Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 47

126K to 129K   out of 139.6K words

abubuwa marasa kyau ita da mahaifiyarta garemu, amman hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, don kwanansu biyu babu abinci, sauran 'yan hayar gidan daman basa shiri sam da ita kishiyar sun hade mata"

"kai, don haka dole tayo nan."

Kai baka ji zance ba sai kace ta samu tabin hankali. Kai! Talauci bai yi ba a duniya. Haka haka na harhada

"mata kayan abinci har da kayan sawa da na yara ta dinga kuka tana godiya. Duniya kenan"""

"Ahmad ya gyda kai ""kadan ma suka gani, duk wanda ba zai iya kallon ikon ALLAH yayi shiru ba sai ya tofa"

"tashi ko yayi kazafi akai ba ai yana da jin haushi da bakin ciki in dai a wannan duniyar ne"""

"Suna ta cin abinci yana tunanin ta inda ya kamata ya bullo mata da abunda ke ransa, can ya daure yace"

"""wai ya naji ki shiru ne an yi watanni da yaye malam fa?"

"Ta dafe kirji ""don ALLAH Yaya kada ka ja min, ina zaman zamana ALLAH ne yace na huta Ka bar ni kawai"""

"Yayi yake ""haka ne, idan kin gaji ba sai na kawo miki kanwa tayi ba"""

Ta kalle shi da sauri da mamakin jin abunda yace amma ta kasa furta komai sai kada kai da yake kawai.

"Ganin haka ya sanya yace ""Nana yanzu ace ga wata mace tana neman rasa rayuwarta ni da kaunata har"

"ta dinga shiga cikin mawuyacin hali na jinya, zaki iya yarda na aureta?"

"Gabanta ya kuma faduwa duk da tasan wasa yake yi tace ""wata kila zan iya wata kila kuma ba san iya ba"""

"Dadi ya cika shi jin ta dan sauko har tana murmushi yace ""wani abu ne ke faruwa mai ban mamaki ma'u,"

"wai kamar ni Alhaji Nura Kwangila ke roko har da durkusawa kamar zai yi kuka, Kodayake yana da gaskiya"""

"""Akan me yake rokonka kuma? Ta fadi da fargabar jin abunda zai fada."

Ya kalleta ganin har lokacin babu wani tashin hankali ko bacin rai akan fuskarta ya sanya ya cigaba da

"magana ""ba zan boye miki komai ba ma'u, Nana ta nuna tana sona naki bata fuska har ta gaji ta sanar da ni da bakinta"""

"Ma'u tayi mutuwar zaune akan kujera, sai taji kamar ya faskara mata gatari ne a tsakiyar kanta, ta kasa"

motsawa. Ganin bata ce komai ba Ahmad ya cigaba da magana.

"""Ban boye mata ba na gaya mata gaskiya bana sonta, hasalima ba zan iya hada matata da kowacce mace"

"ba, ba zan iya yi mata kishiya ba, rannan da bacin rai ta bar ofis dina, Ashe wai har faduwa tayi a gida, bayan an yi bincike aka gano tana dauke da ciwon zuciya da ya kamata cikin dan lokaci."

Bayan mahaifanta sun gano dalilin faruwar hakan suka ritsa ni da magiya kamar zai mini kuka akan na

"auri diyarsa na rasa me zance masa tunda na gaya masa gaskiya bana son diyarshi, daga karshe nace ya bari nayi shawara da iyalina tukunna"""

Har ya kammala bayaninsa ma'u tana jinsa kamar cikin gajimare yake yi mata ihu cikin kunnuwanta. Ta

"daina fahimtar komai, bugun zuciyarta ya sauya abunda ta jima tana zargi ya tabbata kenan ta kuma tabbatar Ahmad karya ya shirya mata yanzu don ya samu damar auren Nana, don haka sai tayi"

murmushi cikin ranta tana fadin zaka iya rubuta littafin hikaya lallai. Amman a fili cewa tayi.

"""Amman bai kamata ka bar Nana ta rasa rayuwarta ba bayan dumbin alkhairin da ta aikata maka ba"""

"Tana gama fadin hakan ya mike ya bita da kallo baki bude ya gaza gano inda zancenta ya dosa, shin da"

gaske take yi ko kuma gatse take yi masa? Ya kamata ya ji cikakken bayani daga gare ta.

