Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   29 / 47

84K to 87K   out of 139.6K words

""kar dai ace yarinyar nan ta koya maka irin shiririyarta Ahmad banda haka"

"kawai sai ku kwana gidan babu dalili? Ya mike tsaye ""gwara na wuce ni domin naga baku da niyyar tafiya"""

"""Ai tafiya ya zama dole kuwa. Ku tashi ku wuce gidanku"" inji malam. Ita dai umma murmushi take yi idan"

zasu kwana anan din haka take so. Ta samu damar ganawa da diyar tata. Domin ta gaya mata dukkan

abinda take son gaya mata. Saboda ta kasa zuwa gidan nasu. Duk DA tana son zuwa. Malam ne ya hana ta yana cewa wai me zata je yi gidan yaran tunda suna zaune lafiya ai shike nan.

"Haka dai ma'u ta tashi tana kumbura sai ga hawaye ya zubo mata, malam ne ya hau salati yace ""Asma'u"

"kuka kuna? To daga yau kin daina zuwa gidan nan tunda haka ne, kar ka kara barinta tazo ahmad"""

"Sai ta fashe da kuka tana fadin ""baba kayi hakuri, shine yake hana ni zuwa ko ina, idan na tafi yau ban"

"san randa zan kara zuwa ba"""

"""Hakan ya kamata yayi, ku je don ALLAH idan muka biyewa shiriritar Asma'u sai ku yi dare"""

Gana dayansu suka nufi kofa banda umma da ta Kamo hannun Asma'u da sauri ta ja ta baya.

"Dadi ya cika Asma'u don tayi zaton cewa zata yi ya zauna, amma sai taga ta hau ta DA fada amma cikin"

"nasiha. ""Kina jina asma'u yanzu kin zama matar aure ba iri daya kike da rayuwarki ta baya, don haka sai kin nutsu kin yi komai yadda ya kamata, ki daina gudu da tsalle ko ba a yi miki aure ba ya kamata ki"

"nutsu haka, ko baki san kin fara zama budurwa ba?"

"Ta rufe ido tana dariya kunya ta kamata, wai don ma umma bata san abinda ya faru da ita ba yau kenan."

"Umma ta katse mata kunyar ""kin ga bude idonki mu yi magana, kin ga babu lokaci"""

"Ta bude idonta da sauri tana kallon umman nata, umma ta cigaba da magana cikin hanzari ""yaya batun"

"girki kin iya yanzu? Kullum idan yayanki yazo na tambaye shi sai yace wai kin iya girki mai dadi, haka ne?"""

"Tayi dariya ""na iya mana umma, na iya dafa indomie da shinkafa da kuma taliya, ki tambaye shi ki ji,"

"rannan har miya na yi"""

"Umma tayi ajiyar zuciya ""har yanzu dai da sauranki, zan saya miki LITTAFIN KOYON GIRKI zan bai wa"

"yayanki ya kawo miki, mu je kada su gaji da jiranki"""

"Suka yi hanyar fita da sauri, umma tana cigaba da yi mata fada."

"Sai da suka isa waje sannan ta kalli umman nata tace ""umma shi kuma yaya baki yi masa fada ba, kice"

"masa ya dinga barina ina zuwa gidan, sannan ya bar ni na koma makaranta, don ALLAH umma'"

"Umman tayi shiru damuwa ta dan bayyana akan fuskarta tace ""a'a babu maganar zuwanki gida kullum,"

"yanzu bai kamata ki fara yawo ba, ki bari sai nan gaba"""

"""to umma makaranta fa, kin san yaya ne yake cewa zan zama likita, zan dinga taimakawa mata, sannan"

duk kawayena suna ta karatu ni ce kawai bana yi.

Daidai lokacin da suka iso gurin su Ahmad dake tsaye a soron gidan maganarta ta karshe ta doki

"kunnensu gaba daya. Ma'u tayi shiru ganin duk sun zubo mata ido, sai ta kama in-ina."

"Gaban Ahmad ya yanke ya fadi, domin in dai ma'u ta hada shi DA mahaifiyarta akan maganar"

"makarantarta ta gama da shi, domin ba zai iya ja da maganar mahaifuyarsa ba sam."

"Maganar malam ce ta katse masa fargabar da yake ciki. ""Ka shiga ku gaida jibril mana"""

Ahmad ya kalli malam din da sauri. Ma'u ta turo baki kamar zata yi magana. Maganar ummanta ta katse

ta.

