Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 47

9K to 12K   out of 139.6K words

yakuma yama dan gayu cikin lokaci kankani yasayi babur dinsa irin wanda samarin zamani ke yayi tsutsun soyayya ...

4ã 4ã ba umma ba hatta mlm yadaina kukan babu domin Auwalu da sani da Ahmad sun isheshi kowa akwai abinda yaware yake siya awata don ma dai Auwalu yatattago Aure amman duk da haka yana iyakacin kokarinsa ko kishin yanda rayuwar gidan ke gudana Lami batayi nata sanya yayanta suzama mutane nagari idan kafidda musa saishegen kishin tsiya da kyashi Raliya kam likkafa taci gaba tazama gogaggiyar yarduniya domin duk tayi billicin tayi fari tas kamar gauta ga tara samari kala kala akofar gidan tun yayyen suna fada har sun gaji sun watsar domin lami ke dauremata gindi tace anayiwa hassada dakyashi cikin wannan sati aka kai kayan Auren Ahmad gidansu ummi saidai mahaifinta yatsaida lokacin biki gabadaya wata hudu wannan abin yafi yiwa Ahmad da ummi dadi domin sunkagu sumallaki junansu Abba da umma kuwa sunyi farinciki da hakan Ahmad kam yadage hada kayan Aure sai Alokacin yagano kokarin da Auwalu yayi dominshi har gini mayayi koda yake tuni yazama cikakken ma.aikaci yana da albashi me kyau shi kam haya zaikama dole amman gaskiya ba zai kama hayar karamin gida ba domin yasan Umminsa yar gayuce gwara ya kama gidan da zaiburgeta saura wata daya biki yagama hada kayan lefensa yayi kokari matuka domin saida yayi akwatuna hudu sanda yakawowa su umma kaya sun cika mamakin kokarinsa daganan yafara kokarin nemo gida da kudin haya dama babansa ya sauke masa sadaki domin tun sanda za.akai kayan lefe yabada dubu ashirin na sadaki biki yarage sauran sati biyu yasami gidan sa makyau acan Unguwar gaida mai dakuna madaidata guda ukku da kichen da bandaki dangin Ummi harsunzo sun gani sunyaba komai gabadaya gidan ansanya masa wuta yaimasa fenti maikyau saidai abinda yafi damunsa da za.ayi bikinsa ma.u bataman domin suna gab dafara jarabawa tunsauran kwana goma biki yafara rabao iv nabiki yabaiwa Ummi nata anshirya shagali daidai na takala ma'u kam harkuka tayi amakaranta domin tana lissafin bikin yayanta yazo saura sati guda biki da magriba Umma tana tsakar gida tana ta aikace aikace mata suka fara shigowa gidan da sallama dauke da akwatuna riki riki mamaki yacikata ta mike tsaye tana tambayar lafiya daga inakuma? Domin tasan basuda wata budurwa daza.akawo kayan aure saida suka gama ajiye kayan babu ko gaisuwa daya daga cikinsu ta kalli umma tace daga gidansu Ummi aka aiko mu mudawomuku dakayan aurenku domin ajiya mukasamu labarin ashe yaron dake neman diyarmu ba danku bane ba shege ne daba.asan asalinsa ba Umma tadafe kirji cike da fargaba daidai lokacin Ahmad yashigo gida inyajikomai akunnensa don haka yatsaya turus a bakin kofa cike da tsananin damuwa datashin hankali MUHADU AKASHI NA BIYU



