Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 47

63K to 66K   out of 139.6K words

yana fadin 'ke bakya ganin mutane ne zaki ture su sai kace wata akuya? baushi ya kara cikata tace 'idan bar baka ce sai kace shegiya ba ai kayi da sauki, ka"

kalle ni da kyau ban yi kama da wacce zara auri shege maras asali irinka ba'

"wani abu mai ciwo ya taso ya tokare masa wuya, idanuwanshi suka sauya zuwa ja, tsigar jikinshi ta tashi"

ya daga hannu da zummar ya wanke ta da mari amman sai wani tunani ya darsu a zuviyarsa ya janye hannunsa da sauri.

"ta galla masa wata muguwar harara tana fadin 'wallahi da ka mare ni da ka gane kurenka a yau, kuma na"

kara gaya maka kai ba sa'an aurena ba ne gwara ka sanar da masu shirin yi suna yin aikin banza ne ma'

"taja dogon tsaki ta wuce ta barshi nan atsaye, zuciyarshi ta dinga wani hankoro hana jin kamar ya finciko"

"ransa daga gangar jikinsa ya huta. ya bita da kallo har ta fice daga soron, daga. yanayin shigarta ya nuna masa yawonta zata, domin wash matsattsaun kayane a jikinta da suka kama ta tsam, kanta ya sha kitson karin gashi, ga wasu farata da ta sanya.fatarta kuwa har wani kore-kore takeyi saboda tsabar bilicin din"

"datayi, ta baza turare wanda duk inda ta ratsa sai ta bar kamshin."

"amman ace wannan ce matar aurensa, hawaye suma dinga zubowa daga idanuwansa, ya hada kai da"

"bango yana kukan zuci tabbas yana cikin tsaka mai wuya da jarrabawa, dama abbansa zai fahimta da yace ya fasa wannan auren zai iya zama haka har tsawon rayuwarsa da dai ace ya zamana ana yi masa"

"irin wannan cin zarafin, wai raliya ke zaginshi wacce ake son ta zama matarshi."

"ya jima jingine da bango har zuciyarshi tayi sanyi ya shige cikin gidan, tun daga wannan lokacin auren ya"

"kuma fita daga ransa domin ya tabbata ko anyi ba za a haifi da mai ido ba, ya kuma so ya tunkari abba da maganar fasa auren saidai shawarar da zuciyarsa ta bashi ce ta hanashi. saboda ita ma raliyar bata so, don haka ba zai yarda maganar kin auren ta fito daga bakinsa ba, ita ya kamata ta tadda abba ta gaya masa bata son auren ba shi ba, shi kam yayi alkawarin yin hakuri da sukkan halayenta koda zata dinga shiga da KWARATA gidan ne kuwa don ya san raliya ba zata daina komai ba, a yanzu ne ma zata yi komai"

domin ta kara gallaza masa.

*

*

*

a juri zuwa rafi dai raliya.

DA ME AKE ADO?

17

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Malam yayi matukar kokari domin shi ne ya sayi duk wasu kayan daki na raliya, aka je aka jere hatta"

"kayan da ya dace ace uwa ce tayi shine yayi, domin lami tace auren da aka yiwa diyarta na dolene, don haka ko tsinke ba zata kai ba, wadanda suka hada su zasuyi komai. saidai mutane da yawa sun gane borin kunya ne, domin babu abinda ta ajiye da sunn auren diyarta. tun can baya daman kudinta yana karewa gurin bin malamai ne balle yanzu da take iyakacin kokarinta na wannan auren bai tabbata ba,"

domin a cewarta diyart kalar masu kudi ce da asali ba ahmad fakiri ba.

"shi kam mahaifinta godiya da sanya albarka ya ding yiwa dan uwans domin ya fidda shi kunya, sai kuma"

a yanzu ya kara yadda da irin kaunar da dan uwan nasa keyi masa.

ranar kamu amarya ba yabo ba fallasa tayi kwalliya kamar gaske koda yake yayyanta sun yi mata fada

har da mahaifinta da abban duk da ahmad bai halarci gurin kamun ba yayi farin ciki kwarai da gaske da labarin da yaji gurin yara na yanda amaryar ta cashe rawa hakan ya sanya ya fahimci ta fara sakkowa.

