Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   38 / 47

111K to 114K   out of 139.6K words

tsalle ya koma gefe daya don saura kiris ta"

buge shi. Ta nufi harabar gidan a fusace tayi parking din motarta ta fito ta tura kofar motar da karfi ta nufi cikin gidan da sauri a fusace.

"Mahaifiyarta Hajiya Batula tana falo tana kallo, masu aiki sai kaiwa da komowa suke yi suna aikinsu nana"

"ta shigo falon a fusace. Hajiya batula ta bita da kallo da mamaki tana fadin ""nana lafiyarki kuwa sai wani kumbiri kike yi?"

"Nana ta fada kan kujera ta zauna ta dafa kai tace ""mommy WALLAHI wani mutum mai girman kan tsiya"

"na hadu da shi a gidan man daddy na nan cikin G.R.A."" nana ta kwashe labarin dukkan abinda ya faru da ita ta sanar mata."

"Hajiya batula ta girgiza kai tana murmushi tace ""ya burge ni kwarai da gaske, da za a dinga samun"

"talakawa na muku bore irin haka da kun rage taka su"" nana ta kara bata rai cikin shagwaba tace ""au mommy kema abinda yayi min yayi miki daidai kenan kamar yanda zuciyarshi ta nuna masa ko?"""

"""Eh mana to ya rantse kema kin rantse, idan shi har ya yarda ya zuba miki man, to ya zama sokon namiji"

"abinda yayi miki shine zai tabbatar da cewa shi cikakken namiji ne ba solobiyo ba. Amma sai dai ina shawartarki da ki bar maganar nan iya nan, don WALLAHI idan daddynki yaji kin san ranki ne zai baci, bai"

"son a wulakanta dan adam kin sani sarai"""

"""Amma mommy ni ba a ga abin da yayi min ba?"""

"""Kome yayi miki ai kece kika jawowa kanki. Da kika shiga gidan man kamata yayi ki fita ki isa kusa da shi"

"ku gaisa, idan kika ga bait gane ki ba sai ki bashi sani ko kuma ki nemi manaja ya sanar da shi, amman sai ki haushi da fada da nuna masa isa da gadara kamar wata uwarsa"""

"Nana ta mike da sauri tana turo baki cikin alamun shagwaba tace ""daman na san mommy ba zaki taba"

"goya min baya ba, da daddy ne yaji WALLAHI sai ya rama min"""

"""Me zai rama miki bayan koran da kika ja masa daga gurin cin abincinsa? Yanzu ba zaki tunanin da me zai"

"ci gaba DA rike iyalinsa da danginsa ba, me zai ci gaba da ba su, a ina zai samu aiki? Saboda kin zuba miki mai duk kin ruguza masa rayuwa. Ki bari baban naki yaji zaki ga yanda zaiyi dake. Duk son da yake yi miki"

"ai bai ce ki wulakanta jama'a ba"""

"Jikinta ya dan yi sanyi, amman har lokacin bata saduda ba ta juya DA sauri ta nufi bangarenta tana cika"

"tana batsewa. Hajiya batula ta gyada kai tana fadin ""ALLAH ya shirye ki nana"""

***

"A can gidan ahmad kuwa ma'u tana tsakar gida zaune tana gyarawa Sayyada kanta da ribon, ta kammala"

"shirya Hajiya. Shi kuma yana daki yana bacci don lokacin shekararsa daya ne. Kawai sai ta jiyo karar babur gidansu. Ko kusa ba tayi zaton mijinta bane ba, domin ta san lokacin dawowarsa bai yi ba, sai da taji ana kokarin shigowa da babur din cikin gidan sannan ta mike da sauri, tuni yaran suka yi kofar gida da gudu suna fadin ""ga Abba ga abba."""

"Ya karasa shigowa da babur din nasa yana dan murmushi. Ma'u na tsaye tana kallonsa da mamaki, ta"

"kasa cewa komai. Ya kafe babur din ya dauki yaran kowanne a hannu daya yana musu wasa sannan ya dire su suna tayi masa gwaranci. Ya durkusa daidai tsawonsu yana taya su shirmen tsawon mintuna sannan yace ""to maza aje a nunawa babar a'ilo kwalliyar domin kun yi kyau"""

"Ai kuwa kamar jira suke yi, don dama suna son shiga gidan innar, amman mamansu ta hana su."

