Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 47

72K to 75K   out of 139.6K words

tana ina?

"ta mike da sauri jikinta yana rawa, tayi zaton wani laifi tayi ko kuma dealing din ne ya motsa na senior"

"hajar, idan akwai abinda ta tsana bai wuce wankin senior hajar ba, domin shegiyar kazama ce kayanta"

"har wani tsami suke yi, da haka ta wuce kanta daga kalbar da maryam keyi mata ta nufi gurin senior hajar tana fadin 'senior hajar gani'"

senior hajar ta kalleta sama da kasa tace 'da alama yarinya uwarki ko ubanki sun mutu domin sit abdul

yace kije ki tafi da dukkan kayanki domin gidanku zaki wuce'

ma'u ta dafe kai cike da fargaba sai ta fashe da kuka tana fadin 'wayyo na shiga uku ALLAH ya sanya ba

"umma ko abba bane suka mutu. wayyo ALLAH.ni ma'u na zama marainiya' ihu take yi iyakacin karfinta, gaba daya hostel din aka yi shiru ana kallonta, kawayenta tuni sun iso inda take suna tambayarta me ya"

faru.

senior hajar ta kama masifa 'ke sakarya ni bance miki wani naki ya rasu ba. cewa nayi kawai ina jin sai ki

hado kayanki mu wuce. ku sai ku tayata debo kayan nata' ta kalli sauran kawayen nata. da sauri ma'u ta nufi gurin kayanta taci gaba da hadawa tana kuka sosai. kawayenta suna rarrashinta.

sanda suka isa gurin sir abdul ya kalle ta da mamaki yace 'ma'u meye ya sanya ki kuka haka? cikin

"shessheka tace 'senior hajar ce tace wai babana ko ummata sun mutu' ya bata rai matuka yace 'in ni uban wa, hajar tana da matsala kawai nace mata tace ki hado kayanki kizo babanki zai tafi dake, shine"

zata ce haka. barta kawai karya take yi'

hankalin ma'u ya kwanta saidai tana cike da tsananin mamakin abinda zai sanya babanta yazo daukarta

"bayan an fara jarrabawa, bikin yayanta kuma an kammala tuni. domin a lissafinta yau dati biyu da bikin yayanta ko kuma dagawa aka yi ne? da wannan tunanin tayi sallama da kawayenta sir abdul ya daukar mata wasu kayan, su maryam da jamila zuna bata sakon abinda zata ziyo musu idan zata dawo tana cewa to, bata san wannan ce rana ta karshe da zata kara komawa wannan makaranta ba da sunan"

karatu ba: yau ne ranar da zata rabu da kawayenta rabuwa ta har abada kuwa.

"ta isa ta tadda abbanta zaune a ofis din principal suna wasu maganganu da bata fahimci komai ba,"

"hankalinta ya dan kwanta saboda ganin abbanta ba kuma cikin wata damuwa ba. ta durkusa ta gaishe da abbanta sannan ta gaida princilal, abbanta ya mike yana fadin 'to hajiya na gode ALLAH ya taimaka ya kuma kara daukaka'"

"principal ta mike tana fadin 'amin amma mun yi missing daliba mai kwazo da hazaka, UBANGIJI ya"

"tsareta a duk inda take' malam yace amin da sauri, principal ta daga kan ma'u tana fadin 'to ma'u ALLAH ya kaddara saduwarmu ki dage bisa kyawawan halayen da na sanki kin ji ko?"

"ita dai ma'u to kawai tace bata san me ake nufi ba, abbanta ya daukar mata wasu daga cikin kayanta ta"

"dauki sauran suka nufi titi, zuciyar yana wasi.wasin abinda ya faru, a kalaman da principal take yi mata sun yi kama da maganganu irin na bankwana, amman ta wanne dalili za a yi bankwana da ita. ko makaranta abban nata zai sake mata ne? gashi ba zata iya tambayarsa ba, illa binsa kawai da take yi"

zugui-zugui kamar jela har suka isa inda ake hawa mota suka hau.

abin mamaki daga jikin wayar bangaren ajujuwan karatu ta hango su maryam na daga ma hannu ta

dinga daga musu hannu itama idonta ya cika da kwalla.

