dai ji abinda na gaya miki saura kuma ki ki bin

maganata' raliya ta tabe baki 'koda baki fada ba dama ra'ayina ne balle kuma kin kara tunatar da ni'

sai suka yi ido hudu da ahmad duk da bai fahimci abinda suke cewa ba yasan ba maganar arziki suka

"tauna ba, musamman yanda suka dan firgita da suka ganshi. lami tayi tsaki tana fadin 'kin ga tafiyata ni sai an jima' ta nufi kofa da sauri."

ta zo daidai inda yake ya durkusa yana fadin 'baba ina wuni' ta kalle shi shekeke a wulakance kamar ta ga

katon kashi tayi tsaki ta wuce ta barshi durkushe bisa gwiwarsa. raliya ma tayi irin yanda mahaifiyarta tayi sannan ta nufi kofar da mahaifiyar ta nufa don yi mata rakiya.

"ya bisu da kallo cike da takaici da bakin ciki tun yana yaro lami bata kaunarsa, balle a yanzu da aka hada"

shi aure da diyarta kuma na dole ai dole kiyayya ta karu akan ta baya. ya mike jikinsa babu kwari ya nufi

"dakinsa. ya kwanta bisa tabarmarsa ya kurasa silin ido tunani barkatai ya dinga zuwa yana wucewa a kwakwalwarsa, wanda ba zai manta guda daya ne."

lokacin yana yaro wata rana abbansa ya siyo musu riga ya fallo da gudu gidan yana kwalawa musa kira

"yana fadin 'musa zo ka ga rigar da babana ya siyo mini yanzu a kasuwa irin ta sojoji zan sanya ta ranar juma'a nayi ado da ita' musa ya kalli rigar daidai lokacin lami ta isa gurin sai ya fashe da kuka yana kallonta yace 'lami kinga rigar da aka siyawa ahmad ran nan ma ummansu ta siya masa ta 'yan ball, ba ki"

sai mini ba kullum sai ya fini ado. ranar juma'a nima sai a sai min'

"lami ta warce rigar tayi wurgi da ita tana fadin 'nasha gaya maka wannan rigar aikin banza ce, domin"

"kowa yana iya zuwa kasuwa ya siyota. kai kuwa kana da abinda ba zai iya siyansa ba kome ya mallaka, don haka ka kwantar da hankalinka da uba ake ado ba da riga ba. zanje gobe na siyo maka irin wannan rigar, shi kuwa akwai lokacin da wani abu ko nace wani bala'i zai same shi wanda bashi da kudin da zai"

siyo abinda ya rasa'

a wancan lokacin tsayawa yayi yana kallonta cike da bacin ran yadda masa riga da tayi amman a yanzu

"da girma da hankali suka shige shi kunci da kuka yake yi, duk sanda ya tuna irin wadannan kalaman na lami na gori, lami ce mutum ta farko da ta fara tsanarshi saidai har yanzu ya gaza gano abinda yayi mata ta tsane shi. yasan koda ya samu zuri'a da diyarta ba zata kaunace su ba, balle shi ma baya wannan fatan,"

"ba zai taba kusantar raliya ba, to ta ina ma ta yaya?"

"surutu. raliya suka dawo da shi duniyarsa, yayi tsai yana jiyo ta tana ta habaici da zage-zage dukkan"

kalamanta ba komai bane illa tunin kalaman da mahaifiyarta ke gaya masa sanda yana yaro har ya girma. bashi da abin yi bayan neman tsari daga shaidan don kada ya tunzura shi ya aikata abinda zai sanya shi danasani a gaba.

yana jin kiran sallar magariba yayi sauri ya fice don bada farali acan masallacin ya zauna yana ta lazimi

"har aka yi sallar isha'i sannan ya nufi wani karamin gidan abinci na masu karamin karfi yaci ya koshi, ya jima a gurin yana tunane-tunane domin ya rage dare, fatansa sanda zai ce gida raliya matar jaraba tayi bacci, don haka sai wajen karfe sha daya ya nufi gidan nasa, ya tura kofar a hankali ya shiga ya mai da kofar ya rufe, kai tsaye cikin gida ya wuce ya dauro alwala domin dai yau daren juma'a ne wato ranar alhamis daran da ALLAH kanyi gaggawar amsar addu'ar bayinsa, don haka yayi alkawarin kaiwa ALLAH"

kukansa shi ma yau ya zaba masa abinda yafi zama alkhairi.

"yana tsaka da sallah ya jiyo bugun kofar raliya kamar zata balle masa kofar, abinda ya bashi mamaki biyu"

"ne, na farko kofar a bude take amman take ta dukanta kamar zata ballata, na biyu kuma me ya kawo ta dakinsa, me tazo yi masa, wadannan tambayoyin sune ke ta yawo a kwakwalwarsa, saidai ya kula ba zata bar shi yayi sallar ba idan har bai kula ta ba, domin da karfi take budun kofar, wanda yasan babu"

"makawa dukkan makota suna jiyowa, yayi kokarin yin sallama ya nufo kofar."

"ya dube ta sanda take kallonsa ta daina dukan kofar, cikin tsananin mamaki yace 'lafiya kika zo kina buga"

min kofa haka kamar zaki ballata ko kin fara hauka ne?

ta kalle shi a raine tayi wani dogon tsaki 'zuwa nayi amsar sallama domin na gaji da zaman wannan

"akurkin naka, na kula baka da zuciya domjn kare ya cinye, duk wani nau'i na walakanci da zai sanya ka sake ni nayi maka amman tamkar tiraka ma ake yi'"

"da zai iya da yanzu zai yi wa raliya saki dubu ma idan ana yi: sai dai ba zai iya bawa iyayensa kunya ba,"

"amma yau ya kamata ya nunawa raliya shi ma fa baya kaunarta ko sau daya cikin izgili yace 'wai kina zaton ina zaune dake domin kyawun fuskarki ko kyawun jikinki, ko wata dabi'a da na gani me kyau"

"agareki. ki yi sani kamar yadda kika tsane ni kika kuma tsani aurena ko don ina son ki, a'a ko daya nima"

"haka nake ji. har nawa ya linka naki ma, babu wani da namiji mai mutunci da kima da ilimi da zai so ko wani guri daya da jaka dabba irinki balle har ace ta kai ga zaman aure, WALLHI ina zama dake ne do"

biyayya ga iyayena kawai'

tayi shewa tayi dariya tana kallon cikin tsakiyar idonsa da tsananin raini da wulakanci 'ahayye wannan fa

"shi ake cewa shege yi da mai zina, kai ko ryuwarka kaya ce? ni kam zan iya duk abinda naga dama na dawo na tuba na kuma auru sabanin kai da an riga an rubuta kai shege ne babu kankara...'"

"'shut up stupid' ya daka mata wata irin gigitacciyar tsawa da ta sanyata firgita, don bata taba jin haka"

"daga gareshi.ba, ya cigaba da magana cikin bacin rai 'koda na kasance shege WALLAHI na fiki albarka da mutunci a idon kowa, dabba shashasha kiyi gorinki da fadar duk abinda kika ga dama, domin halinki daman irin na wawaye ne jahilai, amman ki sani in dai har hannuna saki yake har abada ba zaki ji daga"

gare ni ba sokuwakawai'

ya zuya da zummar komawa cikin shagon saidai riko rigarsa da ta yi ta baya ne ya sanya ya kasa ci gaba

"da tafiyar, ta rike shi katamau tana fadin 'WALLAHI

23 / 47