Taku uku ma'u tayi a na hudun juwa ta kwasheta ta yanke jiki ta fadi tim! Ahmad ya tashi da gudu a

"gigice ya nufe ta yana kurma salati, ya tallafota yana jijjigata gami da kiran sunanta amman ma'u ta suma."

Ya mike da sauri ya samo ruwa ya kamota ya tallafota ya zuba mata a fuskarta ta bude idonta da sauri

"tana ganinta rike shi a jikinshi ta fashe da kuka ta fara kokarin kwacewa daga jikinsa amman ta kasa domin jikinta ya mutu lubus. Cikin kuka take fadin ""me ya sanya baka bar ni na mutu ba Ahmad?"

Mamaki ya Kama shi har ya kasa boyewa ya waro ido yau shi ma'u take kira da Ahmad kai tsaye abunda

bata taba fadi ba tsawon rayuwarta.

"A fili yace ""Ahmad fa kika ce ma'u?"

"Ta yunkura ta mike dakyar tana kuka ""na fada me kuma ya rage tsakanina da kai tunda ka zama"

"mayaudari azzalumi. Ni zaka yaudara, ni zaka cuta bayan ka tauye min rayuwa kaje kuma yanzu kace zaka auro diyar masu kudi da ilimi ban son kara ganin fuskar macuci irinka."""

"Jiwa ta kara dibanta tayi tagal-tagal zata fadi ya mika hannunsa zai tare ta yana fadin ""kiyi hakuri ki"

"zauna ma'u, ki bari nutsuwarki ta dawo tukunna"""

Ta kubce daga rikon da ya so yi mata ta fada kujera ta zauna ta dafe kanta dake juyawa kamar zai fado.

"Ahmad ya matso kusa da ita zai kamo hannunta ta hankade hannuwan nasa tana fadin ""don ALLAH ka"

"bar ni, ka kyale ni na mutu mana, sai kaji dadin aurarta kayi abunda ka ga dama, na san ni ba diyar kowa bace illa wadda aka lika maka dole wata rana zan ga fiye da haka ma"""

Dakyar take magana tana fidda wani irin numfashi.

"Gaba daya hankakinsa ya tashi cikin lallashi yake fadin ""don ALLAH kiyi shiru, ki daina magana ma'u, ki"

"kwantar da hankalinka, WALLAHI ba zan yi abunda ba kya so ba. Bari muje asibiti bugun kirjinki ya sauya"""

"Gaba daya ya rude ya rasa me zai yi, ya mike da sauri ya fara neman makullin motarsa ya nufi dakin"

baccinsu.

Ma'u ta mike dakyar tana jin jiwa ta nufi wani dakin da suke ajiye shirgi ta shiga ta rufo kanta da sakata

"ta matsa can wani sako ta nade kai da gwiwa tana kuka, kirjinta yana zogi tana jin kamar zuciyarta zata faso ta fito waje, da ace idan ta mutu ba za a tambaye ta dalilin da ya sanya ta kashe kanta ba, da ta"

rataye wuyanta ta huta da wannan bakin cikin.

"Ahmad ya samo mukulli cikin daki ya fito, sam ya manta da yaransu dake cikin dakin suna bacci. Sai dai"

"me bai ga kowa a falin ba, hankalinsa ya tashi kwarai da gaske ya fara nemanta a gigice."

"""Ma'u! Ma'u! Ina kina shiga?"

Daga can cikin dakin shirgin ya jiyo numfashinta na fita dakyar. Ya nufi kofar dakin ya leka ta windo

"duhun dake dakin ba zai bashi damar ganinta ba, sai dai yana jiyo numfashinta na fita kadan-kadan."

"A rude ya kira sunanta ""Ma'u! Don ALLAH ki bude kofar nan kada ki cutar da kanki fa, na gaya miki na"

"fasa ki bude don ALLAH"""

Bata kula shi ba sai dafe kirjinta da tayi wanda ke wani irin bugu kamar zuciyarta zata faso ta fito.

"Ahmad ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa, sai ya fara kokarin dude kofar da karfi amman yaji ta kam, ya"

"fara kokarin fasa ta ya kasa, amman hankalinsa ba zai kwanta ba sai can ya koma ya dauko wani katon karfe kamar diga ya fara dukan gefen kofar dakin."

"Duk kwarin kofar nan sai da ya ballata don hankalinsa a tashe yake, musamman da ya daina jiyo"

"numfashin ma'u, a zatonsa ko kashe kanta tayi."