"Ya mike tsaye ya isa gaban ma'u ya lakuce mata hanci yana fadin ""yaya dai 'yan mata, ko kin zama gunki"

"ne?"" Tayi ajiyar zuciya tace ""yaya dai ka dawo da tsakiyar ranar nan, ban taba ganin haka ba, me yake faruwa? Ya karkada kai ""babu komai kawai bana jin dadi ne"""

"Ya nufi daki da sauri ya shiga ya bishi da kallo da mamaki, sai ta bishi dakin ta tadda shi ya kwanta a kan"

gado yayi rigingine amman idonshi a lumshe. Ta isa kusa da shi ta tsaya kamar zata yi magana amman sai ta fasa domin yace mata baya jin dadi.

"Washe gari da safe shine ya fara shirya Sayyada domin tafiya makaranta, ma'u tana kokarin kai masa"

ruwan wanka amma yace mata sai ya dawo daga kai Sayyada makarantar zai yi wanka. Mamaki ya kama

ta shi da yake sauri idan gari ya waye ya tafi gurin aiki. Ita ce ke kai Sayyada makaranta kullum amman dai ta kyaleshi suka fice akan babur dinsa.

Daga can makarantarsu Sayyada gidansu ya wuce. Ya jina suna hira da ummansa da tayi masa maganar

tafiya aiki sai yace ai ya dauki hutu ne.

***

"A can gida ma'u ta gama cika domin ta gano akwai wani Abu da yake boye mata, don kwana yayi yana"

"sallah da addu'a, ta tabbatar akwai wani abu da yake damunsa da ya ki sanar da ita."

"Sai da rana sannan ya iso gidan, koda ya iso bai barta ta tuhume shi ba, ya dinga kwasarta da hira daga"

karshe ta daure ta tamabaye shi batun zuwa gurin aiki yace yau ba zai je ba sun san bashi DA lafiya. Wasa-wasasa sai gashi ya kwashe kwana uku a gida.

"Yau ta kasance lahadi yana kwance a gado yana bacci, ma'u ta kammala gyaran gidan ta tadda shi a daki,"

"idonshi biyu amma ya kurawa silin dakin yana kallo. Tunanin abinda ya kamata yayi yake yi, ba shi da wasu ajiyayyun kudi da zai iya cigaba da wata sana'ar wacce zai cigaba da daukar dawainiyar rayuwarsa. Shin mai ya kamata yayi? Wannan tunanin shi ke kai kawo a cikin ransa, sai ga ma'u ta shigo dakin. Yayi sauri ya rintse idon alamar bacci ya dauke shi, tayi dan tsam tana kallonsa, sannan ta karasa gefen gadon"

ta zauna ta kirawo sunanshi cikin sanyin murya.

"""Yaya! Yaya!!"""

"Yayi shiru bai amsa mata ba a zuwan bacci yake yi. Ta kara matsawa kusa da shi tana fadin ""na san ba"

"bacci kake yi ba, don da ba shigo dakin idonka a bude yake, gara ma ka bude muyi maganar DA ta dace, don na gaji da kumbiya-kunbiyar da kake mini"" ta kai hannunta kan kirjinsa tana masa wani wasa dakan sanya shi dariya."

"Ya mike zumbur da sauri yana dariya ya rungumeta a jikinsa, tayi lamo tana ajiyar zuciya tace ""yaya don"

"ALLAH ka gaya min abin dake damunka, jikina da yanayinka suna sanar da ni akwai wani abu da ya sameka da kake boye min. Yaya nayi zaton nice sirrinka da dukkan nutsuwarka kamar yadda kake fada min, amma me ya sanya kake boye min wani abu yanzu?"

"Ya shafi kanta mai laushi dake burge shi domin ma'abicumiyar yin kitso ce kanana, duk da bata shamfo,"

"tana da santsi da laushin gashi, yana kuma zuwa har wuyanta. A hankali ahmad yace ""ma'u ban boye miki komai ba don baki cancanci na gaya miki ba, sai don nemar miki kwanciyar hankali, amman kila hakan ma ba zai sanya hankalinki kwanciya ba..."""

"Yayi dan shiru kamar ba zai ci gaba DA magana ba sannan yace ""an kore ni daga wajen aiki ma'u"""

"Ta janye jikinta da sauri daga cikin nasa cikin tsananin kidima da tashin hankali. ""Me kace yaya, an kore"

"ka daga gurin aiki, garin yaya? Shike nan mun shiga uku, wai garin ya hakan ya faru yaya?"

