Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 47

114K to 117K   out of 139.6K words

ba, har ya kammala cika"

"mata tankin motar da mai ya iso inda take tsaye yace ""Hajiya na dubu hudu da dari biyu ne"""

Bata yi musu ba ta leka motar ta dauko wata hadaddiyar jakata kirgo dubu biyar ta bashi. Ya amsa ya

"fara kokarin ciro mata canjin, amma tuni ta shiga motarta. Ya matsa da sauri yana fadin ""Hajiya ga canjinki fa"""

"""Ka zuba man sauran canjin a cikin babur dinka don na kula baka shan man cuta"" ta bawa motarta wuta"

ta fice a guje.

Ahmad yabi motar da kallo cike DA mamaki kwarai DA gaske.

"Jazuli yana kallon dukkan abinda yake faruwa ya dan matso yana fadin ""ya aka yi ne dai abokina, kun"

shirya da mutuniyar taka kenan?

"Ahmad yayi murmushi kawai bai ce komai ba, amman a ranshi ya ji da ya sani bai yi mata abinda yayi"

"mata ba a baya. Macen da take dauke da wannan suna mai daraja bata cancanci wulakanci ba. Asma'u mahaifiyarshi, diyarshi kuma matarshi abar kaunarshi. Ya kada kai ya koma ya cigaba da abinda ke"

gabansa.

***

"Duk ranar ALLAH sai nana tazo gidan man nan ta sha mai a gurin ahmad, tun bai sakar mata fuska har"

suka fara sabawa don ya gano tana da matukar kirki yanzu. Ita ma ta gano ahmad din ba miskili bane sabanin yanda take zato a da.

"Yau da dare suna cin abinci ita da babanta da mamanta ta kalli baban nata tace ""daddy wai wannan"

"ahmad din bai da ilimi ne, yanayinsa da mu'amalarsa sun nuna kamar yana da ilimi"""

"Alhaji Nura kwangila yayi murmushi ""ni kaina na fara tunanin wani abu a kansa, yaron nan yana da"

"gaskiya da rikon amana, ban taba jin ance wani abu ya bata a hannunsa ba, abinda ya faru tsakaninki da shi ya kara bashi matsayi mai girma a raina, don irinsu basu hada kai da kowaye gurin cuta ko ha'inci,"

"fatana dai ALLAH ya sanya iliminsa ya dan yi zurfi ko yaya ne"""

"Nana tayi murmushi tace ""gaskiya kam ya kamata ka gwada shi, wata kila yayi maka yanda kake bukata."

"Musamman yanda muke da bukatar karin ma'aikata a kamfani, irinsu muke so"" Hajiya Batula tace ""ba dai wai yaron nan abokin fadanta take magana a kansa ba?"

"Nana tayi murmushi, shima Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yace ""shi mana, yanzu kam sun fahimci"

"juna, shi ne babban customer dinta"""

"Nana ta fashe da dariya tace ""ka ji daddy sai kace wani dan kasuwa"""

Haka suka cigaba da hirar su cikin walwala da jin dadi.

***

"Washe gari DA yamma ahmad yana tsakiyar zuzzuba mai manaja Saddam ya iso gurinshi yace ""Ahmad"

"kasan kamfanin Alhaji Nura Kwangila inda office dinsa da na diyarsa yake?"""

"Ahmad yayi jim sannan yace ""ina zaton na taba zuwa sau daya, shine na can cikin sharada phase II ko?"

"Manaja yace ""good, nan fa gobe can zaka wuce Alhaji yana son ganinka, amma idan zaka wuce ka tafi da"

"takardunka na makaranta domin ina jin interview za a yi na daukar ma'aikata a kamfanin nasa, wata kila kana da rabo a ciki"""

Ahmad ya bude baki da mamaki don abinda ya jima yana nema ke nan sai gashi Yau ya same shi a ruwan

"sanyi. Manaja Saddam ya dafa kafadarsa yana bugawa ""kana cikin mutane masu sa'a, har naji a jikina kana da rabo a wannan kamfanin"""

"Ahmad ya kada kai yace ""na gode ranka ya dade"""

***

"Tun dare ya sanar da Ma'u abinda ke faruwa, don haka bata kwanta bacci ba sai da ta goge masa kayan"

da zai fita da su sannan cikin dare ta tashi tayi sallah ta dinga rikon ALLAH da yi masa magiya akan samun aikin mijinta irin wanda ya jima yana nema.

