Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 47

135K to 138K   out of 139.6K words

yake lallabata da rarrashinta, duk da ta nuna babu komai, kuma komai ya wuce amman ya"

"kula a kasan ranta akwai wani abu linke da take boye masa, bai damu da ya sani ba don ya san kishin ne."

"Ya dinga lallabata da riritata, motsi kadan yace ma'u me kike bukata, me zan kawo miki? Sai tace babu"

komai kawai. Don ko me zai yi mata ba zai wanke kansa ba a wajenta.

Shi da kanshi ya gano rashin kyautawar da yake yiwa Nana.

Bai taba zuwa gidansu da sunan zuwa zance ba duk da kuwa halaccin da mahaifinta yayi masa ya kamata

yayi musu dan wani abu da zasu ji dadi.

Don haka yau daga ofis yace da Ma'u ya wuce gidan babansa amman sai ya wuce can.

***

"Ya tarar da Hajiya Batula da Alhaji Nura Kwangila suna ta hira, yawanci akan bikin ne wanda ya rage"

saura sati uku.

"Sun fi farin ciki da ganinsa ya zauna suka gaisa suka dan taba hira cikin 'yar kunya yace ""kawu wai ina"

"budurwar kauyen nan tayi ne ban gan ta ba?"""

"Alhaji Nura Kwangila ya kalli Hajiya Batula da farin ciki fal fuskarsa yace ""tana can sashinta ko tana kallo"

"ko bacci"""

"Ahmad ta mike tsaye yace ""bari na je na tsokanota"""

"Ya nufi sashin nata kai tsaye. Dadi ya cika su Alhaji Nura Kwangila, wannan shine karo na farko da Ahmad"

ya taba nuna wani abu na kulawa akan 'yarsu Nana.

"Alhaji Nura Kwangila ya dubi Hajiya Batula yace ""kin gani ko? Na gaya miki wata rana za a wayi gari"

"Ahmad yana son Nana. Ai jini guda ba karya ba ne"""

"Hajiya Batula tayi dariya da jin dadi tace ""lallai na yarda da fadinka Alhaji"""

*

*

*

DA ME AKE ADO?

56

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Nana tana bandakinta tana wanka Ahmad ya shigo yana kwala mata kira. ""Ke budurwar kauye kina ina"

"ne?"" Sam bata jiyo shi ba har ya shigo uwardakinta. Daidai lokacin ta fito daga bandakin suka yi ido hudu da juna, gaba daya jikin Nana a waje yake, don dan tawul din da ta yafa bai kai ko rabin cinyarta ba, ga kanta da wuyanta a bude, duk wanda ya san siffar kyau da tsarin mutane ba zai tsaya mamakin hakittar Nana ba wanda Ahmad bai taba kula da ita ba sai yau. Ko don hankalinshi bai taba kai wa kanta bane"

oho!

"Dukkaninsu suka yi saranda kowanne na kame. Ita kunya ce, shi kuma sani abu ya ji ya daki zuciyarshi"

"wanda babu makawa ya san sha'awa da sonta ne yake ratsa shi. Lallai ya yarda UBANGIJI Gwanin hikima ne da ya halittawa maza auren mace sama da daya, da ya so ya cuci kansa."

"Ganin yadda ya kura mata ido ya sanya tayi gyaran murya sai a lokacin ya farga, kunya ta kama shi, ya"

"juya da sauri yace ""ina jiranki a falo idan kin gama shiryawa"""

Wani irin dadi ya shigeta. Lallai ta yarda mahakurci mawadaci ne wata rana.

Bata taba ganin irin wannan kallon daga Ahmad ba sai yau.

Ta yarda yanzu Ahmad din ya fara sonta kamar yadda ita ma take tsananin sonsa da kaunarsa. Tayi tsalle

"ta fada kan gado tana ihun murna, tare da yiwa ALLAH godiya da ya nuna mata wannan lokaci."

Ta ma rasa wacce irin kwalliyar zata yi ta jima tana zabe har ta karke akan wata doguwar riga mai kama

jikinta ta atamfa mai hadi da yadi da ake kawasu daga Dubai masu dan duwatsu.

"Rigar na dacewa da ita kwarai da gaske, kuma tayi masifar yi mata kyau."

Ta fesa turaruka masu kamshi ta fito falo da ta tadda Ahmad yana ciki yana jiranta tana rangwada.

