Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 47

102K to 105K   out of 139.6K words

jakarta dake gefenta, sai ta zura hannunta ta daukota ta mike tayi kofar fita daga dakin tana danna"

wayar.

Gaba dayansu suka bita da kallo ganin yanda ta fice bata kula da nauyin jikinta ba.

"""Hello Ruky Baby ya aka yi ne?"" Daga can bangaren ruky ta fashe da dariya tana fadin ""baby kin makale"

kin ki kiranmu ko? Wai me ake ciki ne akan dan kadafin da ya makale miki ne?

"Raliya ta makale jikin bandaki tana hango gidan taga babu kowa sai tace ""shegiya sai yau kike nemana?"

"To yau dai za a gara shirin yakin ba a yi komai ba, amman ni fa na dan fara shakka kamar ba zai amshi cikin nan ba"""

"""Ke banza kada ki karaya ko ki bata mana shiri, boka ya tabbatar min da lallai sai ya amshi cikin nan, idan"

kika fara karaya kuma yaya za ai ya yarda ya amsa?

"Raliya tayi ajiyar zuciya tace ""ba ki ji yanda ake min tambayoyi ba kamar ina gaban mala'ikan kabari,"

"masu tambayar tashin hankali, ke duk na tsorata WALLAHI ruky da na sani na taho da ke ma"""

"""Ki taho da ni? Ai da shirin ya ruguje domin suna ganinmu tare zasu yarda ribar bariki kika ci har kika"

"samu ciki. Ke dai kiyi yanda boka ce, ki dora a layar akan cikinki, kuma kuma ki kuskure bakinki DA ruwan"

"rubutun nan dole kowa ya yarda. Fatana dai da zarar kin haife masa cikin, ki ajiye ki dawo harka, kar ki yarda su kara kulla ki cikin gidan nan mai kama da akurkin kaji"""

"Raliya tace ""karki damu kawata, bariki ai ita ce gatanmu, cinmu kuma shanmu. Bari na koma sai na kira"

"ki da karin bayani akan yanda muka yi da su"""

"T kashe wayar tana murmushi, amman lokaci guda murmushin dake fuskarta ya dauke saboda ganin"

yayanta Musa da tayi ya fito daga bandakin yana mata wani irin kallo. Babu KO tantama yaji dukkan hirar

"da suke tattaunawa da kawarta cikin waya. ""Sakarya kin yi asara raliya, amman da sannu zaki gane shayi ma ruwa ne WALLAHI"" ya kada kai ya fice."

"Ta lafe jikin bango cikinta na hautsinawa tana zare idanuwa, ta shiga uku. _Amma idan ya san wata ai bai"

san wata ba_ ta raya hakan a cikin ranta. Ta nufi daki da sauri kamar mahaukaciya.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

40

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

A can gidan malam Sulaiman ma'u ce ke zaune akan tabarma tana cin tuwonta suna hira da ummanta

"dake gefe. ""Umma baki kula baba ya shigo cikin damuwa bane? Ko hirar da ya saba yi da ni yau bai yi ba, dakyar ma ya iya amsa gaisuwata ya shige dakinsa"""

"Umma tace ""Na gani mana, wata kila sai yau ya samu labarin abinda raliya ta zo DA shi, kin san daman"

"cikin maganarta yake yi"""

"Sani days fito daga bandaki ya kalle su da mamaki yace ""ciki kima umma? Raliya ce ta dawo dauke da ciki?"

"Suka mai da kallonsu kansa gaba daya, umman tace ""wai duk ba ku san meke faruwa ba ko? To ciki ta dawo DA shi tsoho kuma..."" Sani ya dawo kusa da su ya zauna akan kujera yana salati da sallallami."

A hankali 'yan uwan suka cigaba da shigowa kamar yadda aka sanar da su su zo. Aka ci gaba da tattauna

"matsalar kowa na cikin damuwa. Auwal ya kuta cikin fushi yace ""shegiya ai hakkin ahmad ba zai barta taji dadin rayuwarta ba"" daidai lokacin ahmad ya shigo kamar an wurgoshi, suka mai da kallonsu kanshi gaba dayansu."

"Ya iso wajensu yana fadin ""umma ni fa yunwa nake ji"" ya sami guri ya zauna. Auwal ya kalle shi yace ""kai"

"Ahmad sai kace wanda ya kwana da yunwa babu KO gaisuwa ka fara tambayar abinci? Ahamd yayi murmushin yana fadin ""tuba nake babban yaya, bari na fara ya kan uwata. Umma ina yini?"

