Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 47

87K to 90K   out of 139.6K words

don haka ko da ta idar da sallar asuba bata komawa bacci sai ta cigaba da yin lazimi har sai dan nata ya iso gidan sun gaisa sannan"

ta koma bacci ko kuma ta tashi ta kama aikace-aikacen gidan.

"Yau ma'un tana ta bashi labarin amma sam hankalinsa bai tare da ita, har ta gano wani yana damunsa"

"tace ""yayana ko baka da lafiya ne? Da sauri ya dago kai ya dubeta ""eh bana jin dadi ne ma'u"""

"Gaba daya yanayinta ya sauya zuwa damuwa ta mike ""sannu yayana me zan kawo maka?"

"""Kwantar da hankalinki na sha magani ma, ina son dai naje gurin umma ne yanzu"" ""amman dai da ni"

"zaka je ko? Ta katse shi cikin hanzari. Da sauri yace ""A'a ni kadai zan je"""

"""ALLAH yaya tsoro nake ji"""

"Yayi dan tunani yana son zuwa da ita amman ya san zuwa da ita din zai sanya su kasa samun nutsuwa,"

"ganin ba shi da mafita sai ya dube ta yace ""bari na kira miki a'ilon gidan kasa ku yi kallo, kin yarda? Da"

"sauri tace ""eh na yarda kirata, amma yaya na manta yau fa Hajiya tazo ta kawo maka kaya masu yawa nima haka, kuma tace yana gaisheka, bari na kawo maka kayan"""

"Ya san kowacce Hajiya ce, Hajiya aminansa ce mai sonshi, da sauri yace ""kinga barshi sai na dawo"

"tukunna, bari na kirawo miki ita"" ya fice da sauri."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

32

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"A can gidan umma ta shiga damuwa da jin an tura ahmad legas har tsawon watanni uku, har sai da"

"fuskarta ta nuna hakan a fili. Tace ""babu kuma wani abu da za a yi akai din dole sai kaje? Su ba su da tausayi ne ba su san kana da iyali ba?"

"Malam yayi murmushi a fili yace ""wai yaushe zaki yaye ahmad ne dije? Abin ya basu dariya ita da Ahmad"

"din gaba daya, tace au haka ma zaka ce malam? Baka tunanin nisan da zai yi?"

"Meye Abin nisa ga Namiji don ya tafi legas, yanzu idan ya samu aiki a can ba zaki bari yayi ba kenan?"

"Tayi ajiyar zuciya ""in sha ALLAH ko zai samu aiki a nan zai samu, malam ka dinga yin irin tunanina mana"""

"""Ai tunanin kowa daban ne, na dai san ba za a cinye miki shi a can ba, yanda yaje guda haka zai dawo"

"guda, ki yi masa addu'a da sanya albarka kawai"""

"Ta kada kai ""shike nan ALLAH ya tsare yanzu yaushe ne tafiyar?"

"Ahmad ya gyara zama ""wajen jibi suka ce insha ALLAHU, ina tunanin kawo ma'u gidan ma gobe zan yi"

"kafin na dawo"""

"""Gidan kuma a kan me? Malam ya katse shi da sauri. ""A'a hakan ba zai iyu ba, ka barta a dakinta ta saba"

"da aure. Yanzu ta zama matar aure dole ta koyi juriya irin ta mace mai aure"""

"Yayi dan jimkamar ba zai yi magana ba, sai ya daure yace ""gidan zai yi mata girma ne, gashi tana dan"

"tsoro kuma akwai kuruciya har yanzu tare da ita, ina ganin kamar zamanta a nan zai fi tunda kwanakin da yawa."

"Umma kam tana bayan ra'ayin Ahmad amma ta gaza cewa komai, don kada malam yayi zaton hada baki"

"suka yi. Amma a cikin ranta tana addu'ar ALLAH ya sanya ya amince din, hakan ne kadai mafita."

"Malam yayi jim yace ""shi kenan tunda kana ganin hakan ne mafita, amma da ace tana da karamar kanwa"

"da ita za a kai mata ta zauna har ka dawo"""

"Cikin zolaya umma tace ""ko za a kai mata amina?"

"""Ai ba kanwarta bace yayarta ce, kuma idan taje gidan shiririta da shashanci za a yi tayi"""

"_ko kuma ta bata min tarbiyyar ma:u ba_ ahmad ya ayyana hakan a cikin ransa, don sai da gabansa ya"

"fadi da yaji maganar da farko, dukkan abinda zai hada su da da iyakinsu sam bai kaunarsa."