Ya mai da kan nata kirjinsa ganin tana neman fita daga hayyacinta yana cigaba DA shafar bayanta cikin

"sigar lallashi. A hankali yace ""kwantar da hankalinki ma'u ki yarda dukkan abinda ALLAH ya kaddaro zai sami bawa babu makawa sai ya seme shi. Kiyi mini addu'a ALLAH ya sanya hakan shine mafi alkhairi agare ni DA ku baki daya"""

"Idonta ya fara zubar da hawaye, ta san illar rashin aikin yi, domin wata makociyarsu da mijinta bai DA"

"aiki an kore shi suna cikin matsala da tashin hankali sosai. Hatta ashana sai ta ara ga rokon abinci, har bara wani lokacin yaranta ke yi. Kayansu kuwa haka suke a yayyage gwanin ban tausayi. Idan matar tana bawa ma'u labarin irin halin da suke ciki da kuma irin wadatar da mijin yake DA ita a baya sai taji kamar"

tayi mata kuka. Yanzu ita ma haka zasu koma ita da mijinta da 'ya'yanta kenan?

"Maganar ahmad taci gaba da ratsa kunnuwanta. ""Ma'u na san zaki ji babu dadi, amman tsira da"

"mutuncina yafi komai muhimmanci cikin rayuwata. Diyar Alhaji Nura Kwangila maigidanmu ce tazo har gurin aikin namu zata ci zarafina"""

"Ta kuma janyewa daga jikinsa tace ""diyar Alhaji Nura Kwangila kuma?"" Yace ""eh ita fa"" a hankali ya"

"kwashe dukkan abinda ya faru ya sanar da ita. Bakin ciki da takaici ya cikata, sai taji abinda mijin nata yayi yayi daidai."

"Ta kalle shi tace ""wannan shine dalilin dake sanya ni kara sonka, da kuma yiwa Abba addu'a da duk"

"lokacin da nayi sujjada domin ya zabar min miji daidai da bukatata, ya zabar min rayuwa mafi kololuwar dadi da daraja. Ina son ka yayana"" ta fada tana dariya."

"Wani irin dadi ya cika shi yace ""tunda kin ce kina sona bari na gaya miki wani abu"" ya kamo kunnenta"

"yayi mata rada ta kankame shi tana dariya, kunya ta rufeta tana fadin ""a'a yaya ni dai a'a"" suka zube a tsakiyar gadon suna dariya kamar babu wani abu a cikin ransu."

Da dare ma'u ta dauko saitin dan kunnenta na gold da ummanta ta sai mata ta mikawa ahmad. Ahmad

"ya kalleta cike da mamaki. ""Wadannan kuma fa ma'u?"" Tayi murmushi ""yaya kenan, ni fa ban son kayi ta zama haka gara mu fara neman abin yi, na san ka iya rini sosai, to sai kayi ta yin rininka, tunda ga shago a"

"jikin gidan nan sai ka gyara shi, wata kila shine mafi alkhairi"""

Ahmad yayi murmushi cikin ransa yana godiya ga ALLAH da suka aura masa ma'u. Yace 'ma'u ki bar

"abinki insha ALLAHU ba zamu Kai ga haka ba, tuntuni wannan tunanin yazo min a rains, amman kin san akwai kudin aikina na kwanaki ashirin da za a bani sai na gyara shagon na san abinda ya dace muyi."

"Sannan zan ci gaba da raba takarduna musamman abokina ishaq ya koma abuja da aiki, ina zaton zai iya"

taimaka min yanzu.

"Ta gyada kai tana fadin ""shike nan ALLAH ya taimaka"""

***

Ranar lahadi Alhaji Nura Kwangila ya dawo daga tafiye-tafiyensa don yafi sati biyu baya gari. Nana 'yar

"gata ta sha tsaraba kamar yanda ta saba, dom mahaifinta yana ji da ita kwarai da gaske, ta so yi masa maganar ahmad dake cin ranta amman tana shakkar abinda zai biyo baya, don haka ta ja bakinta tayi"

"shiru, amman ta kasa mantawa da ahmad mai taurin ran tsiya da kuma girman kai a ganinta."

