Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 47

75K to 78K   out of 139.6K words

masa murmushi, wato tayi mafarkin dariya kenan ya maida mata martanin murmushinta ya kada kai ya fice domin dauro alwalarsa. Ya dawo dakin ya tada sallah ya jima yana godiya ga ALLAH bisa sauyin da yayi"

masa na akkhairi na ma'u ya raba shi da raliya.

*

*

*

Lamarin ALLAH kenan da kowa ya dogara gare shi zai kawo masa mafita.

DA ME AKE ADO?

25

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Umma tana kwance da tsananin damuwa, idonta yana zubda hawaye bata san shesshekar kukanta ya"

"bayyana ba Malam ya mike zaune ya kunna fitilar lantarki ya kalle ta, duk da Ta juya masa baya ya sana ba bacci take yi ba."

"Cikin raunanniyar murya ya kira sunanta ""Khadijah ki tashi nasan ba bacci kike yi ba, ki tashi ki sanar da"

"ni dalilin kukanki"""

"Tsoro da fargaba suka kama Ta ashe kukanta ya bayyana har Malam ya jiyo ta, ta shiga uku me ya dace"

tayi yanzu.

"""Nace ki tashi muyi magana khadija"" tsawarshi ta sanya ta mike zaune da sauri jikinta yana rawa domin"

ta kula ran Malam ya baci.

"Ya tsare ta da idonshi Wanda ya kada yayi jajir ""ki sanar dani abibdake ranki khadija, ki gaya min komai"

"day bakinki"" cikin rawar murya tace ""WALLAHI Malam babu komai a raina"""

"""Karya kike yi akwai wani abu aranki da deeje, mutum baya yin kuka haka kawai sai da damuwa, na"

kuma lura dake tunda na sanar dake batun auren ma'u day Ahmad yanayinki ya sauya fuskarki ta nuna

"baki ji dadin hakan ba, shin kina kyamar Ahmad don bashi da uba ne? Kece kike nuna jin haushin abinda wasu keyi masa kafin wannan lokwcin deeje"" bai barta ta bada amsa ba ya ci gaba da fadansa."

"""Idan har kika yi haka kin bani kunya kuma kin ci amanar Ahmad, Ahmad zai tabbatar da lallai ba shi da"

"uwa ba shi da galihu kowa yana kyamarsa"" ya karasa maganar da kunci da zafin zuciya."

"Ta kada kai da sauri tana fadin ""KO daya Malam WALLAHI abinda kake zato ba haka bane ba, ban taba"

"kin Ahmad ba ban taba dana sanin kasancewarsa tare da ni ba, ban taba dana sanin zamansa dana ba, haka bana jin komai game da aurensa da asma'u, kukan da kaga ina yi ba na kin aurensu bane I'll a"

"tausayinsu gabadaya. Asma'u yarinya ce karama bata iya komai ba sai wauta da tsiwa, ban koya mata"

"komai na rayuwar aure ba, na yi sakaci ban taba bata labarin meye aure ba, shi kuma Ahmad yaro ne da"

"bai san komai game da zaman aure ba, shin a yaya zai kalli ma'u day halayenta ina jin tausayin ma'u day kewarta, WALLAHI wannan shine kadai abinda ke damuna. Amman har abada ba zan taba dana sanin hada auren nan da aka yi ba, nayi mamaki ma da wannan zargin ya zo ranks"" ta karasa magana da"

tsananin damuwa.

Yayi ajiyar zuciya cike da farin ciki a ransa yana godiya ga ALLAH da ya sanya ba abinda yake zargi ne a

"ran deejen ba, ya kalle Ta yayi murmushi."

"""Amman shirmenki yayi yawa, wato har abada mace bata girma, dan wannan abin ne kawai ya saki"

"damuwa? Koda yake na sani har da soyayyar ma'u day kukan rabuwa da ita ko?"" Ya karasa maganar da zolaya."

Ta sunkuyar da kai tana murmushi kasa-kasa.

"Malam yaci gaba da jawabi ""ki kwantar da hankalinki daga Ahmad har ma'u duk rainonki ne, wata kila"

"ma Ahmad ya fiki sanin halayen ma'u, don haka babu wani abu da zai biyo baya insha ALLAHU sai alkhairi, nayi imanin zai koyar da ita komai, tunda kin koya masa KO kin manta dan naki ya iya girki kala- kala ne? Ya karasa yana dariya, abinda ya sanyata darawa ita ma ya dinga zolayarta da haka har ya samu"

ta sakko suka fahimci juna sannan suka kwanta.