"Bai jima a gidan ba yayi sallama da su, domin hankalinsa yana kan ma'u da ya baro, don ma akwai 'yan"

"kallo a gidan ya baro su, don haka ya tada baur dinsa ya nufi gidan."

Yana isa ya hango kofar gidan an sakayo ta sai dai gurin bakikkirin kasancewar an dauke wutar nepa. Ya

kafe babur din a gefe ya sauka domin ya tura kofar ya shiga ya tabbatar babu wani abu akan hanya a cikin soron.

"Sai DA ya isa cikin soron ya fara kokarin kunna 'yar karamar tocilan din dake hannunsa, daidai lokacin"

yaji wata uwar kara.

"Ya rude ya fara kallon inda karar ke fitowa, a cikin soron ne daga gefe, kuma muryar ma'un ce. Cikin"

"sauri yace ""ke mene ne ma'u? Nine Ahmad"""

Tocilan din dake hannunsa wacce ke kokarin kunnawa ta fadi saboda damkar da tayi masa tana

shisshikar kuka kamar zata shide.

"Cikin firgici yace ""ke mene ne ya faru?"

"Tana kankame a jikinsa take fadin ""WALLAHI kamar tafiya ake yi a cikin gidan na kasa zama"""

"Ina a'ilon take? Sai ya fashe da kuka ""ana dauke wuta kaninta sale yazo ya kirata, nayi ta magiyar ta"

"tsaya amma taki, tace wai dukanta za a yi, shi ne na buya a bayan gado, sai na dinga jin tafiya shine na gudo na dawo soro na boye"" cikin kuka take bayanin ya kasa cewa komai, domin rikon data yi masa ta saukar masa da kasala da wani irin shauki dakyar ya dake yace ""shike nan sake ni na shigo da babur dina"

"babu komai tsorata kawai kika yi"""

"Ta ki sakinsa ta kuma ki yin magana har lokacin jikinta yana rawa, ya kara kwantar da murya. ""Bari na"

"dauko tocilan din"" ta dan sake shi amma tana gabansa ya sunkuya ya fara laluben cocilan din har ya samu ya kunnata ya haska fuskarta."

"Dariya ta kama shi gani tayi miyau da majina, ya kau da kai yana dariya. ""Ho ma'u! Halinki sai ke. Bari na"

"shigo da babur din to"""

"Ta bishi da sauri a baya. Ya waigo. ""Ina kuma zaki?"""

"""Ni fa tsoro nake ji, ALLAH kuwa yaya"""

"Ya mika mata tocin. ""Shikenn amshi tocin ki rike bari na shigo da shi"" haka ta tsaya ba don ta so ba, har"

"ya shigo da babur din ya shige gaba tana biye da shiba baya suna shiga aka kawo wuta, ya kalle ta yana rike da babur din har yanzu yana mata dariya. ""To gashi babu komai a cikin gidan, matsoraciya kawai"""

Ita dai bata ce komai ba har ya kafe babur din ya dauki buta ya nufi bandaki sai ta tashi da sauri har da

"dan gudu-gudunta, ya waigo da sauri ""malama bandakin zaki bini kuma?"

"""A'a"" ta fada da sauri, ya kuma fashewa da dariya. ""Kinga don ALLAH ki kwantar da hankalinki ki yi ta"

"addu'a babu komai, bari na fito"""

Da haka ya samu ya shiga bandakin yana cigaba da dariya a zuciyarsa.

"Daren ranar tana gado shi yana kasa a kwance, ta kudundune kamar za a shigo a dauke ta. Tana"

"kwanciya kuma bacci ya dauke ta, ya dinga kallonta yana dariya. Ma'u akwai kuruciya da shiririta. Yana son yayi maganar tafiyarsa da ita amma yanda take a firgicen nan ya san ba zai sami komai a gare ta ba don haka ya kyale ta."

"Da safe bai jima da fita ba ya dawo, domin manajan gidan man yace su dawo gida kowa yayi shiri gobe"

tafiya. Sannan ya dan basu kudaden da kowa zai barwa iyalinsa.