"abinda ya kara bata masa rai bai wuce hana shi ma'u da aka yi ba sanda yaje daukarta ba, domin yayi"

"mata alkawari duk lokacin da bikinsa ya tashi zai je dauko ta, saidai shugabar makarantarsu ta bashi hakuri ta gaya masa cewa ana gab da fara jarrabawar sauya aji wato (3rd term exam) duk da bai so"

"hakan ba amman babu yanda zai yi, sai dai ya nemi alfarmar a barshi ya ga ma'un."

"ma'u ta shigo ofis din cike da farin ciki domin bata san abinda ya faru ba, tayi zaton daukarta yazo yi,"

"domin tana ta lissafin ranar bikin yayan nata, ta durkusa tana dariya tace 'yaya ahmad ina wuni? ya kalle ta yana murmushi yace 'nanana lafiyau, ya karatun?"

"'alhamdulillahi yaya ina ta dagewa, domin wacce ta dauki 2nd a jarrabawar zango na biyu rakiya taci"

"kurin wannan karon sai ta kwace mini kambuna wai sai tazo ta daya, shi ya sanya bana bacci kullum sai na yi karatu mai yawa, tun kafin mu fara exam har na haddace komai, ka san da an dawo wani hutun zamu tafi SS1 ne kaga na zama babba ko?"

yayi dariya cike da farin ciki yace 'nanata sarkin zance tunda kika zo baki barni nace komai ba kin hau

zuba' ta rufe idonta tana dariya 'sorry my yaya ahmad' ya kyalkyale da dariya saboda yanda tayi maganar abjn dariya ne.

ta bude idonta tana kallonsa tace 'yaya ahmad ba zan tafi da komai ba domin umma tace idanka kai da

aunty ummi yazo zata min sabbin dinkuna'

gabansa ya fadi gaba daya annurin fuskarsa ya dauke yace 'ma'u ba a barni na dauke ki ba'

ta kalle shi afirgice tace 'yaya ahmad ba a barka ba? ba abokinka malam rabi'u ne zai sanya ka dauke ni

ba ko baka sanar da shi bane?

'na sanar da shi ya kuma kai ni har gaban principal dinku. hujjar da ta kawo min tafi bikin muhimmanci

kiyi hakuri ki zauna'

idanuwanta suka ciko da kwalla tayi. tayi narai-narai da ido gabadaya annurin dake fuskarta ya dauke

"tace 'yaya bikinka da aunty ummi yafi karatun da zanyi, zan iya yadda nayi ko ta karshe ne in dai zan halarci bikin' sai ta fashe da kuka."

"tausayinta mai tsanani y kama shi, yaji kamar ya janyota ya rarrasheta, saidai a yanzu ta girma ta wuce"

"haka amman yana da hanyar rarrashin nata da baki don haka cikin sanyin murya yace 'ki daina kuka ma'u ba ummi zan aura ba, ummi ta ki ni tace bata sona, abba yace ba za a fasa auren ba zan auri raliya'"

ta kalle shi da sauri da mamaki gaba daya kukan ya dauke lokaci.guda tace 'yaya ahmad da gaske aunty

ummi tace bata sonka? bata barshi yace wani abu ba ta cigaba da magana.

'to me kayi mata da ta daina sonka. ance ba a daina son mutum kuma aunty ummi ta taba gaya min

"wata rana tace, ma'u ina son yayanki ahmad idan babu shi ba zan iya rayuwa ba, hakan na nufin yanzu bata rayuwa kenan yaya?"

"ya kurawa asma'u ido ya ma rasa me ze ce mata yarinya ce da bata mantuwa, saidai shekarunta basu kai"

"yadda zata fahimci komai ba, wane bayani zai yi mata da zai gamsar da ita, duk yaji ya rude ya ma rasa abin cewa"

"ta kura masa ido tana jiran taji yace wani abu amman ta kula bashi da abin cewar, don haka ta cigaba da"

magana.

