Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 47

96K to 99K   out of 139.6K words

fadin ""ka ji yaya kamar ka leka littafin"

"kaddararmu ka san komai, ni dai ba zan mutu da wuri ba gaskiya."""

"An ji an bar miki gadin duniyar, amman gaya min abinda kike boyewa yanzu ko na samu kwanciyar"

"hankali, don har Kin daga min hankali yanzu"""

"Ta yi ajiyar zuciya da fargaba, don bata san yanda zai dauki maganar ba. Ta tsare da idanuwanta sannan"

"tace ""yaya ina son ci gaba da karatu ne"" gaba daya annurin fuskarsa ya dauke kamar ha shi ne mai dariya ba yanzu. Hakan ya kara haifar mata da faduwar gaba amman sai ta ji yace ""karatu kuma kamar yaya?"

"Tana kallonshi har lokacin tace ""karatuna na boko mana har da na islamiyya ma, don kaga abokan"

"karatuna har sun yi candy, ni kuwa ina ya zaman banza."""

"Wannan kalmar ta karshe ta shige shi har ya kalleta da sauri yana kuma maimaita maganar. ""Zaman"

"banza fa kika ce ma'u, zaman auren ne ya kasance abin banza?"

"Ta wayance da faduwar gaba tace ""ba haka nake nufi ba yaya, ina nufin wai ina zaune haka babu komai"

"ga abokan karatuna har sun yi candy"""

"Yayi shiru yana sauraronta kamar ha zai yi magana ba, da ya ji tayi shiru ta sunkuyar da kanta kasa ganin"

"yadda yake kara daure fuska duk sakwan daya yaci gaba da magana. Ya kamata ki gane aure shi ne gaba da komai a rayuwar 'ya mace, sannan ina da halin da zan iya rike ki kiyi karatu amman a yanzu lokaci ya kure, ba zan iya kallon ki kina fita kullum da sunan karatu ba wasu na gane min mata, don haka ki cire"

"maganar karatu cikin kundin burikanki"""

"Yana gama fadin hakan ya mike tsam da nufin ficewa daga cikin dakin, amman maganarta ta hana shi"

"fitan. ""Haba yaya kada ka zamto irin mazan nan masu daukar mace tamkar baiwa. Kai ma kana yin abin da ka so, ya kamata ka ba ni dama ni ma ko sau daya ne a rayuwata, gaskiya ba ni da burin da ya wuce"

"ganin na yi karatu"""

Ya waigo baki bude jin kalaman da suke fitowa daga bakin ma'unsa kamar wanda ta rubuta a cikin littafi

take karantowa. Amman sai ya ga ba haka ba ne shi din take kallo kyar! Kuma tana ci gaba DA zakulo abin dake ranta.

Ya so ya kyaleta ta cigaba da maganarta amman sai ya kula bata cikin nutsuwarta don haka da sauri ya

"daka mata tsawa yana fadin ""ki kame bakinki ma'u, in har ni ne mijinki kuma sai da izinina zaki yi karatu, na gaya miki ba zaki yi ba har abada. Don haka ki sanya wannan a ranki. Ina kuma gargadinki akan kada ki Kara yi min irin wannan zancen daga yau"" ya nufi kofa da sauri yana huci."

Wani malolon takaici ya taso ya tokare zuciyar ma'u. Wanne irin miji ne Allah ya bata mai kishin tsiya da

"son kanshi? Ban da son kai kullum shi yana waje amman ita ko unguwa zata sai ta kau ruwa rana da shi, yanzu kuma ya sani sarai karatun nan akwai alfanu a ciki amman ya rufe idonshi ya hana ta don kawai yana takamar yafi kowa kishi."

"Sai ta fashe da kukan takaici da bakin ciki, cikinta ya hautsine, kirjinta ya kama zafi don bakin ciki, ta rike"

cikin tana murkususu tana kuka. Shi kam ya riga ya fice bai ma san abin dake faruwa da ita ba.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

37

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Can ya ji amai ya taso mata, ta yunkura ta mike da gudu ta nufi tsakar gidan, kafin ta isa ga rariya tuni"

"aman ya cimmata, ta tsuguna a nan ta fara kelashi tana dafe ciki da kirji kamar zai biyo hanjinta ya fito waje take ji."

