Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 47

78K to 81K   out of 139.6K words

shara da wanke-wanke,"

"ko wanki shine keyi musu sanda yake da lokaci, sai dai yana shan fama da kuruciyar ma'u da shirmenta."

"Bata da lokacinsa domin bata san me ya dace tayi masa irin na ma'aurata ba, burinta ta Tara yara a yi"

"lido ayi 'yar carafke da 'yar gala-gala, don haka ko ya dawo suna wasa bata dainawa sai dai tace ya ya sannu da zuwa ta cigaba da wasanta, su ma yaran da yake akwai yarinta basa matsawa ko ina, idan suka yi masa sannu da zuwa sai su ci gaba da wasanninsu kawai. Sai dai ya shige daki yayi abinda zai yi yayi zamansa a cikin dakin yayi ta karance-karance ko game da wayarsa, lokaci-lokaci ya dinga lekensu sai dare ya fara yi sannan yace musu kowa ya tafi gida sai gobe kuma, wannan yafi komai yi mata dadi don haka bata da wata damuwa a ranta a yanzu, idan kaga ta samu saidai idan ta tuno makaranta da kawayenta, tasan yanzu sun yi mata nisa, tana kuma bakin cikin ace amina ce ta zo ta daya domin 'yar tsama suke yi kwarai da gaske, wannan ne kadai yake tayar mata da hankali, wani lokaci idan ta tuno hakan har kuka take yi a daki musamman idan 'yan wasan nata suka tafi makaranta basu shigo ba, shi"

"ma yayan nata ya tafi aiki sai tayi ta jin kawaici da kadaici yana baibayeta, kamar ta gudu ta bar gidan."

Yau tun da sassafe ya kammala girkin ya zuba mata a cikin flask ya rufe har ya kammala shirinsa tana

"gindin TV tana kallon tashar NTA, muhawara ce ake yi da daliban makarantarsu da na wata"

"makaranta, cikin harshen turanci, tana jin kamar ta tsalle ta fada cikin tibin, idan anyi tambayar da yan makarantarsu suka kasa amsawa kuma ita ta sani sai tayi caraf tace ""dalla kaza ne kuce kaza"""

"A haka ya iske ta tsahon zamani yana kallonta bata san ya zo ba, tausayinta ya kama shi, ma'u tana son"

"karatu kwarai da gaske shi ma yana son tayi karatun saidai yana da tsananin kishi ba zai taba yadda ace matarsa tana fita makaranta kullum ba, dama dai ace sai da ta kammala karatunta aka yi aurensu. da yaga bata da niyyar dawowa hankalinta sai ya Kira sunanta."

"Ta waigo da sauri tace ""La ya ya har ka gama shiri, zo don ALLAH kaga wadannan sokwaye sun kasa amsa"

"tambayoyi mafi sauki, kuma fa seniors dinmu ne a school"" yayi murmushi yace ""Nana ni da nake sauri"

"zan tafi aiki ina nake da lokacin tsayawa kallo, amshi nan"" ya mika mata kudin. Ta sanya hannu ta amsa"

"yaci gaba da magana ""zan wuce sai na dawo akwai abinci a flask, bana son barna da rawar kai kada ki lalata komai kin ji ko? Idan kuma an dauke wuta ki kashe kayan kallon duka don kada a dawo da wutar ta"

"lalace"""

"Ta amsa da to tana ci gaba da kallonta, har ya kai bakin kofa bai ji tace sai ka dawo yaya ba, ya waiga ya"

"kalleta yace 'yau babu a dawo lafiya ma kanwata' da sauri yace ""La! Na manta.ihuya a dawo lafiya"" tana fadin haka ta maida kanta gurin kalloiya'Yayi dariya ya fice, bai jima da fita ba kuma nepa suka dauke wuta, bakin ciki kamar ya kashe ta domin ta so taga karshen wasan, amma ya ta iya sai ta hakura ta koma kan kujera ta kwanta, ta fara tunane-tunanen duniya, kwatsam yayarta kuma kishiyarta raliya ta fado mata, sai taji gaba daya ranta ya baci, sai dai abindake daure mata kai bai wuce rashin zuwa wajen raliyar da yaya Ahmad ke yi ba, ko maganarta ba yayi sam, Abin yana daure mata kai, tana son ta"

"tamabaye shi amman kishi da haushin raliyar ya hanata, don haka ta bar abin cikin ranta."

