Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   24 / 47

69K to 72K   out of 139.6K words

babu inda zaka sai ka sake ni, maye kawai banda naci"

nace bana son aurenka dole ne. ka sake ni na tafi. WALLAHI yawon karuwanci yafi zaman wannan kallaggen auren naka'

zuciyarshi ta dinga zillo da tafasa a halin da yake ciki idan yace dukan raliya zai yi babu abinda zai sa ba

"zai kasheta ba har lahira, idan kuma ya tsaya haka tana cigaba da shake masa wuya zata iya illata shi, don haka ya waigo a fusace ya hanbareta cikin zafin rai, tayi taga-taga ta zube warwas a kasa tayi karo da bango. ta fasa wata uwar kara domin hannunta ya bugu da alama tayi targade ma. ta fashe da kukan"

azaba.

ya kalle ta da jan ido yana fadin 'sokuwa kin yadda duka guda.zai iya maganinki. ki sani ba wannan

"rayuwarce a gabana ba ta dabbobi ina da hankali da tunani. idan har da gaske kina son rabuwa dani kije ki sami wadanda kika daura ki sanar da su, WALLAHI idan suka bani umarnin sakinki ko kiftawar ido ba za a yi ba tare da na furta ba, nafi kowa kyamar ki da halayenki shashasha mai bin mazan banza a titi da"

"aurenta, kuma WALLAHI koda wasa kika kara zuwa kofar dakinnan sai nayi kasa-kasa dake'"

"ya mai da kofar dakin ya rufe, yana rufewa ya dafe kansa jikin bango hawaye na zubo masa, tabbas"

iyayensa sun kware shi da suka haife shi shege kodayake babarsa bata da laifi domin ita an kusance ta ne

"bata sani ba, tana cikin halin hauka, ko waye babansa da yayi cikinsa ya kuma wofintar da rayuwar"

"mahaifiyarsa, bai ma san watakila an same shi ba, bai sani ba sam, da ya san abinda kusantar mahaukaciyar zai haifar wata kila da bai kusanceta ba, sai kuka ya kwace masa sai kace mace, yana buga"

kansa da bango yana fatan mutuwa tayi awon gaba da rayuwarsa a wannan lokaci.

raliya kam dakyar ta lallaba ta tashi daga faduwar da ta yi tana kuka sakale da hannunta da tayi targade

saidai bakinta bai mutu ba ta cigaba da tijararta.

'ALLAH ya isa shege tsinanne dan mahaukaciyar kan bola da ba a san asalinsa ba' duk abinda da yazo

"bakinta faditake yi a fatanta na tunzura shi ya furta kalmar saki a gareta kamar yadda mahaifiyarta ta bata umarni, ta gaya masa dukkan kalaman da zasu iya tunzurashi amman bai ce uffan ba sai hawaye da yake zubdawa yana tasbihi ga ALLAH a fili da zuciya har zuwa lokacin da ta gaji da tijarar ta kama hanya ta wuce dakinta tana kukan bakin ciki, kukan nata kashi biyu ne. na farko na rashin cikar burinta na sakin"

"da ya ki yi, na biyu kuma buguwar da tayi har tayi targade."

da ya daina jin sautin muryarta sai ya mike ya cigaba da sallarsa yana kuka yana sanar da ALLAH halin da

yake ciki. wanda ko labari aka bashi a baya ba zai yadda wani zai iya shiga cikin wannan halin ba sai gashi shi ya shiga.

"sai wajen karfe uku da wani abu na dare yaji gwiwoyinsa sunyi sanyi idanuwansa sun yi nauyi, babu"

abinda yake bukata illa ya kwanta ya huta don haka yayi addu'a ya koma ya kwanta bisa tabarmarsa. cikin kankanin lokaci kuwa bacci ya dauke shi.

*

*

*

a gai da ahmad namijin duniya.

DA ME AKE ADO?