BOOK 2



1ã DAME AKE ADO 2 Uban waye yagaya muku wane munafuki ne yasanar daku wannan magana Umma tafadi ahasale batabar sunce komai ba tadora da masifa to duk wanda yagayamuku karya yake yi hassada ce kawai nice nahaifi Ahmad nice uwarsa Afusace take maganar Daya daga cikinsu takuma amshewa haba baiwar Allah kiyi hakuri munriga munji komai zance duniya fa baya buya Idan har danki ne mai yasanya aka cireshi daga lissafin sunan yayan gidan kinada Auwalu da sani da rabi'u yaya akayi shi yafita daban? Mu kinga yansako ne kiyi hakuri sai anjima tadire kudin sadaki akan kayan suka juya suka nufi kofar fita Umma tabisu dasauri tana fadin don Allah kudawo nayi muku cikakken bayani don Allah kudawo Basu saurareta ba suka nifi kofa suna ficewa suna ganin Ahmad suka kalleshi suka wuce kawai Umma data biyosu da sauri arude taci karo da Ahmad tsaye ta yi turus cike da tsanani tashin hankali tana kallonsa Ahmad yana tsaye idonsa yana zubda hawaye cikin muryan kuka yake fadin kirabudasu Umma ki kyalesu gaskiya suka fada munyi laifi dabamu gayamusu gaskiya tun farkoba wannan wace irin masifa ce wane irin cin mutunci ne wannan don cuta sai da muka gama komai harmun raba katin biki zasuzo mana dawannan maganar wane irin Abin kunyane wannan shikam tsananin tausayin Umma yafi komai yawa aransa wane irin so ne wannan baiwar Allah take yimasa ina ma itace tazo a matsayin mahaifiyarsa inama ana komawa baya asauya Uwa daya koma yafita daga cikin mahaukaciya yakoma cikin Ummansa mlm sulaiman dake sallama yashigo da hanzari jin kuka matarsa a rude yake yakalli deeje dake kuka yakalli Ahmad cikin tsananin damuwa yace lfy deeje meke faruwa haka kike kuka subhanallahi Dahannu ta nuna masa tulin kayan lefe dake jibge yakallesu yadawo da kallon kanta yakuma shiga rudu kansa ya kulle yace banfahimta ba deeje ? Cikin kuka tace daga gidnsu Ummi wacce Ahmad zai aura waisun fasa auren ...... Takuma fashewa dakuka yawaro ido waje da wata irin kidima mara fasaltuwa gabadaya jijiyoyin jikinsa sun janye saiji tamkar yadaskare dakyar ya iya karfin halin kakalo wani zancen bangane sunfasa Auren ba wani abu akayimusu tadansausata kukan tana goge hawaye

2ã tace ba.ayimusu kome ba mlm saidai munafukai sun shiga ciki lamarin anje angayamusu Ahmad wai shege ne ba shida uba banda wulakacin mai yasanya tunfarko basu ce haka ba saida aka kammala komai malam yayi shiru yama rasa abinda zaice domin iliminsa da tunaninsa suntsaya gabadaya na wucin gadin Lami dake labe tana jinsu tadaka tsalle cike da tsananin murna har da daga hannu sama ta fadi Alhamdulillahi da.anayimin wata fuffuka kullum yaro yana shiga manyan riguna shiga masu gida daman nafadamasa ba da riga ake ado ba da uba ake ado ehe! Takuma zuro kanta tana jiran jin abin da mlm din zaice tasami nadorawa sai jiyo shi yana fadin kunga kuwuce ciki muyi maganar kantabarma suka zauzzauna mlm yadubesu da damuwa yace duk Abinda Allah yakaddara babu makawa sai ya sami bawa daman can Allah baikaddaro ummi matarka bace Ahmad don haka babu yanda za.ayi ka aureta Umma tace Amman mlm baka ganin anbata masa suna kana ganin ko wata diyar yaje aure zata yadda ta aureshi malam ? Ahmad yadafe kai yana kallon umma tausayinta yana kuma karuwa aransa da kyar ya iya bude baki saboda nauyinda yayi masa yace Umma kiyi hakuri kiyi hakuri .......kuka yaci karfinsa malam yadube shi da tausayawa wato Umman yake baiwa hakuri Umma tace Ahmadu kai ya dace mu baiwa hakuri tunda mun kasa kareka daga wannan suna mummuna mun kasa cire kalmar shege daga jikinka Balaifinku bane ba Umma bakuda laifi kunyi duk wani yunkuri na boye wannan mummunan suna daga gareni Amman Allah yakaddara sai najishi Umma idan wanka ba.aboye cibifa malam yakalleshi da hanzari yace kaga tashi kawuce dakinka zansan yanda za.ayi idan takama aje a sulhunta nema zanyi zannemeka yamike dasauri yana tangadi iska naneman kayardashi saboda juwa akarshen kwanar gidan yaci karo da Lami tana lekensu takalle shi da hanzari saita juya tayi cikin gidanta yabita ka llo cike da mamaki mai tsanani bai san abinda yayima matar nan ba tasanyashi agaba yanufi gidansu Ummi yayi shiru yana tunanin idan yacemata shine zata iyakin fitowa kokuma iyayenta suhanata don haka yace da yaro kace Abdul ne bayan tafiyar yaron da kamar sakan talatin saigasu tare da Ummi fuskarta dauke da tsananin mamaki waye kuma Abdul yake sallama da ita mamakin ta yadada karuwa sanda takula bakowa bane sai Ahmad tsaye ya hade hannuwa akirji gabanta ya yanke yafadi tayi dan dum dum kamar zata koma sai kuma ta dake ta bata rai tace gani yaya akayine ? Tana magana babu ko fara.a