"""Malam ai ina ga sun yi barci yanzu"""

"""Ko sun yi bacci ai za su iya zuwa su tashe su su gaisa dai, ku shiga ku gaida su"" malam ya bata amsa."

Ahmad ya shiga gaba da sauri ma'u ta rufa masa baya.

Abin mamaki sai suka hango lami ta fito daga kyauren soro sumi-sumi babu kunya balle tsoron ALLAH.

"Ashe labe take yi musu daman, ta san kuma idan suka shigo gidan dole mijinta zai fara nemanta."

"Umma da malam suka bi ta da kallo. Lokacin da su ma'u suka shigo gidan ta jiyo muryarsu, ta labe a"

"tsakar gidan tana jin hirarsu, sanda ta ji sun gama zasu tafi ta fito da gudu ta boye a bayan kyaure, bata taba zaton zasu shigo gidan ba."

"Lami ta wuce sum-sum ta nufi cikin gidan kai tsaye malam ya bita da kallo baki bude, umma kuwa salati"

"ta sanya tana tafi gami da fadin ""oh ni dije! ALLAH MAI IKO baka damu da mutum ba amma shi ya mai da lamarin rayuwarsa gaba daya kanka"" malam ya daga mata hannun ganin ta fara masifa yana fadin ""kin ga ya isa, wuce mu je ciki mu kwanta."" Dije tayi kwafa ta wuce tana huci da gyada kai. Malam ya bita duk"

da shi ma Ransa ya baci amma yana kokarin boyewa.

"Asma'u da Ahmad suka shiga cikin gidan suna kwalla sallama, jibril ya fito daga cikin daki yana goge"

"idonsa da kokarin gano masu sallamar domin akwai hasken wutar nepa. Mamaki ya dan bayyana akan fuskarsa, ya bude baki yana fadin ""wai wa nake gani kamar Asma'u?"

"Ta dan kalli yayanta tana murmushi. ""Ni ce baba, ina yini?"

"Lafiya lau Asma'u. Ahmad ya dan durkusa da sauri yana fadin ""baba ina yini? Jibril ya kalle shi da sauri ko"

"shi ya sauya amma sauyawar da Asma'u tayi DA girman da ta yi ya fi bashi mamaki kwarai da gaske, don shi yana dan ganinshi jifa-jifa."

Yana amsa gaisuwar Ahmad yana kallon ma'un kafin ya fara kwallawa lami kira.

"Sai gata ta billo daga soro simi-simi cike da borin kunya, ya kalleta cikin yanayin tuhuma. ""Daga ina kike"

"haka kuma lami? Gaba daya suka kalleta suma, sai ta kama susar keya. ""Na dan leka wajen dije ne samo ashana"" ya kada kai yana fadin ""oh!"""

"Su kuwa binta suka yi da Kallon mamaki da tuhuma, domin har suka baro gidan bata shiga ba, kuma basu"

"ci karo da ita ko a soro ba. Malam jibril ya cigaba DA magana ""ga Asma'u sun shigo gaishe mu"" ya mai da"

"dubansa ha su Asma'u ""wai yaushe kuka iso gidan ne ma? Ahmad yace ""ba mu jima da zuwa ba baba"" ya mike tsaye ""bari mu wuce, dare yayi. ALLAH ya tashe mu lafiya"""

"Cikin hanzari malam jibril yace ""amin"" wani irin dadi ya cika ransa ganin yanda ma'un ta zama."

"Suka yi musu sallama suka juya suka nufi kofar fita daga gidan, shi kuma ya bi su da kallo yana kada kai."

"Lami kuwa ta bisu da wata uwar harara kamar idonta zai fadi, ya saki wani uban tsaki wanda har sai da yaran suka juyo, ma'un ce ta waiga da sauri amma yayan nata ya ja hannunta suka fice."

"Malam jibril ya mai da kallonsa kan lami ""ke kuwa lafiyarki kike wannan tsakin sai kace wata tsaka?"

"""A'a macijiya ba tsaka ba"" ta bashi amsa tana murguda baki. Yayi kwafa. ""Yanzu yaran nan basu baki"

"sha'awa ba don ALLAH lami? Suna zaune cikin rufin asiri da kwanciyar hankali, sabanin diyarki da ba a san duniyar da ta shiga ba har yau"""

"Ta murguda baki gami da tafa hannu ""WALLAHI da aure irin na wannan shegen yaron gwara yawon"

"duniyar, da dai a dinga kirana kakar 'ya'yan shege gwara haka. Kuma ni diyata ba yawon duniya ta tafi ba ehe"""

"""Au kin san inda ta tafi kenan"" ya fada da hanzari."