"sanda suka isa gida ana ta kiraye kirayen sallar magriba, umma tana kicin tana kokarin hura wuta da"

"alama tayi daren tuwo ne, ta jiyo sallamarsu ta mike da mamaki tana fadin 'malam kamar muryar ma'u nake ji...' mamakin ya kuma karuwa har ya sanya ta kasa karasa maganar. ma'un dai biye da abbanta ya kalli ma'u yace 'ba kama bace deeje ita ce, yanzu na dauko ta daga makarantarsu'"

"mamaki ya kuma cikata tace 'malam amma ban ji labarin anyi hutu ba, naji kamar jarrabawa suke yi ma,"

lafiya'

ya nufi kofar bandaki ya dauki wata buta da aka ajiye cike da ruwa yana magana 'lafiya kalau ki dai kira

"mini dukkan yaran gidan nan a waya, kice ina son ganinsu, idan na dawo daga masallaci zaki ji karin bayani' ya shige cikin bandakin don kama ruwa."

umma ta maida kallonta ga ma'u kamar zata sake tambayarta sai kuma ta fasa tace 'shiga da kayan cikin

daki kizo ki daura alwala' ma'u tayi abinda mahaifiyarta ta umarceta bayan ta cire unifom din dake jikinta ta sake kaya ta fito ta daura alwala.

"ita kam umma kokarin fara kiran wayoyin yaran gida ta isar da sakon da mahaifinsu ya sanar da ita,"

sannan ta daura alwala ta shiga salla ita ma.

har suka kammala taruwa malam din bai shigo ba domin sai da ya tsaya ya siyo goro da alawa ya shigo

"da su, suna tsakar gida bisa babbar tabarma ana ta tattaunawa akan maganar gudun raliya. rabi'u yace"

"'WALLAHI da ni ta hadu da shi tuni labari yasha bamban shegiya kodaddiyar banza kawai, taje indai duniya ce wanda bai zo bama jiransa take yi'"

"shi dai ahmad jinsu kawai yake yi, yana jin tamkar an raba shi da wata babbar masifa ce a rayuwarsa"

"domin ko kallon raliya baya son kuma yi, yasan ALLAH ne ya amsa addu'arsa yayi gaggawar raba shi da ita. saidai kamar yanda tace din ya san shi da kara aure har abada, domin ba zai iya kara tunkarar mace.ba da sunan yana son ta ba, balle har ya jawa kansa wulakanci ba, zai ci gaba da zama a haka idan"

yaji zai takura sai yayi azumi.

"sallamar malam din ce ta katse musu hirar tasu, ahmad ya mike da sauri ya amso kayan da malam din ya"

shigo da shi niki-niki yana fadin sannu abba.

"ya karasa ya zauna akan tabarmar da yaran ke kai, daya bayan daya suka dinga gaishe shi ya amsa"

sannan ya kalli umma yace 'ina ma'un take kuma?

"umma ta kalli kofa 'tana cikin daki ka san indai yayyanta suna hira bata fitowa cikinsu ta zauna, watakila"

ma tayi bacci'

'ko tayi bacci ta taso' ya kalli kofar dakin ma'u asma'u kina ina ne? ta fito da sauri tana goge idonta 'ina

ciki abba ka dawo sannudazuwa'

ya amsa da 'yauwa sami guri ki zauna' sannan ya turawa umma buhun alewa da goron dake gabansa

yana fadin 'buda ki gani deeje'

umma ta ja buhun ta fara dubawa ta daga kai ta kalle shi da mamaki tace 'goro da alewa ne ko wakilcin

aure zaka yi?

"'ko daya goron daurin auren asma'u da ahmad ne, an daura auren dazu a masallacin juma'a na gidan"

sarki'

"mamaki ya kama kowa har aka rasa mai iya karfin halin fara magana, ita kam asma'u mikewa tayi a"

firgice duk da tana da karancin shekaru amman ai ta san aure ta san abinda yake nufi.

umma ce ta fara karfin hali yin magana 'malam kaji abinda kace kuwa? malam ya gyara zama 'kwarai da

"gaske saidai idan baki ji ba kice na maimaita miki, goron auren diyata asma'u da ahmad ne, wanda aka daura dazu a masallacin gidan sarki'"

"ahmad yaji wani irin abu dim a kirjinsa tamkar an caka masa mashi, gaba daya kuzarinsa da tunaninsa ya"

"kwace, ya ma rasa me ya dace yayi."

auwal ne ya yi kokarin magana cikin yaran 'ALLAH ya sanya alheri ya kuma basu zaman lafiya da zuri'a

dayyiba' gaba daya suka amsa da amin.

sani yace 'baba ya batun karatunta kuma?