"Da sassafe ta kammala shirya masa dukkan abinda yake bukata, ya riga su fita tana zolayarshi da cewa"

"""mijina ka hadu fa, kada ka yarda kowacce mace ya kwace min kai kaji ko?"""

"Ya kada kai yace ""nima ba zan kallesu ba"" suka rabu da farin ciki."

***

Sanda ya isa kofar kamfanin mamaki ya cika shi ganin ganin gurin cike da mutane kowa da doguwar

anbulan alamar sun zo interview ne suma. Ya dinga kallon mutanen dake kan layi yana tunanin sanda layi zai zo kansa har ya shiga.

Yana nan tsaye wata hadaddiyar mota ta iso gurin ya nufi kofar shiga kai tsaye tana horn yabi motar da

"kallo, motar ta iso bakin kofar ta tsaya tayi horn sannan sai bakin glass din gaba ya fara sauka a hankali."

"Mamaki ya cika shi da ya hango nana, cikin murmushi nana ta yafito shi da hannu, ya nufe ta DA sauri yana fadin ""Hajiya barka da zuwa"""

"Ta amsa gami da cewar ""bude motar mu shiga mana don naga akwai layi ko na interview ka zo ba?"

"Da sauri yace ""Eh ita na zo, na gode Hajiya"" ya zagaya ya bude ya shiga suka shige ciki."

"Gurin da ake saukar baki ta zaunar da shi, akwai mutane DA yawa a gurin wadanda suka zo interview din,"

shi ma ya zauna yana ta addu'a a cikin ranshi.

"Bayan fitowar mutum biyu aka kira sunanshi, ya mike da sauri da addu'a a bakinsa ya shiga. Abin"

mamaki Nana ce da wasu mutane su shidda suke yin interview din. Bata nuna masa wata alama ta

"sanayya ba don haka shima bai nuna ya santa ba yayi dukkan abinda ya dace, suka amshi takardunsa suna dubawa suka yi masa tambayoyi."

"Nana ce mai rubutu bisa laptop, sanda takardun Ahmad suka shiga hannunta ta cika da matukar mamaki,"

"don ganin har digiri yayi, kuma jami'a mai tsada kamar B.U.K. sannan ya karanta karatu mai kyau."

"Ta kalle shi ta kada kai kawai, yayi irin wannan karatu haka mai zurfi da nasara ai bai kamata ya kare a"

"gidan mai a matsayin mai dura mai ba, yafi dacewa da aikin ofis fiye da dura mai a mota."

"Har aka kammala komai ya koma, kwanaki biyu yana zuwa gidan manshi yana sane da interview din da"

"yayi, amman bai sanya rai ba don yadda nana ta sha kunu ya dan damu yana zaton ko zata rama abinda ya taba yi mata ne. Gashi tun daga ranar bata kara shigowa gidan man nasu ba sam."

"Wannan ya sanya gwiwarsa tayi dan sanyi, sai dai a rana ta uku yaji sako ya shigo cikin wayarshi, bai"

"damu da dubawa ba don lokacin yana tsaka da aiki, sai da ya gama komai ya koma gida ya kwanta ma sannan ya dauko wayarshi ya fara dan duddubawa, sai yaga sakon daukarshi aiki, kuma yaga daukarshi"

din ta fara aiki nan take.

"Yayi wata doguwar kabbara da ta tashi Ma'u daga bacci ta kalle shi da mamaki tace ""lafiya kuwa yaya?"

Ya janyo ya jikinsa ya kankame sai ta kama dariya domin tasan haka mijin nata ke nuna murnarsa ta

kuma san abinda yake jira bai wuce samun aikin da yayi interview ba.

"Kusan kwana suka yi murna, ranar ma da sassafe ta shiryashi ya fice."

***

SABUWAR RAYUWA

"Ga mamakinsa sai yaji wai nana ce D.G ta kamfanin gaba daya, shi kuma ya sami mukamin mataimakin"

"manaja, wato daga ita sai wani sai shi da kuma albashi mai matukar tsoka da katon office shi daya. Bai"

taba mafarkin wannnan ba cikin rayuwarsa. Manaja ne ya dinga yawo da shi yana nuna masa komai da ko ina.

Cikin bayanin nasa yake gaya masa cewa wannan shine kamfanin Alhaji Nura Kwangila na farko wanda

"ya fara yin man gyada da kayan abinci, kowanne bangare akwai shugabansa, wanda bunkasarsa ce sanadiyyar arzukun Alhaji Nura Kwangila har ya kakkafa gidajen mai DA sauran abubuwan da yake yi na"

neman kudi da juyasu.