"Umma ta amsa tana yake sannan ta mike tana fadin ""ka rabu da su, sai ka koshi zaka gai da kowa. Suka yi"

dariya gaba dayansu.

Duk maganar da ahmad yake yi idonsa da hankalinsa yana kan matarsa ma'u wacce ranta ke bace har

"lokacin, domin tafi kowa damuwa da abinda ya sami raliya, ko don ita macece ita kadai ta san ciwon mace 'yar uwarta."

Ahmad ya kura mata ido yana son yi mata magana amman yana jin nauyi har umma ta iso DA tuwo ta

"ajiye a gabansa da ruwa a kofi da kwano daban tace ""miko hannunka ka wanke a nan"" ya kalli kwanon yayi murmushi ya mika hannu kan kwanon ta tsiyaya masa ruwan ya wanke hannunsa."

"Sani yayi murmushi yace ""gaskiya umma mun gaji da wannan wariyar launin fatar, duk gurin nan don"

"ALLAH wa ta zubawa ruwa ya wanke hannu? Suka kara fashewa da dariya gaba dayansu. Auwal cikin dariya yace ""babu sai dan gatan umma"""

"Umma tayi murmushi cike da jin dadi, domin haduwar yaran haka yana sanyata cikin jin dadi. Bata ce"

"komai ba ta juya suka cigaba DA shakiyancinsu, ma'u tana dan murmushi kawai ba tare da tace komai ba."

"Sai DA Ahmad ya kai loma guda bakinsa sannan yace ""wai ita waccan uwar biyun meke damunta ne na"

ga tayi shiru sai yake kawai take yi?

"Umma dake kokarin zama tace ""abinda bai shafeta bane take kokarin dorawa kanta har yaje ya haifar"

"mata da wata cutar ta jawa mutane tashin hankali"""

"Auwal yace ""haba umma ai kuwa abinda ya shafi raliya ya shafeta, dole ta shiga damuwa"""

"Ahmad ya dauko loma guda zai kai bakinsa yana jin an ambaci sunan raliya ya dakata, ko sunanta bai"

fatan jin an ambata a rayuwarsa balle zancenta. Wani irin bacin rai da takaici ya saukar masa ya kasa sanya lomar a bakinsa ya maidata cikin kwanon.

"Ma'un ce ta kula da hakan, domin su duk hankalinsu yana kan maganar da auwal din keyi."

"Umma tace ""damuwar me zata yi? Dukkan macen da ta bar gidan ubanta ta tafi yawon bariki don tayi"

"cikin shege meye abin mamaki, ko abin daga hankali? To sai tayi domin abin bakin ciki ba zai a kare a gidan kanin ubanku ba har abada in dai ba su gyara halinsu ba"""

Ahmad yaji wani irin gingirin! Ya cika da tsananin mamaki da kuma takaici. Idan ya fahimci abinda suke

"tattaunawa akan raliya, to suna batun raliya ta dawo GIDAN da cikin shege. Nan take jikinsa ya dauki rawa, ransa yayi tsananin baci, domin idan har bai yi ciwon hauka ko na mantuwa ba ya san bai saki raliya ba, don babanshi bai bashi wannan izinin ba, hakan na nufin da aurenshi tayi cikin shege kenan."

"Sani ya kalle shi ya kula ya daina cin abincin yace ""Ahmad ba dai har ka koshi ba? Kai da kake kukan"

"yunwa"""

"Ummata kalle shi da sauri tace ""wai kai ma ja sanya abin a ranka har zai hanaka cin abinci?"

"Fitowar malam Sulaiman daga cikin daki ne ya katse musu hirar da suke yi, gaba daya yaran suka kama"

"kallonshi. Salisu ne ya fara fadin ""au dama baba yana cikin daki bamu sani ba umma"""

"Ta amsa da ""eh yana yin dan wani abu ne, amman na san zai fito ya ganku bayan ya kammala"""

"Suka fara kokarin gaishe shi yana amsawa, hannunsa yana rike da tabarma katuwa."

Ahmad ne ya mike da sauri ya karbi tabarmar dake hannunsa cikin girmamawa ya shimfida. Malam

"Sulaiman ya zauna yana kallonsu daya bayan daya. Kowanne daga cikinsu ya sha jinin jikinsa domin ganin halin da mahaifin nasu yake ciki, saboda basu saba ganinsa a haka ba, domin duk sanda ya shigo ya gansu a haka dadi yake ji, shi ma sai ya shiga cikinsu ai ta hirar da shi, amman yau sun ga sabanin haka,"

"yana gidan ma sun shigo kwata-kwata bai fito ba, basu ma san yana ciki ba sai yanzu."