"Tana kwance tana sakawa da kwancewa har kawayen wasan nata suka fara shigowa, ta mike ta fita aka"

"fara lido din. A'ilo daya daga cikin yaran ta kalleta tace ""wai ke ma'u ba kya yin sabon girki ne kullum saidai muga kin debo abinci a flask? Ma'u ta tabe baki da damuwa ""ban iya girkin ba, yaya ne yake yi ya"

"zuba a cikin flask"""

"A'ilo tace ""cabdijan to idan ba kya jagwalgwalawa yaya za a yi ki iya, kin ganni ban kai girman ki ba har"

"wake da shinkafa nake dafawa a risho ba ma a murhu ba"""

"Mamaki ya kama ma'u tace ""ke a'ilo ko ni da na girme ki ummana bata ba ni girki sai tace kazanta ne,"

"saidai kawai na iza mata wuta amman kice ke har wani girki ake ba ki shekararki nawa duka? A'ilo ta tafa hannu ta doki cinya ""shekara ta sha biyu amma WALLAHI ina girki tambayi sale kanina ma idan ya shigo"""

"Sai ga sale ya shigo da gudu kamar ya san Neman sa ake yi, a'ilo tace ""yauwa sale zo, don ALLAH bana"

yiwa ummanmu girki?

"Sale ya tsaya yana haki ""kina yi mana rannan har dan wake kika yi mana"""

"Ma'u ta dafe kirji ""danwake lallai kin iya girki daman ina son na iya, don ALLAH yaya ake yi? A'ilo tayi"

"murmushi tace ""da akwai fulawa ne da sai na nuna miki yadda ake yi"" ma'u tace ""Bari na duba inda yake ajiye kayan abincin nasa ALLAH ya sanya da fulawar, daman na gaji da cin shinkafa da miya ko dafaduka, shike nan fa abinda ya iya'"

Ta nufi dakin ta duba ga rashin sa'a ba ta tadda fulawa amman sai tace ga kudi a siyo gwangwani uku na

"fulawa su kwaba. Dadi ya cika yaran suna murna yau za su ci girkin amarya, ihu da bidiri suke yi tamkar ranar sallah. Nan dai sale ya fella da gudu ya siyo fulawa, aka Kwana aka kunna risho aka fara kokarin saka danwake gabadaya aka duru a kicin din su kusan goma. A'ilo ce a ganan risho, tun ruwan bai tafasa ba aka fara saka danwake, duk sanya daya sai an yi ihu da tafi, a haka aka kammala sakawa aka koma"

gefe ana jiran ya tafasa.

"Gaba daya danwaken da ruwan ya hadu ya cakude, a haka aka fara kokarin saukewa, an duba babu"

"tsumman da za a sauke, don haka ma'u tace bari ta sauke da bakin zaninta, ta kama tana kokarin saukewa ashe zanin ya laso wuta, zafin wutar da ya tabo ta ya sanya ta fasa ihu ta saki tukunyar da zaninta da ya kama da wuta, nan fa aka yi waje ana ihu domin ruwan danwaken ya fadi a kasa ya"

fallatsawa kowa.

"Zanin ma'u ya cigaba da ci su kuma suna ta ihu ""Gobara! Gobara!! "" har ya fara laso kayan kicin din."

"Kamar an jefoshi Ahmad ya shigo a gigice jin ihunsu, ya hango abindake faruwa ya kalli ma'u dake tsaye"

"tana ihu daga ita sai siket, duk sai ya dimauce ya ma rasa me zai yi, can dabara ta fado masa ya dauko"

"wani omo da ruwa ya kada ya nufi kicin din da gudu ya fara watsawa, dakyar ya samu ta mutu, ya dawo da baya ya tsaya yana haki."

"Sai kuma suka kama ihu wai wutar ta mutu, takaici ya isheshi ya nufe su a fusace ya fara duka, yaran"

"suka yi waje a firgice domin abin ya basu mamaki, domin sun san duk irin ihun da suka yi baya ce musu ko kala, amman yau sai ga shi har da duka."

