Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   45 / 47

132K to 135K   out of 139.6K words

Ahmad, farin ciki"

"akan farin ciki, ku zauna na gaya muku abunda ya faru"""

"Ba musu suka zauna, Alhaji Nura Kwangila ya kalle su yana murmushi yace ""ashe Ahmad dana ne, domin"

"dan dan uwana ne. Shi ya Sanya ni da diyata ALLAH ya jarrabe mu da tsananin sonsa da kaunarsa"""

"Hajiya Batula ta cika mamaki, domin ta san duk abunda ya faru ga yayan mijinta, duk da lokacin ko"

"tunanin aurenta ma ba a yi ba, amma ta yaya hakan zata kasance?"

Nan Alhaji Nura Kwangila ya kwashe labarin duk abunda ya faru ya sanar da su. Nana ta daka tsalle ta

"rungume mahaifiyarta wacce ke yin dariya tana fadin ""sakarya kin manta ba ki da lafiya ne?"""

Sannan ta kalli mijinta da farin ciki.

"""Ban taba jin irin wannan labarin ba ko cikin littattafan hikaya ko kuma cikin fina-finan da ake yi ba. Lallai"

girma da tsira ya tabbata ga ALLAH. Wato a sanda ake tunanin Asma'u ta mutu ashe ita tana can cikin

"mawuyacin hali, sai dai ALLAH ya cika lamarinsa na haihuwar Ahmad sannan ta koma ga MAHALICCINTA. lallai wadannan mutane da suka rike shi sun cancanci Yabo"""

"Yace ""lallai kam shi ya sanya ya kasa hada diyarsu da kowacce mace a duniya, domin sun bashi aure ne"

"sanda kowa a duniya suka ki bashi diyoyinsu. Tsarki da iko sun tabbata ga ALLAH Mahalicccin kowa da komai, mai yin yanda ya so kuma a lokacin da ya so!"""

"Nana tafi kowa farin ciki, wato bayan Ahmad zai zama mijinta kuma zai kasance dan uwanta na jini, ko"

ma ya kasance.

"Su ma dai a haka kowa ya kwana da abunda yake sakawa a cikin ransa, amman duk umman Ahmad tafi"

"kowa farin ciki, don danta ya fita daga sunan shege daga masu yi masa kallon hakan."

***

Washe gari da sassafe Alhaji Nura Kwangila da iyalinsa suka nufi gidan Malam Sulaiman. Lokacin Ahmad

bai karaso ba shi da iyalinsa sai da aka Kira su a waya sannan suka taho.

Alhaji Nura Kwangila ya kalle taho da manyan motoci don tafiyar har da su Umma da Hajiya Amina

Su Ahmad suka iso aka fara gaggaisawa. Ma'u da Nana aka hada ido kowacce gabanta ya fadi da ganin

"'yar uwarta. Shi kam Ahmad dakewa yayi ya kasa kallon inda Nana take duk da yana jinta a jikinsa a matsayin 'yar uwarsa a yanzu, amma yana jin kunyar ma'u don ba zata zaci haka ba."

"Nana ce da kanta ta isa inda suke ta kalleshi tana murmushi da fadin ""yayana wannan ce Auntyna"

"Ma'u?"""

"Ya kalli ma'u yana murmushi wacce ta dan saki ranta yace ""eh ita ce, kin gan ta nan Maman yarana"""

"Nana tayi yake tana fadin ""Antina ina kwana?"""

"Ma'u ta dan saki jiki suka gaisa amma zuciyarta na bugawa. Ashe Nanan ma bata wuce tsararta ba, tayi"

zaton wata katuwar mace ce irin KISAN BOKO din nan.

"Nana kam ta dan tsorata don ta kula Ahmad yana bala'in son matarshi ma'u da ji da ita, kuma babu wani"

"abu da zata nunawa Ma'un, don babu wanda zai taba yin zaton Ma'un tayi auren fari balle ace har ta haifi 'ya'ya."

"Da aka tashi shiga mota sai tace ita motar Ahmad zata shiga, yaran suka koma motar Alhaji Nura"

"Kwangila wanda shine ya bukaci hakan da kansa, don kallonsu faranta masa rai yake yi, don yana ganin sun fara yawa kenan cikin iyalinsu, don duk yanzu sai tsofi da dangi na can nesa."

"Ma'u bata so hakan ba,amman babu yanda ta iya, sai dai kishinta ya gaza boyuwa aka Nana, duk da"

Ahmad yana nunawa ita ce fa matarshi ta gaskiya abar sonsa.