"Ya shigo dauke da maganin sauro da ya je siyowa ya hangota durkushe tana amai, ya kidime ya nufe ta"

"da sauri yana tambayarta abin da ya faru. ""Yaya aka ma'u? Me ya same ki, lafiya?"" Duk ya rikice ya rude."

"Bata iya ce masa komai ba saboda aman da take yi, ya mike ya nufi rubar ruwa ya debo ruwa cikin buta"

"ya nufeta ya fara zuba mata a kanta, don ta jigata da aman tana ta kakari babu komai a cikinta domin ta amayar da dukkan wani abu da ta ci wanda bai narke ba. Ya dinga wanke mata fuska da jikinta har sai DA ya tabbatar ta koma cikin hayyacinta ya kama rigar jikinta ya cire domin duk ta baci sannan ya tallafe ta suka nufi daki ya zaunar da ita gefen gado ya cire mata sauran kayan jikinta ya dauko wata doguwar riga ta bacci mara nauyi ya sanya mata sannan ya kama ta ya kwantar akan filo yana fadin ""sannu ma'u meye"

yake miki ciwo kuma yanzu?

"Ta kada kai muryarta a dashe tana fadin ""babu komai sai dai tashin zuciya kadan-kadan"""

"""Zai daina shima, garin yaya kika fara aman ne? Ta rintse ido ""ban sani ba ni ma"" yayi shiru yana"

kallonta DA tausayawa sai ya mike tsaye.

"""Bari na samo miki magani a chemist din sister Deeja"" ya fice da sauri."

"Ita kuma yana fita taji wani sanyi na shigarta, ta janyo bargon dake gefe ta kudundune. Ya dawo dauke"

"da magunguna ya ajiye ya dauko ruwa ya bude abinda ta lulluba fashi ya tallafo kanta yana fadin ""ma'u tashi ki sha magani"""

Bata yi musu ba ta amsa ya fara sha har ta shanye duka ya maidata ya kwantar ya mike ya fara fita da

kayan ita kuwa ta kara kudundunewa domin har lokacin akwai zazzabi a jikinta.

"Yana can yana kokarin dauraye kayan da ta bata ya kuma jiyo kakarin amanta, ya bazamo dakin da gudu"

ya sameta tana durkushe a gaban gado ta amayar fa dukkan magungunan da ta sha.

"Ya dafe kai da damuwa kamar zai fasa ihu, ya isa dai ya gyara gurin ya dauko kaya ya jibga akan"

"wadancan na wajen ya dawo ya dauko dan ruwa yana bawa matar tashi, ya fasa wanke kayan ma ya rungume ta a kirjinshi yana shafa kanta da lallashi, duk ya dauki laifin wannan cutar ya dorawa kansa, domin da bai yi mata masifar nan ba da ba zata yi aman har haka ba, da zai iya ma da ya janye dukkan maganganun da ya gaya mata, amman ba zai iyu ba saboda magana zarar bunu ce, in ta fito bata"

komawa.

"Haka nan suka kwana tana ta aman, tayi ya kai sau hudu cikin dare, don haka tun da asuba ya fara shirin"

kai ta asibiti.

"Karfe bakwai sun fice. Ya so kaita na kudi amman kuma babu kudi a hannunsa domin wata ya fara nisa,"

don haka na Murtala Muhammad ya kaita.

"Da yake sun fita da wuri sun yi sa'ar ganin likita da wuri, aka rubuta musu magunguna har da karin ruwa"

da kuma gwajin fitsari. Har wajen karfe uku suna asibitin sai da ruwan ya kare tas.

"Sai dai har a sannan Ahamd bai san abindake damun matarsa ba, don haka da za su tafi ya sami wata"

"ma'aikaciyar jinya ya mika mata korafi yana fadin ""sister don ALLAH meke damunta ne, dazu ina rude ban tambayi likita ba, ga shi ya tashi yanzu"""

"Ma'aikaciyar jinya tayi kamar ha zata amsa ba, da tayi ido hudu da ahmad sai ta gaza yin musu, domin"

"shi mutum ne mai kwarjini da haiba, da wuya ka kalli tsakiyar idonsa kayi masa musu."

"Bayan ta gama karanta abindake rubuce a jikin katin ta kalli ma'u tana rariya tana fadin ""ina taya ki"

"murna kin kusa zama mama"""

Sam ma'u bata fahimci komai ba.

