Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 47

123K to 126K   out of 139.6K words

Nura Kwangila ya gigice yace ""suma kuma, me ya sameta?"""

"Ta kalli Nana dake kwance akan kujera tace ""ban sani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi,"

"amma da nayi mata magana sai tace babu komai"""

"""Kin ga bar bayanin haka, zan yi wa likita waya yanzu ya zo, ni kuma zan biyo jirgi na taho yanzu. Ki kula"

"da ita kafin na iso"""

"Ya kashe wayar da damuwa, a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa Kano."

***

"Hajiya Batula ta isa kusa da Nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. ""Sannu Nana"

meke damunki?

"Nana ta runtse ido hawaye ya zubo mata, bata son tunawa, amman ba zata taba mantawa ba, domin"

"soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, ba zata iya rayuwa ba Ahmad ba."

"Ganin hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyar tata tace ""shike nan ya isa daina kukan"""

"Bayan min tuna goma sai ga likita ya iso gidan nasu, hadiman gidan suka yi masa jagora har cikin gidan"

da yake kowa ya san shi a gidan.

"Hajiya Batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin ""Yauwa karaso likita ka duba min ita"""

Likitan ya isa da sauri ya sauke jakar DA yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala-kala. Cikin 'yan

"mintuna kadan ya kammala auna Nana. Yayi mata wasu 'yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da Hajiya Batula sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje-gwajen."

"Hankalin Hajiya Batula ya kara tashi sosai, ta dubi likitan tace ""likita ka gaya min meke damun diyata?"""

"Cikin kwantar da murya likitan yace ""kwantar da hankalinki Hajiya, ba wani abu bane ba, ina dai so na"

"samu sakamakon da nake bukata"""

Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti. A cikin mota tayiwa Alhaji Nura Kwangila bayanin

sun wuce asibiti. A lokacin shi kuma yana cikin airport. Hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amman ya dake.

"Dukkan gwaje-gwajen da ya kamata an yiwa Nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan, don haka ya"

ja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba.

***

"Ana kiran sallar Isha'i Alhaji Nura Kwangila ya iso garin. Kai tsaye asibin Dr. Musa ya wuce, har dakin da"

"Nana take ciki, lokacin an yi mata wata allurar barci, idonta ya rufe. Hajiya Batula kuma tana sallah."

"Alhaji Nura Kwangila ya isa gaban gadon da Nana kr kwance akai ya tsaya yana kallonta, sai kuma ya fara"

"lalubo wayar Dr. Musa, da ya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa."

"Yana shiga Dr. Musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi, amman bai kula da wannan ba cewa"

"kawai yake yi ""Dr. Musa meke damun diyata, me ya faru da ita?"""

"Dr. Musa ya jinjina kai yace ""kwantar da hankalinka Alhaji, zauna nayi maka bayani"""

"Alhaji Nura Kwangila kamar ba zai zauna ba, amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likita."

Dr. Musa ya zauna ya dauko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon Alhaji

Nura Kwangila wanda ya kagu yaji abinda zai ce. Dr. Musa ya fara baya ni.

"""Da farko na fara yiwa Nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau"""

"""Nana, me zai sanya jininta hawa kuma!? Alhaji Nura Kwangila ya tambaya a gigice."

"Dr. Musa yace ""wannan ba shine abindake bani mamaki. Sannan bugun zuciyarta ya sauya yana gudu"

"fiye da yanda ka'idarsa take, wannan dalilin ya sanya nace nu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje- gwaje, ga mamaki sai naga zuciyarta ta dan samu matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga, musamman lokacin da ta fadi, ALLAH ya taimaka anyi gaggawar kawota asibita da wani mummunan"

"abun ya faru da ita"""

"Hankalin Alhaji Nura Kwangila ya kuma tashi yace ""abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa"

"har ta kusa rasa rayuwarta?"""

"""Kwantar da hankalinka Alhaji, wannan ba wata matsala bace, insha ALLAH komai zai zama daidai, zata"

"dawo daidai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri"""

"Alhaji Nura Kwangila ya gyada kai yana cewa ""na gode likita, bari naje gurin mahaifiyarta"""

"Ya tsare Hajiya Batula da tambayoyi abinda ta gaya masa a can shi ta kara gaya masa a nan din ma, dole"

dai su bari diyar tasu ta samu lafiya tukunna.