*

"Tunda asuba ya tashata yin sallah, shi kuma ya fice masallaci bayan ya dawo ya zarto dakin ya zauna yw"

"ci gaba da yin lazimi, ita kam baccinta ta kara komawa, a ranta tana ganin babu abinda yafi gadonta dadi."

"Kamar wacce aka tasa karfe bakwai ta farka, ta tadda yayan nata har lokacin yana ta laziminsa, tw mike"

"tsam ta nufi kofa, ya bita da kallo kamar zai yi magana sai kuma ya fasa don yayi zaton bandaki zata."

"Ita kam kicin ta wuce tayi zaune tana sakawa da kwancewa, akan abinda ya kamata tayi domin sanda ya"

"tafi masallaci umma ta kira wayarshi ta dauka, umman tace ""yauwa daman ke din nake son ki dauka, domin nasan yanzu Ahmad yana masallaci, kina jina idan gari ya waye ki shiga kicin ki girka muku abinda"

"zaku karya, sannan ki share gidan ki goge ko'ina nasan kin iya Sahara da guga don kina yi a makaranta ko?"

"Da sauri tace ""eh na iya umma"""

"Tace ""to ki tabbatar kin yi kin ji ko"""

"Ta kuma amsawa da to, shi ne yanzu tana tsaka da bacci maganar umma ta tashe ta, ta kurawa kicin din"

"ido da mamaki, don ta kula kamar an taba amfani da wasu kaya na kicin din, to waye ya zauna a gidan kafin ita? Tayi saurin kawar da wannan tunanin domin nemowa kanta mafita."

"Hirar maryam da Jamila ta fado mata da suna yi, wata rana maryam tace ""kin san ne zan dinga yiwa"

"mijina na kari, doya da kwai da tea, ko nayi masa yamball, bazan yadda ya fita cikinsa babu nauyi ba, sai ya fita teburin mai shayi"""

"Ta mike tsam cike da farin ciki, ita ma doya da kwai zata yi masa, ai tana gani ana soyawa a bakin titi."

Ta dauko doya ta hau ferewa bayan ta kammala ta yankata gutsi-gutsi kamar zata yi faten doya sannan

ta dauko kwai guda uku ta fasa akan doya ta kunna risho ta dora mai ko zafi bai yi ba ta maka doyar da kwan ta zauna tana jiran ta soyu.

"Daga can cikin daki ya fara jiyo kauri, da sauri ya mike domin zuciyarshi tq bashi ma'u ce, ya nufi kicin din"

"da sauri sai yaga doya da kwai da mai suna ta zabalbala ya rike baki da mamaki yana fadin ""Nana me zaki yi, me kike dafawa?"

"Tayi firgigit ganin irin kallon da yake mata tace ""doya da kwai zan yi"""

"""Sai aka ce miki kuma haka ake yi, waye ya sanya ki girki bayan baki iya ba"" cikin zafin rai yake maganar."

"Tayi jwalkwal da ido tana ha da baya domin tana gudun kada ya doke Ta tace ""umma ce tace nayi"

abincin kari... Kuma...

"Ya doka mata tsawa ""get out me kika iya bayan shirme"" ya dauko kaskon suyar daga kan wuta yayi waje"

"da shi, suka ci karo a bakin kofa tana tsaye tana gunaguni, yayi baya fa sauri don saura kiris ya kifa mata, ya kuma kuluwa yace"

"""amman bakya jin magana Nana, ban Ce bar gurin nan ba? Ya fadi da tsawa, da sauri ta wuce Ta bar"

"gurin ta koma gefe ta tsaya, ya nufi gindin rariya da abincin ya zuba cikin kwando, ya sanya ruwa ya wanke kaskon sannan ya nufi kicin din tana tsaye tana kallonsa, ya dauko wata tukunya ya zuba ruwa ya dora ruwan shayi duk tana tsaye tana hangensa ta cuno baki gaba cike da takaici sai ta buga kafa ta nufi"

"kofar dakin, ta zauna a bakin kofa tana hangensa yana ta kaiwa da komowa a cikin gidan har ya kammala"

"dafa shayin ya juye a flask, ya nufi kofar gida tana ganin ya fice ta nufi kicin din don ganin abinda yayi."