"Ma'u an mike akan kujera ana ta karatun, ALLAH ya sanya ta kammala aikinta gaba daya. Ta jiyo"

"sallamarsa ta dago da mamaki tana kallon kofar dakin kafin ta mike da sauri ta leko, shi ne din kuwa. Da mamaki tace ""yaya Ahmad yau har ka dawo da wuri haka?"""

"Ya kada kai 'ban yi aiki bane na dawo na yi shirin tafiya ne"" 'tafiya kuma? Ta tambaye shi da sauri. Kin ga"

"shiga ciki mu zauna nayi miki bayani"" babu musu ta koma ta zauna shi ma ya sami guri ya zauna ya fara yi mata bayanin dalilin tafiyar har ya kai karshen bayanin."

"Ta yi shiru da damuwa kamar zata fasa kuka. ""Amman yaya ba zan iya zama ni kadai a gidan nan ba, ka"

"tafi da ni can din don ALLAH"""

"Ya kada kai. ""A'a ba zan je da ke ba, a nan zaki zauna ke fa matar aure ce, bai kamata ki dinga yawo ko"

"ina ba, abinda ba wani jimawa zanyi ba, da rana sai kiyi ta wasa da su a'ilo, idan kuma dare yayi sai ki kulle gidanki ki sa sakata babu wanda zai shigo ai"""

"Ta dafe kirji ""na shiga uku! Don ALLAH ka yi hakuri WALLAHI ba zan iya kwana ni kadai ba, sai dai idan ka"

"yarda na dinga zuwa gidan su mairon gidan kasa na kwana"""

"Ya bata ran wasa. ""Gidan kuma fa ya kwana shi kadai ha kowa? Ban yarda ba, gaskiya dole ki zauna ke"

"daya."""

Ta yi shiru ta rasa me ma zata ce amman dai idonta ya fara zubo da hawaye. Da sauri ya mike yana fadin.

"""Lalala! Kada ki yi kuka 'yar amaryata tsokanarki nake yi, tashi ma shirya kayanki mu tafi gidansu umma"

"a can zaki zauna"""

"Ta mike ta daka wani uban tsalle tana ihu. Ya bude baki yana kallonta ""lallai yarinya zaki ja a fasa"" ta"

"gimtse murnar ""yi hakuri yaya ma daina, bari naje naga fara hada kayan"""

"Ko a jikinta bata jin komai akan tafiyarsa don farin ciki, domin damar komawarta ga ummanta tafi komai"

yi mata dadi.

"Yana kallonta ta fice, ya koma ya fada kujera ya lumshe idanunsa, bai son rabuwa da matarshi a yanzu,"

"zaman da suka yi da ita na watannin nan ya shaku da ita fiye da tsammaninsa, ko babu komai yakan so sokwancinta don ya dinga cin dariya kawai,"

"A motar haya taxi suka tafi, domin kayan DA yayi wa siyayya na kayan abinci da kuma kayan sawar ma'u"

suna da yawa.

Ma'u kuwa murna take ta faman yi kamar zata shide don dadi. Shi dai kallonta kawai yake yi ransa babu

dadi.

"A can gidan su umma ma haka ta dinga murna, tana jin kamar za a sanyata a gidan aljanna, umma tana"

"kallonta tana murmushi, shi kuma ji yake kamar kada ya tafi."

A nan yaci abinci har wajen karfe goma bai bar gidan ba gidan ba sai da malam ya masa magana.

"""Ahmad ya kamata kaje ka kwanta haka, domin ka sami damar tashi da wuri tunda kace sammako zaka yi"""

"Yayi shiru da damuwa sai yake ji kamar ya rabu da su kenan har abada. Faduwar gabanshi ta karu,"

idonshi ya taru da kwallah.

"Malam yayi murmushi na son basar dashi yace ""haba Ahmadu sai kace wani karamin yaro, don ALLAH ka"

"kwantar da hankalinka."""

"Sai a lokacin jikin ma'un yayi sanyi, ta zubawa ahmad ido wanda kansa ke kasa. Ita kanta umma kau da"

kai tayi gefe don bata son ganin fuskar dan nata.

"Cikin rawar baki ahmad yace ""baba naji gabana yana ta faduwa ina zaton babu alkhairi a tafiyar nan"

"tawa gwara ma na fasa na samu wani aikin"""

"""Kul na kuma jin wannan maganar Ahmadu. Tun ranar da ka fada min maganar tafiyar na sanar da 'yan"

"uwanka muka yi ta addu'a. Sai kuma da aski yazo gaban goshi sannan zaka ce ka fasa? Ban amince da hakan ba sam, kaje ka yiwa mamanka Hajiya Amina sallama tukunna."