***

"Washe gari tunda safe Ahmad yaji labarin abinda ya faru, hankakinsa yayi matukar tashi, don haka DA"

"wuri ya wuce asibitin, ya tadda mutane anyi dandazo kama daga 'yan fadanci zuwa dangin Hajiya Batula dana Alhajin, amman ba a barin kowa ya ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifanta ka juya ka tafi."

"Shi ma Ahmad da su din ya gaisa, sai dai bai samu ganin Hajiya Batula ba tana ciki, da yake dakin irin na"

masu kudi ne har da wani katon falo.

Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da Alhaji Nura

Kwangila.

"Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyarta Hajiya Batula dake zaune a kusa da ita tayi tagumi, cikin"

"sanyin murya tace ""mommy ba Ahmad ne ya zo ba?"

"Hajiya Batula ta ce""ban sani ba KO kina son ganinsa ne? Ta daga kai alamar eh. Da sauri Hajiya Batula ta"

mike ta nufi falon.

"Alhaji Nura Kwangila ya kalle ta sauri ganin ta fito a rude yace ""yaya dai Hajiya, lafiya?"

"Cikin karewa mutanen gurin kallo tace ""Nana ce tace taji muryar Ahmad wai"""

"""Ba wai bane shine, yanzun nan ya fita, bari na kira shi idan tana son ganinsa ne"""

Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad. Bugu daya ya daga Ahmad din har ya tayar da motarsa

amman yace masa ya dawo maza-maza Nana na son ganinshi.

"Gaban Ahmad ya fadi, yaji kamar kada ya koma din, amma ba zai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita"

daga motar ya nufi dakin gabansa yana faduwa yana ta addu'a a cikin ransa.

"Kai tsaye Alhaji Nura Kwangila ya shige da shi cikin dakin da Nana take kwance, mutanen dake zaune a"

gurin suka rinka mamakin irin matsayin da Ahmad yake da shi a gurin Alhaji Nura Kwangila din da ya samu shiga gurin Nana.

"Nana ta kurawa kofar dakin ido, daidai lokacin da Ahmad ya shigo suka yi ido hudu, tayi doguwar ajiyar"

"zuciya, murmushi ya bayyana akan fuskarta."

"Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace ""sannu Hajiya Nana, ya"

jikin naki?

"Tayi murmushi ""Da sauki, na gode da ka zo duba ni, ka kula da komai kafin na koma"""

"A zahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi ne don kamfani da gaske, sai dai a kadan"

zuciyarta tayi haka ne kawai don ta gan shi.

Alhaji Nura Kwangila da Hajiya Batula suka kalli juna da mamakin abinda tace.

"Ahmad yayi tsaye kamar ba zai tafi ba, sai da ya dan jima sannan yayi musu sallama ya wuce, idonsa ya"

"ciko da kwalla saboda ganin irin halin da Nana ta shiga, idonta ya yi jawur hawaye ne kawai ke zuba daga cikinsa."

"Koda ya isa ofis kasa yin komai yayi, sai tunanin halin da Nana ke ciki, da ace zai iya taimakonta da yayi,"

"amman ba zai iya bari rayuwar Nana ta lalace ba, dole zai san abin yi."

Kwanaki hudu tana cikin asibitin amma babu sauki sai abin dake karuwa. Musamman ga hawan jinin

"gashi an yi an yi ta fadi abun dake damunta ta ki sai dai kuka. Shi kansa Ahmad tun zuwansa na farko ya kasa komawa, don bai son ganin Nana cikin halin da ya san ba zai iya taimakonta ba."

*

*

*

So Sartse...

DA ME AKE ADO?

50

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

BAYAN KWANA UKU

"A bangaren Nana kuwa hankalin iyayenta kullum a tashe yake, yau kam Alhaji Nura Kwangila ya"

"tabbatarwa kansa sai ya san abinda ke haddasawa diyarsa wannan halin da take ciki, don suna jin kukan da take kusan kwana tana yi indai ba a yi mata allurar bacci ba."