"Bata hango komai ba ta fara bubbude kwanika, cikin tsautsayi bata kula da flask din da ya zuba shayin ba"

"ta bangajeshi ya fado ji kake tush. Flask ya fashe murfin ya bude shayin ya zube a tsakar kicin din, ta rike baki cike da tsoro da fargaba, sai ta kasa gaba ta kasa yin baya."

"Kamar an cillo shi ya shigo gidan, tun daga nesa ta hango ta a kicin din ya karasa da sauri yana fadin"

"""Nana me ya kawo ki kicin din nan, ban ce kada ki sake shiga ba?"

"Tayi tsuru-tsuru daidai lokacin da ya karasa, ya dauki dogon salati sanda ya ga flask fa shayin duk kwance"

"a kasa yana ambaliya, ya kalle Ta ya ma rasa abinda zai yi."

"Cikin rawar murya tace ALLAH yaya ban gani ba, ban san da flask a gurin ba"""

"Yayi ajiyar zuciya yayi kokarin hadiye fishinshi, domin ma'u yar fatan gaban goshinsa ce, duk da dan"

"banzan rawar kanta. Ya nuna mata kofa yace ""zo ki wuce daki maza"" ta taho tana rakube-rakube tana goge ido tana gudun kada ya doke ta har ta isa bakin kofa, data Samu ta fice sai ta falla da gudu sai da ta dire a cikin daki sannan ta tsaya tana haki da dariya. ""Wai ALLAH na gode maka, da yaya Ahmad ya mini"

"irin rankwashinsa ai da naga ta kaina"""

*

*

*

A gai da ma'u amarya

DA ME AKE ADO?

26

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Shi kam Ahmad kada kai yayi da takaici sannan ya shiga ya share kicin din ya kara dora wani shayin, ya"

"zuzzuba a kofi ya kai mata nata har daki, ta amsa tana fadin ""na gode yaya"" ya daga mata kai kawai sannan ya zauna ya fara shan nasa, ma'u ta dube shi yana shan shayin tace ""yaya don Allah yaushe zan"

"koma makaranta? Kaga ranar Monday za a fara jarrabawa kuma Abba yace sai ka yarda zan koma"""

"Ya daga kai ya kalleta sai yaga iyakacin gaskiyarta take maganar, babu wani bayani da zai yi ya gamsar da"

ita. Don haka yace ai ba zaki yi wannan jarrabawar ba ki hakura kawai.

"Ta waro ido waje cike da fargaba ""yaya kana nufin na daina karatu kenan, kaine fa kace zan zama likita"""

"Ya jijjiga kai da damuwa ma'u tayi kankanta da aure, tayi kadan da fuskantar irin wadannan matsaloli"

don haka gara ya sanar da ita gaskiyar komai.

"Ya dube tada nutsuwa yace ""Nana kin san yanzu ke matar aure ce ko?"" Ta daga kai alamar eh, ya gyara"

"zama ""yauwa kinga ai makarantarku ta yan mata ce babu matan aure ko?"" Ta kuma daga kai alamar eh."

"""To wannan dalilin ne ya sanya ba zaki kara komawa ba, kin kammala wannan makarantar kenan yanzu"

"zaki zauna zaman aurenki, ki nemi aljannarki kuma..."

"Ta mike a tsorace cike da faduwar gaba ""ya zaka ce haka yaya Ahmad, shikenan ni yanzu ba zan dinga"

"zuwa ko ina ba sai nan gidan kuma ba zan zama likita ba, yaya baka yin karya amma yanzu kayi me ya sa?"""

"Tambayar tata ta caza masa kwakwalwa har ya rasa amsar da zai bata, sai ya sake hade ransa yace ""kin"

"cika ni da surutu Nana, tashi maza ki yi wanka ki share gidan ki wanke kwanika"" tayi narai-narai da ido,"

"domin tana matukar son karatunta tace ""Amman yaya..."" Ya daka mata tsawa ""I said get out ma'u"""

"jikinta ya dauki rawa hawayen da ya makale a idonta ya fara gangarowa, ta fice da sauri tana goge idonta."