"Shine mai tuka motar ma'u na kusa da shi, Nana tana baya sai suka yi kamar basu san da ita ba, suka"

dinga hirarsu sai jefi-jefi Ahmad ke dan tsomata yace ko kanwata?

"Sai tayi murmushin yake kawai har sai da tayi da ta sanin shiga motar, a yanzu kam ta gano waye Ahmad"

"da kuma yanda ya dauki ma'u a cikin ransa bata da hadi da kowacce mace, don haka addu'a kawai ta dinka yi aka ALLAH ya kai su lafiya zuciyarta bata buga ba."

"Wannan abunda yayi shine ya sanyaya wa ma'u rai, ta tabbatar mijinta bai son Nana kwata-kwata kuma"

dukkan abunda yake gaya mata gaskiya ne.

***

"Lokacin da dangi suka ki waye Ahmad sun yi ta murna da mamaki, musamman gidan kakanninsu har"

"yanzu matan nan nasa suna nan cikin gidan gadonsu, Alhaji Nura Kwangila shi ke musu komai tunda ALLAH bai basu haihuwa ba, aka yi ta yawo da Ahmad ana nuna shi da Sanya masa albarka, sai da suka"

kwana biyu a garin sannan suka koma gida.

"Cikin wannan kwanakin kuma Nana ta gano lallai Ahmad da Ma'u sun yi nisa, amman bata karaya ba"

tana nan akan bakanta don ta san idan ta zamo matarsa dole ya sota kuma yayi adalci a tsakaninsu.

***

Duk wani mutum dake kamfani sai da yayi mamaki jin wai Ahmad dan gidan Alhaji Abdullahi yayan Alhaji

"Nura Kwangila ne, randa suka shiga ofis Alhaji Nura Kwangila ya mai da masa da mukamin D.G hannunsa, Nana kuma ta koma kan kujerarsa, don yace shi yafi dacewa da kujerar, sañnan ya fara nemar musu visa da passport musamman Ahmad da iyalinsa, ya kuma bayar da izinin gina wani katon gidansa da ya fara"

"yace a cigaba da aiki, babban gida ne sosai."

Sannan aka sauya Ahmad mota mallakinsa ta kansa tare da ba shi kyautar kudi masu yawa ya fara gyara

"gidanshi da iyalinsa kamar yadda Alhaji Nura Kwangila yace. ""A dukiya irinta mahaifinka ya kamata ace ka sauya"""

"Shi Ahmad rasa me zai yi ma da kudin yayi, sai kai ya dinga yiwa iyayensa da 'yan uwansa da Ma'u abun"

"alkhairi da su, har Ma'un ta dinga fada akan irin kashe kudin da yake yi mai yawa haka."

Ahmad yace bai yi yawa ba don bai ci ko rabin kudin da baffansa ya tura masa cikin account dinsa ba.

Rayuwa ta sauya. Daman dare daya ALLAH kan yi bature.

***

Sun sami tafiya Saudiyya gaba dayansu Nana da Ma'u da Ahmad da yaran da Alhaji Nura Kwangila.

"Idan akwai wani abu dake burge Ma'u ga Nana bai wuce yanda take son 'ya'yanta ba da ji da su ba,"

"tunda suka hadu da yaran ta share iyayen, bayan gaisawa bata kara bi ta kansu ba, don ta kula suna gab da haddasa mata dawowar ciwonta, suka dinga hirarsu da yara."

"Alhaji Nura Kwangila na kallonsu da dariya, ba ya ganin laifin Ahmad, ganin son da yake nunawa Ma'u"

don iyayenta da ita kanta yarinyar sun yi masa halaccin da bai kamata ya juya musu baya lokaci guda ba. Sannan kuma akwai SOYAYYA DA SHAKUWA mai karfi a tsakaninsu.

***

"Sun isa gidan Alhaji Abdullahi wanda yake babban gaske tun daga waje, suka tadda Hajiya Ruma a"

"falonta tana kallo, tsohuwa mai ran karfe."

"Jin dadi da kwanciyar hankali sun bayyana a jikinta duk da fatarta da jikinta ya nuna tsufanta, tayi"

matukar mamaki da ganinsu zuwan babu zato.

"Bayan an gaisa ta janyo yaran gurinta cike da sha'awa. Alhaji Nura Kwangila yace ""Hajiya da da hali hutu"

"ne ya kamace mu, amman abun dake tafe da mu ba zai bar mu mu huta ba idan ba mu fada ba. Ina Yaya Abdullahi yake?"""

"Tace ""Tun safe masu hidima suka tafi harami da shi..."""

Tana cikin maganar sai ga shi nan an shigo da shi cikin wani keken guragu irin na masu hali mai amfani

"da wutar lantarki, da kansa kuma yake tafiya."

