Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   37 / 47

108K to 111K   out of 139.6K words

cikin ihu. ""Ke duba min"

"bandaki ko raliya ta shiga"""

"Amina ta mike da sauri ta nufi bandakin ta fara dubawa, ta dawo da sauri domin taga mahaifiyar tata a"

"rude take tace ""lami bata nana"" lami ta dafe kirji a kidime tana fadin ""na shiga uku kar dai ace yarinyar nan ta gudu ta bar mana diyar nan?"

Ihun jaririyar ya cika mata kunne ta koma dakin da sauri ta dauko jaririyar ta rungume ta tana jijjiga ta

"DA fadin ""ke maza duba mana gidan nan sosai har can gidan su dije ma ki gani ko tana can"""

Amina ta juya da sauri ta nufi hanyar fita. Lami ta cigaba jijjiga jaririyar hankalinta a tashe kamar ta zabga

ihu ko ta ji sanyi a ranta.

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Domin duk inda ake tunanin za a samu raliya an duba

"babu ita babu alamunta, dole lami tana ji tana gani ta wanke mamanta da magunguna ta fara baiwa"

"jaririyar nan nono, domin ba zasu jure siyan madara ba, don malam jibril kokarin ganin ya siyi madarar amma ba zai iya jurewa ba yayi mitar tasa har ya gama."

"Lami kam kukan jini ne kawai bata yi ba, ko tsakar gida bata iya fitowa saboda kunya da nauyi, gashi yara"

da 'yan mata har shigowa gidan suke yi kallon 'yar da aka gudu aka bari bayan an haifeta.

"Umma kam ji take yi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don dadi. ALLAH bai barin hakkin wani akan wani,"

ita ke yiwa ahmad gori akan shi SHEGE ne sai ga SHEGIYA a gidansu. Sannan ita ce ta sanya raliya ta gudu

"da kanta, yau kuma ga gudun raliya ya zame mata matsala da tashin hankali a karo na biyu. Haka nan dama ALLAH yake ikonsa."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

43

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

BAYAN SHEKARU BIYAR

"Rayuwar ahmad da ma'u an samu cigaba da kuma karuwar zuri'a, domin cikin shekarun nan ma'u ta kara"

"haifar yara biyu namiji da mace, an sami Hajiya Amina da kuma Malam Sulaiman, har wannan lokaci mijinta yana matukar kaunarta da nuna mata soyayya, 'ya'yansa kuwa sune abokan rayuwarsa tare suke cin abinci tare suke sallah hatta da su yake yi, domin yana ganin sune sabuwar zuri'arshi a duniya, bashi da kowa bayansu, don sun sha rigima da ma'u ma akan kwanukan da take yi yace WALLAHI bata isa tayi"

"masa tsarin iyali ba, idan ma 'ya'ya dari zata haifa yana so."

"Abin ya sanya musu rikici, don tana ganin ba zata iya ba amman da ya gaya mata wata magana wata"

"rana yana hawaye bayan haihuwar Hajiya ya sanya ta hakura ta sallama masa tana ta kuka ne sanda ta samu cikin malam ya zauna a gabanta ya kwantar da murya yace 'ma'u ba Zan sanya ku dole ki haihu ba, rayuwarki ce kina da damar yin yanda kike so, amman zan so ki tausaya min ki tuna ni bani da kowa da zan kalla da sunan dangina na jini bayan 'ya'yana. Da sune zan haifi zuri'a da za a iya kallo a kirata da DANGINA shin idan baki yarda kin haifa min 'ya'ya ba ta ina zan samu dangi? Haba ma'u ki tausaya min"

"mana, kece kadai wadda zata iya bani abinda nake bukata, ki taimaka min ma'u"""

"Jikin ma'u yayi sanyi ta daga kai ta kalli mijin nata wanda ke durkushe a gabanta yana zubar da hawaye,"

"tausayinsa da sonsa ya dinga shigarta. Ahmad yana sonta yana kuma kaunar duk abinda take so, yana tattalinta, me ya sanya itama ba zata so abinda yake so ba? Tabbas ita ce me daukar cikin ta haihu, amma rainon abun da wahalarsa ne take ji."

Ta kamo shi ta rungume a kirjinta tana shafar kanshi. Sai kawai ya fashe da kuka yana cigaba da magana

"""ki taimaka min ma'u... Ki taimaka min..."""

