Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 47

93K to 96K   out of 139.6K words

kayan DA yayan nata ya kawo mata tsaraba, dukkan su kananan kaya ne sai kuma rigunan"

"bacci, sai kuma kayan gyaran gashi da mayuka kala-kala, komai mai kyau me ta san yayan nata Dan gayu ne. Amma bata yi tsammanin ya iya zabe kamar haka ba sai yanzu da idanunta suka gane mata."

"Ta ma rasa wanne kaya ya kamata ta sanya daga cikin kayan DA yayan nata ya kawo mata tsarabarsu,"

domin kowanne a cikinsu yana da tsananin kyau.

"Daga karshe dai ruwan idonta ya kare a kan wani dogon siket mai roba, da alama idan aka sanya shi zai"

"kama mutum, zai kama jiki sosai. Rigarsa kuma mai kama jiki ce kwarai da gaske, ruwan hoda ce sai dai akwai zanen fulawoyi ruwan golden a jikinsu. Ko da ta saka kayan sun anshe ta kwarai da gaske."

"Kitson kanta shuku ne don haka ya dace da kwalliyarta, kasancewar tana da gashi tayi dauri da wani"

"gyale, kitsonta ya fito ta tsakiya ya sauka a bayanta."

Ta sanya wani dogon dankunne wanda shi ma yana cikin kayan da yayanta ya kawo mata a cikin tsaraba.

"Bayan ta gama tsantsara kwalliyarta ta koma falo ta hakimce tana kallonta, domin an kawo wutar nepa a"

lokacin.

"Sai bayan sallar magriba ahmad ya shigo gidan, domin ya biya ta gurin abokinsa Ishaq sun gaisa sannan"

yayi yan biye-biyensa dai.

Bata damu ba bayan kallo da take yi 'yan matan unguwar su A'ilo suna ta shigowa suna gaisawa da

murnar dawowarsu.

Kai tsaye falonsu ya nufa domin can ya jiyo motsinta.

Bai fita da babur dinsa ba Domin ya san shi ma yana bukatar gyara sai washe gari zai kai shi a duba shi

tukunna.

Haka ya sanya Ma'u bata san ya dawo ba sai da ya shigo da sallamarsa. Ta dago kanta da Sauri ta kalleta

"shi. Sai ta mike daga zaunen da take ta nufe shi tana fadin ""sannu da zuwa yayana"" ta amshi kayan dake hannunsa ta nufi cikin faki domin ta ajiye. Ahmad ya bita DA kallo komai a jikinta juyawa yake yi. Ya bude"

baki sai kace wani sauna. _Anya kuwa wannan ma'unsa ce ba sauya masa ita aka yi ba?_

"Bata san yana yi ba har ya isa ya zauna duk jikinsa yayi sanyi, abinda yake ji game da ita ya dinga dawo"

"masa, ko a can legas yayi fama da irin wannan matsalar, sai dai ya dinga dagewa da yawan addu'a don kada shaidan yayi galaba a kansa. Komai na ma'u ya sauya cikin dan wannan lokaci."

"Koda yake tun kafin ya tafi ya fara fuskantar wasu 'yan sauye-sauye a tare da ita, amman ba su kai na"

yanzun ba.

Ta mike ta nufi kicin ya dauko babban faranti ta juye musu abincin da yayo musu take away dinsa ta

"kawo gabanshi ta ajiye. ""Yaya sauko mu ci abinci, ni fa yunwa nake ji"" ya sauko yana fadin ""nima haka, amman dai a baki zaki bari ni ko 'yar matata? Tayi dariya ta kau da kai, kunya ta rufe ta a zuciyarta cewa tayi ""me zai hana na baka na gwada yanda Alhaji Bashir ya yiwa Fauziyya akanka ta cikin littafin SAWUN"

"GIWA"""

"Amma a fili ba zata iya ba, yayi murmushi ya fara cin abincinsa ya dinga janta da hira yana ba ta labarin"

"abincin ikko, ita ma tana bashi labarin abubuwan da suka faru, wani yayi dariya wani ya bata fuska, a hakahar suka kammala cin abincin."

"Dukkan hankalin ahmad yana kan Ma'u a yau dai yake jin fauriyarsa zata kare, idan bai isa ga matarsa ba"

komai zai iya faruwa a gare shi. Ita kanta ma'un tana jin wani abu yana yawo akanta duk lokacin. Da ta

"kalli mijin nata. Domin ta cika tayi dankam babu wata damuwa ko ta kwabo a ranta, amman kowa ya rasa yanda zai iya tunkarar dan uwansa."