Tana zaune a tsakar gado tana shan ice cream ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna a

"gefen hadadden gadon dake kama da na gidan wani hamshakin sarki don ya sha gyara. Cikin sanyin murya Alhaji Nura Kwangila ya kira sunanta, ta dago kai ta kalle shi gabanta yana faduwa ta amsa."

"Ya sake kwantar da murya yace ""Nana ki taimake ni ki sanar da ni gaskiyar abun dake damun ranki?"

"Nana ki tuna bani da kowacce diya bayan ke, ke kadai ALLAH ya bani, dan uwana guda daya ne yana kwance cikin jinya, ke kadai nake kallo a dangina kuma 'yata, idan kika bari na rasa ki na zan yafe miki ba,"

"don babu makawa ni ma karshen rayuwata ya zo"""

"Yayi shiru yana dan kallonta sannan ya cigaba ""Nana ki taimaka ki sanar da ni abin dake damun ki, ina da"

"kudin da zan iya siyo miki dukkan abun da kike bukata a wannan duniyar, idan kuma yafi karfin soya zan iya taya ki da addu'a ALLAH ya ba ki shi, ko kuma ya sanya sanyi da salama a cikin zuciyarki, ki fada min"

"abun dake damun ki Nana."""

"Nana ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na zubowa daga idanunta tace ""Daddy idan na gaya muku abun"

"dake damun zuciyata zaku ji haushina da abin, wata kila ma hakan ya sanya ku daina tausaya min"""

"""In ji wa ya gaya miki? Dukkan abun da zai sanya shi cuta irin wannan ya wuce mu sauke shi karami. Ki"

"gaya min Nana ko kin manta nine daddy dinki da kike gayawa dukkan damuwarki?"""

"Ta dago kanta ta kalle shi kamar ba zata fada ba, sai tace ""Daddy tun ranar da nayi wa Ahmad wulakanci"

"a gidan mai Na fara kamuwa da sonsa, nayi zaton wasa ne ko zan rabu da son a hankali, amma sai abun"

"ya cigaba DA hauhawa a cikin raina, har ta kai na zamto bani da buri bayan ganinsa kullum, don haka"

"kullum sai naje gidan mansu, daga baya nayi hanyar da ya samu aiki kusa da ni, wannan ya sanya na samu sanyi a cikin raina, ban taba zaton idan na bayyanawa Ahmad bukatata zai juya min baya ba, na gwada masa dukkan abunda zai sanya ya gane ina kaunarsa amma ya kau da kansa, daga karshe da naga son sa yana neman ya hallaka ni ya sanya na sanar da shi, amma sai ya gaya min bai sona bai kuma taba"

"sona ba..."""

Ta fashe da kuka maganar ta kasa ci gaba da kuka. Hajiya Batula da Alhaji Nura Kwangila suka bita da

"kallo da tausayawa, basu taba zaton abun dake damun diyarsu kenan ba. Wato hakan na nuna musu ta"

warke daga cutar dake damunta tun tana da kuruciyarta wacce suke kashe makudan kudade gurin ganin sun samar mata lafiya.

"Alhaji Nura Kwangila ya riko hannunta ya dora kanta bisa kafadarsa yace ""Kwantar da hankalinki diyata,"

"na san illar da soyayya take yiwa zuciyar dan adam, don ta taba illata rayuwata, amma in dai akan Ahmad ne kukanki ya kare, damuwarki ta kare, zan samar miki shi da ikon ALLAH"""

"Ya mike da sauri ""Yanzu zan je gare shi, insha ALLAH kukanki da damuwarki sun kare"""

Idon Nana yana zubar da hawaye tana kallon baban nata da ya nufi kofa kai tsaye zai fita.

"Cikin sanyin murya tace ""Daddy don ALLAH idan yaji yarda kada kace zaka kore shi, ganinshi kadai abun"

"jin dadine a gurina, kada kayi masa dole akan sai ya soni"""

"Alhaji Nura Kwangila yayi shiru bai juyo ba, amman tabbas maganar diyar tashi ta shige shi, tausayinta ya"

"kara kama shi, ashe akwai wani abu a wannan duniyar da diyarsa zata iya rasawa yana raye? Lallai iko yana gurin UBANGIJI. Ya kada kai ya fice."

