Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 47

99K to 102K   out of 139.6K words

""lafiya kalau umma, wani abu na gani ya a soron"

"gidan nan wanda ya daga min hankali"""

"Umma tayi tsaki ta cigaba da cin abincinta tana fadin ""ni WALLAHI har kin tayar min da hankali ma, nayi"

"zaton jikin naki ne ma"""

"Ta tura mata kwanon da take cin abincin. Dambun shinkafa ne da kun un gyada a gefe tana fadin ""ki ci"

"abinci don naga idonki yayi ciki, na san yunwa ce ke dawainiya da ke, wai ni gurin awon ba kwa cin komai ne?"""

"Ta gyara zama ta mike kafafuwanta ""umma muna ci mana akwai kwai da alala amman ni ban iya cin alala"

"sai dai kwan"""

"""Shi yasa kike dawowa a jigace"""

"Umma ta bata amsa tana kokarin mikewa tsaye, ta nufi randa ta debo mata ruwa mai sanyi ta kawo"

mata a kofi ta ajiye a gabanta.

Amma Ma'u ta kasa taba komai saboda takaicin cikin da ta gani a jikin raliya.

"Umma ta fito daga cikin daki ta kalleta cikin mamaki ganin bata ci komai ba. ""Au wai har yanzu baki ci"

"komai ba daga cikin abin dake gaban naki? Ko ruwan baki sha ba"""

"Tayi ajiyar zuciya tana fadin ""umma damuwa ce ta cika ni da takaici. Ko baki hadu da Raliya bane tunda"

ta dawo gidan?

"Umma taja kujera 'yar tsuguno ta zauna tana tabe baki. ""Idan na hadu da ita din ma sai me? Mene ne"

"abin mamaki ko damuwa don raliya tayi cikin shege? Uwarta ce da kanta ta tura ta bariki tace da auren ahmad matsiyaci gwara yawon karuwanci. To ai ga shi nan ta kawo mata lada ko nace tukuici, sai mu ga"

"kuma wanda zata kara yiwa gori cewar shi shege ne"""

"Ma'u ta kada kai cikin damuwa da jinjinawa. ""ALLAH ya kyauta amman WALLAHI raliya ta cuce mu ta"

"bata mana sunan zuri'a, yanzu ace shege zata haifa mana"""

"""Zata haifawa kanta dai"" umma ta amsa. ""Kin ga don ALLAH ki daina yi min maganar mutanen can ki ci"

"abincinki kawai. Shin kin samu ganin likitan ne?"""

"Ma'u ta kada kai ""na samu ganinsa har ya dubani da kansa, kuma yace komai lafiya kalau umma"""

"Ran umma yayi sanyi tace ""Masha ALLAH haka nake son ji. Maza ki gama cin abincin ki shiga ki watsa"

"ruwa ko kya ji dadin jikin naki"""

"Ita dai ma'u kai kawai ta daga, amman hankalinta sam baya tare da ita, domin 'yan magana sun ce"

"_hannunka baya rubewa ka yanke ka zubar dashi_ duk lalacewar raliya jininta ce, kuma KO taki ko taso dole a kirawo raliya 'yar uwarta. Haka nan ma'u ta yini a gidan sololo babu kuzari ko kadan a tare da ita."

***

"Malam jibril ya shigo gidan fakan-fakan ransa a bace, domin bai kaunar ko lekowa gidan idan ba ya zama"

"dole ba, don bai son ganin raliya dake da cikin shege a jikinta wanda yake jin kamar ya harbata ya kashe abinda yake cikin."

"Yana son gayawa dan uwansa amman bai san yanda zai dauki abin ba, don haka ya ja bakinsa yayi shiru,"

amman bakin ciki yana cin ransa da zuciyarsa.

Ya debi ruwa ya zuba a cikin buta ya nufi bandaki DA sauri. Lami ta fito daga cikin daki da sauri ta fara

"kwalla masa kira. ""Malam! Malam!!"" Bai ko kalleta ba ya shige cikin bandaki abinsa."

"Lami ta tsaya turus, ta rike kugu tana masifa. ""Amma wannan wulakanci ne ina maka magana ka min"

"banza ka shige bandaki. To zaka fito ka same ni ina tsaye ina jiranka"" ta cigaba DA tsayuwa tana ta faman mita."

