Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 47

90K to 93K   out of 139.6K words

domin ita kanta ta gaji, amma yaya auwal yace har"

yanzu ba a basu damar dawowa ba ne.

"Sai dai duk karshen wata yana yi musu aike da ta akawun (account) yaya auwal, kadan yake daukar kudin"

ya aiko sauran.

"Wannan abun shine yake farantawa malam Sulaiman rai kwarai da gaske, domin a yanzu KO bai fita"

"kasuwa ba bai rasa abinda zai sanya a bakinsa darajar 'yayansa. Kowanne a cikin yaran nasa yana yin iyakacin karfinsa sabanin dan uwansa da yake cikin damuwa da wahala, domin dan nasa guda daya ne tal, Musa ba kuma wani karatu mai zurfi yayi ba, don haka albashin nasa bai wadatar dasu, musamman"

yadda lami ta dora dukkan burikanta akan kudin nasa ita da diyanta.

"Kafin wata ya kare lami har bashi take ci, ya kasa tsinana komai domin albashin malami na firamare ba"

wani yawan kirki ne da shi ba.

***

INA LABARIN MUTANEN LAGOS?

Ahmad yana cikin tsananin damuwa da takura saboda rashin iyalinsa da iyayensa. A yadda Alhaji Nura

"yayi musu alkawari watanni uku zasu yi, amma ga shi har sun shiga wata na shida, kuma watan yana neman karewa ba a ce musu komai ba."

"Hankalinsa duk ya tashi har ya rasa abinda zai ce a gayawa ummansa da ma'unsa, amman dai ya san"

suna cikin damuwa kwarai da gaske.

"Lokacin da suka cika watanni bakwai ya gama fusta, bai jin komai bayan ya isa ga ahalinsa, don haka"

"lokacin da Alhaji Nura ya iso garin don ya duba yadda abubuwa suke tafiya, ahmad yaji kamar dukkan matsalarsa ta kare, don haka lokacin ya zauna mitin da su ya kuduri aniyar fadin abindake ransa."

"Bayan yayi yabo da jin dadi akan yadda aka samu cigaba da abin da ake bukata ga gidan man, yayi musu"

"albishir da samun albashi mai tsoka, murna da jin dadi ya cika su, amma banda ahmad, domin yawancin"

"wadanda suka taho kamar ba su damu da iyalinsu ba, da yawansu sun saki jikinsu suna ta mu'amalarsu"

har da masu ajiye daduro ma.

"Bayan Alhaji Nura ya gama bayaninsa ahmad ya daga hannu yana fadin""idan yallabai ya ba ni dama ina"

"da maganar da nake son yi"""

"Gaba daya kallo ya koma gurinsa, abokinsa Isuhu Harka ya dan zungure shi alamar kada yayi magana,"

"domin ya san abinda zai ce, saboda kullum sai yayi musu korafi amman ahmad bai kula da shi ba."

"Alhaji ya kada kai ""kana da damar yin magana ahmad"" sai ya mike tsaye ya fara koro bayani. ""Yallabai"

"kamar yadda aka fada a baya kafin mu zo garin nan, kace watanni uku kacal zamu yi amman ga shi yanzu har mun shiga wata na bakwai, kuma watan yan gab da karewa amma babu labarin tafiya gidan, shine"

"nake son a yi mana bayanin yadda abun yake..."""

"""Rufe mana baki mara kunya, kai kadai kake da iyali ko bakin magana? Baka ganin wasu neman aikin"

"suke yi ido rufe"" manajan gidan man ya fadi haka bayan ya katse shi cikin tsananin bacin rai da masifa."

"Ahmad yace ""haka ne amman ka san babu wanda ya isa ya ba wani aiki idan ba ALLAH ya kaddara ya"

"amince ba. Ina ji a jikina aikin da nake yi yana cikin kaddarata, su kuma wadanda basu samu haka aka rubuta a littafin kaddararsu, don haka zaka iya yanke kowanne hukunci akaina"" babu tsoro balle fargaba"

ahmad ya sake fadar maganganunsa.

Manajan ya kara fusata da jin maganganun da Ahmad ya fada masa ba tare DA shakkarsa ko fargaba ba.

"Gurin kowa yayi tsuru-tsuru cike da tsoro musamman Isuhu abokin ahmad. Manaja ya nuna ahmad da dan yatsa cikin fushi da fusata ""kai kada ka sake kayi min rashin kunya, daman na ga take-takenka dan"

"matsiyacin ba za..."""