"wannan yana hannun mijinta dukkan hukincin da ya zartar shine daidai, daman karatun ba dole bane ba."

umma ta girgiza kai tace 'haka ne to yanzu yaya za a yi kenan malam?

"'gyalenta zata dauko ta yafa su wuce gidan mijinta, wannan goron da alewar kuma ki raba shi gidajen"

makota domin su ma su shaida'

"ahmad ya kalli abbansa a firgice daidai lokacin da asma'un ta kalle shi ita ma, sai take ganin abin kamar a"

"mafarki, anya da gaske ne haka daman ake aure?"

umma ta kwantar da kai tace 'amman malam da an bari an shiryata a hankali sai a kai ta...' ya daga mata

"hannu 'babu wani shiri da za a yi, ki dauko mata hijab dinta su wuce da mijinta, duk wanda kika aikawa da goron kice har ta tare a gidan mijinta fakat.'"

*

*

*

da kyau malam dattijon arziki to ALLAH ya basu zama lafiya da zuri'a dayyiba amin.

DA ME AKE ADO?

24

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Aka yi shiru babu mai abun cewa Malam ya Kali Ahmad wanda ya kasa motsi, tamkar an zare masa"

"dukan lakar jikinsa yace 'Ahmad Kama matarka ku wuce gidanku"" Ahmad tayi firgigit ya mike har a lokacin yana tsammanin zolaya ce, Amman yasan abbansa bai masa irin wannan wasan, umma ta mike ta shiga cikin daki ta dauko hijat ta Bawa asma'u tana fadin ""ALLAH yayi miki albarka ya baku zuri'a"

"dayyiba ya sa anyi kenan"""

"Saran suka amsa da amin, ma'u ta amshi gyalen ta sanya ta kasa yin komai don tsabar fargaba."

"""Kamata ku wuce mana"" Malam ya kara ba su umarni. Ahmad sai yake ganin da kunya ya Kama hannun"

"ma'u, musamman da Malam ya ambata matarsa ce wai a yau. Don haka ya wuce da sauri ya nufi soro, a gobe yake kokarin tarkato kayansa ya dawo rayuwa da ummansa ashe bashi da rabon sake zama tare da"

"ita, wato ya bar ta kenan har abada."

"Umma ta Kama hannun ma'u domin ta kula duk ta rude ta rikice gaba daya, abindake damun umma"

"daya ne yadda bata taba koyawa ma'u komai na rayuwar gidan miji ba, a tsammaninta sai ta kara girma ta kara wayo tayi hankali ashe ba zata kai wannan lokacin ba za a yi mata aure. Bata tsammanin ko farar"

shinkafa ma'u ta kware a dafawa. Wannan kadai shi ne abinda zai dame ta har abada.

"Har sai da Ta kai ta bakin zaure wannan ta tsaya yana fadin ""maza wuce kung tafi ALLAH yayi muku"

"allbarka"""

"Malam fa sauran yaran suka taso suka rakosu har gaman babur din, ya hay ya yara babur sannan ya"

"karkata mata ta Kama Ta hau. Ya tuka suka tafi suna daga musu hannu. Malam ya dubi sauran yace ""to masu iyali su wuce gidansu ku kuma marasa iyali sai ku shiga ku taya mahaifuyarku kullin kayan daurin"

"aure, ni zan wuce gidan Malam habu na sanar da shi"""

"Da haka ya wuce su ma ya ran kowa ya Kama gabansa, sai samarin da kanana ne suka shiga cikin gida"

suka fara din.

"Salisu yace ""umma wai daman kun shirya hakan ne ke da Abba ba ku sanar da mu ba? Umma Ta galla"

"masa harara ""ban Sani ba tambai sarkin tambaya, sai naji matsi zan baka amsa"" yadda ta fadi maganar a fusace ya dan bashi tsoro yace ""ALLAH ya huci zuciyarki umma kiyi hakuri"""

"Hakan da tayiwa salisu ya sanya kowa ya kunshe tashi a cikinsa, sai wani lokacin sa amayar kuma."