Kamshin turaren da ya ji mai mai sanyi da dadi shi yasa shi yin saurin dago kai yana murmushi. Koda ya

"kalleta sai ya sake yin murmushi yace ""eye, lallai budurwar kauye ashe kin iya kwalliya?"""

"Ta turo baki gaba tana fadin ""gaskiya yaya Ahmad bana so ka daina ce min budurwar kauye"" cikin"

shagwaba take maganar.

"Yayi dariya da jin Dadi yace ""shikenan na daina, zo nan ki zauna ki bani labarin kuruciyarki naji"""

"Ta fashe da dariya ta zauna suka fara hira. Bai farga ba sai da kiran Ma'u ya shigo wayarsa, ya dubi"

"agogon bango dake kafe a falon yaga karfe goma na dare har ta gota, ya mike da sauri yana fadin ""YA SALAM! Ma'u ta gaji da jirana har ta kira ni. Bari na wuce"""

"Nana ta hade rai da takaici a yau tana murna ta dan fara samo shi amma Ma'u ta bata mata bajat, bai"

kula da halin da Nana ta shiga ba sai ya nufi kofar fita daga falon.

"A lokacin su Alhaji Nura Kwangila sun bar falon da ya same su sun shige daki, hakan yasa Ahmad ya sake"

tabbatarwa lallai hirar tasu da Nana tayi nisa.

"Koda ya isa gida Ma'un bata gano komai ba, domin haka ya rinka bata labarin yaransu da babanshi da"

kakarshi da irin diramar da suke yi tana dariya.

Tun daga wannan ranar kullum da dare sai yaje gurin babansa ya wuce gurin Nana.

"A hankali sabo da SHAKUWA ya fara shiga tsakaninsu, amman koda wasa bai taba yarda Ma'u ta gano ba."

"Ita kanta Nana ta gano Ahmad yana bala'in kaffa-kaffa da duk wani abu da ya shafi Ma'unsa, shi ya sanya"

ma bata hada kanta da ita kwata-kwata.

***

'Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya' in ji masu iya magana. Domin lokacin auren Nana da

"Ahmad yayi, Alhaji Nura Kwangila ne yayi komai, sai dai yayi adalci don duk wani abu da aka sanyawa Nana a cikin kayan lefe an sanyawa a matsayin kayan fadar kishiya."

"Biki ne irin na masu kudi da gata, abun dake bawa Ma'u bakin ciki shine ta rasa wanda zai taya ta bakin"

"ciki, don gidajen 'yan uwanta dake cikin kwatas din nan kowa hidimar bikin ce a gabansa, haka gidansu, haka gidan Alhaji Nura Kwangila, haka gidan Hajiya Ruma, idan akwai mai tausaya mata bai wuce Hajiya ba sai kuma Ahmad da bai nuna damuwarshi ko zumudin auren a gabanta ba sam har takan ji kamar"

dole aka yi masa a ranta.

Hankalin Ma'u bai tashi ba sai da aka zo daurin aure taga irin dumbin jama'ar da aka tara sannan da irin

kudin da iyaye ke kashewa saboda bikin.

"Sai da aka zo jere hankalinta ya gama tashi don bata taba ganin kaya irin na Nana ba ko a cikin fim, don"

"Hajiya Batula da kanta ta dinga nuna irin kayan da za a yiwa diyarta a kasar Dubai, duk da tana ganin"

matukar kyau da tsarin gidan sai da ta raina kanta da taga irin kayan da ake shigowa da su gidan da irin hidimar da ake yi kamar ba a son kudin.

"Shi kansa Ahmad irin shigar da yake yi sai take ganin kamar yanzu yafi karfi ta, don wasu dakakkun"

"shaddoji da yaduka Alhaji Nura Kwangila ya dinko masa a Dubai, kuma a cikin gidan yake shiryawa sai dai ya shigo mata."

Ran da aka daura aure farin cikinsa ya kasa boyuwa don ganin mahaifinsa ya taka kafarsa babu sanda

"yana hawayen farin ciki, sannan danginsu daga can 'yan leman sun zo, yaga duk wannan taron don shi ake yi, don haka ya gaza boye farin cikinsa sam."

"Wannan shine abunda ya kara tayar da hankalin Ma'u don ranar Ahmad bai kula ta kanta ba, tunda ya"

fice tun safe sai kwànciyar bacci ta dawo da shi gidan. Can gidan baban nasa ya zauna ana ta hira da wasa da dariya da 'yan uwansa.