"""Ko bam san inda take ba na san ba zata yi abinda kake fadi akanta ba, insha ALLAHU sai raliya ta baka"

"mamaki, sai ta dawo gidan nan da miji mai usuli da arziki da kuma nagarta"""

"Ya fashe DA dariya. 'Ta ina lallai lami ciwon hauka ya kama ki, na tabbatar banda hauka ta ina raliya zata"

"samu mijin kirki, yarinyar da bata gaban iyayenta, yarinyar da ta bi duniya yawon gantali..."""

"""Bakinka ya sari danyen kashi na kato, abinda kake fada akanta ba zai tabbata ba insha ALLAHU."""

"Ya kada kai ya shige daki yana fadin ""sai kuma ki yi lami ni bacci nake ji, amman zamu gani"""

"Dukkan abinda suke yi yayan raliya Musa yana cikin dakinsa yana jin su, idonshi yana zub da hawaye,"

"zuciyarsa na raya masa me ake yi da iyaye irinsu? Ba don kada yayi sabo ba ma da sai yace ina ma na su ne suka haife ba, kawu Sulaiman ne ya haife shi da matarsa umma."

"Wani lokacin ma gwara halayyar mahaifinsa akan ta mahaifiyarsa, don da ya sami MACE TA GARI ba zai"

yi wasu abubuwan da yake yi ba sam.

Haka dai Musa ya kom ya kwanta cike da takaici da tarin bakin ciki.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

31

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Duk wani taimako da dabara ahmad ya koya ma'u na ganin yadda zata tsaftace kanta. Tun tana jin

"kunyarsa har sai da ta saki jikinta DA shi, bata iya boye masa komai, domin randa jinin ma ya dauke sai da ta taddashi yana kallo tace ""yaya kasan wani Abin dadi kuwa?"

"Ya kada kai yana murmushi ""yau jinin nan ya dauke gaba daya"" yayi murmushi ""Ho ma'u! Wato an daina"

"jin kunyata ma kenan yanzu ko? Shi kenan sai yin wankan haila, kin iya ko?"

"Ta isa kusa da shi ta zauna tana murmushi ""na iya yaya tun a makarantar islamiyya an koya mana. Sai dai"

"wankan yana da yawa. Akwai wankan janaba akwai na haila da na wankan biki da sauransu, to ni wanne zan yi? Ko da yake ma ai duk iri daya ne sai dai niyya ce ta bambanta ko?"

"Ya kada kai ""haka ne, ke zaki yi wankan haila ne don haka sai kice NAWAITU GUSULUL HAILATI FARDAN"

ko kice da Hausa NA YI NIYYAR YIN WANKAN HAILA FARILLA sannan sai ki fara yin wankanki tunda kin ce kin iya ko?

"Ta kada kai ""na iya amma yaya ita kuma janabar mace ce ita, ita ma irin jinin hailan ce ko mece ce ita? Ya"

"tsare shi da ido tana jiran taji amsar da zai bata. Shi kuma duk ya rikice ya ma rasa amsar da zai bata. Ma'u DA tambayar tsiya take, amma bari ya yi mata baro-baro ko ya huta. ""Kin san me ake yi idan an yi"

aure tsakanin miji da mata?

"Kafin ya karasa tace ""na sani mana girki da shara da kuma wanke-wanke ko? Bai san sanda ya fashe DA"

"dariya ba yace ""ba wannan bane raya sunnar ma'aiki ne aure"

"Ta kuma katse shi ""raya sunnar ma'aiki kuma, yin sallar dare ko azumin litinin da alhamis?"

"""Duk ba su bane, bari na nuna miki raya sunnar ma'aiki"" sai ya kamo hannunta ya ja ta jikinsa ya"

"kankameta domin hakan zuciyarsa ke ayyano masa yayi tunani. Ya tuara bakinsa cikin nata, jikinta ya dauki rawa tsoro DA firgici ya shige ta, ta kama kokarin kwace kanta DA fasa ihu amman ta gaza. Ta fara"

ja da baya kafin ta fashe DA kuka. Tana ganin ana yin irin wannan a cikin fina-finai wanda a ganinta sai

yan iska ne suke yi. Me ya sanya yayanta zai yi mata haka?