"Ahmad ya dan fahimta, amma duk da haka sai ya sake kallon ma'aikaciyar jinyar da sauri ""sister kina"

"nufin wai ciki ne da ita""?"

"Ma'aikaciyar jinyar tayi murmushi tace ""ka cire kalmar wai"" ta mika masa katin tana murmushi. Tace"

"""ALLAH ya raba lafiya"""

"Ma'u kam kunya duk ta kama ta kamar ta nutse a gurin, ta kau da kanta gefe daya tana murmushi."

"Ahamd ya kura mata ido yana kallonta, ya ma rasa wanne irin farin ciki ya kamata yayi, ya dan kalli mutanen dake kai wa DA komowa, ban da gudun baki DA ya suri matarsa yayi rawa da ita sannan ya kai ta har bakin titi inda za su hau mota, amman dai ya daure ya riko hannunta kawai yana ta wage baki"

"tamkar mai tallan makilin yace ""ma'u mai ya sanya kika boye min wannan farin labarin?"

"Bata iya kallon fuskarsa ba don kunya. ""Ni ma fa ban sani ba yaya"""

"Zai kara magana ta katse shi ""Yaya mu tafi gida mutane suna kallonmu sannan kuma yunwa nake ji"""

Wannan abibda ta fada ne ya sanya ya dan nutsu ya kama hannunta suka nufi titi. Shatar adaidaita sahu

ya daukar musu har kofar gida.

Daman ya tsaya ya sai mata abincin _Take Away_ don haka suna shiga gidan shi ya fara shirya mata a

gaba yace ya cinye tas sannan tayi sallah.

"Alluran da aka yi mata na tsai da amai sun yi aiki sosai a jikinta, bata jin aman ko tashin zuciya a yanzu,"

"don haka ta dan ci abincin da yawa. Ranar dai ko gurin aiki Ahamd bai iya zuwa ba, sai waya yayi ya sanar musu matarsa bata da lafiya a gayawa manaja. Ya ci gaba da kula da ma'unsa kamar zai kashe ta."

BAYAN WATA TARA

Kwanci tashi babu wuya a gurin ALLAH domin zuwa yanzu cikin ma'u har ya shiga watanni na tara.

"Dukkan wata kulawa da gata tana samunsu a wannan ciki kamar ranshi haka ahmad ke tattalin cikinta, da ta yi motsi zai yunkuro yace ""mene ne ma'u?"

Kai hatta wajen aiki ma ban DA dole ba zau dinga zuwa ba.

Jama'a kuwa kowa ya san ma'u na da ciki tun yana watanni hudu musamman Hajiya da umma sune

"abokan hirar cikin da neman shawararsu kullum, sam baya jin kunyarsu in dai akan cikin nan ne."

Ma'u takan yi mamakin yanda ahmad ke tsananin son haihuwa kamar yayi hauka akan kula da cikin. Aiki

ma don dadi ance ana bukatar shi a wajen me dole shi yasa yake kyaleta ya tafi.

"Yau tana kishingide akan kujera tana kallo, ta yi wata irin kiba cikinta ya fito sosai. Ahmad ya shigo falon"

"da sallama hannunsa dauke da manyan ledoji guda biyu. Ta yunkura dakyar tana kokarin mikewa gami da amsa sallamar. Ya karaso kusa da ita da sauri yana fadin ""kin ga ban ce ki taso ki tareni ba, cigaba da hutawarki na gode"""

"Ta yi murmushi ""wato kayi mini haramiyar wannan ladan ko yaya? Kai ni ka hanani samun ladan dake"

"cikin aure na baki daya"""

"Ya ajiye kayan hannunsa yana murmushi ""ban da ladan da kike samu ma daukar wannan cikin mai nauyi"

"ma'u? Ya fara kokarin fito da kayan dake cikin ledojin da ya zo da su. Ta katse shi. ""Yaya ka fara cin abincin kafin kayi komai bari na dauko maka"""

"Ta sake yunkurawa zata mike tsaye, yayi saurin dakatar da ita. ""Dakata ma'u, na ga alamar dai so kike sai"

"kin tashi nan dole to ni a koshe nake"""

"""A koshe yaya? A ina kaci abinci kuma? Ta tambaya yanayin fuskarta ya fara sauyawa zuwa damuwa."