"Bayan an gama gaisawa sai yayi shiru yana kallonsu, hakan ya kara sanyayar musu da jiki gaba dayansu."

"Daga can malam Sulaiman yaja numfashi ya dubi Salisu yace ""kai Salisu jeka wajen su jibrilu kace yazo shi da maidakinsa da kuma raliya"""

Salisu ya mike DA sauri domin cika umarnin mahaifin nasu.

"Ahmad ya yunkura da nufin ya tashi, don baya son ya kara koda kallon fuskar raliyan, amman malam"

"Sulaiman din ya katse shi ta hanyar yin magana. ""Ahmad ina kuma zaka je? Ai wannan zaman naka ne koma ka zauna"""

"Ahamd ya koma ya zauna yana mamakin jin abinda malam Sulaiman rada, amman yayi zaton ko akan"

maganarsa da ita ne malam din zai yi masa umarnin akan ya sake ta ne ya huta.

"Umma juws bata so hakan ba, don ba ta ga dalilin da zai sanya ya gayyato su cikin gidansu ba, gwara ma"

ya tafi can gidan ayi maganar tunda su ta shafa.

Kowa yayi shiru ganin yanda mahaifin nasu yayi shiru.

Bayan shudewar wasu mintuna kalilan Salisu ya dawo da sauri yazo gaban mahaifin nasa ya risina yace

"""ga su nan zuwa"""

"Malam Sulaiman yace ""shikenan kai ma samu guri ka zauna"" ba musu ya koma wajen da ya tashi ya"

"zauna, aka sake yin shiru ana sauraron abinda malam din zai ce, amma sai suka ji shi ma yayi shiru bai ce da kowa komai ba."

Can malam jibril ya shigo lami da Raliya na bin bayansa har da amina. Ma'u da sauran 'yan uwanta suka

bi raliya da kallo wacce ta zunduma katon hijabi kamar gaske. Ahmad ya kasa ko dago kai ya kalleta

saboda bakin ciki da takaici. Ko jin muryarta baya son ji balle kamshinta mai tayar masa da zuciya. Ya kara yin kasa da kansa bai son ko dago idonsa har suka sami guri suka zauna.

Abin mamaki sai ga raliya na kallon ahmad da yake akwai hasken wutar nepa tana son ta gano yanda ya

"koma, shin ya cigaba ko ya koma baya? Ta kasa dauke idonta daga kansa."

Malam Sulaiman ya kalle su saya bayan daya bayan sun zazzauna yayi gyaran murya ya kurawa malam

"jibril ido ya fara magana. ""Yauwa kamar yadda ya faru dazu jibril ya kira ni akan maganar ahmad sa raliya"

"wanda nayi tunanin mun wuceta a baya, amman yau ya dawo da wata sabuwar magana wacce ya dace ku ji ta daga bakinsa ba nawa bakin ba, domin masu salon magana sun ce waka a bakin mai ita tafi dadi"""

"Malam jibril yayi wuki-wuki yana kallon mutanen wajen, shi kana yana da shakku akan abinda zai fada"

"din balle su, yana jin kamar ana iza shi lallai sai ya fada. Ya kalle su yace ""eh to, akan maganar cikin dake jikin raliya ne, daman wai tace cikin na ahmad ne..."""

"Gaba daya suka kalle shi da mamakin jin abinda yace. Umma kam kai tsaye ta mike tana fadin ""kan uban"

"can! Wannan wacce irin magana ce maras kan gado haka?"""

*

*

*

DA ME AKE ADO?

41

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Umma kam kai tsaye ta mike tana fadin ""kan uban can! Wannan wacce irin magana ce maras kan gado"

"haka?"""

"Lami tayi caraf ta amsa ""daman ba zata yi kan gado a gurinki ba dije, amma mu a gurinmu tafi maganar"

"shahararren malami tasiri, ki karkade kunnenki da kyau ki ji..."""

"""Kai! Meye haka ne, wannan wanne irin hauka ne, kune kuke yin magana ko mune, waye ya sanya"

"bakinku a cikin wannan maganar?"" Malam Sulaiman ya doka musu tsawa ta hanyar fadin wadannan maganganu."

"Shi kuwa ahmad baki ya saki yana kallon ikon ALLAH, sai yake ganin abin kamar shirin fin din nan."