21

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Saboda rashin baccin da bai yi da wuri ba ya sanya ya makara,bai tashi da asuba yayi sallah ba sai da"

"hasken rana ya shigo dakin ya haske masa ido sannan ya farka a firgice ya duba agogon dake jikin wayarsa sai yaga yanuna masa karfe bakwai nasafe, ya mike da sauri yana istigfari ya nufi kofa yabude kai tsaye cikn gidan ya nufa don daura alwala, abinda ya bashi mamaki yau bai jiyo sautin kidan raliya ba,"

wanda kullum dashi take farkawa kamar shaidaniya.

ya shiga bandaki ya kama ruwa ya tsuguna gindin rariya yana daura alwala yana satar kallon kofar dakin

"nata, yana addu'ar ALLAH ya sanya har ya kammala ya fice bata fito ba, domin baya son kallon fuskar raliya. cikin ikon ALLAH kuwa har ya kammala bata fito ba ya nufi shagonsa."

yayi turus cike da tsananin tsoro domin ganin kofar gidan a bude sam bai kula ba sanya ya wuce yin

"alwala, abinda ya bashi tsoro kuwa tunda suke a gidan raliya bata taba bude kofar da safe ba, ko karfe"

nawa zata kai bata budewa har sai yazo ya bude kuma duk yawonta bata fita da sassafe har sai rana ta daga.

"ya waiga cikin gidan sai ya ga ba takalman raliya a bakin kofa,ya nufi cikin gidan da sauri ya daga labule"

"ga mamakinsa sai yaga an watsar da kayan cikin sif dakin yayi kacakaca da alamar an debi wasu kayan. gabansa ya kuma faduwa ba dai guduwa raliya tayi ba. daga can kan gado ya hango wata takarda a yashe ya isa da sauri ya dauka ya bude, cikin wani cukurkudadden rubutu yaga sakon nata ya fara"

karantawa.

"-ba ka bukatar sallama domin bata dace da shege irinka ba, duk wasu hanyoyi da zanbi don ganin ka"

"sauwake min wannan kallagaggen auren naka nabi amma kaki sakina. don haka nabi hanyar da tafi dacewa wato na gudu na barka da aurenka, idan kaga dama ayanzu zaka iya aikawa iyayena takardar sakina domin sanda zaka ci karo da wannan takardar tuni nayi maka nisa kai da rayuwrka. sai kuma aci"

gaba da zaman gwaurantaka don na san har ka koma ga ALLAH ba macen da zata yarda ta auri shege.

sai wata rana: raliya.

ya runtse idanuwansa sanda ya kai karshen takardar sako mafi muni da zafi da idanuwansa suka taba cin

"karo da shi, koda bayan an yaga takardar an konata rubutun ba zai gogu akan zuciyarsa ba, zai ci gaba da karanta shi zuciyarshi na zafi idanuwansa na fidda hawaye mai kuna."

ya jima a tsaye yana tunanin me ya dace yayi farin cikin rabuwa da raliya ko kuma bakin cikin gudunshi

"da tayi shi da sake aure har abada kamar yadda tace, domin yasan babu macen da zata yarda ta auri"

"shege mara asali, saidai in dole aka yi mata irin na raliya, wanda yasan iyayansa ba zasu taba yadda su yi masa irin wannan auren ba."

dakyar ya lallaba dakinsa yayi sallar asuba cikin sujjdarsa ta karshe ya jima yana sanar da ALLAH halin

dayake ciki yana kuma rokonsa ya sanya tafiyr raliya alkhairi ce ga rayuwarsa. bayan ya kammala ya nufi

gidansu babu tsayawa yin wanka ko kalaci. ya shiga gidan da sallama. umma tana kicin tana dama koko ta leko da mamaki tana fadin 'murya nake ji kamar ta ahmadu'

da sanyin murya yace 'nine umma' ta karasa fitowa da faduwar gaba tana fadin 'ALLAH dai ya sanya

"lafiya' yayi jim ya kasa magana. ganin hakan ta sanya ta gane ba lafiya ba, don haka ta kalli kofar dakin abba tana kwala masa kira. 'malam fito! fito ga ahmad daga yanayinsa ya nuna babu lafiya'"

malam sulaiman ya daga asabari ya fito yana fadin 'deeje me kike cewa ne? hango ahmad ya sanya shi

"yin shiru yana kallonsa da mamaki kafin ya karasa fitowa ya nufe shi. 'ahmd lafiya, me ya faru nagan ka cikin wannan yanayin? ahmad yazame ya durkusa yana fadin 'abba ina kwana'"

"'ba wannan na tambaye ka ba me yake damunka, kaga yanda ka fita daga hayyacinka kamar wanda yayi"

"cutar shekara, idanuwanka duk sun kumbura ko dama bashi da lafiya ne baki sanar da ni ba?ya karasa maganar yana kallon umma."