"""Kai manaja dakata!"" Alhaji Nura Kwangila ya doka masa tsawa."

"Jikin manaja ya dauki rawa, ya guntse bakinsa da sauri, domin yau dai asirinsa ya tony. Duk yanda ya so"

ya kare abun ya faskara.

"Alhaji Nura yana huci ya kalli ma'aikatan yace ""a cikinku waye ya samu manaja da maganar yana son a"

barshi anan idan har za a dinga bashi alawus din da zai rinka aikawa iyalinsa?

"Kowa yayi shiru ana kallon-kallo. Manaja ya fara hada gumi, ji yake kamar kasa ya tsage ya shige cikinta"

saboda tsananin kunya.

"Alhaji Nura kwangila ya bisu da kallo daya bayan daya yace ""BABU?"" suka yi shiru wanda ya tabbatar"

"masa da babu din kenan. Ya kada kai cikin takaici. ""Na yi matukar bakin ciki da manaja ya aikata wannan zaluncin da sunana. Tun lokacin da kuka cika wata uku na same shi da maganar komawa ga iyalinku. Idan kuma akwai wanda yake da bukatar zama a nan legas ya ci gaba da zamansa, amma sai mutumin nan"

yace min ai duk kun ce a nan zaku zauna indai za a dinga ba ku alawus kuna turawa iyalinku.

"Nace ya ware wasu kudi ya dinga baku dukkan sati, ashe karya ce ya shirga min ba haka bane gaskiyar"

al'amari.

Na ji dadin wannan magana da kayi ahmad ina son mutum irinka da baya tsoron fadar gaskiya duk

dacinta a ko ina yake.

"Kai kuma manaja ka tafi gida na dakatar da kai tsawon wata uku babu albashi, mataimakinka zai maye"

"gurbinka. Kuma dukkan mai bukatar tafiya gidan sai ya fara shiri cikin satin nan sai ku wuce. Sannan albashinku yana nan kamar yadda na gaya muku da karin da nayi muku. Na gode."""

"Manaja ya dafe kai DA tsananin tashin hankali, dakatawar watanni uku babu albashi da me zai dinga"

"ciyar da iyalinsa har wannan lokaci balle kuma kudin da zai nemi mata, domin dukkan abinda yake samu jikin matan banza yake karewa."

"Bayan sanin halin babban manaja da ya roke shi arziki akan yayi hakuri, to ya san ko sauraransa na ba zai"

yi ba.

"Ahmad kam yafi kowa farin ciki, sai ga shi ya fara shirya jakarsa, domin babu komai acikin sai tsarabar"

"kayan ma'u, dukkan abun da ya gani irin na mata ya ba shi sha'awa in dai bai fi karginsa ba sai ya siya mata."

"Isuhu kam yana ta zolayarshi akan yanda yayi magana ga babban manaja babu tsoro, mutumin da kowa"

yake tsoro fa shakkarsa.

"Ahmad bai sanar da kowa zai komo cikin satin ba, domin yana son yayi musu bazata ne kawai."

***

"Ranar asabar da dare suka bar birnin legas, mutum daya suka bari wanda yace shi yafi son aiki a nan"

"legas. Ba su yi mamaki ha domin kowa ya san Magaji Abusa da bin matan tsiya, da shaye-shaye zai fi jin dadin zaman kurmi fiye da arewa."

"Wajen karfe Tara da rabi na safe suka iso garin Kano. Motarsu tana tsayawa yaji wani farin ciki ya cika shi,"

a ranshi umma da ma'unshi kawai yake son gani. Amman kuma yaji ya fi dacewa ya fara zuwa gidan

"Hajiya Amina domin idan ya shantake a gidan umma ba zai iya zuwa can da wuri ba. Idan kuma ta ji ya san zai sha fada, don haka daga nan tasha can ya nufa da lodin kayansa."