"A hanya suna tafe bisa babur kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa, ita kam ma'u har lokacin bata"

"yarda ba mafarki take yi ba, domin ko a cikin littafan hikaya bata taba jin irin wannan labari mai ban mamaki ba."

"Shi kam Ahmad jinjina kyautayi da karamcin bayin Allahnan ne a ransa, dama zai iya zaka musu wannan"

"karamcin day suke yi masa, waye zai iya aikata irin wannan abinda suka aikata a wannan zamanin da ya"

"lalace da rayuwa irin ta jari hujja. Tabbas sai an tona, har suka isa kofar gidan kowa yana sakawa da"

"kwancewa, ya tsaida babur din ya sauka ya rike yana fadin ""sakko"""

"Ta kama tana kokarin sakowa har tayi kamar zata fadi domin tana jin jikinta kamar ba nata bane ba, tana"

jin ta a wata duniya daban a wani bigire da bata taba tsammanin zata halatta ba.

"Ya kalle ta da kulawa sai yaji duk kun ya sa fargaba sun kama shi, wai ma'unsa kanwarsa ita ce yau Ta"

"zama matarsa, ALLAH sarkin iko da buwaya, ya daure yace mata muje mana."

"Ta shige gaba yana biye da ita har suka isa kofar gidan ya sanya mukulle ya bude suka shiga, ta tsaya a"

"tsakar gidan tana kare masa kallo. Bata kawo komaia a ranta ba sai daman an shirya komai ita ce kawai ba a sanarwa ba, tunda gashi har gida an tanada an sanya komai, ya kalle Ta amma bai bari sun hada ido"

"ba yace ""kije ga daki can ki yi sallah ki kwanta"""

"Da sauri tace to ta nufi dakin kamar wacce ke kan kaya daman, ya bita da kallo har Ta shige sannan ya"

"nufi dan dakinsa na shago ya samu guri ya zauna ya dafe kumatu, raliya ta tafi asma'u ta shigo, shin ita wanne irin zama kuma zasu yi kenan, ko a mafarki bai taba hango wannan rana ba balle idan ya farka yayi mata wani nazari koda a cikin ransa ba ne, Hakan ya sanya ya kasa tabuka tunanin komai sai gyada"

kai kamar kadangaruwa.

"Tana shiga daki ta zauna gefen gado tana karewa dakin kallo, da gani nata ne sabuwar amarya, amman"

"yaya aka yi ba a sanar da ita komai ba duk wannan shirin da ake yi, me ya sanya sanda yaje bai sanar da ita za a hada su aure ba sai ya bata labarin aurensa da raliya, amman da alama shi ma bai da masaniya"

akan komai.

"Tuno raliya da tayi ya sanya zuciyarta yin kunci, wato daman ita kishiyar raliya ce, a iya tunanin bata taba"

"tunano cewa za su hada miji da raliya ba, me ya sanya su abbanta suka yi mata haka, ta dafe kirjinta yana bugu kamar zai ballo ya yo waje, idanuwanta suka ciko da kwalla jikinta ya dauki karkarwa, sai take ji kamar an lika mata kiyayyar raliya a ranta. Kishi mai girma ya rufe ta, sai ta fashe da kuka me ya sanya"

rayuwa tazo mata da wannan akasin ashe ita ma matar yayanta Ahmad ce.

Ta jima tana kuka kafin ta yunkura ta fito tsakar gida ta dauro alwala ta koma daki domin yin sallar isha'i.

Ta idar da sallah ta tsaya tana kallon dakin tana lazimi tana sakawa da kwancewa har zuwa sanda ta gaji ta mike da hijab din jikinta da komai ta haye gado ta kwanta.