"Ma'un ce ta fara duguwa dakin baccinsu ta sanya kayanta, don akwai rigunan bacci kala-kala don haka a"

"ciki ta zabe wata mai kyau ta sanya, duk da dukkan rigunan ana hango komai na mutum idan ya sanya, ita kuma ba zata iya yarda yayanta ya ganta a haka ba, don haka ta haye gado ta kudundune cikin bargo."

"Shi ma bai wani jima a falon ba ya biyo bayanta, sai ya tadda ta a gado a kudundune, ya isa kusa da ita ya"

"zauna a gefen gadon yana fadin ""Ma'u sanyi kike ji ne haka? Kin ga bude na gayanda rigar tayi miki kyau, duk kayan da basu yi miki kyau ba sauya su za a yi"""

"Ta kunshe kai tace ""tayi min kyau ma yaya"""

"""A'a sai na gani da idona, bari na gani"" ya fara kokarin janye bargon tana rikewa da 'yar kissa, amman sai"

da ya cire ya zubawa halittar matarsa ido. _wai da gaske daman haka ma'unsa take?_

Ta kara kudundunewa zuciyarta na cigaba da bugawa. Tabbas yau zai abibda take karantawa a cikin

"littafi zai faru a kanta, duk da bata san a wanne haki yake ba shi mijin nata."

"Jikinta ya bata cewa ya kura mata ido ne, don haka ta kara matse jikinta gabanta yana ci gaba DA faduwa."

"Yayi wata doguwar ajiyar zuciya ya mike tsaye yace ""taso Ma'u"""

"Tayi shiru bata yi magana ba kuma bata motsa ba, har ya dan juya ya fara tafiya amman sai ya sake"

"waigowa yace ""Ma'u kina jina fa, daure tashi kiyo alwala, zan gaya miki abinda zaki yi idan kinyo alwalar"""

"Ta yunkura kamar kifanya har lokacin jikinta yana nannade ta rike zanin gadon, yana kallonta kada kai"

"yayi murmushi ya fice. Tayi ajiyar zuciya bayan ta hango inuwarsa ya gama ficewa ta dafe kunci, ta kara mai da hannunta ga kirjinta da yake ta bugawa, tayi dan murmushi sannan ta mike ta fito."

"Yana tsakar gidan kusa da bandaki yana daura alwala. Ta rakube tana jiran ya kammala, yayi kamar bai"

"ganta ba yana ganawa sai ya shige falo, sai ta nufi bandakin ta shiga. Ta jima a tsakar gidan bayan ta kammala alwalar gabanta yana faduwa ya kasa shiga dakin. Ta jima tana sakawa da kwancewa. Kukan"

wata mage da ta zo wucewa ne ya bata tsoro sai ta shige dakin da sauri

"Yana zaune a kan sallaya ya tankwashe kafafunsa yayi shiru, amma bakinsa yana dan motsi alamar lazimi"

"yake yi. Ta isa kusa DA shi ta tsaya daga bayansa, yaji alamun shigowarta don haka ya mike da kansa ya dauko hijabin sallarta ya mika mata ba tare da ya kalle ta ba yace ""sallah zamu yi raka'a biyu Ma'u"" ya"

"shige ba yana kokarin tayar da sallar, ta bi shi a baya ta tayar."

Bai ja dogayen surori ba yayi sallama ya juyo ya kamo kanta ya fara karanta addu'a

"""ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA KAIRAHA WA KAIRA MAJA BALTAHA AKAIHIM WA'AZUBIKA SHARRIHA"

"WA SHARRA MA JABALTAHA ALAIHI"""

"Yayi dan shiru bayan ya gama karanto addu'ar yana kallonta cikin kwantar da murya yace ""Ma'u na san"

"kin iya dukkan farillan addini da ya kamata ki sani, ko akwai wani abu da baki sani ba? Ma'u ta girgiza kai kawai, ya sake yin murmushi yace ""ai ban gane me kike nufi ba, ki bude baki ki sanar da ni eh ko a'a zaki ce min shi ne zan fahimta kuma har na gamsu"""

"""Eh na sani"" ta fada da sauri. Yace ""yauwa na san haka, tashi ki je ki sanya rigar da kika sanya dazu ki"

"kwanta"""

"Bai jira jin abinda zata ce ba ya mike ya fice ya nufi kicin dinsu, ya duba yayi sa'a akwai kalanzir don haka"

ya dora ruwan zafi kadan ya dafa shayi a dan karamin kofi ya sanya koren ganyen shayi (Green Lipton) ya shanye karamin kofi sannan ya nufi dakin.