"Ya koma kan ma'u ya zabga mata mari ya kuma zabga mata, ta fasa ihu ta rike kunci, maimakon ta ba shi"

"tausayi sai ma kuluwa da yayi ya hauta da bala'i, sai da yayi iyakacin son ransa sannan ya nufi kicin din ya fara gyarawa."

"Ranar dai har dare yana bala'i da masifar da bat a san yana da ita ba, tayi kum a daki sai kuka, washe gari"

"bai je ko ina ba, ya kuma hana kowa shigowa gidan, duk yaron da ya zo sai ya fatattake shi ya fita da gudu. Don haka a daki ta wuni tana kuka, saidai ta gama saka abinda zata yi."

Lokacin da ya fita sallar isha'i ta dauko kayanta data kulle a dankwali ta nufi hanyar Soto tana tafe a

"firgice cike da tsoro domin bata son kowa ya san inda zata gudu, ta gaji da zaman gidan tunda ai ba birsina ba ce ba."

"Ta fito ta janyo kofar gidan a hankali, ta bi gefen duhuwar dake kofar gidan ta fara sauri tana waige don"

bata son wani ya gan ta.

*

*

*

"ALLAH sarki Ahmad Raliya ta gudu ta bar ka saboda tana kin ka, ga Asma'u ma ta kulle 'yan kayanta ta"

fece saboda ka fusata ta. ALLAH ga bawanka.















DA ME AKE ADO?

28

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Ma'u tana tafe cikin duhuwa tana ta sauri, burinta tayi nisa da gidan, cikin ranta tana saka ba zata je"

"gidan kowa cikin yayyenta ba, ko gidan umma ba zata ba, domin za su iya dawo da ita gidan yaya Ahmad, shi kuma ya cigaba da dukan ta yana kulle ta cikin gidan ita daya kamar mayya."

"Bata ankara ba tayi karo da wani mutum, kayanta suka zube, tayi taga-taga kamar zata fadi, ALLAH dai"

"ya sanya bata fadi din ba, mutumin ya zabga salati yana kokarin bata hakuri, sai gabanta ya hau bugawa domin muryar yayan nata ne, hakan ya sanya ta gimtse bakinta bata ce komai ba, ta suri kullin kayanta ta wuce shi DA sauri."

"Cikin ikon ALLAH aka kawo wuta daidai lokacin, Ahmad dake ta bata hakuri ya dan bita da kallo da"

"mamakin jin wace ce ya buge din bata ce komai ba, har ya ayyana a cikin ranshi ko kurma ce sai kuma ya hango kamar ma'unsa ce, mamakinsa ya kara karuwa ganin tana ta sauri tayi gaba, ya fara kwalla nata kira. ""Ma'u! Ma'u!! Ma'u!!!"""

"Jikin ma'u ya dauki rawa saboda tsoro ya gama shigarta ta tsaya cak, ta kasa matsawa daga inda take, ta"

"kuma kasa cigaba da tafiya har ya isa inda take tsaye, ya leka fuskarta don kara tabbatarwa ita ce, hankalinsa ya tashi da ya tabbatar ita ce din."

"Har lokacin ta kasa magana sai idonta dake zub da hawayen tsoro, kamar ya kara yin magana sai kuma"

"ya fasa ya kama hannunta kawai ya fara tafiya. Asma'un ta fara binsa tana hawaye. Shi kenan ta shiga uku, ta san yau mai raba ta DA yaya Ahmad sai dai ALLAH. ga shi gidan babu kowa babu mai kwatar ta."

Haka tayi ta binsa zaro-zaro tana rungume da kayan nata har suka shiga cikin gidan.

"Suna shiga ya mai da sakata ya datse, hakan ya kuma kada mata ciki ta fashe da kuka sosai, ya kalle ta"

"har lokacin hannunta yana cikin nasa bai ce mata komai ba sai da suka dangana da cikin dakinsu. Ya zaunar da ita gefen kujera yana fadin ""ina zuwa bari na zo"" ya fice ya nufi daya dakin."