"Ta sha mamaki da ta ganshi, dadi ya cikata ta mike yace ""Ahmadu kai ne haka babu sanarwa? Jiya ma"

"can gidanku na yini, koda wasa ban ji sun ce zaka dawo ba"""

"Ya yi murmushi da jin dadin ganinta cikin koshin lafiya yace ""mama so nake na ba ku mamaki, tunda an"

"yi ta sanya lokaci amman bana zuwa sai yanzu ALLAH ya nufa"""

"""Kaga zauna ka sha ruwa ka karya tukunna"""

"Bai yi musu ba ya zauna ya kawo masa abinci da abin sha yaci ya koshi, suka dan taba hira. Ta so ya kai"

"shi gidan ma da kanta sai dai bakin da tayi ya sa ta fasa, sai dai ta dauko kudin mota ta bashi, dariya ta Kama shi yace ""haba mama sai kace wani karamin yaro, ai yanzu ina da kudina"""

"Ta bata rai ""ban son sakarci, ka amsa mana nace"""

"Ya zura hannu ya zari naira ashirin yace ""wannan ta isa na nemi albarka da ita mama, na gode"""

Ya rataya jakarsa ya nufi fita. Ta bishi da kallo tana murmushi.

Sai da ta dawo dakin ne ma tana yiwa bakinta magana ta hango jakar ledar da ya bar mata babba mai

"kyau, ta isa da sauri ta buda, leshi ne mai kyau da takalmi da turarruka, ta kada kai da jin dadi tace"

"""Ahmadu ke nan, babu dama"""

*

*

*

DA ME AKE ADO?

34

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Yana kokarin shigowa gidan ya ci karo DA Amina kanwar raliya. Taci kwalliya duk tayi bilicin ta koma

"kamar wata karuwa. Gabansa ya yanke ya fadi, domin kamanninta da kallonta sun tuno masa da raliya ne, gaba daya ta koma kamar raliya, cikin rawar baki tace masa, ""yaya Ahmad sannu da zuwa"""

"Ba tare DA ya kalle ta ba ya amsa mata da ""yauwa"" ya shige ciki da saurinsa ta bishi da kallo DA mamaki"

"baki bude, gaba daya ya sauya yayi haske yayi kyau kamar ba shi ba, sai ta koma ciki da sauri domin ta bawa babarta labari, ita da kullum take addu'ar ALLAH ya sanya jirgin kasa ko mota ta taka shi ya mutu, ko 'yan fashi su tare shi sun harbe shi domin ta fara kishi da ganin yadda ma'un take komawa kullum,"

kuma a gidan ba a da magana sai ta ahmad. Sai kace shi kadai ne DA a duniya.

"""Lami! Lami!!"" Ta shiga da gudu tana kiranta. Lami ta fito daga cikin daki da sauri tana kallonta. ""Yaya dai,"

"lafiya na gan ki kin shigo agigice kamar an koro ki?"""

"""Lami Ahmad ya dawo"" wanne ahmad kuma? Lami ta tambaya da sauri don bata fatan taji ahmad din"

"gidan ne. ""Ahmad din gidan baba Sulaiman mana, kin ga yanda ya zama kuwa, kuma da wasu manyan jakunkuna WALLAHI shikenan sun gama yin arziki lami kin ga girman jakar jikinsa kuwa?"

"""Oh ni lami dukkan addu'ar da na yi ta tashi a banza kenan sai da yaron nan ya dawo amman muje zuwa"

dai wai mahaukaci ya hau kura.

Ma'u tana durkushe tana wanke-wanke da T. Shirt a jikina da dogon siket ta daura kanta da dankwali

"tana 'yar wakarta ta jiyo sallamar ahmad. Ta daga kai da sauri da mamaki sai ta fasa ihu da jin dadi tana fadin ""Yaya ahmad da gaske kai ne don ALLAH? Ta wurgar da kwanon dake hannunta ta nufe shi da gudu ta kankame shi tana ihu."

"Umma dake kicin tana kokarin dora sanwar rana, ta jiyo ihu ta fito da sauri ta leko. Dadi da mamaki ya"

"cikata, tayi wurgi da ashanar dake hannunta tana fadin ""ahmad kaine da tsakiyar ranar nan haka? Ke sake shi mana kin bi kin kankame shi kamar zaki kada shi"""

"Kunya ta kama Ma'u ta sake shi da sauri, shi kam ji yayi kamar su dauwama a haka. Amman dai ya dake"

ya ajiye jakar hannunsa da sauri ya isa ga ummanshi ya durkusa yana gaishe ta. Umma ta dinga kallonsa cikin farin ciki da jin dadi tana amsawa. Ji take kamar ta goya shi a bayanta don dadi.

Ma'u kuwa ta yi tsaye tana ta kallonsu yayan nata ya canja mata gaba daya.