"Sanda ya dawo ya tarar da gidan cike da mutane, don haka kai tsaye dakinsa ya wuce ya watsa ruwa ya"

fito da nufin kiran Ma'u sai kuma ya kama hira da Nana da ta kira shi. A nan ya shantake har bacci ya dauke shi bai nemi ma'u ba.

"Yana tashi da safe ma da shirin fita ya fito, kasancewar abokinshi Jabir ya shirya masa 'yar walima su da"

"abokansu da suka yi karatu tare, sanda ya shiga dakin Ma'u don yin magana da ita aka ce tana wanka shi kuma ba zai iya tsayawa jiranta ba, saboda can an dame shi da Kira a waya, don haka ya juya ya fice."

"Wannan abun ya karawa Ma'u tsoro a ranta har take ganin tata ta kare gurin Ahmad, ba shi da sauran"

"lokacinta, kuma bata kara ganinshi ko jin wayarshi ba har dare sai 'yan kawo amarya suka fara jerin gwano da motoci, tun tana iya ganin adadin motocin da suke ta zuwa har ta kai ga gaza yin hakan, harabar gidan kato ne zai iya cin motoci kanana hamsin, kuma bangaren Ma'u da Nana daban, akwai 'yar"

tazara mai nisa.

Asalin gidan Alhaji Nura Kwangila ne da ya bata shekaru yana ginawa ya bai wa Ahmad da zummar shi

zai kara gina wani gidan nasa.

"Gudar kawo amarya da ake yi kamar cikin ran Ma'u ake yin ta, ga shi lokacin babu kowa a gidan, duk jiya"

"aka zo mata, daga ita sai masu aiki sai ta fashe da kuka ta hada kai da bango tana kuka. Gaba ki daya gidan yayi zafi da kunci, babu abunda take so illa ta fita ta barshi ko zata huta. Tana nan har 'yan kawo amarya suka watse."

"Can wajen karfe goma da mintuna Ahmad ya iso gidan. Kai tsaye dakin Ma'u ya nufa, ya sha mamaki"

"ganin bai ga komai a kan fuskarta ba na bacin rai, don ita kadai ta san abunda ta kudurce a cikin ranta."

Ya dan zolaye ta tana murmushi ya bukaci suje sashin amarya tace ba dai yau ba yau ba sai gobe.

Ya ajiye mata kasonta da ya shigo da shi yayi mata sai da safe ya nufi sashin Nana cikin dokin da ya kasa

"boyuwa akan fuskarshi don yau kusan tare ya yini da Nana, kwalliya ta dinga yi ta tsuma shi kwarai da gaske, wannan abun yayi wa Ma'u ciwo kwarai da gaske,yana fita ta kara fashewa da kuka."

Wai yau Ahmad dinta ne ke nuna zumudi akan wata mace ba ita ba?

***

Shi kam Ahmad yana shiga dakin amaryarsa ya dan zokayeta ta ki sakin jiki sai ya sureta cak suka yi

"bandaki yin alwala idonta a rufe da kunya. A gaskiya a matse yake da Nana don tun ranar da ya ganta kusan tsirara sha'awarta ta gama nuna a cikin ranshi, don haka suna idar da sallah ya farà nuna mata"

bukatarshi da yake ita ma ta jima tana jiran wannan lokaci bata yi wani noke-noke ba ta bayar da kanta.

"Abunda ya bashi mamaki bai wuce ganin bai sha wata wahala kamar yadda yasha akan Ma'u ba, nan da"

"nan yaji ya gamsu. Bayan ba haka ya so ba, yayi kyakkyawan shirin da zai yi yanda ya so sai dai bai samu ba, yanayin mace 'yar Shekara sha shidda sha bakwai da mai Shekara ashirin da uku hudu da bambanci,"

"don ita 'yar sha komai bata kankani yake bai saki ba, sabanin na wacce ta dan yi shekaru ashirin."

"Sannan kuma a daren ya fuskanci Nana tana da tsawon bukata, sai yayi mamakin dalilin da ya Sanya bata"

"yi aure da wuri ba. Koda yake da alamun bata taba yin mu'amala da wani namiji ba don ta dan wahala, amman sai yaji daren farko shi da Ma'u yafi wannan nesa ba kusa ba, amman ya bar abun a cikin ranshi."