"Da sauri ya mike ta fara zagaya dakin tana kuka, hannunta bisa kanta ta fara magiya. ""Don ALLAH yaya"

"kayi hakuri WALLAHI ina daina ba zan kuma ba"""

"Daidai lokacin DA ya shigo DA zabgegiyar belt sai ta kuma zabura ta fara ihu da karfi, ya sanya hannu bisa"

"lebensa yana fadin ""shisshi! Ki daina kuka ma'u ba dukan ki zan yi ba, ma dauko ta ne domin ku dake ni ki rama dukan da na yi miki, yanzu ma gano illar abinda na aikata, amshi ki rama ma'u"""

"Ya mika mata belt din, mamaki ya cikata, ta fara ja da baya domin bata yarda har zuciyarshi abinda yake"

"nufi ba kenen, ta fi yarda yana yin hakan ne don ya samu damar kama ta kawai."

"Ganin tana ja da baya ya sanya ya cafko hannunta gam cikin nasa, sai ta ta fara kara jikinta yana rawa, ya"

"damka mata belt din yana fadin ""da gaske nake ma'u ba dukanki zan yi ba, ki rama dukan da nayi miki in dai har zaki daina yunkurin guduwa ki bar ni ma'u"""

"Kalamansa suka sanya ta yin saroro tana kallon shi rike da belt din a hannunta, duk da karancin"

"shekarunta maganar yayan nata ya girgizata. Ya sakar mata hannu da belt din, ya juya ya zauna akan kujera yana mai cigaba da kallonta."

"""Ki daina kuka ma'u, ki rama don ALLAH gani na zauna yanda zaki iya dukana, bana fatan ki kara"

"yunkurin guduwa, idan kika gudu na shiga uku, ban san inda zan sanya rayuwata ba, ko baki san raliya ma guduwa tayi ta bar ni da aurena ba?"

"Ta dan zaro ido tana mamakin abinda yace, ta daure tace ""da gaske raliya ta gudu, ita ma dukanta kayi ta"

gudu yaya?

"Yanda tayi maganar sai Abun ya ba shi dariya, amman ya dake yace ""ban dake ta ba, kin san halin raliya"

"ban isa ma na taba ta ba balle duka, ban so kema ki gudu, idan kika gudu kowa ba zai yafe min ba har ummata mai sona. Ki rama don na tabbatar kin huce kin ji ma'u"""

"Tayi murmushi zuwa yanzu hankalinta ya dan kwanta, ta isa gabansa ta durkusa ta mika masa belt din"

"tana fadin ""yaya ba zan iya dukanka ba, na san ni ce nayi laifin ma, kayi hakuri ba zan kara ba"""

"Ranshi yayi haske yace ""shi kenan na hakura, amma ki min alkawarin ba zaki kara yunkurin guduwa ki"

"bar ni ba"""

"""ALLAH yaya ba zan kara ba, na daina ba zan yi maka irin abinda raliya tayi maka ba,"""

"""Alkawari na biyu ne mai girma ma'u, ki yi kokarin rikeshi"" ta daga kai alamar to tana murmushi, ya mike"

"tsaye. ""Shikenan kin huce yanzu me kike so na dafa miki kici ki kwanta"""

"Ta turo baki da shagwaba. ""Yaya kaine kace na dinga yin Abu irin na matar aure, amma kaki bari na koyi"

"girki, daman umma ma bata koya mini nakasai tace jagwalgwalo nake yi wai, kuma matan aure ai sune suke yin girkinsu da kansu na gani"" yayi murmushi 'ma'u ko buhun shiririta' ya kamo hannunta."

"""Zan fara koya miki abinci daga yau, amman ba za ki fara yin girki ba har sai kin iya sosai, kin yarda da"

hakan?

"""Eh na yarda, sai randa kace nayi zan yi, ba zan kara saba maka ba' ta fada cikin hanzari. ""Shikenan muje"

me zamu dafa?