Yini aka a cikin hidima da murnar dawowar ahmad. Su Ma'u kuwa an kule a cikin daki sai aikin hada kaya

"take yi. Gaba daya gidan umman DA take doki a baya yanzu ya isheta domin shagwabar da take yiwa umma da yanzu ta daina, kuma tana son gwada irin abinda take koya a littafi a gidan mijinta musamman ma girke-girke da ta kware yanzu a kansa."

Umma ta shigo dakin daukar abu ta hango ma'un ana ta hada kaya dariya taso kwace mata amman ta

"dake tace ""Asma'u mene kike yi haka kuma?"

"Babu kunya tace ""umma kayana nake hadawa, ko ba yanzu zamu koma bane? Umma ta rike haba da"

"mamaki tana kada kai. ""Au har zaman gidan namu ya ishe ki kenan?"

"Ma'u ta rufe fuska kunya ta kama ta tana dariya, umma tayi murmushi tace ""ai sai ki huta da hada kayan"

"domin ba yau zaku koma ba, sai an je an gyara gidan"" ta fice ta barta, murnar Ma'u ta koma ciki ta turo baki gaba."

"Shi kansa ahmad abinda yake bukata kenan, ya koma gida ya kebe da matarsa ko hira su yi, amma yaya"

"ya iya da hukuncin umman nasa dole yayi shirin kwanciya a dakin gwaurayen gidan, amma basu kwanta da wuri ba ana ta shan hira."

"Sassafe kafin kowa ya fito Ma'u ta sallara wankanta, sanda umma ta fito domin dama koko taci karo da"

"ita ana shafa hoda da fesa turare. Umma ta rike baki ""na shiga uku Asma'u, ba dai nan shirin tafiya gidan miji kike yi haka da sassafe ba?"

"Malam ya dago labule yana kallonsu bayan ya dawo daga masallaci yayi murmushi. ""To laifi tayi kenan?"

"Ke fa kike mata gori kullum, yau kuma sai ki damu?"

"""Amman dai ta bari a yi karin kumallo ko?"

"Shi ma ahmad tun sassafe ya shirya, ya bawa kowa tsarabarsa sai ta matarsa kawai ya bari a cikin jakarsa."

"Ummansa iri daya ya siyo mata da na Hajiya, sai dai na ummansa ya hada mata da wani babban hijab,"

domin ya san tana son hijab. Shi kuma malam Sulaiman turare mai kamshi da tsada kawai ya samu da takalmi mai kwari. Hatta yaya sani da yaya auwal sai da ya kawo kusu takalma.

"Haka malam jibril ma, ita kanta lami sai da ya kawo mata takalmi kito mai kwari, umma ta hada da lemo"

"da ayaba tace ma'un ta shigar musu da shi. Takaici ya cika Ma'u, yaushe rabon da ta shiga gidansu, amman yaya ta iya, dole taje ta amsa ya nufi gidan."

***

"Su lami suna tsakar gidan, 'yarta amina tana fadin tsefe kitson da tayi mai karin gashi, lami tana gyara"

"mata gashin da ta cire, da alama za a kara yi mata wani DA shi ne. Ma'u ta shigo gidan DA sallamarta mai cike da nutsuwa. Babu wanda ya amsa mata a cikinsu, sai ma binta da suka yi da kallo suna turo baki"

gaba da nuna tsantsar takaicinsu da ita.

"Ta karasa kusa DA su ta mikawa lami kayan dake hannunta. ""Ga shi umma tace a kawo miki tsarabar"

"yaya ahmad ce..."""

"""Ke ba a koya miki gaisuwa bane mara tarbiyya?"

"Ma'u ta murguda baki ""mutanen da ba su iya amsa sallama umarnin ALLAH ba ai ba bukata a gaishe su"""

"Lami ta nuna ta da yatsa tana kada shi. ""A Kul dai kika sake kika zage ni, domin na ga take taketakenki"

"kenan, kina ganin kanmu daya dake ko? To auren naki ai mun san da yanda aka yi shi 'yar karoro kawai"""

"Haushi da takaici ya cika Ma'u da jin abinda lami take fada mata. Zuwa yanzu ta mallaki hankalin kanta,"

"ta san meye kishi da bakin ciki da habaici, ta san magana lami ta gaya mata don haka ta ga gwara ta rama ko ta huce. Don haka ita ma ta dubeta a wulakance tace ""zaman auren karoro ya fi yawon ta-"

"zubar"""

Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta nufi kofar fita.