"Gaba daya hankalinta ya tashi, cikin rawar murya take fadin ""na daina mijina ba zan kara ba, zan yi maka"

"dukkan abinda kake so, zan haifa maka 'ya'ya insha ALLAHU"""

"Ya rungume ta a akan jikinsa wani dadi yana shigarsa, yana mata godiya, wannan ya kwantarwa da ma'u"

hankali suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin soyayya da nishadi.

"iskaKasancewar ya jima a gidan man da yake aiki, wato 'YAN LEMAN PETROLEUM na kurna aka sauya"

"masa zuwa wani sabon gidan man DA maigidansu Alhaji Nura Kwangila ya gina a cikin G.R.A. duk DA gurin ya yiwa ahmad nisa sosai bai damu ba, domin Alhajin yayi masa karin albashi har yayi sabon"

mashin don haka bai da matsala wajen zuwa aiki da komowa gida.

"Yau an tashi da rade-radin kamfanin mai zasu yi yajin aiki cikin satin, don haka mai ya fara ja da baya,"

"gidajen mai da yawa ya kasance a ciki, ciki kuwa har da na su ahmad, layi har kan titi sai hayaniya ake tayi. Daga can nesa ahmad ya hango wata hadaddiyar mota ta shigo cikin gidan man. Ya jima bai ga mota jai kyan wannan motar ba. Amma ga mamakinsa sai ya ga mota ta wuce layin tana tunkaro shi kai tsaye, har ta iso kusa da shi ta ja gefe ta tsaya. Gaba daya hankalin mutanen dake kan layin yayi kan mitar"

"musamman da horn ya fara fitowa daga cikin motar da karfi, a bayan motar an rubuta 'NANA ONE'"

"Wani mai taxi dake jingine jikin motarsa wanda layi ya kusa zuwa kansa yace ""aikin banza wai su masu"

"kudi ba zasu bi layi ba sai dai su shigo a basu kawai"" wani mai hayis dake kusa da shi yace ""kai baka ga wani rainin hankali ba ma, wai ba zasu fito daga cikin motar su roki arziki ba sai dai aje a zuba musu saboda takamar suna da kudi, ko gilas din motar ma Anni saukewa. Kai 'ya'yan masu kudin garin nan"

"suna abinda suka ga dama WALLAHI"""

"Ahmad yana jin duk abinda suke tattaunawa a kai, a ransa cewa yake ""saidai su dige a nan, amma"

"WALLAHI idan basu bi layi ba ba zan zuba musu man ba"" horn din motar ya ci gaba DA cika kunnen mutanen dake wajen, su kuma mutane suna ta surutai kala-kala. Shi kuwa Ahmad ko kallon tsiya motar bata ishe shi ba balle kallon arziki. Can sai aka bude motar a fusace aka fito. Takalma ne hadaddu cikin"

wata hadaddiyar kafa suka fara bayyana sannan ta karasa fitowa.

Hadaddiyar budurwa ce akin farko akin farko ta fito tana sanye da doguwar riga ta yadin material mai

tsada irin wacce ake yowa daga kasashen larabawa. Ta yane kanta DA dan siririn mayafi idonta sanye da gilas baki.

"Ta nufi ahmad tana haki kamar tayi tseren gudu. Gaba daya hankalin jama'ar dake gurin yayi kanta, wasu"

"na fadin ""ikon ALLAH ashe ma mace ce"" wasu ko na fadin ""ai lallai kam kya yi izgilanci don kina da kudi"

"kuma ga kyau"" shi kuwa Ahmad bai na kalli inda take ba ma balle ya san wace ce ita ko ya kamanninta suke."

"Ta iso ta tsaya a kansa cikin zafin rai tace ""kai malam kai kurma ne baja jin horn ne? Ahmad ya dago kai"

"ya kalle ta yana rike da bututun zuba mai yace ""koda ba kurma bane ni horn dinki bai DA alaka da ni tunda ba don ni kike yinsa ba, me zai sa nace Sai na kalli inda yake fitowa?"

"Ta Kara kumbura tace ""wai kana nufin baka fahimci kiranka nake yi ka zuba min mai ba kenan? To ka"

"sanyani har na fito sai kaje ka zuba min ko"" ta rikr kugu tana wani girgiza tana kallonsa, amma ahmad bai yi magana ba, bai ma kara kallonta ba ya nufi motar dake kan layi zai zuba mata."