Washe gari da safe Alhaji Nura Kwangila ya fice domin bincikar gidajen mansa da sauran kamfanoninsa

"dake garin. Bai samu isa gidan man su ahmad ba sai rana wajejen karfe daya. Bayan gaisawa da masu zuba mai wadanda ke girmama shi kamar suyi sujjada, Bayan ya kammala ya tadda manaja a ofis dinsa Bayan sun gaisa suka tattauna akan gidan man. Cikin bayanin ne manaja yake gayawa Alhaji Nura"

Kwangila sallamar ahmad daga aiki da yayi.

"Mamaki ya kama Alhaji Nura kwangila yace ""Saddam dama kana da ikon korar wani ko daukar wani aiki"

"a kamfanina ba tare da na sani ba KO na amince?"" Ba tare da ko dar ba manaja Saddam yace ""yallabai bani da ikon yin hakan, sai dai wannan din ya zama dole ne domin abin ya shafi diyarka ne Hajiya Nana"""

"""Nana kuma, me ya faru tsakaninta da ahmad kuma?"""

Manaja Saddam ya kwashe labarin dukkan abinda ya ya faru ya sanar da Alhaji Nura Kwangila yana

"kallon yanda zai dauki maganar, domin ya san yana matukar ji da nana, amman sai yaga sabanin haka domin yanayinsa sauyawa yayi zuwa bacin rai lokaci guda. Ya dubi manaja yace ""aikin banza, akan dan"

"wannan abun sai a kori mutum daga gurin aikinsa? Wannan ba dalili bane"""

"Ya dinga fada ya inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, har sai da manaja Saddam ya raina kansa har yayi"

"da ya sanin aikata dukkan abinda ya aikata. Daga karshe Alhaji Nura Kwangila ya dubi manaja Saddam khan yace ""sai ka kirawo shi ko?"""

Da sauri Saddam ya fara laluben lambar wayar Ahmad a cikin wayrsa. Dakyar ya samo lambar ya fara

kokarin kira.

***

"A lokacin suna tsakar gida shi da ma'u suna ta wanke kayansu da na yara suna hira. Wayarshi ta fara kara,"

"ya mika hannu ya dauka bayan ya goge hannunsa. Sunan manaja Saddam DA ya gani akan screen din wayar yayi matukar bashi mamaki, har ya ja hankalin ma'u ta kalle shi da tuhuma. Da kamar ba zai daga"

"kiran ba, amma sai ya danna ok ya kara akunnensa tare da yin sallama."

"Bayan sun gaisa manaja Saddam yace ""daman Alhaji ne ke son yin magana DA kai"" ga tunanin ahmad"

"Alhaji Nura Kwangila zai yi magana DA shi ne akan abinda ya faru tsakaninsa da diyarsa, koma dai meye baya shakkar abinda zai biyo baya."

"Saddam ya mikawa Alhaji wayar da sauri cikin ladabi. Alhaji Nura kwangila ya dauka yace ""malam Ahmad"

"kana ina?"""

"Gaban Ahmad ya fadi amma sai ya dake yace ""ina gida ne alhaji, lafiya?"""

"""Ina son idan kana da dama ka dawo aikinka yau, dukkan abinda ya faru kayi hakuri ka dawo bakin"

"aikinka"""

Wani irin mamaki da jin dadi ya kama ahmad. Wannan mutumin Alhaji Nura Kwangila mutum ne mai

"kirki da karamci. Cikin jin dadi yace ""To yallabai, godiya nake"" kamar zai durkusa kasa."

"Ahmad ya kashe wayar bayan sun yi sallama ya kalli ma'u DA sauri wacce ke kallonsa ita ma. ""Ya ya aka"

"yi yaya?"""

Ya fasa ihu gami da surarta ya fara zagaye gidan da ita yana ihu da rawa.

Ta waro ido tana rokinshi akan ya sauke ta kada ya fadar da ita. Sai da ya gama hajijiya da ita sannan ya

direta. Ta kankame shi suna dariya.

"Yana gaya mata abinda ya faru ta bude idonta cikin farin ciki, amma har lokacin tana rike da shi tace"

"""ALHAMDULILLAHI! Tsarki da godiya su tabbata ga ALLAH. shiga wanka kaje da wuri yaya"" ta ja shi da sauri suka nufi bandakin suna dariya."

Wannan shine sanadiyyar komawar Ahmad bakin aikinsa.

***

Daga nan shi kuma Alhaji Nura Kwangila gidansa ya wuce ransa a bace. Yayi sa'a ya tarar da nana a gida

"tana kallo ita da mahaifiyarta, ya rufeta da fada. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba."