"Ma'u kam mutuwar zaune tayi, zuciyarta har ta fara raya mata miyagun abubuwa. Kar dai mijin nata"

"zagayawa yake yi gurin raliya suna watsewarsu ba tare da ta sani ba? Koda yake ai ance bai sake ta ba, matarsa ce kenan, in dai haka ne kuwa lallai yaci amanarta. Wani tukuki ya taso ya tsaya mata a wuyanta"

mai daci da ciwo. Ta dinga kallon mijin nata wanda shi kuma yake kallon raliya da mamaki da takaici.

"Gaba daya gurin aka yi tsit, kamar mutuwa ce ta gifta. Amman fuskar kowa ta nuna abindake zuciyarsa a"

fili.

"Malam Sulaiman ne yaci gaba da cewa ""ka cigaba da bayaninka mana jibrilu"""

Malam jibril ya kalli raliya wacce ke sunkuyar da kanta kamar ta nutse a kasa tana kara matsa layar dake

"jikinta wacce take ganin da ita ce zata iya magana a yarda da ita babu tantama. ""Ke raliya gaya musu su ji daga bakinki mana"""

"Raliya ta fara inda-inda tana zare idanuwa ""Daman... Cikin jikina..."""

"Lami ta amshe ""meye kike wani in-ina? Ki fito ki fadi gaskiya kada ki ji shakka ko tsoron wani"" raliya ta"

"dan samu kwarin gwiwa ta cigaba da magana ""cikin dake jikina na ahmad ne shine ubansa"""

"Ahamd ya mike a gigice yana fadin ""ni karya kike mini WALLAHI, karya kike yi..."""

"Malam Sulaiman ya kalli ahmad wanda jikinsa ya dauki rawa yace ""ahmad sami guri ka zauna kada na"

"kuma jin bakinka"""

"Umma ta kalli malam Sulaiman da tsananin mamaki, domin tana ganin kamar malam din yana goya"

"musu baya ne, kuma yana nufin dole ahmad din ya amshi cikin dake jikin raliyan."

Ahmad da sauran 'yan uwansa suka dinga kallon babansu da tuhuma suna ganin ko mahaukaci ya san ta

yanda zai yi wannan shari'ar balle shi.

"Malam Sulaiman ya mai da dubansa ga raliya yace ""ki ci gaba da bayaninki muna sauraronki"""

"Raliya ta dan ji karfin gwiwa tana zaton har ta fara gamawa da malam din ne tace ""tun kafin na bar"

"gidansa da cikin na tafi, kuma ya sani, shi kuma cikin ya kwanta nayi zaton ya fadi amma sai cikin watannin nan naga ya tashi, shine nace bari na dawo na gaya masa don ya sani"""

"Aka sake yin shiru dai ana kallonta tana ibda-inda, umma tana jin kamar tayi zage-zage ta huce, sai kwafa"

kawai take yi.

"Lami kuwa sai gyada kai take yi tana fadin ""haka ne kam"""

"Auwal ya daga hannu da sauri yace ""baba ina son zan yi magana don ALLAH"""

"Malam Sulaiman yace ""in dai akan maganar raliya da ahmad ne baka da ikon cewa komai, wannan"

"magana ce da ta shafesu su kadai"""

"Ya kalli raliya yace ""kin kammala bayaninki ko?"""

"Tace ""eh na gama, amma WALLAHI baba cikinsa ne ya sani"""

"Malam Sulaiman ya kalle Ahmad dake zaune baki bude kamar an dasa shi yace ""kace duk abinda ta fada,"

shin da gaske kafin raliya ta tafi daga gidanka akwai cikinka a jikinta?

"Gaba daya aka mai da ido kansa, idanuwan ma'u yayi kwalo-kwalo, kirjinta ya dinga bugu tamkar ana"

"lugude a ciki, jikinta kuwa tana ji kamar ya mutu, domin yayi sanyi lakwas. A cikin ranta addu'a kawai take yi."

"Ahmad ya dukar da kanshi kasa yana kada kai ya fara magana ""Abba kuyi hakuri da abinda zan fada dole"

"zata sanya ni fadinshi. WALLAHI TALLAHI tunda aka daura aurena da Raliya ko magana mai dadi ban taba yi da ita ba balle wata harkar aure ta shiga tsakaninmu, ban taba kusantar raliya a matsayin matar"

"aurena ba WALLAHI"""

Umma tayi ajiyar zuciya cikin ranta tana hamdala ga ALLAH.