Hajiya Batula ta matsa kusa da Nana don rarrashinta.

***

Ahmad yana zaune a ofis wayarshi ta fara kara. Ya dago da sauri yana kallon screen din wayar. Lambar

"Alahji Nura Kwangila ya gani, gabansa ya fadi amman dai dole ya daga."

"Yana shirin gaisar da Alhaji Nura Kwangila din ya katse shi da cewa ""kana ofis ne?"

"Da hanzari Ahmad yace ""Eh ina ofis Alhaji"""

"Alhaji Nura Kwangila yace ""OK to ga ni nan zuwa"""

Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake yi kamar ya gudu kada ya bari Alhaji Nura Kwangila ya

"zo ya tarar da shi, amman babu halin yin hakan, dole ya zauna ya jira zuwanshi."

"Lokacin da Alhaji Nura Kwangila ya turo kofa ya shigo, Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar,"

saboda wani bugu da yaji kirjin nasa yayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana yiwa Alhaji Nura Kwangila sannu da zuwa.

"Alhaji Nura Kwangila ya dube shi yana murmushin yake yace ""zauna Ahmad ina son yin magana da kai ne,"

"kuma magana ce mai matukar muhimmanci a gare mu"""

"Ahmad ya koma ya zauna cikin sanyin jiki, gabansa na dukan dari-dari."

Alhaji Nura Kwangila ya janyo kujera dake fuskantar wacce Ahmad yake kai a zaune ya zauna ya tsare

"Ahmad da ido yana fadin ""ba sai naji komai daga bakinka ba, na san Nana bata yin karya ko yaudara, abin da nake fata daga gare ka kawai shine ka amince Ahmad, bani da kudi ko ikon da zan iya siyan"

"soyayya, domin da zan iya DA tun tuni na siyowa wani soyayyar Nana na aurar da ita."

"Tunda Nana ta taso ta ki jinin kula saurayi har zuwa girmanta, hakan ya jagoranci tunaninnu da kuma"

"fadin wasu nalamai cewar wai bakin aljani ne ya aure ta, yanzu kuma sai ga shi ALLAH ya kawo mana maganin abun rana daya, Nana ta furta da bakinta cewa tana sonka Ahmad."

"Ahmad kayi duba da kyau ga wannan lamari. Nana yarinya ce mai kyau da tsari, kamar Nana ace ta"

"tunkari namiji tace masa tana sonshi ka san ba karamin abu bane, ka taimake ni Ahmad ka auri Nana don ALLAH!"""

"Ahmad yana kasa tunda Alhaji Nura Kwangila ya fara magana, da akwai mutumin da zai yiwa wani abu"

"ko ranshi baya so to bai wuce Alhaji Nura Kwangila ba, amman ba zai iya yiwa ma'unshi kishiya ba, don yiwa ma'u kishiya kamar yiwa umanshi ne. Mutanen da suka raineshi suka bashi mace yaya zai iya yi musu haka?"

"Ba shi da amsar da zai iya bai wa Alhaji Nura Kwangila, don haka ya dukar da kansa kawai."

"Alhaji Nura Kwangila ya zuba masa ido da mamaki sannan yace ""Ahmad ko akwai wani da Nana take yi"

"wanda ranka bai bukata? Ko kuma tana da wata illa ne ka gaya min, ban yi zaton wani namiji zai ki diyata ba a wannan lokacin"""

"Ahmad ya girgiza kai yana fadin ""ko daya babuvwani abun ki da na gano a wajen Nana amman..."" Sai"

kuma yayi shiru ya rasa ma me zai ce.

"""Lallai Ahmad ka nuna min kai namijin duniya ne, hakan kuma ya sanya na kara yarda Nana tayi zabi"

"nagari, don nayi imanin wani zai so Nana ko don arzikinta ko kyanta ko nasabarta, amman kai ko daya bai burge ka ba daga cikin wadannan abubuwa."""