"Ya banko dakin a rude ya fara laluben inda take, can ya samo ta kwance male-male, bai yi wata-wata ba"

ya kwashe ta don ya gano suma ta kara yi.

Kai tsaye dakin baccinsu ya wuce da ita ya kwantar da ita ya kara dauko ruwa ya yayyafa mata yana kiran

sunan ALLAH.

Zafi da duh un dakin nan kansa azaba ce.

"A hankali ma'u ta bude idonta, tana yin ido hudu da shi ta kau da kanta gefe hawaye na zubowa daga"

idonta don jikinta yayi lakwas. Ba zata iya yin komai ba.

"Ya durkusa a gabanta idonsa ya ciko da kwalla kamar zai fashe da kuka yace ""ma'u don ALLAH ki taimaka"

"ki rufa min asiri, idan na rasa ki ina zan tsoma rayuwata, na miki alkawari na bar maganar Nana daga yau"

"ma na bar kamfaninsu da gidansu, ba zan aureta ba koda zata mutu, ALLAH ya gani ba zan yarda na rasa ki ba, ki hakuri ma'u ki yafe ni"""

Yanda ya gigice yake sambatu ya dan sanyaya zuciyarta har ya bata tausayi tayi shiru amman fuskarta ta

"nuna ta dan sauko, wannan ya sanya yaji dadi yace ""na kawo miki fresh milk ki sha?"

"Ta dage kai alamar eh, ya mike da sauri ya dauko mata ya tallafota ya dinga bata tana sha har sai da ta"

"shanye, sai ga idanuwanta sun dan fara dawowa daidai, ya kara daukarta cak kamar wata 'yar baby ya nufi bandaki da ita ya hada musu ruwan wanka cikin baho suka shiga mai dumi."

"Haka ya rinka tattalinta har sai da ya tabbatar ta dan huce, a kirjinsa tayi bacci."

"A daren ma shine ya kula da yaransu, duk wanda yace ruwa ko fitsari shine yake kai su."

Fatanshi dai ma'unshi ta samu.

***

"Da safe ya makara zuwa aiiki, sai wajen karfe goma na safe ya fita saboda sai da ya tabbatar matarshi ta"

samu nutsuwar zuciya da ta zahiri.

Fitar tashi ma kiran Alhaji Nura Kwangila ne ya ishe shi. Ma'u tace yaje kawai ta warware. Dakyar ya

samu ya fita yana tunanin halin da zata shiga.

Sai dai yana fita ta kara komawa daki ta haye gado ta dinga kuka don tana jin kamar ta rasa mijinta ne

kawai.

"Malam da bai zuwa makaranta shi ya haye kanta yana mata gwaranci da surutu, sai ta rungume shi"

kawai tana kuka don bata san me zata gaya masa ba.

***

A can ofis aiki ya san Ahmad a gaba amman a ranshi yana jin kamar aikin karshe yake yi don babu

"makawa dole zai bar ofis dinshi. ALLAH dai ya sanya yana dan adana kudi a cikin account dinsa, zai Iya kama hayar gida kafin Musa ya samu damar tashi daga nashi har ya nemi Sana'ar yi ma, lokaci yayi da ya"

kamata ya samu gashin kansa ma yanzu.

Yana ta sakawa da warwarewa yaji an kwankwasa ofis dinsa Alhaji Nura Kwangila ne ya turo kofar ya

"shigo, Ahmad ya mike tsaye da sauri don girmamawa, Amma Alhaji Nura Kwangila ya Mika masa hannu da alamar ya samu guri ya zauna, babu musu ya samu guri ya zauna jikinsa a wannan karon har rawa"

yake don fargaba.

"Alhaji Nura Kwangila ya kalle shi yace""Ahmad jiya Nana bata yi bacci ba, don ban gaya mata yadda muka"

"yi ba, nayi mata karya abunda ban taba yi mata ba tsawon rayuwata, nace mata kace ka amince zaka aureta, wannan dadin ya sanya ta kasa bacci har likita ya ba da tabbacin zuwa yanzu jininta ya sauka, ina"

"fatan zaka taimaka min ka fitar da ni daga karyar da nayiwa diyata"""

"Ahmad yayi shiru da damuwa yana kada kai, sannan yace ""kayi hakuri kamar yadda baka son rasa"