"Mamaki da takaici ya cika nana akan wani can babanta yau yake yi mata rada. Cikin kuka tace ""Daddy ka"

san abinda yayi min kuwa? Sai ta kara fashewa da kuka.

"Sai kuma jikinsa yayi sanyi yace ""ai kin san na hana ki ciwa dan adam mutunci, baki san irin baiwar da"

"ALLAH yayi masa ba, musamman mutum irin Ahmad mai magana daya da bin dukkan ka'idojin aikinsa. Idan kina son mu shirya dake sai kin sauya wadannan dabi'un naki dole"""

Sai kuma ya koma rarrashinta.

"Hajiya Batula ta dinga dariya tana fadin ""yau dai na ganku a rana. Ai da idan na fadi laifinta gani kake yi"

"kamar bana son jin dadinta ne"""

"Alhaji Nura kwangila yace ""to ina ruwanki ke kuma, wannan magana ce tsakanin uba da diyarsa"""

Ita dai dariya kawai take yi don jin dadin fadan da yayi mata.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

45

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Tun ranar da ahmad yayi mata wannan abun take mamakin waye shi, me kuma ya taka a rayuwarsa har"

"yake yin abin da yaga dama? Abin da babanta yayi mata yau kuma akan ahmad din sai ya kara bata mamaki kwarai da gaske, don haka koda ta isa gadon baccinta kasa rintsawa tayi ta dinga tunanin kamanni da yanayin ahmad, surarshi ta dinga bijiro mata. Ta damu ranta da son gano wanene shi, me"

yake da shi da yake yin abun da ya so?

"Dogo ne shi sosai bai DA jiki akwai yanayin karfi da mazantaka a tare da shi. Ba fari ba ne, amman"

"yanayin fatarshi yana da matukar kyau, irinsu ne ake cewa wankan tarwada. Akwai wani gyaran gashi da yake yi wanda ya zagaye bakinsa zuwa kasan hancinsa ko na komai dole a kira ahmad da kyakkyawan saurayi. Sai ta lumshe ido a cikin zuciyarta tana fadin ""to wai me ya sanya ta damu da tuna shi ne ma?"

"Bata da amsar da zata bai wa zuciyarta. A haka tana tunanin har tayi bacci, a cikin barcin nata na wannan"

dare sai da tayi mafarkin Ahmad.

Da sassafe ta fara shirin tafiya aiki inda take yi a karkashin kamfanin mahaifinta amman zuciyarta fal da

"tunanin ahmad. Sai ta tsinci kanta da sanya kaya masu matukar kyau, ta san ba don ta burge ahmad ba ne, amman zata so ya ganta cikin shiga mai kyau. A haka ta wuce ofis."

Karfe goma na safe ta janyo ofis dinta ta rufe ta nufi motarta ta shiga ya tasheta ta fice daga kamfanin.

"Kai tsaye gidan man su Ahmad ta nufa. Motar da ta hau yau ba irin ta rannan bace, don ita NANA FOUR ce don haka har ta isa inda yake bai kula da ita ce ba. Cikin sa'a kuma yau gidan man nasu babu layi."

"Yana tsaye har ta ISO gab da shi ta bude motarta ta fito, bai ganeta ba sai dai yaga kamar ya Santa,"

"domin rannan da bakin gilas ta iso gurin nasu, yau kuma babu. Ya kau da kansa da sauri daga kallonta domin ba dabi'arsa bace kallon mata."

"Ta isa kusa DA shi ta tsaya tace ""ina fatan za a zuba min man ko? Ya kalle ta DA sauri yana son tuno inda"

"ya santa. Tayi murmushi har fararen hakoranta suka bayyana tace ""sunana NANA ASMA'U"" sai a lokacin ya gano ta, yayi yake saboda jin sunan, yakan girmama dukkan macen dake da wannan sunan a duniya. Yace ""Hajiya barka da war haka. Na nawa za a zuba miki"""

"Mamaki ya kara kamata don tunda take zuwa gidan man mahaifinta bata taba bayar da kudi ba, amman"

"yau gashi ana tambayarta na nawa za a bata, koda yake ta riga ta gano waye ahmad, kaifi daya ne don haka tace ""ka cika min tankin sai mu ga na nawa ne"""

Bai ce komai ba ya nufi tankin motarta ya fara zuba mata.

"Ta dinga satar kallonsa, ta jima bata ga namijin da yake burgeta kamar ahmad

38 / 47