"""Naje daga can muka yo nan. Tace tana gaishe ku"""

"""Muna amsawa, maza tashi ka wuce"""

"Ya mike yana kallon ummansa har lokacin kanta yana kallon wani sashi yace ""umma zan wuce"" sai a"

"lokacin ta waigo idonta ya cika da kwalla yace ""ALLAH ya kiyaye hanya. Ka kula da kanka Ahmad, ka kula da addininka da matsayinka na musulmi a duk inda ka tsinci kanka. ALLAH yayi maka albarka"""

Kalmarta ta karshe tafi komai dadi a gareshi. Yanzu da a gidan marayu ya tashi waye zai dinga sanya

"masa albarka kamar haka? Yayi kokarin goge kwallar da ta zubo masa yana fadin ""amin umma na gode, baba na tafi"""

"""ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya, ma dinga gaisawa ko a wayar yayanku ne"""

"Ma'u tana zaune tamkar an dasa ta gaba daya murnarta ta koma ciki, sai zare ido take yi. Sai yanzu take"

"jin ciwon tafiyar yayan nata. Kalamanshi sun sanyayar mata da jiki har kwalla ya ciko idanunta. Ummanta ta dubeta tace ""ba zaki je ku yi sallama ba ne?"

"Ta kalle shi DA sauri, maganar ummanta ta sanya ta mikewa da sauri babu shiri don bin bayan ahmad da"

ya fice da sauri yana goge idonsa.

Cikin gaggawa ta bishi don ganin ya nufi soro kai tsaye da sauri.

"""Yaya ahmad!"" Ta kwalla masa kira sanda ta iso soron taga zai fice. Ya tsaya gami da waigowa ya kalleta."

"""Ma'u yaya aka yi ne? Cikin dakiya da kokarin boye damuwa yake maganar. ""Yaya bamu yi sallama ba zaka tafi, naga kamar ranka ya baci. Don ALLAH ka yi hakuri idan nayi maka laifi"""

Yayi murmushi da jin dadi. Lallai ma'unsa ta fara samun hankali DA nutsuwa. Ya isa kusa da ita ya riko

"hannunta yana jin kamar ya rungumo ta jikinsa, amma gudun abinda zai faru ya sanya ya dake, cikin dakiyar zuciya yace ""ma'u baki yi min komai ba, amma ina jin kewa na kadaicin rabuwa da ku. Na ga ke kamar murna kike yi domin kin dawo gidansu umman ko?"

"Ta sunkuyar da kai kunya ta rufe ta, amma sai ta girgiza kanta alamar a'a ba haka ba ne. Ya kura mata ido"

"cikin hasken da ya ratso soron yana cigaba da magana. ""Ki dinga min addu'a ma'u, naso kafin na tafi ma na sai miki waya ko gaisawa mu dinga yi, amman ba ni da kudi, kudin da na samu na yiwa umma siyayya na sanya miki wasu kudin cikin kayanki, idan kina bukatar wani abu ki dinga siya, kada ki tambayi umma"

"ko baba kin ji ko"""

Ya janye hannunsa daga cikin nata yana dan ja da baya yace 'sai na dawo ma'una' ya juya da sauri ya fice.

Ma'u ta kurawa kofar ido kamar ta bishi.

"Sai a yanzu take jin kaunar mijin nata, can a waje ta jiyo muryarsa suna gaisawa da Musa har sun dan"

"tsaya suna hira ma. Tayi tsaye tana sauraron muryarsa. Sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Haka ta koma gidan salo-salo babu kwari balle karsashi a jikinta. Sanda ta isa dakin sai ta tadda babanta tuni ya tafi dakinshi, ummanta tana can da alama hirarsu suke yi ma. Ta nufi gadon da take mayatar kauna da mafarki ta kwanta, ta nannade jikinta ta lumshe ido, a hankali irin hirarrakin da suke yi ita da yayanta kafin su kwanta bacci suka dinga fado mata, sai ga idonta ya kekashe ta kasa yin barci har dare"

ya fara rabawa.

"Ummanta ta dawo ta kwanta a gabanta, sai dai lumshe ido kawai tayi har bacci ya dauke umman ma."

