Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   44 / 47

129K to 132K   out of 139.6K words

a san waye mahaifin"

"Ahmad ba"""

"Alhaji Nura Kwangila ya waro ido cikin tashin hankali da fargaba yace ""wai kana nufin shege ne bai da"

uba?

"Malam Sulaiman ya kada kai ""ko daya! Har yanzu dai bamu sani ba Ahmad yana da uba ko bai da uba. Na"

"gaya maka ne tun kan magana tayi nisa kuce an munafurceku. Shekarun baya wata mahaukaciya da take zaune akan bolar bayan gidana mai suna Asma'u ita ce ta haife shi"""

Malam Sulaiman ya kwashe labarin Ahmad kaf ya sanar da Alhaji Nura Kwangila tun lokacin da aka

haifeshi har zuwa yau.

"Gumi ya soma karyowa Alhaji Nura Kwangila, shike nan murna ta koma ciki, amman sai ya kalli Malam"

"Sulaiman yace ""ko zaka iya rike shekarun da abun ya faru?"

"Malam Sulaiman yace ""gaskiya ban rike ba sai dai akwai takaddu da hoton matar na ainahi da aka dauka"

"randa ta mutu, don danta ya amsa yaje an ciro fuskar mahaifiyar tasa yayi babban hoto dashi ya kafe a cikin dakinsa."

"Alhaji Nura Kwangila yace ""ka dauko su, bai kamata a zauna tsawon shekaru haka ba a yi cigiya ba."

"Sannan kuma ni jikina yana gaya min wani abu, amma don ALLAH yi gaggawa ka dauko mini hoton"""

"Da sauri Malam Sulaiman ya mike ya shige cikin gida, Alhaji Nura Kwangila ya kasa zama ya mike yana"

kaiwa da komowa da damuwa cikin ranshi yana ta addu'a.

Can sai ga Malam Sulaiman ya fito bayan dogon lokacin da ya dauka cikin gidan to rike da wata tsohuwar

"bakar leda ya miko masa. ""Wannan shine dukkan bayanansa har hoton mahaifiyarsa yana ciki"""

"Da sauri Alhaji Nura Kwangila ya karbi ledar ya kwance, hoton yake fatan ya gani."

"Ya dauko shi da sauri ya kura masa ido, sai ya fasa salati da kabbara yana fadin ""ANTI ASMA'U dama kece"

"mahaifiyar Ahmad? Tabbas Ahmad dana ne WALLAHI dan yayana ne. Wannan matar yayana ce da ta sami tabin hankali shekaru kusan talatin da biyu baya"""

"Malam Sulaiman ya cika da mamaki har ya kasa cewa komai, ya tsaya yana sauraron sambatun Alhaji"

"Nura Kwangila. Can yace ""bari na sanar da cikin gida, ciki zaka shigo sai mu yi maganar a nutse don na ga har yara sun fara taruwa"" ya juya ya shige cikin gida."

"Mintuna kadan sai gashi nan ya dawo ya dauki tabarmar da butarsa yana fadin ""biyo ni nan Alhaji"""

A cikin gidan ma Umma mamaki abun ya dinga bata. Aka ce a kirawo Ahmad din a waya.

Ana kiransa ya dauka hade da yin sallama.

Malam Sulaiman yace masa yazo yana son ganinshi amma ya tabbatar ya biya ya taho da iyalinsa baki

"daya yanzu"""

Hankalin Ahmad ya dan tashi amman da Malam Sulaiman yace masa kada ya damu alkhairi ne ya sanya

"hankalinshi ya kwanta, lokacin daman yana kan hanyar zuwa gida, don haka yana isa ya sanarwa da Ma'u sakon Malam."

Ita ma ta tsorata amman ya tabbatar mata babu komai kada ta damu.

Yaran su daman suna shirye cikin kwalliyar Juma'a don haka aka dunguma aka wuce gidan nasu.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

53

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Malam Sulaiman da Alhaji Nura Kwangila suna zaunne suna tattaunawa Ahmad da Ma'u da yara suka

"shigo suna sallama. Mamaki da tsoro ya dan kama Ahmad ganin Alhaji Nura Kwangila zaune a tsakiyar gidansu, amman dai ya dake ya karaso ciki."

"Alhaji Nura Kwangila ya kura masa ido yana kallo, sai yake gani kamar yayansa yake kallo. Ya jima yana"

jin Ahmad da kaunarsa ashe jininsa ne. Duk sanda ya ga Ahmad sai ya dinga jin kamar ya san shi ashe jinin dan uwansa yake kallo.