"Ya lakuce mata hanci ""kada kiyi kuka matata kanwata, daga gidan Hajiya nake ba wata ce ta ba ni abinci"

"ba. Ita ce ma ta ba ni wannan kayan wanda ta tara ne weai tace a kawo miki"""

"Ta fan saki fuska tana dariya. ""To ai ka ci gurin wata matar mana idan zaka iya. Na ga kayan hajiyar"""

"Ya daga ledar farko. ""Wannan tawa ce ni na siyo su, wannan kuma na hajiyar ne, wanne zaki fara gani?"

"Tayi shiru tana kallon ledojin duka, sai tayi murmushi ta nuna ledar da yace nashi ne kayan. Yayi dariya"

"ya ajiye mata a gabanta. Ta ja ledar ta fara dubawa tana fadin ""na san mijina dan gayu ne yafi Hajiya iya zabe"""

"Ta fara daga kayan (over roll) ne biri da wando da takalma na jarirai da safa. Kayan sun matukar kyau, ta"

"dinga kalla da fara'arta cikin farin ciki tana dubawa har ta kammala ta dube shi tace ""yaya kayan nan sun yi kyau, ka iya zabe WALLAHI. amman kamar sun yi yawa ko?"

"Ya harare ta a wasance ""in ji wa? Yarinya da ace kudin ne da ni WALLAHI akwati ma zan ciko na kayan"

"dana ko diyata..."""

"""To wai yaya ma aka yi ka sami biyu ga naka ga kuma na Hajiya, ai daya ya hakura tunda daya ya siya"""

"""Da kowa bai siyo ba fa? Ya ba ta amsa da tambaya."

"Bai bari tayi magana ba ya dora da jawabinsa. ""Wasu kudin da muke dan karamin adashi aka hada min"

"yau a gurin aiki, shine naje kasuwa nayo siyayyar nan, sai na yanke shawarar naje na nunawa Hajiya abinda babu sai ta gaya min na karo. To ina zuwa tana ganina ta kama fada akan me yasa da zan siyo ban yi shawara da ita ba, domin ita ma ta rigada ta siyo nata kayan. Daga karshe dai ta hado ni da natan ma"

"tace sai na karata tunda wai bani da kunya balle kara"""

"Ma'u tayi dariya. ""Gaskiya ta fada WALLAHI ka zama wani babban maras kunya akan cikin nan, ko gaban"

"umma da Abba baka jin kunyar yin maganar cikin nan"""

"Yayi yake yana fadin ""ma'u kenan laifina kika gani? Idan ban yi dokin cikin ba me ya kamata nayi dokinsa?"

"Kada ki manta fa shine dan uwana jinina kuma tsatsona. Na kasance bani da kowa da ya zamto mun hada wata alaka ta jini a wannan duniyar, abibda zaki haifa ne kawai zai zamto min haka"""

"Idonsa ya dan taru da kwalla. Jikin ma'u yayi sanyi, bata son ya dinga yin irin wadannan maganganun"

"kwata-kwata, tun ba ta jin damuwa akan halin da yake ciki har ta fara."

Ya goge wani dan hawaye da ya zubo masa ya wayance don kada ma'un taga sanda ya goge ya cigaba da

maganarsa.

"""Ina son ki haifa min yara guda ashirin ma'u yanda zan raya sabuwar zuri'a daga bangarena nima tunda"

"bani da kowa a wannan duniyar sai mahaifiyata mahaukaciya da ta rasu, da ace ta rayu ma da ta iya zame min abar kallo ko kuma ta kaini gurin babana da yayi mata cikin shege har aka haifeni..."" Ta sanya hannu ta toshe masa baki da sauri tana kada kkowaDon ALLAH ka daina wannnan maganar"" sai kawai ya fashe da kuka ya dora kansa akan kafadarta yana kuka, sai ita ma ta rasa abinda ya kamata tayi masa sai"

kawai itama ta fashe da kukan.

Yayi shiru da sauri ya dago ido yana kallonta ya janye jikinsa.

"""Yi shiru ma'u, kuka bai kamace ki ba, ke fa 'yar gata ce, kina da uwa da uba DA yayye da kuma miji kuma"

"yayanki, ni kuma bani da kowa da ya kasance jinina sai wannan abin dake cikinki."