"Bayan ahmad ya dawo office dinsa yayi shiru yana karewa office din kallo, wai yau shine a nan a"

"matsayin mafi kololuwar dukkan shugabannin sashen mai da kayan abinci da sauransu da kuma ma'aikata kusan dari a karkashinsa suke, wacce irin godiya zai yiwa UBANGIJINSA NE?"

"Aka turo kofar office din aka shigo, nana ce ya mike DA sauri yana yi mata barka da shigowa taja kujera"

"ta zauna tana murmushi, shima ya koma ya zauna yana murmushi. Ta kalli office din nasa sannan ta kalle shi. ""Ya kaga office din naka ahmad, yayi maka? Yayi murmushi ""yayi mana Hajiya. Na gode ban zaci samun wannan matsayi ba, nayi interview da tunanin za a dauke ni a matsayin ma'aikaci ne wanda bani"

"da mukamin komai, sai kuma gashi offer ta fito da babban mukami. Na gode kwarai da gaske."""

"Tayi dan murmushi sannan tace ""mahaifina Alhaji Nura Kwangila ALLAH ya hore masa dumbin dukiya,"

"yana da kamfanoni kala-kala, amman wannan shine yafi alfahari da shi a rayuwarsa, don silar arzikinsa, asalin kamfanin na yayansa ne wanda yake kwance cikin halin jiyya a kasar saudiyya tsawon shekaru, yakan dan samu sauki lokaci zuwa lokaci ya dawo, amman da ya dawo Sai ciwon ya dawo, daga karshe ya sayi gida a can saudiyya inda ya ajiye 'ya'yansa da mahaifiyarsa a can, bamu da yawa a cikin family"

"dinmu, don bamu da yawan haihuwa hakan ya sanya muke da karanci."

"Nayi karatuna tun daga primary har jami'a a kasar waje, bayan na dawo mahaifina ya damka min"

"ragamar kamfanin a hannuna, kasancewar tsawon karatun da nayi na degree da masters duk a kan harkar kasuwanci nayi, kafin nazo kamfanin nan yana hannun wani dan abokin yayan mahaifina ne wanda daga baya muka gano yayi sama da fadi da kudi masu dama don haka aka kore shi lokacin da ya"

kasa kare kansa akan kudin da akan kudin da ake tuhumarsa da shi.

Manajan na yanzu Alhaji Sani shima mataimakinsa aka matsar dashi gaba zuwa manajan aka baka

kujerarka ta mataimaki.

Kalle ni da kyau bani da shekaru amma ina da sani da gogewa akan duk wata harka da ta shafi kasuwanci

"da kamfani, ina fatan yanda nayi zatonka haka kake, kuma ka cigaba da kasancewa a haka domin nice na ba da shaidar waye kai da halayyarka"" tayi shiru tana kallonsa."

"Ahmad yayi doguwar ajiyar zuciya yana fadin ""na gode insha ALLAHU zan yi kokarin ganin na fidda ki"

"kunya na gode"""

"Ta mike tana murmushi ""ayi aiki lafiya, amma za a kawo maka sabuwar laptop ta nan zamu dinga"

"magana akwai wi-fi a ofis din zamu dinga tattauna komai ta sky-pe gmail da sauransu, sai an jima"""

"Ta juya ta fice. Ahmad ya bita da kallo, sai yake ganin kamar mafarki yake yi wanda zai iya farkawa"

kodayaushe amma dai ya san zahiri ne wannan ba mafarki bane illa ikon ALLAH da bai da iyaka.

***

"Duk wani dake da alaka da ahmad ya taya shi murnar wannan cigaban da ya samu, ALLAH ya daga"

"rayuwarshi lokaci guda, ka'idar kamfanin ce su baka gidan da zaka zauna da motar zuwa aiki indai kana babban ma'aikaci, ahmad ya so kin karbar wadannan abubuwa amma Alhaji Nura Kwangila dole ne ya karba ba wai alfarma ba ce, don haka aka bashi mukullin gida da motar hawa, dole ahmad ya karba yana"

godiya.

"Ahmad bai taba iya mota ba, don haka dole ya fara koya a ranakun da babu aiki, gidan dai bai yi saurin"

"tarewa ba don sai yayi siyayyar da yake bukata, da wata ya kare yaji alert ya shigo ya cika da jin dadi, shi da yake daukar dubu ashirin da biyar a wata sai gashi yanzu ya koma dubu dari da hamsin, me ya fi wannan jin dadi?"