"Farin ciki ya cika fuskarsa da ganin Alhaji Nura Kwangila da Nana, shi kuwa Ahmad zabura yayi ya mike"

"da sauri yana kallon mahaifinsa. Tabbas babu makawa wannan mahaifinsa ne! Sai yanzu ya gano da waye yayi kama, don yana kallon hoton mahaifiyarsa ya kasa gano kamarsu, ashe da shi yayi kama."

"Shi kansa Alhaji Abdullahi yaran ya fara suje gurinshi, suka tafi da gudunsu suna dariya da mamakin"

kekensa.

"Sai da aka nutsu sannan aka fara gaisawa, sannan Alhaji Nura Kwangila ya kalli yayansa yace ""yaya da wa"

"wannan matashin yayi kama?"""

Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad da sauri wanda bai maida hankalinsa akansa ba tunda ya shigo.

"Ya kura masa ido sai idonsa ya ciko da kwalla yace ""da ace Nana Asma'u ta haihu da zan ce danta ne"

"wannan, domin babu abun da ya taba kamanninsa da nawa lokacin da ina cikin kuruciyata. Duk inda wannan yaro ya fito jininmu ne, jinin Buba Wali wanda muka hada kaka na hudu da shi, don iyalan gidansa ne ke kama da ni"""

"Hajiya Ruma tace ""wannan haka yake"""

Ahmad yayi ajiyar zuciya da jin Dadi. Lallai ya kara sakankancewa wannan ne mahaifinsa.

Alhaji Nura Kwangila ya mike yana murmushi ya ciro hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji

"Abdullahi da shi ya nuna masa yace ""yaya ka shaida wannan wace ce?"""

"Alhaji Abdullahi ya karbi hoton ya kura masa ido, sai ya hau salati yana fadin ""Subhanallahi! Wannan ai"

"Nana Asma'u ce, Ma'una ce!"""

"Hajiya Ruma ta mike da gaggawa ta amshi hoton, sai ta koma ta zauna tana salati tare da fadin ""Nura ina"

"ka samo hoton gawar Asma'u, yarinyar da aka ce mana ta rasu a cikin mota ta kone kurmus ko tokarta ba a samu ba?"""

Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yana kallonsu ganin duk sun gigice sannan ya fara ba su labarin

abunda ya faru da Asma'u da danta da ta haifa har zuwa yau.

"Yana kaiwa karshe Alhaji eya kalli Ahmad yace ""WALLAHI wannan shine dana, kai jinina ne, zo nan na"

rungume ka naji dadi don ALLAH!

Ahmad ya mike da sauri ya isa ga mahaifinsa ya dora kansa bisa cinyarsa ya fashe da kuka yana goge kan

kamar wani karamin yaro.

"Alhaji Abdullahi ya Shafa kansa yana hawaye shi ma. Ahmad ke fadin ""Ashe ina da iyaye masu daraja"

"haka na dinga shan gori da hantara saboda rashinsu, ashe ni dan gata ne gaba da baya? Amma na godewa ALLAH da iyayena da na rayu a gurinsu basu tagayyara rayuwata ba. Na godewa ALLAH da ya"

"hada ni da ku sanda nake tsananin bukatarku"""

"Maganganunsa sai da suka dinga sanya kowa hawaye. Alhaji Abdullahi yace ""ka daina kuka Ahmadu,"

"WALLAHI ban taba jin dadi da jinin jikina yana tafiya kamar daidai kamar na yau ba. Dana ina jin kamar zan iya mikewa tsaye yanzu, kama ni na gani zan tashi, domin naji kamar na warke babu sauran ciwo a"

"jikina"""

"Ahmad ya mike da sauri ya kama mahaifin nasa, sai ya mike tsaye dakyar! Amma ya kasa tsayuwa sai ya"

"kwanta jikin dan nasa yana fadin ""ashe zuciyata ce ta mike ba gangar jikina ba, nayi zaton na tashi daga yau"""

"Alhaji Nura Kwangila ya isa kusa da shi ya kamoshi zai zaunar da shi sai Ahmad yace ""bar shi kawu zan"

"iya"" wannan kalma da ya gayawa Alhaji Nura Kwangila ya Sanya shi jin wani irin dadi da nishadi. Yace ""lallai yaya yanda zuciya ta warke insha ALLAHU kafafuwan ma zasu warke da yardar ALLAH"""

Hajiya Ruma da Ma'u sun kasa koda motsi sai hawaye. Ita kuwa Nana kallon Ahmad kawai take yi da jin

"dadi, dukkan sakwan sonshi na kara shiga ranta."