"Amina ta mike tsaye a fusace tana fadin ""ke karamar 'yar iska, ki iya bakinki ki kuma kama kanki, domin"

"naci uwarki a rashin kunya, banza sakarya. Dube ki kina auren wani banza talaka matsiyaci amman kina hurawa mutane anci, da ba a san asalin barbela ba sai tace daga madina take"""

"""Oho! Ko ma dai meye ai ya fi masu yawo a kwararo an rasa mai tayi balle tayi daraja, 'ya'yan bakin uwa"

"da uba kawai"" tana fadin haka tayi waje da sauri."

"Amina ta kara fusata tayi kofar da sauri, lami ta yi hanzarin rikota tana tirjewa da bakin ciki, ""ki sake ni"

"don ALLAH lami, yau sai na cu uwar yarinyar nan a gaban uwar tata"""

"""Amina kada ki jawo min bala'i ko a baya da kuke yi ma ba ki taba samun nasara ba balle yanzu da ta"

"zama DIYAR GATA ki barta zamu rama cikin ruwan sanyi muddin kere na yawo zabo na yawo wata rana dole za a hadu"""

"Amina ta koma ta zauna tana huci, ba don ta hakura ba sai dai ta tabbatar zata rama wata rana."

*

*

*

DA ME AKE ADO?

35

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Umma da malam suna ta zolayar Ma'u da ahmad da suke ta hada kayansu, suka fice suna dariya. Shatar"

"mota taxi suka dauka har zuwa kofar gidansu. Gidan yayi fututu cike da tsananin kura kamar an yi shekara ba a shiga cikinsa ba, don ma ma'un takan zo duk karshen wata ta gyara shi, ummanta ce ke"

sanyata yin hakan.

Ma'u ta cire gyalenta ta sakale shi a jikin igiya ta fara karewa gidan kallo tana tunanin ta ina ya dace ta

"fara gyaran ne. Ahmad ya bita da kallo tunda ya dawo yake mamakin irin girma da cikar da ma'un tayi, sai kace yayi shekara rabon shi da ita kamar ha ma'unsa ba."

"Kamar ance ta kalli inda yake ta juya tana fadin ""yaya ta ina zan fara ne...? Ta kasa karasa maganar ganin"

"irin kallon da yake yi mata. Ta dauke kanta da sauri, domin ya zuwa yanzu ta sana ma'anar kowanne irin kallo, domin tabkaranta a littafin Nafisa Lili 'Yar Nijar ta fayyace kowanne irin nau'in kallo."

"Shi ma ya dan ji kunya, amma sai ya dake yace ""wannan aiki ya fi karginki kr kadai Ma'u, dole sai na"

"taimaka miki, bari ki gani"" sai ya fara kokarin cire kayansa shi ma yana ajiyewa a kan igiya, ya rage daga shi sai gajeren wando da singileti. Ta kalle shi da mamaki yaushe rabon da ta ga yayan nata a haka, duk jikinsa ko ina gashi kwance lublub, gabanta ya yanke ya fadi, domin har ta gama fayyace surar mijinta, domin ta gani a littafin Lili mai suna MU SAN KANMU MAZA DA MATA kuma da alama mijinta yana daga cikin maza masu kirar zaki ne. Bai kula da yadda take kallonsa ba ya fara aikinsa. Ta sanya hannu suka ci"

gaba da yi tare.

"Sai wajen karfe hudu sannan gidan ya dawo hayyacinsa yadda suke bukata, sun yi butu-butu da kura."

"Shi ya fara shiga bandaki yayi wanka bayan ya fito ya sanya kayan DA ya bari a kan igiya, ya fice domin"

yaje ya siyo musu _Take Away_ saboda yamma tayi babu damar yin girki yanzu.

"Yana fita ita ma Ma'u ta fada wanka, bayan ta fito ne ta fara gyara jikinta da turare masu kamshi, domin"

umma wannan karon bata yi sanya gurin hada mata kayan kamshi da gyaran jiki ba. Wata kila ta fahimci har lokacin ma'un budurwa ce ita. Kafin kace meye wannan tuni gidan ya dauki wani irin kamshi dadi da

tsananin sanyaya zuciya.

"Ta fara duba

31 / 47