Sauran ma duk ajiyar zuciya suka yi da jin dadi ban da Raliya DA lami da kuma malam jibril da yaji kamar

"ya kasa ta tsage ya shige cikinta don kunya. Ma'u kam wani irin hawaye mai dadi ne ya zubo mata, sai taji dukkan damuwarta ta yaye."

"Raliya kam fashewa tayi da kukan bakin ciki da takaici, domin ta tabbatar shegen bokan nan yaci kudinta"

"ne kawai a banza, tunda gashi aiki bai yi ba, amman dai bari ta kara jarrabawa."

"Cikin kuka tace ""kaji tsoron ALLAH ahmad WALLAHI wannan cikinka ne"""

"""Karya kike yi ban san komai game da shi ba, koda ace cikina ne ma me ya sanya baki haife min shi a"

"gidana ba ko anan gidan kafin ki tafi, sannan me ya sanya kika gudu daga gidana? Balle ma ni ban taba"

"kama hannunki ba, kuma ke ma kin tabbatar da haka. Raliya kiji tsoron ALLAH ki tabbatar zaki mutu, ki fadi gaskiyar wanda yayi miki ciki"""

"Cikin kuka tace ""WALLAHI cikinka ne, don ka auri ma'u ne kaki amsa'"

"Musa ya shigo da sauri yana fadin ""karya kike yi munafika ba cikin ahmad bane wannan"" gaba daya"

idanuwan kowa ya koma kansa ana kallonsa da mamaki. Kamar daukewar ruwan sama kukan raliya ya dauke ta fara wara ido.

"Lami kuwa fusata tayi ta cika ta batse ta dube shi da fushi tace ""ubanka ne ya sako bakinka cikin wannan"

"magana? Idan baka kiyaye ni basai nayi maka baki. Tsakanin miji da mata babu wanda ya san tsakaninsu sai ALLAH"""

Umma ta kalleta tana tabe baki don dai malam ya hanata magana ne da lami taji amsa sai kwafa kawai

tayi tana gyada kai.

"Musa ya cigaba da magana ba tsoro balle shakka. ""Lami ko zaki tsine min yau WALLAHI sai na tadi"

"gaskiya, domin wannan diyar taki raliya a komai bace face bala'i da masifa, dukkan abinda ya sami gidan nan itace ke janyowa, da ta riki aurenta tayi biyayya ga iyayenmu da hakan bata same ta ba, amman ta rufe ido ta watsa mana kasa cikin idonmu. Tabbas wannan cikin ba na ahmad bane, domin na jiyo hirarta da kawarta dazu ina bandaki a lokacin da ita kuma tazo kusa da bandakin bata san ina ciki ba, suke"

"tattaunawa akan maganar cikin."""

Nan ya kwashe labarin dukkan abinda yaji suna tattaunawa a wayar ita da kawarta ya sanar musu.

"Raliya ta kara rudewa, kunya duk ta cika ta kamar kasa tsage ta nutse a cikinta."

"Umma ta daga hannu sama tana fadin ""Alhamdulillah yau sakayya ta bayyana, ga SHGE ya tabbata a inda"

"ake ambatonsa kullum"" lami kuwa wuki-wuki tayi cike da tsananin kunya tana muzurai. Raliya ta gama cutarta."

"Shi kam malam jibril fashewa yayi da kuka yana fadin ""kin cuce mu raliya, kin zubar min da kima, ALLAH"

"ya isa ban yafe miki ba"""

"Malam Sulaiman ya daka masa tsawa yana nuna shi da yatsa ""kai rufe min bakinka jibrilu. A haka ma"

"baka yi mata baki ba ina kuma ga kayi mata baki? Ka barta kawai duniya ce ta ishe ta Riga da wando da duk wani abinda take takama da shi, tsakaninka da ita addu'a ce kawai ALLAH ya shirye ta"""

"""Amman dai yaya yanzu sai a hana ni la'antar wannan yarinyar wacce ke yawon duniya da aurenta?"

"Malam Sulaiman ya ce ""Ai maganar aure ta kare. Kai ahmad saketa yanzun nan duk da dama ta samu"""

"Ahmad yaji wani irin farin ciki ya baibaye shi wanda bai taba jin sa ba tsawon rayuwarsa, sai yaji kamar"

"mahaifiyarsa Asma'u mahaukaciya ce ta dawo duniyar ta sanar da shi waye shi. Cikin kwarin gwiwa yace ""Ni Ahmad na janye dukkan igiyoyin aurena akan raliya, na haramtawa kaina ita har abada"""

Raliya ta ja baya a tsorace

35 / 47