Yayi sa'a akwai wutar nepa fanka tana kada dakin nasu.

"Yanda ta kwanta dazu yanzu ma haka ta kwanta, ya sanya hannu ya kashe kwan fitilar dake dakin, ya"

"karasa gadon ya kwanta daga gefe daga inda yake yana jin sautin ajiyar zuciyar Ma'u. Ya dan matsa gab da ita har yana dan gogar jikinta, amma bai shafe ta ba sai yace ""Ma'u ba ni labarin me da me ya faru bayan tafiyata? Tayi shiru ta kasa magana amma sai dai faduwar gaban nata ya dan ragu. Ya ci gaba DA"

magana a hankali daidai saitin kunnenta.

"""Tunda kin ji ba ni labari bari na ba ki nawa labarin. Lokacin da aka ce an daura aurena da ke sai nake ga"

"abun kamar wasa, kamar shiririta har na tare da ke bana jin komai a kanki sai kulawa ta kanwata, sannu a hankali damuwa da tunaninki ya fara shiga raina, lokacin da zan tafi legas nayi tsammanin na damu da rabuwa da ke ne, domin sabo da shakuwa da ta kuma shiga tsakaninmu, sai dai bayan naje can na gano"

"kaunarki da soyayyarki ne na gaskiya ya shiga zuciyata..."""

"Ya dan yi shiru yana murmushi shi daya cikin duhu, wani irin shauki da bakon abu na sake shigarsa. Ya"

dan kara matsawa jikinta ya kamo hannunta ya rike cikin nasa ya fara wasa da shi.

"""Tsarki da buwaya sun tabbata ga UBANGIJI da yake halittar zuciyoyi ya sanya Soyayya a cikinsu. Ma'u"

"yanzu babu abun da nake so a duniya bayan ALLAH DA MANZONSA da kuma ummata kamarki"""

"Tsigar jikinta ta tashi yarr! Ta dinga jin wani Abu yana shigarta wanda ba zata iya fasalta shi ba, ta dinga"

"jin kamar ta juya ya rungume mijinta, amman sai ta ji tafukan hannunsa sun saki hannunta sun fara kai komo cikin jikinta, ya cigaba da magana cikin kunnenta."

"""Ban taba zaton zan yi wa ma'una irin wannan soyayyar ba, ki gaya min Ma'u me kike ji a kaina yanzu?"

"Domin tunda na dawo na gano wani abu a cikin kwayar idanunki, juma gangar jikinki kamar tana nuna min wani abu na yadda..."" Ya sake yin kasa da murya yana cigaba da magana. ""Ma'u kin yi wayo yanzu, kin san meye aure kin amince min na zama mijinki na gaske a gare ki ba suna ba? Ki bar ni na fara raya sunnah da ke a farkon duniyata. Ki bar ni naji abibda kowa ke ji a cikin aurensa ma'u."" Ya kankameta a"

jikinsa kamar zai mai da ta cikin nasa.

"Ita kam ta gaza cewa komai domin yayi mata dukkan abun da zai kashe mata jiki, tana jin jikinta da"

"zuciyarta ya gamsu da amsar mijinta, ta karanta littattafan Soyayya masu dama, amman bata taba karanta irin soyayyar da mijinta ke gwada mata ba. Cikin duniyar shauki ta jiyo shi yana cigaba da"

sambatu da rokonta.

"""Ba ki ce komai ba ma'u, ki ba ni dama don ALLAH ki amince na zama miji a gare ki da gaske"""

"Cikin rawar baki tace ""na amince maka yayana"" domin ta fuskanci yana gab da shide mata. _ALLAH MAI"

"IKO_ kawai Ahmad yake iya ayyanawa a cikin ransa, har ya kai ma'un ga matsayin da kowacce mace ke shiga wato CIKAKKIYAR MACE."

"Ba ma'un kadai ba, shi kansa ya sha wahala, domin tare suka bare junansu a kwali, amman ma'un ta ba"

"shi mamaki domin tayi matukar dauriya, don haka har bacci ya dauke ta tana kan kirjinsa yana shafar gashin kanta da jin dadi cikin ransa gami da yiwa ALLAH godiya da ya nufe shi da yin aure har ya dandani zakin dake cikin auren."