3ã tsananin mamaki yacika Ahmad yau Ummi ke masa haka yadaure da kyar yace Ummi babu gaisuwa kenanko? Takara hade rai tana fadin baikamata nagaida mayaudari ba kacuceni matuka Ahmad kasanya nabata lokacina daduk wani tunanina akanka Ashe kai shege ne bakada Asali maganar tadakin kirjin kwarai dagaske idonshi yakuma cikowa da kwalla kamar zaifashe da kuka yakwantar da murya cikin lallashi yana fadin

Ummi yanda muka gina soyayyarmu cikin aminci banyi zantan dan Abu kalilan irin haka zai iya mana itaba...... Takalleshe afusace tana fadin Au kai agurinka wannan yar karamar matsalace kenan amman ka bani mamaki matuka to idan kai ta zama karamar matsala a gurinka kana ganin doka kasance shege bawani abu bane to nikam Allah yasani babbar matsala ce bazanso nahaifi ya ya adinga cewar Ubansu shege ne mara asali ba maganar mungina soyayyarmu kuwa daman can akan tubalin toka da karya muka ginata don laillai dana san kai shege ne da banta lokacina akanka ba na soka Ahmad ashe kai mara asali ne ka boyemini kacuceni wlh kayaudaran .... Saita fashe dakuka 4ã DAME AKE ADO ....... Ahmad yaji duk yatsani kansa da rayuwarsa tabbas Ummi tayi gaskiya waye zaiso hada zuri.a da shege mara.asali hawaye dayake ta hadiyewa suka ci gaba da biyo kuncinsa yakasa cewa komai domin bashida sauran abinda fada din Ummi ta kalleshi afusace tace idan abinda ya kawoka kenan nizan koma domin inada abinyi a gida yayi dum yana kallonta da tsananin mamaki da damuwa jiyake kamar ya bita yakamota shikenan Ummi tayimasa nisa haka yajuya yanufi gida baisan yanda akayi yajeba yasandai Allah ne yakaishi Acikin gidama duk wanda akasanar da shi abinda yafaru cikin yan uwansa sai hankalinsa yatashi abinda suke tambaya shin Uban waye yaje yafada duk yanda sukaso ganin Ahmad sulallasheshi abin yatura don ya kargame kansa acikin daki Malam sulaiman kam yajima yayi shiru akan dakali yana tunanin mafita har zuwa lokacin da ya cimma burin tunanin nasa yasanya yaro yakira masa dan uwansa mlm jibril bada jimawa ba ya fito ya zauna kusa da yayansa yace malam gani naji ance kana kira na yakalle shi tsahon lokaci sannan yace kaji abinda yafaru da Ahmad kuwa? Dasauri yace naji wlh dazu na shiga gida Lami take sanar dani Abin kam baiyi dadi ba mlm sulaiman yanisa yace tunda abin nan yafaru nake tunanin mafita har Allah yasanya tunanina yafado kan diyarka Raliya da hanzari yadubeshi yace Raliya kuma mlm yagyada kai yana fadin ita kuwa kamar yanda kasani nima nasani Raliya tazama gagararriya wacce duk wani kokari namu dana yan uwanta yagagara gyara ta saidai addu.a gashi tayi girman daya dace ace tafidda miji amman anrasa wanda zaifito dagaske yace yana sonta saboda sanya shashanci datayi agabanta hakan nakeganin abune mawuyaci Raliya tasamu miji nutsattse don haka tunani yasanarda ni mezai hana tunda anyi haka amaida ranar auren Ahmad kanta kada acanza komai ayinan da wata gudan amman kai yakagani domin ka fini hakki akanta yayi shiru tsawoh lokaci yana nazari can yadaga kai yakalli yayanasa yace yaya duk abinda kayanke yayi saidai kana gana ganin Ahmadu bashida wata illah da zata iyayiwa rayuwar Raliya illah ? 5ã mlm sulaiman yaduberhe da sauri yace kada kace mini kacikin mutane masu jahilci dakama wani da laifin wasu wlh bagori zanyiwa kaina ba Ahmadu yafi duk yayanda muka haifa nagarta balle Raliya da kai kanka kasan irin abubuwan kunyar da ta daukowa gidan nan auren nasu shi zai zama rufin Asirinsu baki daya jibril ya girgiza kai yana fadin wannan haka yake to Allah yasanya Alkhairi mlm sulaiman yayi murmushi cike dajin dadi yace Amincewarka tafi komai agareni kuma koda hakan batafaruba kayan dakin raliya daman akaina suke tunda dai nine waliyinta dahaka suka rabu ran malam yahaskake yasan yana da damar kara kyautatawa Ahmad da mai dakinsa Adaki yatta Umma tana lazimi da alama addu.a take yiwa danta yasami guri yazauna yana murmurshi yace Allah dai ya.amsa Addu.arki saiki kwanta ki soma bacci Umma tadubeshi damamaki