"Suka karaso suna gaida su, abun da ya dan fadar musu da gaba bai wuce kallo su da suka ga kowa yana yi"

"ba. Ita dai ma'u bata san ko waye Alhaji Nura Kwangila ba, shi ya sanya damuwarta bata da yawa."

"Suka zauna bayan an gaisa Malam Sulaiman ne ya fara yin magana ""Ahmad ka san wannan?"" Ya nuna"

Alhaji Nura Kwangila.

"Da sauri Ahmad yace ""na san shi maigidana ne Alhaji Nura Kwangila"""

"""Daga yau kada ka kara kallonsa a mai gida sai uba kuma mahaifi"" Malam Sulaiman ya bashi amsa."

Abunda ya fara fadar da gaban Ahmad da Ma'u kenan suka kalli juna da mamaki. Malam Sulaiman ya cigaba da magana.

"""Ya zo da wata bukata sai kuma bukatar ta sauya zuwa wani abu daban. A yau mun gano Alhaji Nura"

"Kwangila kanin mahaifinka ne da ya haife ka uwa daya uba daya! Abunda ka jima kana nema, ka dauwama cikin damuwa da bakin ciki saboda shi"""

"Mamaki da fargaba ya kama Ahmad domin har cikin ransa bai yarda da wannan maganar ba, yana ga"

"wata makarkashiya ce kawai Alhaji Nura Kwangila ya shirya don ya auri diyarsa, banda haka ta yaya ya gano shi dan dan uwansa ne yau bai gano tuntuni ba? Kamar Alhaji Nura Kwangila ya san abunda Ahmad"

"yake sakawa, don yana kallon irin yanayin da ya nuna."

"Ya fara magana ""Ahmad bayan dukkan kokarin da muka yi ni da diyata na ganin ka aure ta abun ya"

"faskara sai na taho gurin mahaifinka don neman alfarma, shine yake sanar da ni waye kai, bayan yayi min alkawarin hada aurenka da Nana."""

Ma'u ta kalli Ahmad da mahaifinta a gigice da damuwa hankalinta ya tashi gaba daya. Alhaji Nura

"Kwangila ya cigaba da maganarsa ""sunan da ya fada na mahaifuyarka da cewar tana hauka ya sanya nace idan akwai hotonta ya ba ni. WALLAHI Ahmad kai dan dan uwana ne Alhaji Abdullahi"""

"Ahmad ya kalle shi da wani irin yanayi, yanzu zancen ya fara shigarsa ya tattara hankalinshi gaba daya"

kan Alhaji Nura Kwangila wanda ya cigaba da bayaninsa.

"""Bamu da yawa cikin danginmu irin karamin iyali ne da mu, don kowanne bai wuce mutum zuwa uku ake"

haihuwa ba sai dai shi mahaifunmu shi daya babansa ya haifa duk da baban nashi yayi ta aure-aure don samun haihuwa bai samu ba sai shi daya kawai.

Duk da ALLAH ya sanya ba mu da yawa amma muna da arziki irin na gadon da muka gada kasancewar

iyayenmu asalin 'yan kasuwa ne na garin 'yanleman. Mahaifunmu Alhaji Abba bai samu haihuwa ba har sai da ya Shekara kusan goma sha biyar da aurensa duk da matansa hudu ne.

"Cikin ikon ALLAH a shekaru na kusan ashirin da aurensa ALLAH ya bai wa matarsa ta uku ciki, wacce ita"

"ce ta haife mu. Mahaifinmu yayi murna Kwarai da gaske da samun wannan ciki, ALLAH ya sauke ta lafiya dan ya sami soyayya da gata gurin kowa, hatta matan suna kaunar yayana Abdullahi."

"Daga kanshi ba a kara haihuwa ba shi kuwa daman mahaifinmu bai sanya aka ba, don haka ya dora"

"yayana akan harkokin kasuwancinsa tun yana da shekaru bakwai don haka don haka yafi mayar da hankali ga harkar kasuwanci tunda ya tashi, abun mamaki da dadi ga mahaifinmu shine samun cikina lokacin yayana Abdullahi yana da shekaru goma sha bakwai (17) a duniya, an fidda rai da haihuwa ALLAH Ya kawo ni, wannan ya sanya na Zama dan gata ta ko ina, amma ni na samu ilimi mai zurfi domin lokacin"

mahaifinmu ya fara gano amfanin ilimi.