"diyarka haka bana son na rasa matata, halin da Nana ta shiga kadan ne akan Wanda matata ta shiga. matata da iyayenta sun min abunda ba zan iya saka musu ba, ba zan iya biyansu ba, ba kuma zan so rayuwar diyarsu ta halaka ba saboda ni. Kayi hakuri Alhaji kamar yanda na fada naka ba zan iya hada rayuwar ma'u da ta kowa ba har yanzu ina kan haka, na san mutane da yawa zasu ga wautata domin dole zan rabu da aikina da gidana da motata, amman WALLAHI hakan yafi min kwanciyar hankali don ba zan yarda na rasa ma'u ba, ba zan iya yiwa iyayena butulci ba, ka baiwa Nana hakuri ka sanar da ita ba zan manta da ita ba, ba zan manta da taimakon da tayi min ba, ka dan bani lokaci ko zuwa gobe ne zan"

"hada kayana duk na ofis dinka"""

"Jikin Alhaji Nura Kwangila ya mutu lakwas, hankalinsa ya tashi, ya kada kai da damuwa yace ""Ahmad ka ji"

"nace na sallameka aiki ne? Kada ka dauke ni karamin mutum, kin auren Nana bai da alaka da aikinka, sai dai ka sani idan na rasa Nana ta sanadiyyar sonka ba zan yafe maka ba har abada"""

Ya mike a fusace ya fita daga ofis din.

"Ahmad ya koma ya jingina jikin kujera, maganganun Alhaji Nura Kwangila na dawo masa. Shin da gaske"

ne Nana zata iya rasa ransa saboda shi?

"To wai rayuwar wacece tafi daraja a gurinshi tsakanin Nana da Ma'u, ban da Ummi dake can gefe tana"

hauka kamar ita ma zata mutu akan sonshi?

"Kai dole ma'u ta fi su muhimmanci a gurinshi, ita ce matarshi uwar 'ya'yanshi, 'yar uwarshi, diyar"

ummanshi.

"Da wannan tunanin ya karasa yininsa. Da ya koma gida bai tayarwa da Ma'u zancen ba, ita ma kuma bata"

"tayar masa ba, kowa ya ja bakinsa yayi shiru."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

52

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"A bangaren Nana ta dan samu sauki har an sallameta, sai dai tana mamakin rashin zuwan Ahmad gareta"

indai har da gaske ya amincewa aurenta amman dai ta bar abun cikin ranta tana son kuma ta Kira shi a waya amman tana tsoron yanda zai amsheta ko kuma kada ta Kira yana tare da Ma'un tashi ta bata

masa rai.

***

Kwanaki suka dinga tafiya kowa abunda ke damunsa ransa na ci gaba da girma.

***

"Ga Ahmad da matarsa ma'u sun kwantar da hankalinsu, domin yace mata yana tsumayin takardar"

"sallama ne, sannan zai fara nema musu gidan haya, sai ya sanar da Musa ya bashi ko Shekara daya ne ya samu inda zai koma shima."

"Wannan labarin ya mata dadi a zahiri, amman a badini tana damuwar irin sana'ar da mijinta kuma zai yi"

"a nan gaba, tana tsoron kada su koma cikin matsala, musamman yanda yake taimakonta da iyayenta da 'ya'yanta, tana son ta saduda amma kuma kishi ya hana ta yin hakan."

***

"Ga Alhaji Nura Kwangila ya rasa me ya dace yayi, dukkan al'amuransa sun tsaya cak, yana son zuwa yaga"

"yayansa da mahaifiyarsa ma amma abun ya faskara don dama duk bayan watanni shidda yake zuwa gashi lokaci yayi yana fargaba, babu Wanda ya san abun da yake ransa sai shi daya."

"Daga karshe dai mai dakinshi ta tare shi a daki don jin gaskiyar abun dake faruwa, bai boye mata duk"

yanda suka yi da Ahmad ba.

"Ita ma ta shiga tsananin damuwa da tsorata har ta rasa abun cewa, don ta san idan Nana taji wannan"

labari komai zai iya faruwa.

"Alhaji Nura Kwangila ya kurawa Hajiya Batula ido yana fadin ""wannan shine halin da nake ciki, ban iya"

"bin malaman tsubbu ba balle nace zan bi su dawo min da hankalin yaron nan kan Nana ba, sannan ba zan iya siyan shi da dumbin dukiyata ba, yaya zan yi yanzu?"

"Tayi shiru tana kada kai sannan tace ""shi Ahmad din bai da iyaye ne?"