"Gajiya da kasala suka taru suka yi musu rubdugu, don haka sun kusa makara, shine ya fara tashi ya dora"

"ruwa ya shiga wanka, kafin ya fito daga wankan an idar da sallah a masallaci."

"Bai ji dadin hakan ba, amman ya san ALL AH zai yafe masa tunda ba da niyya ya aikata hakan ba. Sai da"

ya fara yin sallah sannan ya girka ruwa mai dumi ya nufi daki.

"Har lokacin ma'u tana bacci, domin ta sha matukar wahalar da bata taba sha ba a rayuwarta. Cak ya"

"dauke ta kamar 'yar bebi, sai sannan ta farka tana jinta a jikinsa ta kara mai da idonta ta rufe domin kunya ta gama rufe ta."

Yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Cikin faffadar robar da ya kusa cikawa da ruwan zafi ya tsunduma

"ta a ciki bayan cire dan yalolon zanin dake jikinta, tayi doguwar ajiyar zuciyar sanda ruwan ya fara ratsa"

"jikinta, amman har lokacin idonta yana rufe ta kasa budewa. Yayi murmushi ya juya ya fice ya bar ta a bandakin ita kadai."

"Ta yi wanka ta gasa jikinta, sai ta ji kwarin jiki. Kafin karfe takwas na safe tayi ahmad ya gama yi musu"

komai na kayan karin kumallo.

"Sai da yayi DA gaske ta ci domin kunyarshi ta hana ta sakat, shi kam dariya kawai yake yi mata da"

tsokanarta.

Ranar haka nan suka kare shi cikin nishadi da jin dadi gami da kaunar juna.

"A ranar tare suka fita sayayyar kayan abinci, da yake akwai dan kudi a hannunsa har dan karamin cooker"

"gas ya siya mata, ya kuma yi mata siyayyar kayan kwalliya da na shafa daidai karfinsa."

***

Rayuwar Ahmad da ma'u ta zamo abar sha'awa domin kullum soyayyar junansu kara karuwa take cikin

"ransa, sun saba da juna sun shaku da juna."

"Ahmad ya iya Soyayya ya kuma koyar da ma'u Soyayya da sonsa, domin idan ya fita aiki ta kagu ya"

"dawo, don ma dai karatun littafi yana dan dauke mata hankali kadan."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

36

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

BAYAN SHEKARA BIYU

Ma'u ta zama cikakkiyar mace da ta iya rike mijinta. Zuwa wannan lokaci duk wata kira ta halittarta ta

"kammala fitowa. ALLAH yayi halitta mai tsananin daukar hankali, musamman tsarin jikinta da ake cewa mai kirar kalangu. Bata cika haske ba, amman mai sheki ce da sulbi. Doguwa ce sambal bata DA jiki ko"

kadan. Amman kirarta da cikar kirjinta ta sanya take dab ciko ido.

"Mijinta bai gajiyawa da kallonta, musamman idan tayi kwalliya har yakan rasa a ina matarshi take koyo"

"abubuwan da takan yi. Ita dai ba wasu kawaye take da su ba, domin yan matan dake dan shigo mata ma a baya yanzu duk sun daina, domin ta fara kishin mijin ta, wasunsu kuma suna makarantar kwana."

"Ahamd ya kasa gano sirrin matarsa, daga karshe ya bawa zuciyarsa amsar kawai Allah ne ya halicceta a"

haka.

"Amman duk lokacin da zata fita unguwa sai an kai ruwa rana, ya dinga kallon irin shigar da zata yi, yayi"

"mata tsari, ta cire wannan kayan Santa wancan shi ne zai kai ta kuma ya dawo da ita, tun tana dariya tsananin kishinsa har abun ya fara damun ta."

"Yau tana zaune tana gogewa mijinta kayan da ta wanke masa jiya, ta jiyo sallamar Maryam kawarta daga"

"kofar falon. Tayi saroro da mamaki don tana tantamar abinda kunnenta ya jiyo mata na muryar kawar tata. Maryam ta dago labule tana fadin ""ko matar gidan bata nan ne?"