Kunya da fargaba duk suka baibaye shi wai wanne irin rashin hankali ne ya jagorance shi ya aikata haka

ba ma'u? Yarinyar da bata san komai ba?

"Ya mike ya isa inda ta takure tana shisshikar kuka. ""Ma'u meye Abin kuka kuma? Wai baki san meye aure"

"ba ne? Wannan abinda nayi miki shine soyayyar aure..."""

"""Ba shi bane wannan iskanci ne, turawa ne suke yi a cikin fim, kuma umma da baba ma idan ana yi ko a"

"talabijin kashewa suke yi, haka ma a gidan yaya auwal idan ana yi fada yake yi, kai me ya sanya kayi min yaya?"

"Ya dafe kai da damuwa, wai wacce irin yarinya ce ma'u, ga ta haihuwar birni kuma 'yar makaranta"

"wadda ya kamata ace ta san komai amma babu abinda ta sani. Ya gyara murya yana shirin sake lallaba ta, amma tuni ta fice daga cikin dakin tana ci gana da kuka. Ya bita DA kallo ya ma rasa me zai yi."

Washe gari da sassafe ya shirya ya fice gurin aikinsa ya bar mata rubutu a takarda ganin bata tashi daga

"bacci ba. Yau basu kwana daki daya ba ma shi can falo ya kwana don ganin duk ya firgita da shi yau, zuciyarshi fal da tunani ya fice."

***

"Kamar yanda suka saba, kullum sai sun yi meeting kafin su fara aiki da manajojin gidan man, sannan ayi"

lissafin Abin dake cikin litar kowa.

Yau mai gidan man ne baki daya da kansa yazo. Wato ALHAJI NURA KWANGILA 'YAN LEMAN duk

"ma'aikacin da ya ganshi sai gabanshi ya fadi, domin ya riga kowa isowa Ahmad ne kusan na karshe a shigowa."

"Gabansa ya yanke ya fadi, amma da ya dubi wayar hannunsa ya ga har lokacin bakwai bata karasa ba, ya"

"dan ji dadi a ransa, domin ya san bai yi latti ba kenan."

Bayan duk sun taru babban manajan ya sanar da su ya bude sabbin gidajen mai ne a legas yana son zai

debi wasu daga cikin ma'aikatan nan suje su hadu da wadanda za a diba sabbi a can suyi aiki na tsawon

"watanni uku da su, har wadancan su sami gogewa, don haka kowa ya kasance cikin shiri sunansa zai iya"

fadawa.

"Da wannan yayi sallama da su ya tafi, kusan kowa bai son sunanshi ya fada don ba mai son yayi nisa da"

"iyalinsa. Musamman shi ahmad da yake da danyar amarya shakaf, ina zai wuce ya bar ta har tsawon wadannan kwanaki? Don haka a fili da cikin ranshi yake addu'ar ALLAH ya sanya babu shi din."

Yana gab da tashi daga aiki yaya auwal ya kira wayarshi bayan sun gaisa auwal yace idan ya tashi daga

"aiki ya biya ta can gidan. Ya amsa masa da to suka yi sallama. Sanda ya isa gidan yaya auwal matarshi Hafsat ta sanya shi a gaba da tsokana da zolaya, tun yana ramawa har bikinshi yayi shiru da ta fara"

hadawa har da matar tashi.

"Yaya auwal yace ""kin ga Hafsat idan zaki taimaki yaron nan ki bashi abinda kika ce to, idan kuma ba haka"

"ba yayi tafiyarsa"""

"Ta mike tana dariya ta shiga cikin daki, suka cigaba da hirarsu da yaya auwal. Minti biyu Hafsat ta fito"

"daga dakin hannunta rike da bakar leda ta karaso wajensu ta mika masa. ""Amshi wannan ka kaiwa matarka tayi ta karatu Hausa novels ne"""

"""Wai kina nufin irin littafan soyayyar nan ne anti hafsa?"

"""Eh sune tunda yayanka ya bani labarin halin da kuke ciki da ma'u naga babu mafita bayan bata"

"wadannan littattafan tayi ta karantawa, domin idan nace zuwa zan yi da kaina gidan na fahimtar da ita,"

"to zata jima kafin ta fahimci abinda zan koyar da ita har ta koya ta kware, amma cikin wannan labaran zata koyi komai kuma ta san komai"""

"Ya karba yana jijjiga kai, cikin ranshi yana fadin ""na zata ai babu komai a cikinsu sai hirar soyayya mara"

"kan gado, amma dai ba a kin ta mutum"" yayi mata godiya sannan yayi musu sallama zai wice don yaga dare yana shirin yi masa."