'ko kusa malam ban san bai da lafiya ba sai yanzu' ta kalle shi da damuwa 'meke damunka ahmad'

ganin yadda suka gigice ya sanya yayi saurin warware musu komai 'lafiyata kalau saidai bana cikim

"kwanciyar hankali, domin na wayi gari yau raliya bata gidan da alama tun cikin dare ko asuba ta fita'"

umma umma ta kama salati tana tafa hannu cike da damuwa 'ni dama na zan za arina don dai kada

"malam yace anyi masa gaddama ne, amman yarinya wayayya da ta san ta kan duniya irin raliya ce zata tsaya zaman aure kuma auren ma na dole'"

malam sulaiman ya kalle shi yace 'kun sami sabani da ita ne ahmad?

kansa yana kasa yace 'abba ai tunda muke tare gida daya da raliya bamu taba ko zaman minti guda na

"kwanciyar hankali ba, hasalima taci gaba da fita yawonta duk inda taga dama sannan tana matsa min da gori da cin mutunci da zagi, wai dole sai na saketa. daren jiya har kusan karfe daya ta kai tana cin"

"zarafina. duk wata kalma ta cin mutunci tayi min ita, amman ban kulata ba"

sai da na wayi gari da safe babu ita sai takardarta naci karo da ita ta kuma kwashe dukkan wasu kaya da

suka kasance mallakinta na tadda wannan takardar akan gadonta'

ya mika musu takardar malam ya amshe da sauri ya fara karantawa a fili kasancewar ya san umma bata

san karatun boko ba sai na ajami kawai.

"yana kaiwa karshe umma ta kara jan salati 'lallai raliya ba diyar kirki bace, koda yake ai barewa ba ta yi"

gudu danta yayi rarrafe ba. na godewa ALLAH da yayi gaggawar rabaka da ita tun bata kashe min kai ba'

malam sulaiman yayi shiru cike da tsananin damuwa ya ma rasa me ze ce.

rabi'u yana tsaye cike da damuws. tunda ya jiyo salatin iyayansa ya san ba lafiya ba. ya shigo yana son

tambayar abinda ya faru yana kuma jin tsoro. malam ya dube shi yana fadin 'maza shiga cikin gida kace da jibrilu da matarsa su zo yanzu ina son ganinsu'

"rabi'u ya wuce da sauri cike da damuwa domin bai san abinda ya faru ba, minti biyu kacal suka kwashe"

"sai ga shi tare da su malam jibril, yanayin da malam din ya gansu ya tabbatar masa ba lafiya, lami kam babu wata damuwa a fuskrta. kallo day ahmd yayi mata ya tabbatar da sanya hannunta a gudun raliya musamman da ya tuno maganganun da yaji suna yi sanda ya taddata da maraice amman ba zai furta"

hakan ba domin ba ya son abinda ya faru baya na mutuwar auren lami ya kara afkuwa.

"malam jibril ne ya fara tambaya 'ya aka yi yaya, ALLAH dai ya sanya lafiya domin na ganku cikin samuwa'"

malam sulaiman ya mika masa takarda yana fadin 'karanta ka gani'

*

*

*

kin fa yi gaskiya umma barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba saboda duk mugun halin lami raliya

ta kwashe.

DA ME AKE ADO?

22

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Malam jibril ya kalli takardar ba tare da ya amsa ba yace 'yaya ai ka san ban iya karatun boko sosai ba,"

balle wannan da nake ganinsa kamar zanen tsutsotsi' malam sulaiman ya gyara tsayuwa ya nuna masa takardar yace 'ka ga wannan takarda ce da raliya ta rubuta kafin ta tafi yawon karuwanci' malam jibril ya

dafe kirji da damuwa 'yaya wanne irin yawon karuwanci kuma? a iya sanina raliya tana gidan mijinta'

"'naji dadi da kace a iya saninka, alama baka san gaibu ba kenan, to ka bude kunnuwanka da kyau kaji."