"Ya shafa cikin nata yana dan murmushi. Ta kai hannu ta toshe masa bakinsa tana fadin ""ya isa haka yaya"

"idan ba so kake ka daga min hankali ba"""

"Yayi shiru yana ajiyar zuciya, Kala manta sun ratsa zuviyarsa cikin kunnensa tace ""gobe zan je aso yaya za"

a yi ne?

"""Zan kai ki idan an gama miki sai ki wuce gidan umma, idan na tashi daga aiki sai na biya ta can na taho"

"da ke."""

"Dadi ya cikata tana son zuwa awo, duk ranar da taje awon sai ta biya ta gidansu ta yini a can."

"Sai wajen karfe biyu ta kammala komai DA komai na awon, ta tako dakyar ta nufo bakin kofa, sai take jin"

duk jikinta yayi nauyi yanzu. Dakyar ta isa bakin titi ta sami shatar mota har gidansu.

"Ta biya mai mota ta shiga soro, sai ta ja ta tsaya turus! Da fargaba don ganin raliya tsaye a bakin kofar"

gidansu tana yin waya.

"Hankalin raliyar yayi kanta itama suka yiwa juna kallon-kallo, kowacce mamaki ya bayyana akan fuskarta"

"ganin 'yar uwarta dauke da ciki. Amman raliya bayan mamaki har tsananin takaici da kishi, domin bayan ta dawo taji labarin ma'un aka aurawa ahmad, sai kuma ta ganta kwatsam da ciki babu zato babu"

tsammani.

Ita kuma ma'u tana mamakin ganin raliya da ciki tsoho bayan ta san ba aure ne da ita ba.

"_""ko cikin shege tayo ne?""_"

Raliya ce ta ja wani dogon tsaki ta juya cikin gidansu da sauri.

*

*

*

Ashe fa Hajiya Raliya uwargidan Ahmadu an dawo gida daga gudun DA tayi bayan shekaru biyu.

DA ME AKE ADO?

38

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Lami tana zaune akan benci tayi tagumi, raliya ta shiga tana kwalla mata kira da karfi. ""Lami! Lami!!"

"Lami!!!"""

"Lami dake zaune ta dago ido ta kalle ta da sauri cikin fargaba, bakin cikin duniya duk ya isheta tace ""yaya"

aka yi ne kike ta kwala min kira haka?

Ta isa gabanta tinkis-tinkis da ciki ta zauna tana haki tace.

"""Yarinyar nan ma'u ce ta shigo yanzu na ganta da ciki, kuma cikin ma tsoho. Wai kina nufin har ciki ta"

samu da mijina?

Lami ta tabe baki.

"""Ba gashi nan idonki ya nuna miki ba raliya? WALLAHI ko ganinki bani kaunar yi raliya, na gama kuri da"

"cika baki akanki, amman ki dawo min da wannan abin kunyar, da wanne ido zan kalli duniya da makiyana masu neman gazawata su yi mini dariya?"""

"Raliya ta turo baki ta kuma kumbura ""haba lami sau dubu nawa zan gaya miki banyi iskanci da kowa ba,"

"wannan cikin na ahmad ne, kwanciya yayi nayi zaton ma ya fadi tuni sai cikin watan nan ya tashi, idan ke ba ki yarda cikinsa bane waye zai yarda da ni har a kwantar min 'yancina?"

Lami ta kalleta ta dan fara yarda da abinda diyar tata ta fada.

"Lami ta kuta ta cigaba da magana. ""Laifinki daya ne da baki sanar da ni kina da cikin ba, ni baki ma nuna"

"min wata alaka ta taba shiga tsakaninku da shi ba, da na sani ai da ba zan barki ki tafi da ciki ba, ya kuma"

kwanta miki tsawon shekarun nan kina fama da shi. Amman dai bari babanki ya shigo dole za a yita ta

"kare. Idan kuma ya watsa mana kasa a ido shi ya sani, domin har shi ginin zai cinye ba mu kadai ba"""

***

Ma'u ta shiga cikin gidansu da sanyin jiki bayan doguwar tsayuwar da tayi cikin mamaki da fargaba.

Ummanta tana zaune akan tabarma tana cin abinci ta shiga gidan da sallama. Umma ta dago kai da sauri

"ta kalleta ta kura mata ido, ganin yanda take tafiya kamar tana tafiya ne akan kwai. ""Ke kina lafiyarki kuwa ma'u?"

"Ma'u ta isa kusa da umma ta zauna tana nishi tace

33 / 47