"Lokacin DA ya iso gidan ya tarar da yara a falon suna ta kallo, amma yana shiga yaran suka fara ficewa."

Domin tun ranar da yayi musu barin makauniya suke tsoronsa. Ya tsaya daga bakin kofar rike da labule yana kurawa ma'u kallo da ta kau da kanta gefe tana wasa da yatsan hannunta.

"""Ma'u baki gan ni bane ba?"

"Na gan ka mana, sannu da zuwa. Ta fada a fili, a ranta kuwa cewa tayi ""me zan yi maka kuma?"

"Yayi murmushi don ya san shi mai laifi ne a gurinta ya karasa kusa da ita, ya mika mata ledar dake"

"hannunsa. ""Karbi wannan ledar inji aunty Hafsat yace ki yi ya karantawa har ki gama da su cika"""

"Ta leka cikin ledar ya waro ido ""duk wannan sai kace wata jaka, na dai karanta wasu kawai"""

"""Duk yadda kika gani haka zaki yi. Me kika dafa ne yau a gidan?"

Dan wake mana

"Dan wake ma'u a wannan daren? Ya tambaye ta da damuwa. ""Babu kyau ne cinsa da dare yaya? Ta mai"

da masa da tambayarsa.

"""A'a ban ce ba, zubo min amma kadan"""

"Ta mike ta nufi kicin din, ya dafa kai cikin zuciyarsa yana addu'ar ALLAH ya sanya ma'un ta sauya sanadin"

karance-karancen kamar yadda anti Hafsat ya fada masa.

***

"Washe gari bayan ya fita aiki tayi shiru tunani duk ya cika ranta domin babu yaron da ya shigo mata,"

"kusan kowa yana makaranta. Tunanin kawayenta ya dinga fado mata a rai, tana tina irin rayuwar da suka"

"yi a baya. ""Yaya suke yanzu? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta. Idonta ne ya ciko da kwalla damuwa fal a cikin ranta."

"Can sai littattafan da yayan nata ya kawo mata suka fado mata. Ta mike da sauri ta nufi daki ta dauko su,"

daya bayan daya dakyar ta zabi daya daga cikinsu ta haye kujera ta fara karantawa. Wasa-wasa dai littafi ya mata dadi har ta kasa ajiyewa.

"Koda 'yan hirar nata suka zo mata yau bata kula su ba, ko abincin rana bata ci ba, don bata iya tashi ya"

"girka ba balle wanke-wanke ko shara, sai da taga yayan nata yana gab DA dawowa sannan ta mike ta fara gyara gidan."

"Soyayyar jaruman littafin ta burge ta kuma ta matukar kayatar da ita, domin har sun yi aure sun fara"

"gudanar da rayuwar aure. Nan gurin kam ta jima shi ma tana tunani, wannan shi ne aure kenan?"

"Itace irin hirar da take ji siniyoyi suna yi a makarantarsu, har yayan nata ya tadda ta bayan sallar magriba"

"tana ta karatun. Yayi murmushi ganin yadda ta gwaggwafe ya kula bata san ya biya ba ma. Yayi gyaran murya, ta mike da sauri tana yi masa sannu da zuwa. ""Yaya aka yi kanwata, da dadi kenan littafin?"

"""Da dadi yaya, ka yi wanka kaci abinci na baka labari, labarin akwai dadi WALLAHI"""

Ya kada kai ya wuce. Yana cin abinci tana bashi labarin littafin da take karantawa. Ranshi yayi wasai

"domin ta fara sakar masa jiki, kuma ya gano karatun zai rage mata kewa da kadaicin makaranta. Haka yayi ta jin labarin yana kada kai. Kwanaki kusan uku kullum idan ya dawo daga aiki da labarin da zata"

bashi.

"Yau ya dawo ransa a cunkushe, domin yana daga cikin wadanda Alhaji Nura Kwangila ya sanya a tafiya"

"legas, dukkan abinda zai nisantashi da ummansa da ma'u baya kaunarshi, domin kullum da safe kafin ya tafi aiki sai ya biya duk sammakon da yake yi, ita kanta umma har ta saba,

29 / 47