"'yaya idan fada kuka yi da anty ummi kaje ka bata hakuri ku shirya, itace tafi dacewa ka aura ba raliya ba,"

"raliya bata da kirki tana bin maza shagonsu, tana zagin yayyanta tana yiwa mamanta rashin kunya, gashi tana karin gashi da bilicin abinda duk ALLAH ya hana, raliya bata iya yin sallah ba fa yaya. bata dace da kai ba sam'"

"zuciyarshi ta karye yaji kamar ya fashe da kuka, wacce amsa ta dace ya baiwa ma'u baya son yace mata"

"ummi ta ki aurensa don yana shege ne ba, ba kuma ya son ta ginu akan yaci amanar ummi ne, ilai kuwa haka ne maganarta ta karshe."

"'yaya ahmad kaci amanar anty ummi tana sonka da yawa, da nace a gidanku zan dinga hutu, amman"

"yanzu tunda raliya zaka aura ba zanje gidanka ba, ko naje fada zamu yi' tana gama fadin haka ta juya da sauri ta bar ofis din tana kuka."

"ya mike tsaye da sauri yana kwala mata kira, amman ina bata waigo shi ba sai fella gudu take yi, ya fice"

"da sauri yana hangenta, gata da dan banzan iya gudu tamkar barewa, idanuwansa suka kada suka yi jajir"

"makwallaton wuyansa ya dinga kaiwa yana komowa ya kura mata ido tana cigaba da gudu tana kuka, har"

"ta bacewa ganin sa. yaya zai yi da ransa ma'u bata san komai akan soyayyarsa da ummi ba, ba kuma zata taba yi masa uzuri ba. tabbas da ummi tasan yadda shi da kanwarsa suke sonta data aureshi kowani irin"

aibu ne kuwa da shi.

dafa kafadarsa da aka yi ne ya sanya shi juyowa da sauri. abokinsa ne malam rabi'u yayi murmushi yace

'naga mutuniyar taka ta fella da gudu tana kuka. nasan daman sai haka ta faru don taci burin bikin nan'

"bai son ya sanar da abokin nasa komai, domin babu wanda ya gayawa ba ummi zai aura ba har yanzu,"

"baya ga gidansu babu wanda ya sani, don haka ya bishi da haka kawai, ya samu suka yi sallama ya wuce."

a mota kafin ya kai gida maganganun ma'u ne suka dinga yi masa kuwwa a cikin kunnuwansa _'ba zan je

"gidanka ba, idan na je ma fada zamu dinga yi da raliya_"

"wadannan sune kalamai masu muni da zai jima suna yawo a ransa, domin yaci burin daukar ma'u ya rike"

"ta, ya kyautatawa rayuwarta amman auren raliya duk ya ruguza masa komai, wannan shine ake kira da"

"kaddara mummuna. wacce bawa bai isa ya kauce mata ba, ahaka ya karasa gida bikin na kara fita daga cikin ransa."

*

*

*

ALLAH KA RABA MU DA MUMMUNAR KADDARA AMEEN.

DA ME AKE ADO?

18

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Daran daurin aure yayansa auwal ya taho masa da wata dakakkiyar shadda da tasha aiki, harda malum-"

malum zai iya cewa tunda yake bai taba sanya malum malum ba sai a wannan karon. yayi dinkuna uku na fitar angwanci amma sai yaga wannan shaddar tafi dacewa da ya sanyata ranar daurin auren don

haka ita ya sanya din.

"daurin auren yayi cika sosai domin gayya ce ta kusan mutum shida, duk 'yan uwansa sai da suka gayyato"

"abokansu ga gayyar abbanshi da ta baban raliya ga kuma ta yayanta itama, duk da zuciyarshi bata farin ciki ya daure ya nunawa jama'a yana farin ciki abunda ya kara sanyaya zuciyar baban nashi."

"lokacin da aka shafa fatihar aurensa da raliya sai da hantar cikinshi ta kada, wato ya tabbata raliya ce"

"matarshi ba ummi ba, wannan yana cikin tsarin ALLAH, abinda yafi dacewa kawai yayi yanzu nemawa matarshi shiriya a gurin ALLAH, tunda ta tabbata. haka aka watse daga daurin aure kowa cikin farin ciki."

"raliya ihu ta dinga kwarmawa sanda taji an daura tana fadin ta shiga uku an cuce ta, sai da musa ya shiga"

"da bulala ya dinga carkwada mata sannan tayi gum da bakinta, lami ta dinga masifa da kumfar baki wai don me za a dokar mata diya, a kyale taji da bakin cikin wannan kaddarar auren da aka daura mata mana."

shi dai musa bai ce komai ba ya juya ya fice daga gidan.