raliya tabar gidan ahmadu yau da asuba. bayan tayi duk wani cin mutunci da zagi bai kula taba. ta bar wannan wasikar ta kuma ce da zaman auren ahmadu gwara taje tayi karuwanci ya fiye mata. kaga

abinda nake nusar da kai tun a baya ko?

malam jibril yayi shiru cike da tsananin damuwa ya ma rasa abinda zai ce idanuwansa sun kada sun yi

jajir gwanin ban tausayi. ita kuwa lami babu damuwa ko kyas a tattare da ita sai wani fici fici take da ido irin na mara gaskiya tana kara tsare gida.

malam jibril yace 'to yanzu yaya zamu yi kenan ko bin sahunta za a yi ne?

"'a bita ina, raliya ba yarinya ba ce tunda har ta iya hada kayanta ta gudu ta kum furta kalmar tafiya"

"karuwanci abin ya kai intaha, saidai abinda tace a yau zan karyata shi da tace saidai ahmadu y mutu babu aure, to tayi karya ita ce zata mutu babu aure ba ahmadu yaron kirki ba. taje duniya fadi ne da ita, wanda bai zo ba jiransa take yi'"

"ya kada kai ya shige dakinsa yana huci, umma kam sai cika take tana batsewa tamkar ta shako lami"

"domin ta riga ta gane da sanya hannun lami. ta kuta tace 'idan an guji ahmad don wata illa a banza,"

"domin shi bai da laifin komai. wanda kuma yake aikata irin laifin kama fa? karuwanci sana'a ce babba mai lasisi saidai tana da darussanta, muna zuba ido mu ga karshen butulci da rashin tarbiyya'"

"lami ta kulu da kalaman umma ta yamutsa fuska tana fadin 'oho kome za a fada ta baya ta rago, tunda"

"ai ba mu muka ce raliya ta tafi ba, duk kuma inda take ALLAH zai kare ta'"

"'ALLAH ba zai kare raliya ba lami, yarinyar da ta tafi da hakkin minjnta da aurenta da na iyayenta kike"

"zaton zata samu kariyar ALLAH. WALLAHI ta barranta daga rahamar ALLAH. ba kuma zan yafe mata wannan tozarcin da cin mutuncin da ta ja min ba, ahmadu da yake namiji yayi hakuri amma ita ta kasa, taje duniya ce' malam jibril ya karasa maganar tamkar zai rushe da kuka domin yana ganin iyakacin"

tozarci raliya taja masa.

"lami ta kuma cika a fili tace 'ALLAH shi ke raba rahamar ba mutum ba, don haka bakin kowa ya fada"

"masa baki ba zai cinye raliya ba insha ALLAHU' tana kaiwa nan ta juya ta nufi cikin gidan tana huci, malam jibril ya bita da kallo yana huci kamar ya shakota, amman sai ya dake ya kyaleta ya gyada kanshi."

"yana kallon kofar dakin yayansa yace 'malam da ka fito mun karasa maganar nan, kayi hakuri'"

"ahmad dai yana durkushe yana kallonsu, domim kafafunsa ba zasu iya daukar gangar jikinsa ba, malam"

"sulaiman ya fito ya sanya malum malum akan kayansa ya kuma sanya hula yana kokarin daura rawani yace 'jibrilu ai zan fito daman, shiryawa dai nake yi. maganar raliya kuma ai mun kammala, ko yanzu ta dawo WALLAHI tayi kadan ta koma gidan ahmadu, mutumin da yayi maka irin wannan cin mutunci a"

takadda da yasan kowa zai iya gani zai yi maka fiye da haka idan kuka hadu daga kai sai shi'

"malam jibrilu ya gyara tsayuwa 'ma maganar raliya ba ce, da cewa zan yi ko amina kanwar raliyan za a"

mayar dakin yayar tata'

"ahmad ya daga kai da sauri cike da tsananin faduwar gaba yana kallonsu, kunnuwansa har wani rawa"

"yake yi domin tsoron jin amsar da malam din zai bada, ita kam umma tamkar tace baya so saidai bata isa ta shiga maganar tsakanin dan uwa da dan uwa ba, amman ta zubawa malam din ido tana jiran taji me zai ce."