Ita kuma Nana wannan shine dare mafi alkhairi a rayuwarta. Sai a yau ta gano ashe tana kwarar kanta da

"rayuwarta, jikinta yana bukatar wani abu da take tauye masa. Lallai Ahmad ya kai ta gurin da bata taba zuwa ba, ba ta ma taba mafarkin zuwa ba."

Da safe duk da Ma'u tana ranshi gajiya da kasala bai bar su sun fito da wuri ba sai wajen karfe goma sha

daya na safe.

Lokacin sun shirya yace da Nana tazo su shiga wajen Ma'u su gaisa suka jera suka nufi sashinta.

"Masu aiki suna ta hidimarsu suka shiga suka dinga gaishe su, sai wata Yaya Abu ta fito daga kicin da sauri"

ta mikawa Ahmad wata takarda tace in ji Hajiya tace a baka.

"Da mamaki yace ""wacce Hajiya kenan?"""

"Cikin ladabi ta amsa ""Hajiya Ma'u mana"""

"""Tana ina yanzu?"" Tace ""Ta fita tun asuba..."""

"Ya katse ta da fargaba ""Ma'un ina ta tafi?"

"""WALLAHI ban sani ba ni ma Alhaji"""

"Damuwa da tashin hankali suka bayyana aka fuskarsa, sai yace ""Babu damuwa jeki kawai"""

Ya kalli Nana dake kallonsa da fargaba sannan ya mai da hankalinsa ga wasikar ya bude. Ga abunda ta

kunsa.

Mijina Ahmad.

"Nayi iyakacin kokarina na danne zuciyata na zauna da kai, amman na kasa don na gano yanzu kayi min"

"nisa, ka girmi rayuwata, wancan Ahmad din mijina da muke daidai shine talakan nan mai kula da ni da cina da shana, mai kula da yanda na kwana da yanda na tashi, ba kai ba babban mutum."

"A yanzu rayuwarka tafi dacewa da diyar masu kudi da arziki irinka ba wadda kake taimako ba, mai ilimin"

degree da master's da wayewa.

"Rayuwarka ta girmi ta Ma'u yanzu, don haka naga yafi dacewar na matsa ba baku guri, na san ba zaka iya"

"sakina ba saboda kunya da tunanin kada duniya ta zage ka, don haka na hutar da kai na tafi inda ba zaka kara ganina ba, ba zaka ji kunyar iyayena ka sakeni ba, amma ina son wata rana ka furta sakina ko cikin ranka ne, don kada nayi ta yawo da aurenka."

Ga kuma amanar 'ya'yana wata kila zan gan su wata rana.

A lokacin da zaka ci karo da wannan wasikar tawa tuni nayi nisa daga inda kake! Ina yi maka fatan

alkhairi kai da matarka.

ASMA'U

Matarka a baya.

"Wani irin abu ya bi ta jininshi ya wuce zir! Kamar wutar nepa ta jashi, ya waro ido da fadin ""what? Me"

"kika aikata haka Ma'u, ya kike tsammanin zan rayu babu ke?"

"Nana ta kalle shi ganin kamar yana shirin zarewa ne tace ""yaya Ahmad lafiya, me ya faru?"

"Cikin kidima yace ""Ma'u ta gudu, tabbas cikin satin nan na wofintar da rayuwarta, ban damu da"

"damuwarta ba, hakan ya sanya tayi zaton na daina sonta ne. Yaya zan yi na shiga ukuna, WALLAHI idan babu Ma'u ba zan rayu ba, bari naje na gayawa Abba da Umma"""

"Sai ya juya ya nufi fita daga falon, Nana tayi hanzarin riko shi da sauri tace ""haba yaya Ahmad wannan"

"matsala ce tsakaninka da matarka, ka san ko ina Ma'u zata je ba zata yi nisa da kai ba, bacin raine ya sanyata tafiya, idan ka gayawa iyayenta kamar ka tona muku asiri ne, zaka iya janyowa suyi fushi da ita"""

"Maganganun Nana suka shige shi yace ""haka ne yanzu me ya kamata nayi? Don ALLAH gaya min Nana"

"kaina ya kulle, ina tsananin son matata"""

"Ta ciza baki tace ""ka je kowanne gida da ka san zata je ba da sunan cigiya ba da sunan kaje gaishe su ne,"

"ta haka zaka gano inda ta shiga"""

"Yace ""yauwa haka za a yi bari na dawo"" ya fice da sauri a rude. Ta bishi da kallo idonta ya cika da kwalla."