Umma har sai da tayi kukan jin dadi lokacin da ya isa gidan da siyayyar kayan abinci da komai na

"bukatarsu sannan ya bata kudi masu kauri ita da mahaifisa, 'yan uwansa ma sai da ya rarraba musu kudade."

"Ma'u kam tafi kowa cabawa ita da yaranta, kusan rabin albashin nasa a kyautatawa iyayensa da iyalinsa"

"suka kare da kuma kansa, don dole sai ya sayi 'yan kayan zuwa aiki."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

46

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

BAYANA SHEKARA GUDA

Shekara daya tamkar kwana ce a rayuwar dan adam! Amma ga ahmad sai yake ganinta tamkar shekara

"dari, don ta sauya masa abubuwa da yawa cikin rayuwarsa, hatta fatarshi da ta matarshi da yaransa ta"

"sauya, rayuwarshi ta zama abar sha'awa ga kowa, ya samu wadataccen gida da abun hawa, sannan yana"

"iyakacin kokarinsa a gurin aikinsa har ya shiga zuciyar Alhaji Nura Kwangila kwarai da gaske, sannan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsa da nana. Wannan shi ne abinda ya fara taba rayuwarsa, domin nana bata shakkar kiransa ko tura masa sako ta gmail ko WhatsApp ko skype, wanda hakan ya fara"

damun Ma'u tun yana boye mata wacece nana har ya gaya mata gaskiyar komai.

"Hankalin Ma'u ya kasa kwanciya da nana, duk da mijinta yana iyakacin kokarinsa wajen nuna mata ba"

"kowa bace nana bayan abokiyar aiki kuma uwardakinsa, amma gareta hankalinta ya kasa kwanciya, don bata son ko kalle mata miji ayi balle wata doguwar magana."

"Ga lami da amina kuwa, abin yafi karfinsu, sun yi hassadar sun gaji sun sallama. Amma suna cikin takaici"

mai yawa.

***

"Yau ya kasance ranar asabar ce babu aiki, Ahmad yana falo yana kallo, Ma'u tana ta kaiwa da komowa"

"gurin hada musu abincin rana cikin kananun kayan da suka amshi jikinta, ba zaka taba yin zaton tayi aure ba balle ace har ta haihu bama sai idan ka sani, saboda yanzu kuruciyarta da yarintarta ke kara fitowa."

"Wani lokacin idan Ma'u tazo wucewa ta gaban Ahmad yakan jata jikinsa, sai ta kwace kanta dakyar ta"

"dangwale masa hanci sannan ta wuce, ko kuma ya tsikareta yana tare mata hanya da kafa, ko dai wani abun, ma'ana ba dai zata wuce batare da yayi mata wani abun ba suna yin dariya."

"Ma'un tana daga kicin cikin gyara manyan kifi wanda aka fi sani da ragon ruwa, don yau farfesunsa take"

"son yi masa don yana son farfesunsa. Ta jiyo wayarshi yana kara daga inda take, tana jiyo shi yana magana"

"""Hajiya nana an tash shi lafiya"""

"""Eh ina gida...aiki?... Oh my God, ba za a daga min kafa manaja yayi ba... Ok shikenan gani nan zuwa"" ya"

kashe wayar da damuwa akan fuskarsa.

"Ran Ma'u ya baci amma bata motsa daga inda take ba ta cigaba da aikinta, daga can falo ahmad yayi"

"tsaye yana sakawa da warwarewa, bai san ya inda zai tunkari Ma'u da maganar fitarshi ba, musamman"

"yanda yaga tana cikin shirin faranta masa rai, tun jiya ta kai yaran gidan umma hutu saboda kasancewar"

an yaye malam sai ita daya a gidan da shi suna ta sha'aninsu.

Ya dai daure yayi ta maza ya nufi kicin din.

"Ta jiya baya tana ci gaba DA aikinta ya lallabo ya rungumeta ta baya yanda ya saba yi mata, amman ga"

"mamakinsa sai ya ga bata yi dariya ba yanda ta saba, sai ma cewa tayi ""kada ka jefa ni cikin ruwan kifi"""

"Ya juyo gabansa da ita yana fadin ""ke yarinya bana son tsiwa"""

"Ta lakuta masa ruwan kifin akan hanci, ganin yanda yake tsokanarta yaja da baya yana fadin ""na tuba"

"kada ki bata ni, zan dan fita na dawo yanzu"""

"""Ina zaka je?"" Ta fadi ranta a bace."

"Gabansa ya fadi bai son yi mata karya bai kuma son ganin ranta ya baci, wai me ya kamata yayi?"