Da yawa mutanen dake gurin abinda yayi ya burge su don wasu har sai DA suka furta. Ta bishi da sauri

"tana fadin ""kai malam wanna irin dan rainin hankali ne kai, yaya ina yi maka magana kana wani share ni?"""

"Ya tsaya ya kalleta cikin idonta yace ""da alama kina da ciwon ido ko kuma ciwon rashin fahimta, baki"

"kula da duk wanda ya shigo layi yake bi bane, idan har da gaske kina son man nan sai ki koma ki biyo kayi kamar yadda kowa yayi"""

"Ya fara zuba man cikin motar dake kan layi mai motar yana fadin ""ka mini daidai samari, kowa ma ai"

"mutum ne, tun safe muke kan layi haka kawai don kina takamar kudi sai ki shigo kice sai an zuba miki, kibi layi kawai Hajiya"""

"Maganar mutumin ta kara fusata budurwar tace ""wai kai ka san wacece ni kake min irin wulakancin"

"kuwa? Ahamd yayi dan murmushi. ""Na sani mana ke yarinya ce diyar mai kudi amma kuma mara tarbiyya"" ta kara fusata ainun har ma ta rasa ne zata kuma cewa. Tunda take ba a taba yi mata cin mutunci irin wannan ba. Mai zuba man dake kusa DA ahmad ya karaso yana rarrashin ahmad. ""Kaga don ALLAH share ka zuba mata kawai, kaga ai macece"" Ahmad ya kalle shi yace ""WALLAHI ba zan zuba mata"

"ba, da tana son taimako da sai ta zo da mutunci da girmamawa ba ta irin haka ba"""

"""Kai din banza! Waye kai da har zan girmamaka, rashin sani wacece ni ya sanya kake yin komai, zan nuna"

"maka kai karamin Dan iska ne yanzun nan"""

"Ahmad yayi murmushin takaici yace ""ni babu abun da ya hada alakata da iska balle har na zamo karamin"

"danta"" mutanen gurin suka sanya dariya. Jazuli abokin zuba man nashi yace""taho ki matso da motar taki gurina na zuba miki, ahmad ba kanwar lasa bane baya daukar wargi"""

"""ALLAH ya sanya wuta ne shi amman shi zai zuba min man don dolenshi, kuma WALLAHI zan nuna masa"

"iyakarsa yau"" ta fara kokarin danna wata hadaddiyar waya dake hannunta."

"Jazuli ya kada kai domin ya fuskanci ita ma ban kanwar lasa bace yace ""shikenan Hajiya ma ga wanda zai"

"karya rantsuwarsa tsakanin ke da shi"" ya juya ya cigaba DA aikinsa."

Shi kuma Ahmad bai Kara bi ta kanta ba ya cigaba DA zubawa wadanda suke kan layi mansu suna tafiya.

"Daga bangaren budurwar cikin isa ta fara magana a waya. ""Hello Sadam kana ina ne? Ko ma ina kake"

"kayi gaggawa kazo gani nan a gidan manku"" ta kashe wayar tana kallon ahmad tayi kwafa ta koma jikin motarta."

"Sarai ahmad yaji sunan wanda ta fada Saddam shine manajan gidan man DA yake aiki yanzu, amman ko"

"dar bai ji a jikinsa ba. Jazuli ya kuma matsowa gurin daidai kunnen ahmad yace ""kai abokina duk yadda aka yi yarinyar nan tana da matsayi babba, ko baka ji sunan manaja ta kira bane?"

"Ahmad yace ""sai me din ta kira sunan manaja, koda ace sunan Alhaji Nura Kwangila ta kira ni babu"

"abubda ya shafe ni don akan aikina nake ni"""

"Jazuli ya koma da baya ya kada kai, ya san halin Ahmad da taurin kai ba zai tankwaru ta dadi ba."

Budurwar tana jiyo su sai huci take yi. Tabbas yau sai ta nunawa wannan mutumin iyakarsa zata ga da

abinda yake takama.

Minti biyar a tsakani sai ga motar manaja sadam tana shigowa gidan nan a guje. Kai tsaye gaban

"budurwa ya isa ya tsaya ya fito daga cikin motar ya isa gabanta da sauri kamar zai durkusa mata don ladabi yace ""Hajiya barka da zuwa wani abu ne ya faru?"