"An jima ana hira sallah ce kawai ke tashinsu, sai da dare yayi sannan kowa ya nemi makwnacinsa."

Alhaji Abdullahi yana jin kamar ya lashe Ahmad da iyalinsa.

Hajiya Ruma kuwa ta rike Ma'u katamau a jikinta suna jin kamar su cinyeta saboda kasancewarta mata

"mai son dansu, don Ahmad ya ba su labarin irin son da Umman Ma'u da iyalin gidanta ke masa."

Sai dare kowa ya nemi makwancinsa.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

55

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Cikin gidan nan kowa ya koma sashinsa da yake babban gida ne, Ahmad ba zai iya rabuwa da ma'unsa sa"

"ba, don haka sashi daya suka dauka, amman yaran suna gurin Hajiya Ruma, sai dai yini suke yi gurin Alhaji Abdullahi."

"Su kansu likitoci sun yarda Alhaji Abdullahi ya samu lafiya, dama sun san ba ainahin ciwon shi ya hana shi"

tafiya ba sai dai bakin ciki da ciwon zuciya ne wacce ta warke yanzu garas! Babu sauran rauni a tattare da ita.

Kafin sati gida sai gashi ya fara kokarin mikewa tsaye.

"Ahmad ya mai da rayuwarshi gaba daya ga mahaifinsa yana taimakonsa, shine yake yi masa komai,"

wanda kullum ke kara faranta masa ranshi yana Sanya shi cikin nishadi da samun sauki.

Ga ma'u kuwa tun bata sakin jiki ga Nana har ta hakura ta sakar mata saboda yanda take kaunar

"'ya'yanta da janta a jikinta, da ta ga kuma kowa ya gane tana kishin mijinta ne bayan ko babu komai"

"kanwar Ahmad ce wacce ta dalilinta mijinta ya gano danginsa. Kuma ta ga babu wani aibu na soyayyar da Ahmad yake yiwa Nana, ko ita ke yi masa, hakan ya Sanya ta ga babu amfanin cigaba da shariyar."

Nanan ce ta dinga janta zuwa harami suna addu'a da salloli. Cikin zuciyar Nana addu'a take akan ALLAH

ya sassauto zuciyar Ma'u ta bata Aron mijinta koda sau daya ne a Shekara.

Ita kuma Ma'u godiya take yiwa ALLAH bisa rahamar da yayi musu. Wai yau ita ce a gaban dakin ALLAH

"mai girma, me yafi wannan dadi?"

***

Satinsu uku suka fara shirin komawa Nigeria amma Alhaji Abdullahi da Hajiya Ruma suka dage su ma sun

"gama zaman Saudiyya tunda mai jinyar ya samu sauki yanzu har yana tafiya da sanduna biyu irin na masu kudin larabawa, don haka tare suka tattara suka dawo Nigeria."

"Da yake Alhaji Abdullahi yana da gidanshi bai sauka a can ba, sai ya sauka a gidan dan uwanshi aka bada"

umarnin a gyara masa nasa.

"Cikin kwanaki uku aka sauya komai na gidan, ya koma sabo dal! Hatta fenti. Suka koma shi da"

mahaifuyarsu da masu aikinsu wadanda dama tare suka tafi da su can kasa mai tsarki (Saudiyya).

"Lokacin da aka hadu da su Malam Sulaiman da Alhaji Abdullahi, kuka kawai Alhaji Abdullahi ya fashe da"

"shi, don ya rasa bakin da zai yi godiya ga su Malam Sulaiman, karshe yace dole zasu bar wannan gidan nasu cikin sati guda su koma wani sabo cikin rukunin gidajen da ya gina shi da iyalinsu gaba daya."

"Gini aka yi irin na quarters guda, manyan gidaje da manyan dakuna da za a sanya 'yan haya da amman"

"yanzu ya zama na Malam Sulaiman da iyalinsa. Da yake Ahmad dan halak ne sai da ya sanya har da sunan Musa cikin jerin wadanda zasu mallaki gidan da Hajiyarsa. Yayyensa kuwa kowa sai da ya samu daya, ALLAH ya raba su da yawon haya, don daman kusan duk yawon haya suke yi. Yaya Auwal ne ma ya fara gini a wani filinsa rabi wanda har yau ba a yi ko rabi ba, kuma abun jin dadin kowa kyauta aka ba shi"

"ba aro ba, da sunanka da takardun gidan mallakinka."

Alhaji Abdullahi yace wannan kadai zai yi ya san yayi dan wani abu daga cikin taimakon da suka yiwa

danshi.