"wannan ya sanya aka yi yinin biki ba cikin dadin rai ba, amarya ko kwalliya bata yi ba, duk da kawayenta"

"sun zo sun cika gidan, sam bata yi kwalliya ba haka suka karaci tsiyarsu a cikin dakin, yinin wani iri kamar bikin beraye."

"karfe biyar motocin daukar amarya suka iso, raliya tayi wanka duk.da bata yi wata kwalliya ammaan tayi"

"fes domin wata yayar lami ce ta kama fada tana fadin 'tunda aka daura auren ya kamata su watsar da makaman yakinsu su rungumi kaddara, yaushe za a ce akai amarya haka? wannan ya sanya ta dan kimtsa. irin kukan nan da amare suke yi bat yi shi ba. idonta kemdagas babu alamun kunya, ita kadai"

tasan irin tandin da tayiwa angon nata na rashin mutunci buhu buhu haka aka wuce gidan mijin da ita.

"sai wajen karfe tara na dare ahmad ya kammala shirya kayansa tsaf cikin jakarsa, don haka ratayawa"

kawai yayi ya nufi gurin umma.

tana zaune a rumfarta da sauran 'yan biki basu watse ba ya durkusa yana fadin 'umma zan wuce ina

"bukatar addu'arku, idan na bata muku ku yafe min don ALLAH'"

ya sunkuyar da kansa jin muryarsa tana rawa tamkar zai fashe da kuka.

idanuwan ummansa ya ciko da kwalla tana jin kamar zata rabu da danta ne har abada. ALLAH ya

jarabceta da tsananin son ahmad bata son duk wani abu da zai nisanta su sai gashi yau aure zai raba su.

"tayi shiru tsawon lokaci sannan ta daga kai ta kalle shi, yana tsugune kan kafafuwansa kansa yana kasa, daga yanayinsa ta san yana cikin damuwa mai tsanani, tayi karfin halin fara magana."

"'tunda nake tare da kai ban taba ganin wani abu na ashsha ko na kaico a gareka ba, na san raliya zata iya"

"yin komai domin ta tunzuraka ta kuma hasala ka, bana son jin komai daga gare ka sai alkhairi kada ka yadda wani abu na bacin rai ya fito daga gurinka, kayi komai domin ka farantawa babanka rai, kiyayyar mace takitacciya ce wata rana zata daina, ranar da aka wayi gari kun fara tar zuri'a shikenan komai ya"

zama tarihi. ALLAH yayi maka albarka.'

"idanuwansa suka dinga zubda hawaye, ina ma yanda yake da iyaye nagari suka yi masa wannan fadan"

"yaji haka raliya ma take da su, da aurensu ya zauna lafiya. daga can saman kansa ya jiyo muryar umman nashi tana fadin 'tashi kaje kada dare yayi ALLAH yayi maka albarka'"

"ya mike sumi sumi yana fadin 'amin' ya wuce, shikenan yau zai bar gidansu zai bar cjn abincin ummansa"

"da kulawarta, zai shiga wata rayuwa da bai san yaya zata kasance masa ba, fatansa ALLAH ya sanya ya haye wannan jarabawar ALLAH zame masa gata."

"ya isa kofar gidan nashi da babur dinsa. ya sauka ya tura kofar, ga mamakinsa sai ya ga kofar a bude take"

don haka ya tura babur din ya shiga.

tun daga tsakar gida ya fara jiyo kugin rediyo an kure wakokin zamani. mamaki ya cika shi domin dai

"daga dakin dake kulle yake jiyo kidan, yasan wannan dakin baccin raliya ne abinda ya kara bashi mamakin kuwa bai wuce me take fahimta a wakokin ba, yasan dai raliya jaki da kayan littafai ce babu"

arabiyya balle boko a tattare da ita. ko kuma jin kidan gayu ne.