"Tana ta ayyanawa a ranta ko wane hali yayan nata ke ciki yanzu, ko ya kwanta a kan gadon ko a kan leda"

ya kwanta? Dakyar dai bacci ya lallabo ya saceta tana cikin tunane-tunanen yayan nata.

Da safe gidan nasu cike yake da yayyanta dakan shigo su gai da iyayansu kafin su wuce gurin aiki.

"Yawanci sai sun ci dumame na gado a gidan sannan suke tafiya. Hakan ya sanya ta dan ji dadi, nan aka yi ta hira da cafta sannan suka watse."

"Shi ma malam ya nufi kasuwa, ummanta ta mike yace ""maza ta tashi ta fara gyaran gida"" haka nan ta"

"wuni suku-suku babu walwala a tattare da ita, ga shi yini tayi yin aiki, sai can yamma ta samu kanta a hannun umma, ta dauko littafi ta fara karantawa. Wannan ya dan rage mata damuwa."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

33

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Ga su ahmad sai dare suka sami isa garin legas. Kai tsaye gidan da za su sauka suka isa, da yake a motar"

kamfaninsu suka tafi. Gida ne irin jinin legas amman babu laifi yana dw kyau. Kowa da dakinsa daban aka ba shi. Dakyar suka iya cin dan abinci suka kwanta baccin gajiya.

Washe gari da safe kuma aka kwashe su a motar aka kaisu sabon gidan man mai suna 'YAN LRMAN

PETROLEUM & 10 dayake duk sunan gidajen man nasa daya ne.

"Sun tarar da ma'aikatan gurin wanda a ranar zasu fara aiki, babban gidan kai ya gina wanda yafi na can,"

"kasancewar shi kadai ne da shi a legas kuma na farko a jahohin kudu, dayake yana da kishin jama'arsa HAUSAWA kusan kaso sittin na ginin duk Hausawa ne sai sauran yarbawa."

"Basu sha wahalar fara aikin ba, kasancewar an rage kudin litar da kaso biyu (2%) cikin dari (100%)"

saboda gidan man sabo ne. Hakan ya sanya aka yi ta samun masu siya.

"A wannan rana dakyar Ahmad ya samu dan lokacin yin tunanin ummanshi da ma'unsa, kodayake ma"

"lokacin da yana aikin ma yakan tuno su jefi-jefi, kuma a duk yayin da ya tuno da su sai yayi murmushi."

***

Kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa zuciyoyi na kara shiga cikin damuwa. A wannan lokaci ma'un ta

"fara fahimtar meye aure, meye miji, domin tayi nisa cikin karance-karancen, sannan umma ta ajiye kunya tana tayi mata bayanin meye aure, me ya kunsa, mene ne alfanunsa. Wannan yake sanyawa tana kara son mijinta, idan tayi kwance a gado sai tayi ta tunaninsa, burinta bai wuce ya dawo ba, musamman lokacin da Hajiya amina ta tadda ta tana karatun littafi ta siyo mata jaka guda tace a yi ta yi. A nan ma ta"

samu abubuwan karuwa kwarai da gaske.

"Takaicinta daya tunda ahmad ya tafi bata taba jin koda muryarsa ba, kullum sai dai yaya auwal ko yaya"

sani ya zo yana basu labarin yace sun yi waya da shi sun gaisa.

"Tana son tace a bata shi idan ya kira amman ba zata iya ba sam, su kuma sun kasa yin karar su bata din."

"A haka har wata har watanni biyar suka cika, zuwa lokacin ma'un ta koyi abubuwa masu dama, ta kara"

"girma ta cika ta zama budurwa domin ta cika Shekaru sha shida kenan, ga shi kullum umma sai ta bata"

"kunun daka irin na mutanen Niger <ØóÝ<ØêÝ da tukudi tun bata son sha har ya Zame mata jiki, dukkan halittarta ta kammala fitowa ta zama cikakkiyar mace."

Idan ta tuno abin da tayi wa mijinta a baya sai tayi ta dariya tana ganin wautarta.

Gaskiya Ahmad yayi kokari tsawon shekara da wata bakwai ya zauna da ita a gidansa bai yi mata komai

"ba. Ta tabbar yayan nata yana matukar kaunarta a yanzu. Sai dai abun dake dmunta bai wuce rashin dawowarsa ba a yanzu, kullum sai umma tayi mita,

30 / 47