"Ahmad ya kada kai ""tunda nake ban taba sanya kwadayin abun kowa cikin raina ba, na wadata da abun"

"da nake samu, amman kayi hakuri Alhaji ina cikin halin DA ba zan iya aurar wata ba"""

"Alhaji Nura Kwangila ya sake kallon Ahmad da tsananin mamakin irin karfin halinsa, amman hakan kara"

burge shi yake da kuma nuna shine mijin da ya dace ga diyarshi Nana.

Yanzu cikin kwantar da murya Alhaji Nura Kwangila ya cigaba DA magana.

"""Yanzu kam alfarma bake nema ka dubi halin da Nana take ciki, bani da kowacce diya ko daya sai ita, zan"

"iya rasa ta saboda sonka, ka ceci rai Ahmad, ka ceci rayuwarta daga cikin bakin cikin dake damunta"""

"Jikin Ahmad yayi sanyi lallai ya kamata yayi wani abu a kai, amman kuma ba zai iya yi kai tsaye ba don"

"haka yace ""Alhaji ka bani dan wani lokaci zan yi shawara tukunna"""

"Ran Alhaji Nura Kwangila ya dan yi sanyi, ko babu komai ya samu magana mai dadi, amma cikin ransa"

"mamaki da tu'ajabi ne ke cikashi yau kuma haka ALLAH ya kaddara a kansa kamar shi ya buge da rokon wani abu da bai da iko akansa, bayan shi da kullum ake roko."

Wannan kadan kenan daga ikon ALLAH.

"Alhaji Nura Kwangila ya girgiza kai yana fadin ""hakan ma yayi, amman ba zan ba ka dogon lokaci ba,"

"gobe kamar wannan lokacin zan dawo naji shawarar da ka yanke. Na gode."""

Alhaji Nura Kwangila ya juya ya fice. Ahmad ya bishi da kallo da fargaba da tsoron abin da zai biyo baya.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

51

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Yau kam ransa a sake ya isa gida, halin da ya ga ma'u ya kara sanya ransa dadi, ita da 'ya'yanta suna cikin"

"kyakkyawar shiga gwanin sha'awa. Ma'u ta mike ta taro shi da jin dadin yanda ta gan shi cikin farin ciki,"

ya mannata a kirjinshi yana sumbatarta suna dariya. Tayi masa dukkan abun DA ta saba yi masa suka wuce daki.

"Yau suna cikin farin ciki, gurin cin abinci ne take bashi labarin zuwan Amina gidan da yake tayi aure"

"shekaru hudu da suka wuce, ALLAH ya hada da wani dan kasuwa a kantin kwari da yayi mata karyar shima mai kudi ne, yana da katon gida da mota, aka yi aure sai gashi ta tare a daki falle biyu a gidan, haka nan ta tarar zaman da zata yi ita da kishiya ne da kuma tarin 'ya'ya guda shida tayi kuka da bakin"

ciki amman bata da zabi bayan zaman auren.

Malam Sulaiman shi yayi komai na auren nata tare aka hadasu da Musa wanda yanzu yake zaune a gidan

"Ahmad da ya bashi aro saboda yawon haya ya ishesu, kuma tunda taje gidan gidan mijin ALLAH ya jarrabeta da haihuwa ga babu, don aikin karya yayi, irin mutanen nan ne 'yan kayi-nayi, masu tsayawa a bakin hanya wadanda suke tsayawa idan mutum zai yi siyayya su nuna maka shago, wata ran ma sai aje a wuni ba a samo komai ba, ga iyayenta suma babu ta ko ina, su abarsu suji da hidimar diyar dake gabansu wacce suke kiranta da 'YAR RALIYA don na a yi mata radin suna ba balle ragon suna ko wani abu"

ba.

Wannan kadai ya zamewa lami ishara.

"Sai da ya kai loma bakinsa sannan ya kalleta yace ""ina jinki ma'u yaya tazo nan gidan kuma ita da tace"

"har abada babu ita babu mu?"""

"Ma'u tayi murmushi tace ""bari kai dai yaya, yunwa da bala'i ne suka isheta taje can gidansu babu shine"

"tayo nan tana zubar da hawaye DA fadin na taimaka mata bayan ni babu mai bata cikin dangi, tasan tayi

42 / 47