"Tana aiki tana kuka, yana juyo sautin kukan nata amma bashi da zabi babu yanda zai yi, Abba ya gama"

"yanke hukunci daga karshe ma sai yayi wanka ya fice ya bar gidan. Wannan abin shine abinda ya kara daga mata hankali, sai taji gidan yayi mata girmata zauna tsuru babu abin yi, sai tsoro ya fara shigarta, ta mike ta nufi soro ta kama leken waje tana hango mutanen dake kaiwa da komowa, sai taji sanyi a ranta, don haka sai ta zauna a kofar gidan tana kalle-kallenta da karamin hijab a kanta, idan taga abin dariya tayi idan taga abin mamaki tayi, mutane suna wuceta suna kallonta, babu Wanda yayi zaton matar gidan ce, domin ko makota basu san an kawo amarya ba, sun yi zaton raliya ce ita kuwa daga yanayin kawayenta da gantalin da take fita kullum ya sanya suka gano ba matar arziki bace don haka babu wani"

wanda ya rabeta.

"Tsahon lokaci tana nan zaune tana cike da nishadi, shi kam Ahmad gidansu ya wuce kai tsaye, ya tadda"

"yan uwansa sun zo dayake asabar din kashen sati ce, Ana ta cafta, sai ya zauna Ana yi da shi. Umma sai shige da fice take tayi gurin ganin ta kammala girkin rana, kunya da nauyi sun hana ta tambayar ma'u, ta kula shi na Ahmad din kunyar yi mata maganar ma'un yake yi, amma daga yanayinsa ta lura babu wata"

matsala.

"Anan suka zauna suka ci abinci, lokacin da Umma ta zubo abincin ne ma ya tuna da ma'u da abinda Zata"

"ci, saidai ALLAH ya tai make shi Umma ta cika flask da dambun da tayi ta dire a kusa da shi tace gaba 'yar gidanka Ahmad. Allah yaji dadin hakan don haka yana kammala cin abincin ya dauki flask ya hau babur"

dinsa ya nufi gida. Da yake aikin yamma yake da shi a gidan man nasu.

"Abinda ya bashi mamaki da tsoro bai wuce hango ma'unshi zaune a kofar gida daram ba, tana ta hira da"

"wasu yara da alama 'ya'yan makota ta samu Ta biye musaurenYana cigaba da karatowa mamakinsa na kara linkuwa har zuwa sanda ya iso inda take da babur dinsa, ta daga kai ta kalle shi sai ta dan firgita, musamman ganin yadda yanayinsa ya sauya lokaci guda, ta kalli yaran dake gabanta tayi duru-duru sai ta mike Ta shige cikin gidan da gudu, bata yi birki a ko ina ba sai a bayan gado tana huci, ta labe can kurya tana maida numfashi, ya shiga gidan ransa yana suya, ya iso har bayan gadon ya danko kunnenta, ta fasa"

ihu jikinta na cigaba da bari.

"""Don ALLAH yaya Ahmad kayi hakuri"""

"""Uban wa yace ki fita waje ki zauna, ko mun koya miki wannan tarbiyyar a gida ne?"

"Cikin shisshikar kuka tace ""a'a gidan ne shiru ga tsoro shi ne na leka waje don ALLAH kayi hakuri"" ta"

fashe da kuka.

"Ya dunkule hannunsa ya rankwasheta yana fadin ""koda zan hakura sai kin ji a jikinki, ki fita kofar gida ki"

"zauna kamar wata sokuwa, ina kika kai auren naki?"" Ya kuma rankwasa mata rankwashi kwas a kanta ta gantsare ta kuma sanya ihu, sai da ya jera mata guda 4 sannan ya sakar mata kunne."

"Ta kara fashewa da kuka tana rike da kunnuwanta lokacin da ya fice daga dakin, ya nufi shago domin ya"

"sanya uniform dinshi ya tafi gurin aiki, saidai yana shirin kukan ma'u yana dukan zuciyarsa, tun can baya ba ya son bacin ranta, yakan yi komai don kada a bata mata rai, balle kuma da yaji sunan mahaifiyarsa ne aka sanya mata, hakan ya kara soyayyarta a cikin ransa, yanzu kuma ga shi ta zama matarsa, wato soyayyarta agare shi yanzu hawa 3 ce, don haka dole idan tana kuka ya dinga ji har ikin bargonsa, dakyar ya iya kammala shirinsa ya nufi soro da zummar ya fice sai kuma yaga rashin dacewar hakan, don haka"

ya juya cikin gidan ya nufi dakinta.