"Ya kalle ta da sauri sannan yace ""abunda ban sani ba kenan, amman ina zaton iyayensa suna nan da"

"ransu don na taba jin yana maganarsu tun lokacin da ya taba zuwa lagos sai dai ban sani ba ko suna raye yanzu"""

"Hajiya Batula ta kada kai ""ALLAH yasa suna raye, idan har suna raye su ya kamata ka samu, ka fara kallon"

"yanda suke da irin halinsu, idan kaga za a iya siyan su da kudi a shirye muke mu mallaka musu dukkan abunda muka mallaka, idan kuma kudin bai da daraja a gurinsu kamar dai shi Ahmad din sai ka sanar da"

"su gaskiyar komai da halin da diyarmu take ciki, na san zasu tausaya mata"""

"Yaji dadi har ya bayyana akan fuskarsa yace ""wannan tabbas shine abun yi, insha ALLAHU zamu samu"

"nasara ta nan"""

***

Sau uku ana sanar da shi ana zuwa nemansa da wani mutum a cikin hadaddiyar mota amman bai kawo

komai a ransa ba.

Yau yana zaune kan tabarmar kofar gidan da yake Juma'a ce ya dawo daga aiki da wuri daga masallacin

Juma'a ya taho gida.

Mota hadaddiya ta tsaya a kofar gidanshi daga can nesa direba ya bude da sauri ya zagaya ya budewa

Alhaji Nura Kwangila.

"Daga inda Malam Sulaiman yake zaune yana hangen motar yana tunanin ko gurin wa tazo cikin layin,"

don bai taba ganin mota mai kyan irin wannan ba.

"Sai dai ga mamakinsa sai yaga kai tsaye gurinsa mutumin da aka budewa kofar motar yake nufowa, har"

ya iso inda yake yayi masa sallama. Malam Sulaiman ya mike da sauri yana amsa masa sallamar ya ba shi hannu suka gaisa.

"Alhaji Nura Kwangila yace ""don ALLAH ko kai ne Malam Sulaiman mahaifin Ahmad?"

"Cikin sauri yace ""zahiri nine lafiya dai ko?"

"Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yace ""lafiya kalau sai alheri, mu zauna nayi maka bayani idan da"

"hali"""

"Suka koma suka zauna, bayan sun kara gaisawa Alhaji Nura Kwangila ya fara yi masa bayani abun dake"

"tafe da shi tun daga farko har karshe, ya kare zancen nasa da roko kamar zai fashe da kuka."

"Malam Sulaiman yayi yake yace ""wato yaran zamani basu da dama, ban da shiririta ko dumbin halaccin"

"da aka yi masa ba zai kalla ba, kishin banza kuma na matarshi shi da ALLAH ya hore masa ikon auren"

"mace hudu zai zauna yana wannan shirmen? Ka kwantar da hankalinka insha ALLAHU kamar anyi an gama wannan auren"""

"Alhaji Nura Kwangila yaji dadin wannan maganar, wato bai nuna kudi ko wani abu don ya samu abun da"

"yake so ba, lallai ya yarda ya samu surukai da mijin diya nagari Wanda ko bayan ranshi zasu rike dukiyar diyarshi da ita kanta da daraja don haka ya dinga godiya."

Can Malam Sulaiman yayi shiru da damuwa a fuskarsa.

"Alhaji Nura Kwangila yace ""lafiya dai ko Malam?"" Malam Sulaiman ya gyara zama yace ""eh to akwai"

"wani hanzari ba dugu ba, ban sani ba ko idan kaji zaka yarda diyarka ta auri Ahmad, bana so sai abu yayi nisa irin abunda ya faru a neman aurensa na farko ya kuma faruwa, duk da ba shine ya nemi auren ba, a yanzu abunda zai biyo baya zai iya yi masa ciwo har ya fama masa mikin dake ranshi da ya jima da"

"narkewa"""

"Alhaji Nura Kwangila ya kalle shi da rashin fahimta, amman bai yi magana ba ganin kamar Malam"

Sulaiman din bai gama bayani ba.

"Malam yayi dan Jim, yanayinsa ya sauya zuwa damuwa gaba daya dakyar ya daure ya cigaba da magana"

"""Kamar yadda aka fada maka nine mahaifin Ahmad haka ne, amma ba wanda ya kawo shi duniya ba"""

"""Mahaifinsa rasuwa yayi kenan? Alhaji Nura Kwangila ya tambaya da sauri."

"Malam Sulaiman ya girgiza kai gami da fadin ""ko daya har zuwa wannan lokaci ba

43 / 47