Mahaifinmu ya rasu lokacin Yayana Abdullahi yana da mata biyu ya Zama cikakken dan kasuwa. Yayana

"Alhaji Abdullahi ya sami nasibi a harkar kasuwancinsa da ya gada gurin mahaifinmu da yake ya dan sami ilimi kalilan na zamani, kuma yana da nasibi akan kasuwancin."

"Yayana shine ya dauki dukkan nauyin rayuwata, naji dadi fiye da lokacin da mahaifinmu yana raye, sai na"

kasance matsayin dansa kuma kaninsa.

Uwargidansa ta kasa Zama saboda rashin haihuwarshi da kuma fitinar matarshi ta biyu Hajiya Lami

"wacce ta kasance mace mai fadan tsiya da iko.hatta ni kaina ina samun matsala da ita, fitar uwargidan ya sanya Hajiya Lami ta kara mike kafa tana yin duk abunda taga dama tsawon shekaru. Da yake Alhaji Abdullahi bai da fada balle fushi, shi ya sanya ta sami abunda take so, sannan mahaifiyarmu ma mace ce"

"mai kau da kai, a haka har shekaru suka ja."

Lokacin da na kammala sikandire yayana ya fara neman auren ASMA'U wacce ta kasance 'yar dan uwan

"mahaifinmu wato kakanta da namu abokan wasa ne. Dangi sun yi murna da hakan, don kwata-kwata ba za a iya cewa ga auren da aka yi na zumunci a cikin wannan iyali namu ba."

Sai dai Hajiya Lami ta tayar da hankalinta ta kuma yi dukkan abunda zata iya ganin hana auren amma sai

da ALLAH ya kaddara aka yi auren.

"Bayan an yi auren a nan ma tsugune bata kare ba duk da ba gidansu daya ba, a wannan lokacin Yayana"

"ya biya min kudi na tafi kasar waje karatu, amman ina jin labarin gida."

Hajiya Lami ta dan sassauta bala'inta ganin shekaru sun ja har kusan biyar ASMA'U bata samu haihuwa

"ba, sai take ganin kowa zai zauna haka ne."

"Shekarar da na dawo daga karatu na hada degree na da masters a shekarar komai ya faru, kasancewar"

yayana ya Gina katon kamfani a Kano wanda shine ya Zama na sarrafa mai da kayan abinci kuma ALLAH ya sanya nasibi a kai. Hakan ya sanya ya dauko Asma'u ya ajiyeta a nan ita kuma Hajiya Lami tana can

garin mu na 'yan leman a cikin jigawa.

"ALLAH ya sanya nasibi da albarka akan wannan dukiya ta yayana a garin Kano, sannan kuma ALLAH ya"

kara saukar masa da rahamar samun cikinka Ahmad. Babu Wanda ya san mahaifiyarka na da ciki har yayi wata uku a jikinta sai da ciwo ya dameta na kai ta asiniti daga nan aka tabbatar da ciki ne da ita na tsawon wata uku. Yayana yayi farin ciki da jin wannan labari har ya kasa boye murnarshi ya sanar

danginmu na can 'yan leman.

Cikin kankanin lokaci labari ya fasu har ya isa kunnen Hajiya Lami. Tayi matukar bakin ciki da jin wannan

"labarin, ta kuma kuduri aniyar ganin bayan cikin nan."

Kwatsam wata rana ina dakina kasancewar ina Kano gidan Asma'u lokacin Yayana yana can 'yan leman

daga ni sai ita a gida.

"Cikin dare daga dakina na dinga jiyo ihu da hargowarata, abun ya bani mamaki don na san ita ba"

"ma'abociyar rigima bace, don haka na fita da gudu sai na taddata cikin falonta tana ihu tana wurgi da duk wani abu dake cikin dakin."

"Na nufe ta da sauri da mamaki ina tambayarta abunda ya faru, amman sai na kula sam bata cikin"

"hayyacinta na fara kokarin riketa amma abun ya faskara, don watsi tayi da ni gefe, na kuma mikewa da sauri na fara kokarin rike ta, a wannan karon ma ta kara watsar da ni."

Da abun ya faskara sai na fice gurin Masu gadin gidan suma suka kawo mini dauki muka tura ta cikin

dakin baccinta muka kulle ta a ciki.

Nayi ta buga wayar gidan Yaya Abdullahi land line amma ba a dauka ba.

"Haka muka kwana cikin damuwa da tashin hankali, sai da gari ya waye sannan Hajiya Lami ta daga kiran"

"ta sanar da ni yayan baya nan, da yake wancan lokacin babu wayar hannu haka na hau mota na nufi garin 'yan leman na sanarwa da iyayenmu da yayana. Muka dingumo gaba daya cikin tashin hankali da"

tsananin damuwa muka dawo Kano.