"Tayi murmushin mugunta tana kallon Ahmad tace ""wannan ma'aikacin naku ne ke neman raina min"

"wayo, na iso ina ta horn ya zo ya zuba min mai ya ki, har na fito NA isa inda yake nayi masa magana"

"amma yayi min wulakanci da rashin mutunci har ana bashi hakuri akan ya zuba min yace ba zai zuba ba, shin waye shi da me yake takama?"

"Manaja Saddam ya fusata ya waiga gurin Ahmad da sauri yace ""kai ahmad baka san wacece wannan ba"

"kayi mata rashin kunya ba, diyar mai gidan nan ce gaba daya Alhaji Nura Kwangila fa"""

"Ko dar ahmad bai tsorata ba ya dai sakale abinda yake zuba man yace ""to manaja don tana diyar Alhaji"

"Nura Kwangila sai tazo har inda nake sana'a tace zata yi min iko da gadara? Naga ba kyauta ake biyana albashi a gidan man nan ba, sai nayi aiki da karfina da tunanina akan me zan yarda a taka ni? Da tazo da"

"sai tayi bayanin wace ita ba wai ta dinga kallon mutane kamar dabbobi ba"""

"""Kai malam ya ishe ka haka, wai kai dan uban waye da kake gaya min duk abinda kake so eye? Budurwar"

ta fada da bacin rai ganin bai ko risina ba.

"Kalmar uban da ta ambata ita ce ta kashe masa jiki, amman ta kara fusata shi bai DA uba ma ko"

matsiyaci ne balle har ace za a zageshi.

Ganin yayi shiru bai ce komai ba ya sanya tayi zaton ya fara risina ne ta cigaba DA rashin mutuncinta.

"Manaja Saddam ya ce ""don ALLAH Hajiya kiyi hakuri bari a zuba miki man"" ya kalli Ahmad dake huci"

"yace ""ka dauko bututun ka zuba mata"""

"Ahmad ya girgiza kai ""kayi hakuri yallabai ai na rantse ba zan zuba mata ba, ba kuma zan yi azumin"

"kaffara har uku saboda ita ba"""

"Manaja Saddam ya san halin taurin ran Ahmad don haka ya kama fadan karya. ""Banda shashashanci"

"meye abin rantsuemwa akan wannan yar matsalar, ni bana son irin wannan abun da kake yi sam, baka san waye mutum ba bai kamata ka dinda saurin rantsuwa ba"""

"Ya kalli budurwar dake ci gaba DA huci yace ""Hajiya nana don ALLAH kiyi hakuri muje can gurin jazuli ya"

"zuba miki man, bai san ke wacece ba shi yasa ya aikata hakan, amma daga yau ba zai kara ba, dole zanyi masa hukunci daidai da laifin sa"""

"Nana ta yamutsa fuska tace ""manaja WALLAHI shi ne zai zuba mini man nan, idan shi mara mutunci ne"

"no na fishi. Dole shi zai zuna min"""

Ahmad ya kalle ta DA mamaki yana kada kai. Shi kansa manaja gumi ne ya karyo masa cikin ranshi yake

"fadin ""na shiga uku! Wadanne irin yara ne wadannan marasa mutunci? Amma yaya na iya, dole a kyautatawa diyar Alhaji"" don haka yace da ahmad"

"""Kaga ahmad tunda Hajiya nana tayi rantsuwa kuma ta dage kaine zaka zuba mata kayi hakuri ka zuba"

"mata din, idan yaso sai ka kiyaye yin saurin rantsuwa a gaba"""

Ahmad ya kalli nana wacce ke kallon sa tana murmushin mugunta sannan ya kalli manaja Saddam yace

"""gaskiya yallabai ba zan iya ba. Ai ni na fara yin rantsuwa don haka ni ya kamata ayiwa uzuri ba ita ba"""

"""Kai ahmad bana son iskanci, yaya ina yi maka magana kana yi min gardama, zaka iya rasa aikinka akan"

"yarinyar nan fa. Musamman idan kaki zuba mata man nan, kaje ka zuba mata kana bata mana lokaci"""

"Gurin yayi shiru kallon ahmad kawai ake yi, gaban jazuli sai bugawa kawai yake yi, yana addu'ar ALLAH"