Fuskarta babu yabo ba fallasa tace malam kenan kana zaton hankulanmu zasu kwanta cikin sauki kuma wannan kankanin lokaci ? Yakuramata ido yana karantar yanayinta yace Amman ai tunda abin nan yafaru Allah muke gayawa ba kyazato zai kawo mana mafita cikin gaggawa tayi saurin yadda da batunsa har daga fuskarta yafimci hakan ta hanyar yin murmushinta tana fadin duk abinda da akace Allah magana takare Amman taimakeni sanar dani wannan Abin dadin yayi dariya yana kokarin tattaro farin cikinsa suyi rabonshi tare yace danki dai yasami matar aure kuma awannan rana za.ayi bada fashi takalleshi datsananin murna da mamaki wacce tagaza boyuwa akan fuskarta tace najima banji labari mai dadin wannan ba dan Allah mlm wacece dan Uwanane ya.amince da baiwa Ahmad auren diyarsa Raliya kinga Asiri yarufu ko ?

7ã DAME AKE ADO Anacigaba dagudanarda sha anin biki Abba duk yaraba iv ga dangi da abokansa abin mamaki har sanarwa yasa agidan radio itama Umma tadauki dukanin burinta tasanya akan bikinnan hakanne yasanya yadanne zuciyarsa da damuwarshi ake gudanarda komai cikin farinciki duk da bahakanne akasan ranshiba Abinda yabashi mamaki da tsoro ya kuma sanya Raliya tafita daga ranshi baiwuce rashin mutunci datayi mashi cikin soron gidanba malam yayi matukar kokarinsa domin shine yayi duk wasu kayan daki na Raliya akaje akayi jere hatta kayan daya dace ace uwa tayi shine yayi domin lami cewa tayi Auren da akayiwa diyarta na dole ne donhaka ko tsinke bazatayi ba wadanda suka haka suzasuyi komai saidai mutane dayawa sungane borin kunyane domin babu tsiyar dataaje domin Auren diyarta tuncan baya kudinta wurin bin malamai yake karewa balle yanzu datake iyakacin kokarinta na wannan Auren baitabbataba domin acewarta diyarta kalar masu kudice da Asali ba kamar Ahmad fakiri ba Ranar kamu amarya ba yabo ba fallasa tayi kwalliya kamar gaske koda yake yayyanta sunyi mata fada harda mahaifinta da Abban duk da Ahmad duk da Ahmad bahalarta wurin kamun ba yayi farinciki kwarai dagaske da lbr dayaji gurin yara na yadda Amarya ta cashe rawa



13 April 2015 at 09:38 · Public

Save · More

Like

React

Comment

Share

LikeSadAngry78

Write a comment...



·

Halima Ibrahim

Allah yabiya

Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Zuhra Maigari

TANX,amma dan Allah adinga mana posting kullm.

1 · Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Bernges Kanu

duk maisan group din hausa novel na whatsap to yamin magana ta account dina dan samun shiga group din

Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Ya'aqub M Sabo

Hm daman can ummey bason ahmad din take b . Da tanasonsh jin cewa shi shege ne bazai sauya ra'ayinta ko taji cewa za ta iya wulakantashi b. Kawai tanunamasa halinsu na mata wato yaudara hakan na nuni da cewa koda ya aureta taji shi shege ne cewa zatai yasaketa. Kugyara halinku mata. Daga SULEIMAN MUSA SABO COPING.