Kai tsaye aka wuce da ita gidan nasu tabin hankali amman tsawon wata guda babu wani ci gaba da aka

"samu game da warkewarta, kullum sai dai a kulleta a cikin daki sai dakyar ake samu ta dan daina buge- bugen da take sai rawa da waka. Ga kuma ciki a jikinta."

Daga karshe dai likitocin asibitin suka bamu shawara akan gaskiya mu gwada na aljanu don abun nata

"yayi kama da sammu, amman sunce zasu yi mata allurar bacci yanda zamu ji dadin tafiya da ita gida."

"Hakan ko aka yi bayan an mata allurar bacci muka sanya ta a bayan mota muka dauki hanyar yan leman,"

muna tafe nine ke tuka motar yayana yana baya kusa da Asma'u ya dora kan Asma'u akan cinyarsa. Muna tafe muna hira har bacci ya dauke yayana ya jingina da kujera ya fara bacci sosai.

Kwatsam muna tsaka da tafiya sai naji an shaku wuyana an rike kam. Na fara kokarin kwatar kaina na

saki kan mota ina salati ina kiran yaya don na gano Asma'u ce ta shako min wuya.

"Yaya ya tashi a gigice yaga abunda ke faruwa ya fara kokarin bambareta daga wuyana abun ya faskara,"

motar ta kara gudu tana yawo akan titi muna ta ihu da salati har hatsarin ya afku.

"Ba mu farka ba sai a gadon asibiti, ni kam bayan buguwa babu abun da ya same ni, yayana ya samu"

"karaya da buguwa a baya, sai dai bayan ya farka matarshi da cikin jikinta ya fara tambaya, sai dai mummunan labari ya riske mu cewar mu kadai aka gani zube a gefen titi motarmu ta kama da wuta. Wannan ya sanya jikin yayana ya kara rikicewa don an ce matarshi ta mutu da kuma cikinsa wanda ya"

sanya rai da shi.

"Tun daga wannan lokacin har yau ba a kuma samun lafiyar yayana ba, shi da kansa yace a maidashi"

Saudiyya don ya fi jin dadin likitocin can da kuma Zama a can. Hakan ya sanya aka sai masa gida mahaifiyarmu ma ta koma can da Zama.

Bayan ALLAH ya toni asirin Hajiya Lami ta hanyar zuwan wani dan uwanta gidan suna hira naji ashe itace

ta shiryawa Asma'u wannan ciwo da bokanta.

"Nayi kuka saboda jin irin mugun tuggun da Hajiya Lami ta shiryawa Asma'u, na sanar da yaya abunda ya"

"faru aka hada meeting na gaggawa na iyalinmu da Hajiya Lami na fara fadin dukkan abunda naji tana fada, nan da nan hankalinta ya tashi ta fashe da kuka tana fadin ""tsautsayi ne ya kai ta ga aikata hakan"""

Yayana yana kuka yace ya saki Hajiya Lami saki uku! Ta sanya hannu aka tana ihu da rokon ayi hakuri ba

"zata kara ba, wannan ma wai tsautsayi ne da sharrin shaidan."

"Babu wanda ya kula ta don ta illata rayuwar yayana, ba zai kara samun macen da zata aure shi ba tunda"

ya Zama Mara lafiya. Wannan shine dalilin rabuwar yayana da Hajiya Lami wacce yanzu take cikin mugun hali na ciwon hauka ga rashin gata.

Alhaji Nura Kwangila ya goge hawayen dake zubo masa yana dariya lokaci guda.

"""Naji dadi na godewa ALLAH da ya kaddara Asma'u bata rasu ba sai da ta haihu. Ina zaton ganinka"

"Ahmad zai iya sanyawa yayana ya samu sauki daga ciwo da azabar da yake ciki tsawon shekaru, don ya"

"kasa mantawa da matarshi Asma'u, mace tagari mai KARAMCI. Saboda kyautayi da gatan da ta nuna min ya sanya da na haifi diyata na mai da sunanta akanta, wato NANA ASMA'U"""

"Wani farin ciki ya mamaye Ahmad har ma ya rasa abunda zai furta, sai yake kawai yake, kaunar Nana ta"

fara shiga ransa.ganin abun yake kamar a cikin mafarkin da ya saba idan ya kwanta bacci. Wai yau shine

ya san asalinsa da dalilin haukar mahaifiyarsa? Ashe mahaifiyarsa bata aikata wani abu na sabon UBANGIJI ba!