"Ya dake dai yace ""zan fita ofis ne, yanzu aka yi kirana wasu kaya sun zo"""

"""Amman babu wanda zai je sai kai yaya? Ina sauran ma'aikata suke?"""

"""Dukkan abinda kika fada sai da an fada amman daga karshe an gani nine din dai ya kamata naje dole, ki"

"yi hakuri ba zan jima ba, kin yarda?"

"Tayi kokarin danne fushinta tace ""a dawo lafiya amman kada ka dade don ALLAH yaya?"""

"Ya sumbaci goshinta yana fadin ""na gode matata"""

Ya juya ya fice da sauri yana murmushi. Ta bishi da kallo zuciyarta tana tafarfasa kamar zata fashe da

kuka. ALLAH ya sani bata son alakar mijinta da matar nan sam.

***

"Ya isa ofis din, cikin 'yan mintuna suka kammala yin abinda zasu na shigar da kaya da komai, yana ta"

"sauri cikin ransa ya wuce gida. Nana ta shigo ofis dinsa taja kujera ta zauna. Ya kalleta da mamaki ""Hajiya baki wuce gida ba daman? Ta bata fuska ""amma nace ka daina ce min Hajiya ko? Sunana nana ka fadi haka kawai"""

"Yayi murmushi ""zan kwatanta hakan"""

"Tayi murmushi tana kallonsa ""yau fa kaine zaka sauke ni a gida ahmad"""

"Mamaki ya kama shi. ""Baki zo da mota ba ne"""

"""Na tashi da ciwon baya, direbana ya kawoni ya kuma koma nace sai na kira shi, ko akwai wani Abu da"

zaka yi ne?

"Da sauri yace""a'a daga nan gida kawai zan wuce, karki damu zan sauke ki. Yanzu zaki wuce ko sai an"

"jima?"""

"""Eh akwai wani dan aiki da zan karasa zaka jirani? Ta karasa maganar DA shagwaba. Yayi murmushi ""ba"

"fa Alhaji bane ni da zakiyi min shagwaba"""

"Tayi murmushi ta mike ""waye ya gaya maka shagwaba nake yi, bari dai naje na karasa na dawo"""

"Ta fice daidai lokacin da wayarshi ta fara kara alamar kira ya shigo, tun bai dauka ba ya san wacece, don"

"ringing din na mutum daya ne a duniya ya dora. Ya kara wayar a kunnensa bayan ya danne OK yana fadin ""ya ya aka yi ne babyna?"""

"Daga can bangaren Ma'u ta bata rai tace ""wai kana kallon agogo kuwa?"

"Ya dan yi yake, ya san meke damunta kishi ne yace ""ban duba karfe nawa ba baby"""

"Ta kuma bata rai ""ka daina ce min wata baby sunana Ma'u malam, idan baka da lokacin da zaka iya"

"kallon agogo to shikenan sai an jima"""

"Cikin dariya yace ""sorry ma'una bari na duba agogon"""

"Ya kalli agogon da sauri sannan yace ""yanzu nayi hours da fitowa, amman ki dan kara min one hour kin"

yarda?

Idan ma ban yarda ba ya zan yi da kai. Ta kashe wayar.

"Ya dafe kai yana murmushi, ya fara kokarin kiranta amma bai sameta ba, da alama ta kashe wayarta ne"

"gaba ki daya, sai yaji ransa ya sosu, sam bai son damuwar ma'u balle bacin ranta, ya kuma san ba zata kunna wayar ba a lokacin don haka ya tura mata sakon lallashi."

"Sai da nana ta bata kusan awanni biyu sannan ta iso, dama ya gaji da jiranta, amma dai ba zai iya tafiya"

"ya barta ba ta shigo da sauri tana fadin ""tuba nake yi na yi zaton ma ka tafi"""

"Ya mike DA sauri yana fadin ""ni na isa na tafi na bar hajiya"""

"""Na gaya maka ka daina ce min hajiya ko Ahmad? Bari dai na dinga ce maka Alhaji kaima, hajiya sai kace"

"wata tsohuwa"""

"Yayi murmushi 'ni ban je ko airport ba ya sunan Alhaji zai hau kaina? Wuce mu je"" ya nuna hanyar fita"

daga ofis din DA dan yatsansa. Ta wuce suka fice har suka isa gurin motar tashi.

"Wannan shine karo na farko da nana ta taba shiga motar ahmad, ko lekawa ma bata taba yi

39 / 47