"ya sanya Ahmad ya hakura ya zuba mata man nan, amma sai ga Ahmad ya girgiza kai yana fadin ""gaskiya manaja ba zan iya zuba mata man nan ba"""

"""Sai dai ka bar aikinka kuwa, waye kai da har diyar Alhaji Nura Kwangila zata Sanyaka abu kace kai ba"

"zaka yi ba? Baka isa ba karya kake yi WALLAHI ka zabi daya ko ka zuba mata mai ko kuma ka bar aikinka"""

Nana taba kallonsu tana murmushin mugunta domin ta san bashi da zabi bayan ya zuba mata man.

"Ahmad ya girgiza kai ""gara na bar aikin don ALLAH ke ciyarwa ba kai ba"" manaja Saddam ya bude baki"

"yana kallon ahmad da matukar mamaki. Ita kanta nana mamaki ya bata, bata taba ganin mutum mai taurin rai kamar shi ba."

Ya juya ya nufi can gurin da ya ajiye babur dinsa da jakar kayansa. Manaja ya fara kwala masa kira yana

"fadin ""Kai Ahmad"". Amman ahmad bai waigo ba sai da ya isa ga babur dinsa ya dauko jakarsa ya cire rigar uniform ya gidan man ya sanya tashi ya cikin jaka, ya goya jakarshi a baya sannan ya kama babur dinsa ya haye kai."

Mutanen dake wajen sao binsa da kallo kawai suke yi musamman nana.

Ya isa inda suke tsaye ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo cinikin da yayi ya mikawa manaja.

"Manaja ya dube shi cikin takaici yace ""wai kai wanne irin soko ne Ahmad? Kai yanzu da ka zuba mata"

man ka gwammace ka rasa aikinka?

"Ahmad yace ""ba zuba mata man ne kawai illa a gare ni ba, zubar da mutuncina ne ba zan taba yarda bayi"

ba. Manaja zan iya yarda na rasa komai amma ba zan yarda na rasa mutuncina da darajar da ALLAH ya

"bani ta mutum dan adam ba. Na gode. Ga cinikin da nayi na wannan ranar. Yau kwanan wata ashirin idan ya cika zan zo a cire kudin kwanaki goma a bani hakkina"""

"""Kai namijin duniya! Irinku ne suka yi mana karanci a wannan zamanin. Gaskiya ka burge ni. ALLAH ya"

"sauya maka wani aikin mafi alkhairi a rayuwarsa"" wani dattijo dake gefe guda ya fada cikin karfafa masa guiwa."

"Manaja Saddam ya amshi kudin jikinsa yayi sanyi, don bai yi zaton Ahmad zai iya hakura da aikinsa ba,"

barazana ce kawai yayi masa.

Nana kam mamaki da takaici ne ya cika ta wato ita ce tayi rantsuwar banza kenan?

Ahmad ya kunna babur dinsa yana goye da jakarsa a bayansa ya nufi hanyar ficewa daga gidan man.

Jazuli da sauran mutane suka bishi da kallo cike da mamakin abinda ya aikata har ya fice daga gidan man.

"Manaja ya kalli Nana da sanyin jiki yace ""Hajiya bari na zuba miki ni"""

"""Bar shi kawai na fasa"""

"Ta juya a fusace ta nufi motarta ta shige, jama'ar wajen suna ta cece-kuce, wadanda ke kan layi suka kalli"

"manaja da takaici. ""Malam sai ka ci gaba DA zuba mana man ko?"

"Ya bi su DA kallo da bakin ciki yace ""sai dai ku yi hakuri ku sake bin wani layin"" ya bar gurin da sauri."

"""Amman dai wannan zalunci ne yaya zamu yi ta bin layi tun safe akan wata banza ace sai dai mu sake bin"

"wani..."" Wani tsageran mai adaidaita sahu ke fadin hakan. Sauran ma suka kama surutai da zage-zage."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

44

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Nana ta isa kofar gidansu a fusace tana danna horn da karfi, don ta fasa zuwa ofis din da tayi niyya yau."

"Maigadi ya tashi da sauri a gigice ya bude kofar don ya san horn din nana ne, idan har bai bude da sauri ba ranshi zai baci."

"Ta shiga gidan a fusace kamar zata bi ta kan mai gadin, yayi

37 / 47