"Tana biye da shi sai da suka nufi kicin din tace ""danmalele da wainar fulawa mai manja"""

"""Wannan duk ba abinci ba ne, kayan kwadayi ne kuma ni ban iya su ba. Yanzu dare yayi indomie zamu"

"dafa da albasa mu ci"" ya bata amsa. ""Ai ita ma tana da dadi yaya, amman ni na iya, ita fa ba sai an sanya ta a wuta ba, idan aka jika ta DA ruwa ta dade sai ka ga ta yi laushi sai aci"""

Ya kalle ta DA sauri DA mamaki sai da ya fara dauko indomie din daga cikin kwali a kicin din sannan yace

"""waye yace miki haka ake dafa indomie? Ta sami kujera ta zauna tana dariya ganin yanda ya saki baki"

"yana kallonta. Tace ""a makarantar boarding haka muke yi tunda ba a barinmu kunna risho, kuma a kicin ma ba a barinmu sai siniyoyi kawai suke bari"""

"""To ba haka ake yi ba, zan koya miki yanzu ki ga yanda ake yi"""

"Ya fara kokarin bude indomie din yana zubawa a cikin tukunya, ya dauko albasa ya yanka ya zuba a kai."

Tana kallonshi ya kammala hadawa ya zuba akan ruwan zafin dake kan risho ya juya ya rufe bayan 'yan mintuna ya bude.

"Ta rike baki ""wai har ta daho kenan yaya? Lallai ta fi sauri a haka, da a makaranta ne sai ta wuni a jike """

"Haka dai ta dinga surutu ratata yana jin ta kawai yana murmushi har ya juye a faranti suka nufi daki,"

sanda suka zauna aka fara ci din ma surutun ta cigaba da yi har lokacin sai dai yayi murmushi sai dai wata tambayar data yi masa ce ta sanya shi saurin dago kai da sauri ya kalleta.

"""Yaya wai ya aka yi ka fasa auren aunty ummi ka auri raliya ne, bayan na san aunty ummi tana matukar"

"sonka, me ya sa ka guje ta ja auri raliya? Ta kuma tsare shi DA ido tana jiran ya bata amsa, jikinsa yayi"

"sanyi hankalinsa yayi matukar tashi, ta tsokano masa mikin dake ranshi wanda yayi zaton ya warke ashe har yanzu da saura."

"""Yaya baka ce komai ba don ALLAH ka gaya min"" yayi ajiyar zuciya yana son ya shirya abinda gaya mata,"

sannan ya fara magana.

"""Iyayen ummi ne suka ce ba zata aure ni ba domin ba ni da kowa..."""

"""Waye yace musu baka da kowa? Ba gani da umma da malam da yaya auwal da su yaya sani ba, me yasa"

baka gaya musu haka ba? Ta katse shi DA sauri.

"Yayi murmushi yace ""haka ne Ina jin ummi ta gaji da sona ne shi ya sanya ta yarda da abinda iyayenta"

"suka ce akaina"" ya fada idonshi ya fara sauya kala juwa jawur."

"Tausayinsa ya rufe ma'u ganin yadda kamanninsa lokaci guda suka sauya ta bata fuska tace ""daman an"

"ce ai mata mayaudara ne, wata kila wani mai kudi ta gani shi ya sanya tace bata sonka, amma yaya DA aunty ummi tace bata sonka ai da ka nemi wata ba raliya ba, kasan raliya fa 'yar iska ce amman ka aure ta"""

"Ya shiga uku yau da tambayar ma'u, amma yaya ya iya dole ya bata amsa kada tayi fishi ta gudu ta bar"

"shi, ba tare da yin tunani ba yace ""ba ina sonta bane, ba kuma ni nace a aura min ita ba, su baba ne suka yi min auren dole da ita, bana son ta"""

"""Auren dole yaya? Da girmanka suka yi maka auren dole ka yarda? Kaga ita da bata sonka AI ta gudu, da"

"ka sani kai ma ka gudu"""

"""Gwara dai da ban gudu ba domin gudun nawa zai iya bata ran mutane da yawa. Kuma idan ba gudu ban"

"san gidan wa zani ba, wata kila ma ran umma da baba ya fadi su tsine min. Shi da nagari duk abinda iyayensa suka yi masa amsa yake yi sai ya ga alkhairin a gaba"""

"Ta kada kai alamar gamsuwa da abinda yace tana fadin ""haka ne, shi ya sa ma da aka yi mun auren dole"

"da kai nace zan zauna don kada su umma su tsine min"" ya waro ido da fargaba yace ""ma'u auren dole aka yi miki ba kya sona ashe? Ta rufe bakinta da sauri ta dan ja da baya.

27 / 47