"malam jibril yayi dariya mai ciwo yacd 'ai diyoyinka sun nunaaa duniya ban isa da su ba, daga kan raliya"

"na daina karambani a gidanka insha ALLAH, kuje can ku baiwa diyoyinku irin mazan da suke so amman ni kam har abada idan maganar daman kenan zan wuce'"

"ahmad yayi ajiyar zuciya cike da tsananin farin ciki, cikin ransa yace masha ALLAH duk da aminatu bata"

"da hali irin na raliya amman ai duk rainon lami ne, idan har aka bashi ita zai zamo irin abinnan da hausawa ke fadi wato an rabu da bukar kuma an haifi habu, ita kanta umman taji dadin amsar da malam"

sulaiman din ya ba shi.

"malam jibril yayi kasake cike da tsanan damuwa, malam sulaiman ya kalli ahmad 'ka tashi ka wuce dakin"

rabi'u ko na salisu ka kwanta ka huta. ALLAH yayi maka albarka'

"ya kalli umma. 'zan je unguwa sai na dawo kenan' ta bishi da doguwar addu'a sanda ya nufi soro, shi kam"

"ahmad tuni ya mike ya nufi dakin rabi'u ko don ya kwanta ya huta ma, malam jibril jikinsa sanyi yayi ya nufi cikin gidansa da tsananin damuwa."

DA ME AKE ADO?

23

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

MASALLACIN JUMA'A NA GIDAN SARKI

"Malam sulaiman ya shigo niki-niki da buhun goro da kwalin alawa dana biskit, kasancewarsa ya shiga da"

"wuri wajen sha biyu na rana ya sanya ya samu sahun gaba daman abunda yake da bukata kenan, domin yana son yayiwa na'ibi magana, na'ibi yana shigowa ya matsa kusa da shi ya masa magana bisa bukatunsa, na'ini ya dauki goro da alawa da biskit din ya wuce da su aka yi kiran sallah aka yi huduba karfe biyu daidai aka daura auren ahmad da asma'u, aure mai cike da albarka domin yasha addu'a daga bakunan mutane masu daraja, farin ciki ya cika malam sulaiman sanda aka shafa fatiha ta uku. sai yaji tamkar ya sauke wani gungumemen bashi ne dake kansa. ya daga hannu yana yiwa ALLAH godiya domin"

cika masa wannan burin da yayi yana raye.

daga masallaci kai tsaye makarantar su asma'u ya nufa domin ya dauko ta.

***

"asma'u tana cikin kawayenta a kwanar wata kawarsu aisha ana tayin kitso ana hirar duniya, abinda ya"

daukewa ma'u hankali bai wuce hirar da maryam ke yi ta saurayinta bala ba. kullum aka zauna maganar kenan guda daya hirar takan tuno mata da yayanta shu'aibu da kalamansa. aisha ta zunguteta sanda tayi

"shiru tana tunani tace 'malama ya kamata yau dai ki fada mana sunan saurayinki, kullum sai dai ki dinga"

jin hirarmu kina wani gwale mana ido' suka kyalkyle da dariya gaba dayansu.

"ma'u tayi ajiyar zuciya tace 'ni fa bani da saurayi, yayana yace ban girma ba. sai na kammala secondary"

na shiga level 2 ya dace na fara kula samari' suk rude da ihu maryam tace 'yarinya an barki a tasha. duk rayuwar da babu soyayya bata cika ko ya kuka ce kawayena? ni kama ina son man dina da yawa'

"suka kuma fashewa da dariya, ita dai ma'u kallonsu kawai take yi tana jin abin bako agareta, ta yaya ake"

"gane ana son wani. yaya wani kuma zai iya gaya maka yana sonka. ita da ta taba yin saurayi sau daya kafin yayanta ya hana ta zancen dashi, wato da ta jima tana hira da shi da tasan meye so kenan, amma kamar yadda yayanta ya fada mata tayi kankanga ace ta fara soyayya yanzu duka shekarunta 14 fa, kuma ajinta 3 kacal amman yaya kawayenta kuma sa'anninta suke yin soyayya, kalamansu ke kara kanainaye ta kodayaushe har taji bata da wani katabus. daga can bakin kofa taji wata senior tana kwala mata kira"

'asama'u sulaiman! asma'u sulaiman

24 / 47