"Sai dai me haushin karnuka da take jiyowa can kan titi da kukan gyare sun hadu sun birkita mata tunani,"

"sun assasa mata tsananin tsoro bata taba kwana ita kadai a daki ba, idan tana gida tana nakale a bayan ummanta har bacci ya dauke ta, sai cikin dare umman ke zamewa ta guru dakin maigidanta da an yi kiran sallar farko ta dawo ta kwanta, a makaranta kuwa dakinsu su wajen goma sha tara ne, don haka bata taba kwana ita daya ba, ta mike a firgice tana waigen dakin, to me ya kamata tayi ne shin yayanta zata kira ko kuma rufe kota zata yi? Har ta kama kota zata tura sai taji kamar an mata kuwwa cikin kunnenta don haka ta fito daga cikin dakin cikin sauri, don ma da hasken wutar nepa ta jima a tsaye a tsakar gida tana sakawa da kwancewa ta rasa madafa, sai ta ga kamar gidan ma yana mata gizo don haka tayi soro da sauri tayi sa'a kofar dakin nashi a bude take don haka Ta samu guri ta tsuguna ta nannade"

"jikinta cikin hijab tamkar mai jin sanyi, a haka har bacci ya fara daukarta."

"Ahmad yana ciki bai san abibdake faruwa a soron ba, tunda ya zauna ya kasa motsawa ya rasa abinda ya"

"dace yayi, tsohon lokaci yana wannan hali har dare ya fara ja, sai yaga dacewar ya tashi ya daura alwala"

"yayi sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan ya nemi yardar ALLAH da amincewarsa bisa wannan auren da ya zo masa bagatatan, ya mike ya nufi kofar dakinshi."

Yayi baya a tsorace yana ambaton Sunan ALLAH domin karo da yaci da ma'u wacce ke ta shirgar baccinta

"haikan babu wata fargaba, sai da ya nutsu sannan ya fahimci ita ce, mamaki ya kuma kama shi ya matsa kusa da ita yana kallonta me ya kawo ta nan me ya sanya ta yin bacci a haka?"

"Cikin daga murya ya fara ambaton sunanta domin yaga alamar bata san da shi a gurin ba, ta farka a"

firgice cike da tsananin tsoro da firgita tana waige-waige ya durkusa a gabanta.

"""Ni ne Nana kwantar da hankalinki, me ya kawo ki nan kina bacci?"

Ya fada cikin rarrashi domin ya kula duk a kidime take.

"Tayi narai-narai da idanunta cikin tsoro don tana gudun kada ya doke ta tace ""ALLAH yaya tsoron dakin"

"nake ji, sai naji kamar ana motsi a bayan kyauran'"

Yayi murmushi yace 'nana har yanzu ke sokuwa ce ko to me ya sanya baki sanar da ni ba?

"Ta sunkuyar da kanta tana sosa keyarta cike da tsananin kunya, ya kula tunda suka iso gidan ma'u take"

"jin kunyar hada ido da shi, shi ma nauyinta yake ji Kwarai da gaske."

"Jin bata da niyyar cewa komai ya sanya ya mike ya kama hannunta yana fadin ""taso muje ki kwanta kada"

ki kuma kwanciya amusuv

Babu musu ta bishi amman hankalinta a tashe domin rike mata hannun da yayi sai ya sanya tsigar jikinta

"tashi, a haka har suka isa dakin, ya zaunar da ita a gefen gado yana fadin ""to kwanta bari ni na kwanta a kasan"" ya dauko filo guda daya bisa gadon ya jefar kan tayil ya kwanta ya juya mata baya."

"Ta kura masa ido tana sake-sake cikin ranta, to me yw sanya bai tafi gurin raliya ba yau, kuma tunda suka"

"zo bata ji motsin raliya ba, ko ba a gidan take ba, ta jima zaune tana sakawa da kwancewa har daga karshe ta yanke shawarar kwanciya ta kwanta tana kallon shi wai yayanta ne ya zama mijinta, ko yaya su maryam za su ji wannan labarin, su ji an yi mata aure ta daina karatu? Amma tasan yayanta zai bari ta cigaba da karatunta. Har bacci ya dauke ta tana sakawa da kwancewa, da ya ji alamun tayi bacci ya mike"

zaune don dama ba bacci yayi ba lambo yayi.

"Ya kura mata ido yana kallonta tamkar mai bacci cikin ruwa fuskarta tayi 'yar kuyas, kuruciya da yarinta"

"sun cika ta, ko ta yaya Abba ya yanke wannan hukuncin har yau ma'u bata wuce a koya mata daura zani ba, shekaru goma sha hudu ai ba wasu shekaru ne masu yawa ba. Sai yake ganin kamar tana yi

25 / 47