"ya kada kai ya nufi daya dakin da aka jera kujeru a ciki, domin yasan dakin da raliya take ba zai samu"

damar kwana acikinshi ba ko bata rufe kofar ba balle dakin a bame yame ma.

har ya kwanta akan kujera yaga dacewar ya koma shagon gidan kawai da kayansa ya zauna nan ne

"dakinsa. don bai dace ya tare a falo ba. wannan shawaran ya dauki kayansa ya nufi soron gidan, ya tadda shagon da kura, ya ajiye kayansa a soron ya gyara shagon tsaf ya dauko tabarma ya shimfida sannan ya kwanta."

"da asuba ya tashi ya nufi masallaci yayi sallah ya dawo ya fara lazimi kamar yadda ya saba, dama bai"

"sanya ran raliya zata tashi tayi sallah ba, domin yasan bata da wannan tarbiyyar, sai wajen goma na safe take tashi. ai kuwa yau dinma hakane sai darana ta take ta tashi, lokacin tuni ya jima da karyawa domin flask ya dauka yaje ya siyo shayinsa ya sha ya bar mata nata a flask, duk yana can daki yana hangota ta windo ya ga ta fito, amma abinda ya bashi mamaki har karfe goma na safe raliya bata fito ba, kuma gidan ba irin na 'yan gayun nan bane mai bandaki a ciki balle yace tayi alwalarta a ciki, can sai ya jiyo"

sautin radiyo an saki irin kidan jiya na turawan zamani.

"ya so ya share amman sai ya tuna yanzu hakkin raliya da tarbiyyarta duk suna kanshi, dole ya tunatar da"

"ita gaskiya don haka ya mike ya nufi dakin nata. ya tura kofa da sallama, ta daga kai cike da tsananin mamaki tana dubansa, shi kam yanayin da ya taddata ne ya sanya shi tsananin firgita da rudewa domin wata 'yar figigiyar ribar bacci ce a jikinta, dukkan surarta tana waje jikin nan nata yayi jajur ta sha man"

"kanti, gashi tana kan kuruciyarta, sai wani sheki da sulbi fatarta ke yi."

wani abu ya dinga yawo a cikin kanshi saboda bai taba ganin wata mace cikin irin wannan yanayi ba. tayi

masa wani kallon banza sama da kasa tana yatsuna fuska tace 'ina zaton kayi batan kai ne ko malam'

"yanayin yanda tayi maganar yayi gaggawar dawo dashi hayyacinsa, yayi kokarin tattaro jarumta da"

"nutsuwarsa ya sanya akan fuskarsa, duk da zuciyarza na kokarin bijire hakan. sannan yayi kokarin zakulo abinda ya kawo shi yace."

"'ina ta sauraron ganin kin fito kin yi sallar asuba sai kuma naji kin kunna rediyo ma, alamar baki da niyyar"

gai da ubangijinki'

tayi dariya tayi shewa tayi masa irin kallon da ake yiwa 'yan tasha 'au ashe fa ustaz aka kakaba mini ko?

"wai kayi zaton zuwa nayi zama a gidanka don ALLAH ka dube ni ka dubi fatata ai ka san ban yi kalarda zan iya zama a cikin irin wannan gidan kirar talakawa ba, talauci ya haife ni na kuma yarda na rayu a ciki amman ba zan yadda na dawwama har na kare rayuwata acikinsa ba, batun sallah kuwa kada ka matsa"

"mini domin ba kabarinmu daya ba, ba kuma na zo zama bane jira nake ka shigo ka bani red card dina'"

"ransa ya baci ainun banda kaddara meye hadinsa da raliya, jahilar da bata iya komai ba sai wauta"

"amman ace itace matarsa ta kuma zage tana zaginsa haka. yayi kamar ya kara magana sai yaga rashin dacewar hakan, don haka ya juya da zummar ficewa sai ya jiyo ta daga bayanshi tana fadin 'malam fita fa"

bata kama ka ba gwara ka sallame ni tun ban yaga maka rigar mutunci ba'

"bai kula ta ba ya fice domin tunainta irin na dabbobi ne, idan ya cigaba sauraronta komai zai iya faruwa,"

kawai sai ya fice daga gidan ma.

*

*

*

a taka a hankali dai raliya domin duniyar nan fa ba matabbata bace.

DA ME AKE ADO?

19

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"kai tsaye gidan abokinsa ishaq ya nufa, da yake lokacim hutun karshen sati ne ya

22 / 47