"Lallai Ma'u tayi nisa a zuciyar mijinta, idan kuma tace sai tayi gasa da ita zata iya zamtowa cikin takaici, abu daya be zai janyo sonta ya zama daya da na Ma'u ko ma ya fishi shine asiri, wanda bata taba sha'awar yin sa ba, don wadanda taji labarin sun yi ma bai amfana musu da komai ba."

Ta goge hawayen dake zubo mata ta nufi sashinta.

Ga Ahmad kuwa dukkan inda ya san zai samu Ma'u sai da yaje har yamma tayi masa ya gaji likis ba tare

"da ya gano inda take ba, ya farà sarewa da tunanin ko ya sanar da iyayenta, don duk wayoyin Ma'u a kulle suke."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

57

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Tunda Ma'u ta isa garin Zaria gidan kawarta Maryam wacce tayi aure kusan shekaru uku da suka wuce ta

"auri wani soja, Ma'u taje mata tana muka dakyar Maryam ta rarrasheta ta sanar da ita abunda ya faru ta hada da rokonta akan ta rufa mata asiri ta barta kada ta gayawa kowa tana gurinta har zuwa sanda zata"

san inda zata tafi don ba zata taba komawa gidansu ba ko gurin danginta ba har abada.

"Maryam ta matukar mamakin jin labarin da Ma'u ta bata, amma san bata ga laifin Ahmad a cikin wannan"

"labarin ba, ko din ita ma tana da kishiyar ne? Ita ce ma amarya. Da Ma'u ta san irin halin da kishiyarta ta shiga sanda zai aureta da tace Ahmad dan aljanna ne, don haka ta farà baiwa Ma'u hakuri da labarai"

"kala-kala na mazajen da zasu yi aure, duk jikin Ma'u yayi sanyi amman tace mata ita dai ta kyaleta."

Daga karshe ta dora da ce mata 'yanzu haka mijin nata Yana gidan uwargidanta zai mata kwana biyu ba

"zata kara ganinsa ba sai bayan kwana biyu koda cuta zata kasheta ita da danta kuwa, ga rashin wadatasu"

"da take yi, aikinta shine gatanta (da yake tayi karatu mai zurfi har degree) amman tana lallaba aurenta domin ta jima bata samu yinsa ba'"

"Duk da maganganun Maryam sun shigi Ma'u amman KISHI ya rufe mata ido tace ita a kyaleta, sai"

"Maryam ta roke ta Ko message ne tayi wa 'yan gidansu ta sanar da su inda take don hankalinsu ya kwanta, Sai Ma'u tace ashe ma tana fatan Ahmad ya dawo mata ma kenan."

"Haka suka dinga tataburza har dare yayi, sai dai wani abu da yake bawa Maryam mamaki shine, tsawon"

"yinin wannan rana Ma'u tana kallon hoton Ahmad mijinta a wayarta da ta Sanya sabon layi, abun sai ya baiwa Maryam dariya."

Wajen karfe goma na dare aka farà buga kofar gidan da yake gida ne na irin na kananun nasu rifin asiri

"babu maigadi. Da sauri Maryam ta dauki wayarta tana cewa ""yauwa ka karaso? To gani nan zuwa"" ta nufi kofar sam Ma'u bata kawo komai a ranta ba. Tana kwance akan kujera ta runtse idonta har suka"

turo kofa suka shigo.

"Kamshin turaren da taji ne ya sanya ta bude idonta da sauri, turaren Ahmad daya ne tun yana talakansa"

"har zuwa yanzu da yayi kudi, don haka ko cikin bacci ba zai bace mata ba."

"Yana tsaye jikin kofa idonshi yayi jajir, kamar gauta, duk yayi baki ya rame yini daya tal. Bakin ciki ya cika"

Ma'u ta kalli Maryam da tsananin takaici da harara.

"Maryam tace ""kiyi hakuri Ma'u idan har na bar mijinki da iyayenki cikin damuwa bayan na san halin da"

"kike ciki ban yi musu adalci ba, ban kuma cika masoyiyarki ta gaskiya ba"""

"Ma'u ta mike a fusace ta nufi kofar fita,

46 / 47