Malam Sulaiman yayi doguwar kabbara da godiya ga ALLAH cikin tsananin farin ciki da murna.

Umma kam bakinta ya ki rufuwa ashe zata ga wannan rana a rayuwarta?

"Kowa jinsa yake wani iri daban, kallo daya zaka yiwa kowa kaga mamaki da farin ciki karara akan"

fuskarsa.

A take a nan aka yiwa Hajiya Amina waya ta iso gidan. Ita ma tayi mamaki da farin cikin jin Ahmad dan

"gidan manya ne, aka dinga murna da mai da yanda aka yi."

"Hatta Malam jibril ma sai da ya shigo da ya ji hayaniya tayi yawa, don duk mazan gidan sai da aka Kira su"

a waya suka zo. Mamaki da tu'ajabi ya kama shi saboda ganin Alhaji Nura Kwangila a cikin gidan zaune a tsakiyarsu Malam Sulaiman suna tattaunawa don duk wanda ya kwana ya tashi a garin nan ya san Alhaji

Nura Kwangila.

"""Yau kuma masu dukiya babu iyaka ne suka zo gidansu?"" Ya ayyana hakan a cikin ransa sai kuma ya ji wai"

"kanin baban Ahmad ne, iko sai ALLAH."

"Dakyar Alhaji Nura Kwangila ya iya barin gidan, amma da rokon gobe za a bashi dama ya tafi da Ahmad"

can garinsu na 'yan leman sannan zai yi masa visa shi da iyalinsa su tafi Saudiyya gurin mahaifinsa da kakarsa.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

54

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Wannan dare mai muhimmanci ne ga Ahmad da duk wani mai kaunarsa. Bayan sun koma gida ya

kankame ma'u yana kukan dadi da farin ciki.

"""Ma'u ashe ina da rabon ganin dangina da mahaifina har da kakata? Ashe ina da rabon yin farin ciki har"

da alfaharin yanda kowanne da keyi da iyayensa da danginsa?

Ma'u me ya fi wannan dadi a gare ni? Me zan yi na godiya ga ALLAH? Tabbas ni din dan gatan UBANGIJI

"ne, bai taba tozarta rayuwata ba, bai taba wulakanta ni ba. Me zan cewa ALLAH?"

"Yana magana yana kuka, amman daga gani kukan farin ciki ne. Ita ma ma'u kukan take yi na taya mijinta"

murna da kuma rarrashinsa.

"Tace masa ""sallah zamu kwana muna yi da yin godiya ga ALLAH da ya kaddara mana ganin wannan lokaci,"

"wannan shine kadai hanyar da zamu nunawa ALLAH farin cikinmu"""

"Ya kada kai yana fadin ""haka ne tashi mu fara"""

***

"A cikin gidan su Lami kuwa, wuki-wuki Lami tayi jin asalin Ahmad tana zare ido, lallai ta ga dumbin darasi"

a rayuwarta.

"Malam jibril yace mata ""shi ya Sanya kullum nake gaya miki babu kyau wulakanta dan Adam. Yau dai ga"

"iyayen Ahmad da kike yiwa gori kullum shi shege ne to danginsa dangi ne masu asali da arziki. Ke yanzu ina dangin jikarki diyar raliya suke? Kin ga hakan ya tabbatar miki ke ce mai shege ba shi ba"""

"Sai kawai Lami ta fashe da kuka tana fadin ""lallai nayi kuskuren da ba zai gyaru ba, me ya Sanya na"

"biyewa zuciyata har na aikata wannan abun? Kaicona!"""

"Malam jibrul yace ""Lami ai baki daina kuka ba tunda har yanzu har yanzu baki san halin da diyarki raliya"

"take ciki ba"""

"Diyar raliya ta iso ta zauna akan cinyar Lami tana fadin ""ke Lami me aka yi miki kike kuka?"""

"Lami ta kalli yarinyar da tausayin halin da ta janyowa rayuwarta, da yanzu ita ce zata kasance cikin"

wannan daular.

***

"A gidan Alhaji Nura Kwangila kam dan karamin fim aka yi, domin yanda ya shiga da farin ciki yana"

kwalawa matarshi da diyarshi kira ya ba su mamaki don ba halinsa ba ne. Suka fito da tsananin mamaki suna tambayarsa abunda ya faru.

"Hajiya Batula tace ""duk yanda aka yi an tsai da auren Nana da Ahmad"""

"Dadi ya cika Nana. Alhaji Nura Kwangila ya kada kai, ""wannan abun yafi auren Nana da

44 / 47