Ma'u ta mike da sauri tana ihun farin ciki ta rungume Maryam suna tsalle cikin farin ciki. Maryam ta

"janye jikinta tana fadin ""rufa min asiri na koma gidanmu lafiya, kada ki ji ciwo mijinki ya tayar min da kayar baya"""

"Ma'u tayi murmushi tana fadin ""naji dadin ganinki Maryam, nayi zaton ai kin manta da ni ne tunda su"

"Aisha sun watsar da ni"""

"""Wace ni kin san makarantar ce ke hana ni zuwa, amman yanzu tunda mun yi candy ai har sai kin gaji"

"mda ni kafin na samu admission"""

"Admission kuma Maryam? Ma'u ta tambayeta da sanyin jiki da damuwa. Marayam ta bata amsa da ""eh"

"kin san baban yana sin na cigaba da karatu kamar sauran yayyena, idan result dina yayi kyau medicine nake son karanta ko pharmacy"""

"Da damuwa ma'u tace ""kin ji dadinki dama no ce, ni yanzu sai zaman gidan ban san a halin da nake ba,"

"ko da a ce candyn ma nayi to da da dan sauki"""

"""A zatona kece baby ki son karatun amma Yayanki ahmad bai yi kama da wanda zai hana ki karatu ba,"

domin ai shi ma yayi karatun ma gani ko?

"Ma'u tayi murmushi kawai tare da mikewa tsaye tana fadin ""ba ki san halin yaya Ahmad ba, dan banzan"

"kishin sa ba zai kyale ni nayi karatu ba. Bari dai na kawo miki abin sha muna ta zuba hira ban sauke ki da ko ruwan sha ba"" ta nufi kofa kai tsaye."

A nan gidan ma'u Maryam ta yini har sai da ta gaya ma'u girkin dare ita ma ma'un na sha'awarta na

"kammala karatun ta, ita kuma tana sha'awar ma'un na yanda tayi sa'ar aure duk da mijinta ba mai hali bane amma suna cikin rufin asiri."

"Sai gab da sallar magriba Maryam ta bar gidan, amman ta tafi ta bar zuciyar ma'u DA miki, wanda tayi"

nufin amayar da shi yau ko ta huta.

"Kamar yadda ahmad ya saba dawowa da magriba, yau ma haka ya shigo gidan. Tunda soro ta taro shi ta"

amshi jakar da yake goyowa a bayansa ta uniform da takalminsa irin nasu na ma'aikatan gidan man.

Ya karaso tsakar gidan ya kafe babur dinsa sannan ya janyo ya jikinsa ya matse. Tayi dariya tana fadin

"""gaggawar ta meye bayan taka ce ni jai kadai, babu mai gutsirar maka?"

"""To meye don na taba kayana kuma za a damu?"

"""Bar maganar haka je ka cire kaya kayi wanka tukunna"""

"Bai yi musu ba ya sumbaci wuyanta sannan ya wuce domin yana dawowa wanka yake fara yi kafin komai,"

domin an yini cikin rana.

"Har sai da ya ci abinci ya koshi, suna falo suna kallo sannan ma'u ta bijiro masa da abinda ke ranta. A"

"lokacin kanta yana kan cibyarsa yana wasa da gashinta suna cikin nishadi. Ta dan dago ido ta kalle shi tace ""yaya akwai wani Abu dake damun zuciyata, ina son gaya maka kullum amman ban san ya zaka"

"dauki abun ba"""

"Ya lakace mata hanci yana murmushi ""yaushe muka fara 'yar haka da ke ma'una, ki boye abu a ranki ya"

"sanya miki ciwon zucuya, idan na rasa ki me kike tunanin zai sami rayuwarta?"

"Tayi murmushi ""sai ka sake wata matar 'yar gayu..."" Tayi kara saboda mintsininta da yayi ya bata rai."

"Wacce mace ce zata auri mutum irina? Ai idan na rasa ki ni ma na rasa kaina, bayan su Abba babu Wanda zai kara ba ni matar aure har abada..."

Ta mike zaune da sauri tatoshe bakinsa.

"""Ya isa haka, ba zan mutu ba sai ka riga ni mutuwa da shekara ashirin da daya"""

"Ya kuma mintsininta yana dariya, ta sanya ihu ta Zame tana fadin ""kai yaya Wallahi ka iya mugunta"""

"mugunta ko gaskiya? Yaya za a yi ba yarda na mutu na bar ki har tsawon Shekaru ashirin da daya? Wato wani ya aure mini ke ko? Na ki wayon, rana daya za mu mutu ni da safe ke da yamma"""

"Yanda yake maganar babu dariya ya sanya ta fashe da dariya tana

32 / 47