Like · React · Reply · More · 14 Apr 2015

Musa Yusuf Shariff

Thanks

Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Khadija Haruna

Thnks

Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Jabeeru Inuwa

thanks alot

Like · React · Reply · More · 14 Apr 2015

Adama Adam Maidala

kash na so ace an hadashi aure da Asma'u

Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

Nabanje Samaila Saidu

Allah abin godiya

Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015

Bala Sani Hafsat

Tnxxx

1 · Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015

View more comments&



Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

------>DAME AKE ADO part 5.

8⣠DAME AKE ADO Karfe biyar daidai motonci daukar Amarya suka iso Raliya tayi wanka duk da batayi wata kwalliyaba amman tayi fes domin wata yayar Lami takama fada tanafadin tunda akadaura ya kamata su watsarda makaman yakinsu surungumi kaddara yaushe za ace akai amarya haka wannan yasanya tadan kimtsa idonta kemadagas babu alamun kunya itakadai tasan tanadin datayiwa Angon nata narashin mutunci buhu buhu haka akawuce gidan mijinta da ita saiwajen karfe 9 nadare Ahmad yagama kammala shirya kayansa tsaf cikin jakarsa don haka rataya kawai yayi yanufi gurin Ummansa tana zaune arumfa dasauran yan biki basu watseba yadurkusa yanagadin Umma zanwuce inabukatar Adduarku idan nayimuku wani abu kuyafemin don Allah yasunkuyarda kansa jin muryansa tana rawa tamkar zaifashe dakuka idanuwan Ummansa sunciko da kwallah tanajin kamar zata rabu da dantane har Abada Allah yajarabeta da tsananin son Ahmad bata son Abinda zainisantasu saigashi yau Aure zairabasu tayi shiru tsawon lokaci sannan tadaga kai ta kalleshi yana tsugunne kan kafafuwansa Kansa yana kasa Tunda nake dakai banta ganin wani abu na ashsha kona kaico agarekaba nasan Raliya zata iyayin komai domin ta tunziraka ta kuma hasalaka banason jin komai daga gareka sai alkhairi kada kayadda wani abu nabacin rai yafito daga wurinka kayi komai domin kafarantawa" babanka rai kiyayyar mace takaitacciya ce wata rana zata daina ranar daza awayi gari kunfara tara zuria shikenan komai yazama tarihi Allah yayimaka Albarka idanuwansa suka dinga zubdaí ½í¸­ inama yanda yake da iyaye nagari sukai masa fada yaji Raliya ma tanada su da Aurensu yazauna lfy daga can saman kansa yaji umma nafadin tashi kaje kada dare yayi Allah yayi maka Albarka yamike sumu sumi yana fadin Amin yawuce shikenan kyau zai bar gidansu zai bar cin abinci Ummansa ya isa kofar gidan nashi da babur dinsa yasauka yatura kofar ga mamakinsa sai yaga kofar abude take donhaka yatura babur dinsa yashiga tundaga tsakar gida yafara jiyo kugin radio ankure wakokin turawan zamani mamaki yacika shi domin dai daga dakin dake kulle wakokin suke fitowa yasan wannan dakin baccin Raliya ne yakada kai yanufi dakinda aka jera kujeru aciki domin yasan dakin da raliya take bazaisamu damar kwana acikiba ko bata rufo kofarba balle dakin abame yake ma har ya kwanta akan kujera yaga dacewar yakoma shagon gidansa kawai da kayansa ya zauna nanne dakinsa da asuba yatashi ya nufi masallaci tayi sallah yadawo yafara lazimi kamar yanda yasaba daman baisanya ran raliya zata tashi tayi sallah ba domin yasan batada wannan tarbiyar sai wajen 10 nasafe take tashi ai kuwa yau dinma hakane saida rana tatake sannan tatashi lokacin tuni yadade da karyawa domin flask yadauka yaje yasiyo musu shayi dayasha yabar mata nata aflask duk da yanacan daki yana hangota ta windo yaga tafito amman abinda yabashi mamaki har karfe goma raliya bata fitoba kuma gidan ba irin na yangun nan bane mai bandaki aciki balle yace tayi Alwala aciki can saiyajiyo sautin radio ansa kidan jiya naturawan zamani yaso yashareta amman sai yatuna yanzu hakkin raliya da tarbiyar ta duk suna kanshi dole yatunatar da ita gaskiya don haka yamike yanufi dakin nata yatura kofa dasallama tadaga kai cike da tsananin mamaki tana dubansa shikam yanayin daya taddata

4 / 47