"Sannan wadanda ke bukatar ajiye aikinsu suyi tare da shi, yayi musu alkawarin ninka musu albashinsu"

sau uku. Shi kuwa Yaya Auwal asibiti za a gina masa maimakon chemist din da yake yi a gida.

Bangaren su Umma aka sanya 'yan haya da suka fara addabar Lami da gori da tsokana.

"Cikin wannan lokaci aka kammala ginin gidan Ahmad, Alhaji Nura Kwangila ya sanya masa komai na jin"

"dadin rayuwar duniya, don gidan kanshi gari guda ne, don har su gama rayuwarsu wani gurin ma ba lallai su zauna a cikinsa ba."

"Ranar da suka shiga wannan gida daga Ma'u har Ahmad sai da suka yi kukan dadi, rayuwa ta sauya, farin"

ciki ya dawo sabo a gare su da duk wani mai kaunarsu.

***

Alhaji Nura Kwangila da Malam Sulaiman sun cigaba da shirye-shiryen bikin Ahmad da Nana kamar

yadda suka tsara.

"Ahmad ya kasa sanarwa da Ma'u don yana gudun irin halin da zata shiga, sai da ya rage saura wata daya"

"sannan Umma tace ya kamata su sanar da ita don haka suka kirawo ta har gida, ta taho cikin motarta domin Ahmad ya koya mata,"

"Umma da Malam Sulaiman suka sanya ta gaba cikin hadadden falonsu suka fara yi mata nasiha, ta kasa"

"gane akan mene ne, sai da aka ce mata ita matar mutum kabarinsa ce, kuma shi aure nufi ne na ALLAH sannan ta gano inda maganar ta dosa."

"Umma tace ""an sanya ranar auren Ahmad da Nana yau saura wata guda"""

"Ma'u ta zabura a firgice tace ""shi ne ba a gaya min ba don munafurci? Macuci mayaudarin banza"" ta"

fashe ta fashe da wani uban kuka.

"Umma tace ""ke kama bakinki mijin naki kike gayawa haka? Dukkan halaccin da yayi miki bai yi ba kenan?"

"Yaron da ya ki komai na duniya ya gwammace ya rasa komai saboda ke amman kike fadin haka a kansa?"""

"Malam Sulaiman yace ""ai ni ya dace ta cewa munafiki kuma mayaudari, domin har yau Ahmad bai san"

"me ake ciki akan maganar aurenshi da Nana ba, sannan bai taba cewa kala a kai ba, hasalima kamar nine nayi masa dole zai aureta tun farko, don haka ni ya dace ki gayawa haka ba Ahmad ba"""

"Ma'u ta kara fashewa da kuka, yaya zata yi da ranta ta shiga uku, amman da iyayenta suka sanyata a"

gaba da nasiha da ban baki da kawo aya da hadisi sai gata ta warware ta hakura.

"Sanda Ahmad yayi mata waya bata dauka ba, ya dan damu da yake yaran basa gidan suna gidan babansa"

"da kakarshi shi ya sanya su ma basu dauka sun gaya masa komai ba kamar yanda suka saba idan bata kusa da wayar, don haka ya nufi gidan kai tsaye, amman mai gadi ya sanar da shi ta fita."

Sai ya wuce gidansu kai tsaye anan gidan ya tarar da ita a gaban iyayensu tayi kuka idonta yayi jajir yayi

luhu-luhu. Hankalinshi ya tashi ya fara tambayarta abunda ya faru. Malam Sulaiman ne yace masa sun gaya mata maganar aurensa ne.

"Shima hankalinshi ya kara tashi yace ""baba kun bar ni na gaya mata kun ga yanzu kun sata a damuwa, ku"

"kalli idonta don ALLAH"""

"Umma tace ""ka ci gidanku rufe mana baki, kai da ka san yakin da muka yi da ita da baka ce haka ba, ka"

"tadda ta tayi laushi ne yanzu akan KISHI duk yarinya tabi ta haukace"""

"Ahmad yace ""da gaskiyarki fa, ke fa Umma baki san KISHI ba tunda baba bai taba yi miki ba"""

"Suka fashe da dariya gaba dayansu, Umma ta dauki filon kujera ta wurga masa tana fadin ""kaci gidanku"

"Ahmadu"""

"Malam Sulaiman yace ""gaskiya ya fada fa ko a gwada a gani ne?"""

"Suka kara kwashewa da dariya ban da Ma'u dake yake kawai, ita kadai ta san me take ji a cikin ranta."

Ahmad ya amshi mukullin motarta ya damkawa Malam yace zai turo direba ya amsa zasu wuce a tashi.

***

"Tun a hanya

45 / 47