"Tana rakube a inda ya barta a bayan gado tana kuka, ya isa inda take ta hada kai da gwiwa tana ta"

"sharbe, ya yarfe hannuwa da damuwa ya kira sunanta. Ta dago ta kalleshi da faduwar gaba don bata san"

"ya dawo dakin ba, tayi zaton kara dukanta zai yi, don haka ta fara ha da baya, tana sharbe majinarta tana kuka. ""Don ALLAH kayi hakuri WALLAHI ba zan Kara fita ba na daina*"

"Ya kada kai yana kare mata kalli, da Abba yayi shawara da shi da zaice abar ma'u ta kammala karatunta"

"ta zama cikakkiyar mace kafin ayi mata wannan auren, yarinya ce tsana, yanzu ta fara kirgen dangi irin na mata, babu wani Abu da zai nuna ta cika mace dayake bata da girman jiki, bai kallonta da komai har yanzu sai kanwarsa 'yar uwarsa. Ihunta ya dawo da shi hayyacinsa yace ""kinga ba dukanki zan yi ba,"

"cewa zan yi ki daina fita waje, idan na fita zan turo miki yaran su dinga taya ki hira kin ji ko?"

"Ta gyada kai da gamsuwa tana cewa ""to"" tuni kukan nata ya koma ciki ta fara kokarin dariya abin yaso"

"bashi dariya, sai ya tuno da maganar yara da kance me kuka yana dariya ai mata dan kwadon daddawa, ya zura hannu cikin aljihunsa ya zaro dari ya mika mata. ""Ga wannan idan kina son cin wani abu ki siya,"

"ga kuma abinci can a flask Umma tace a kawo miki"""

"Ta amsa da hannu biyu tana godiya, ya nufi kofa har ya kai ya juya ya kalleta ""kada ki kara fita waje ki"

"zauna a gida kin ji ko ma'u"" ta daga kai ""ALLAH ba zan kara fita ba, in dai ka turo min yaran..."""

"""Au idan ban turo su ba sai kin fita kenan? Ya katse ta da mamaki. Da sauri tace ""a'a WALLAHI ba zan fita"

"ba sai dai na tsaya a soro"" yayi murmushi ba a rabu da bukar ba an haifi habu, ya kada kai ya fice, ta bishi da sai ka dawo yaya, kamar yanda ta saba yi masa a gida. Ya amsa da ALLAH ya sanya ya fice"

"Ta kalli darin nan ta daka tsalle cike da murna, wai yau ita ce day dari, duk wannan tata ce lallai ALLAH ya"

sanya yaran su shigo su siyo mata agwalima.

"Yayi sa'a kuwa 'yan yaran da ya tadda a zaune da su har lokacin suna zaune suna wasansu, don haka"

"yace maza suje su taya ta hira, da hanzari suka shige cikin gidan suna murna."

"Sallamarsu ta tsinkayo a tsakar gida tayi waje da guru cike da murna, sai a lokacin ta hango flask din"

"abincin ta shiga kicin tw dauki faranti ta debi nata suma ta zuba musu nasu, suka zauna suna ci suna hira tana kwasar dariya."

*

*

*

Duniya ta yi dadi kenan Hajiya ma'u

DA ME AKE ADO?

27

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Tun daga wannan rana gidan nata ya zama gidan yara, domin ance laifin yaro kiyuwa laifin babba rowa,"

"Asma'u kam hannunta a sake yake akwaita da kyauta. Ahmad hankalinsa ya kwanta shi ke hada musu abincin da zasu ci safe da rana da dare, sai dai idan ya san yana da aikin safe tun asuba zai dora girkin rana ya zuba a flask ya ajiye nata. Da dare kuma ya zo mata da (take away) abincin tafi da gidanka."

"Domin yace bata yi wayon da zata iya girki har ta kunna rusho ba, aikinta kawai

26 / 47