Raliya ta fito daga cikin daki ta sami guri ta zauna ita ma. Malam jibril ya fito daga cikin bandaki ya sami

"guri ya durkusa ya fara alwala. Lami tayi kansa DA sauri. ""Malam wai ko cutar rashin ji ce ta fara shigar ka ban sani ba"""

"Ya daga kai a fusace ""ALLAH ya kiyaye, sai dai ki ga wannan bala'in a kanki ba dai ni ba"""

"""Ni ma din ba zata same ni ba aniyarka ta bika, ashe kana jina kayi min banza. Naga ka sauya hali da"

"lokacin shigowa gidan nan tunda yarinyar nan ta dawo, kaki zama kaji damuwarta sai fushi da kumburi kake yi'"

"Malam ya kuma fusata ya dago kai ya kalli lami. ""Damuwar me zan ji bayan wacce manne a jikinta? Ai ko"

"me ya same fa kece kika sai mata da kudinki, sai ta haifa miki shegen ki raine shi, ba haka dama kike bukata ba?"

"Lami ta daga masa hannu idanunta cike da masifa. ""Tsaya-tsaya malam ka daina kiran cikin diyata shege,"

domin wannan ciki ba shege bane WALLAHI da ubansa'

"Malam jibril ya mike tsaye da sauri ya fasa alwalar yana fadin ""au ko kin daura mata aure ne ban sani ba,"

"wato tayi aure kan aure kenan, laifi biyu akanta"""

"""Babu batun aure kan aure, auren nan dai guda daya shine akanta har yanzu na ahmad, kuma ciki nasa"

"ne ya san da haka shi..."""

Malam jibril ya fashe da dariya yana kallon lami wacce ta fara kuluwa da irin dariyar da yake yi mata.

"Yace ""WALLAHI na yarda lami baki da hankali. Yarinyar da bata tare da mijin nata tsawon shekaru ta tafi"

yawonta amman ta samo cikin shege kice nasa ne. Tana yayi mata cikin ta iska ko kuma ta wayar salular zamani?

"""Ko ma meye cikinsa ne idan kuma baka yarda ba sai kaje ka yi tambaya akan haka. Tunda ta bar gidansa"

"da ciki ta fita wanda ya kwanta mata sai a wadannan watannin ya tashi. Kuma shi kansa ya san tana dauke da cikin, kuma kowa ya san ciki yana kwanciya ko a cikin addininmu da gurin likitocin zamani, za a iya sakin mace bayan shekaru ta haihu in dai ba wani mijin ta aura ba idan cikin ya kwanta, balle ita da bai saketa ba, bacin rai ne ya sanyata guduwa kuma yanzu ta dawo masa da rabonsa, don haka dole ya amsa, idan kai ba zaka iya kwatar mata 'yanci ba ni zan yi. Duk kotun dake duniyar nan na shirya shigarta"

"domin kwatarwa diyata hakkinta"""

Ya tsaya yana kallonta kyar! Yanda ta dage take zuba bayani yayi kama da na masu hankali amman kuma

yana da tantama.

Tabbas mace kan yi shekaru da ciki kuma ta haihu daga baya. Indai da gaske raliya da ciki ta gudu kuma

"Ahmad ya zan da haka to babu makawa wannan cikin nasa ne. Ya dire butar dake rike a hannunsa ya karasa kusa da Raliya dake zaune tana kallonsu yace ""ke raliya ki sanar dani gaskiya, shin da gaske ne kin"

tafi da ciki a jikinki daga gidan ahmad ko karya ce kika shirya kawai?

"Ta karkace baki. ""WALLAHI da gaske ne baba, wannan cikin na Ahmad ne, domin ya san DA shi tun kafin"

"na tafi, ni nayi zaton ya zube ne da na ga ya daina girma, sai kuma daga baya cikin watannin nan naga yana tashi. Idan kuma shi ahmad din ya musa muje asibiti a gwada a gani za a ga jininsa ne a jikina"""

"Malam jibril yayi shiru hankalinsa ya dan soma kwanciya. Idan haka ne lallai ya sami mafita, ya tsira daga"

"abin kunyar da yake tunanin ya shiga a baya. Ya kada kansa. ""Shi ke nan bari na je masallaci na dawo sai mu yi maganar da yaya. Ina zuwa"""

Ya durkusa ya karasa alwalarsa ya fice daga cikin gidan.

"Daidai lokacin da yake fita sai kuma Musa ya shigo ya gansu a tsaye cirko-cirko, yayi tsaki ya dauki buta"

ya nufi bandaki domin bai son kallon raliya shi ma.

"Lami ta doka masa tsawa ""uban wa kake wa tsaki da wannan hararan iye?"" Tayi kansa kamar zata rufe"

"shi da duka. Ya dan dakata yace ""ni fa ba da ke nake ba, shin baki bakin cikin abinda yarinyar nan ta aikata. Banza zata batawa mutane suna. Koda yake hakkin ahmad ne..."""

"""Hakkin ahmad ko kuma rabon ahmad ne? To idan baka da labari bari na gaya maka, wannan cikin dake"

"jikin raliya na ahmad"" ta nuna cikin DA hannunta. Raliya ta murguda baki ta tafa hannu. ""Gwara dai ki sanar da shi ko ya sama min lafiya"""

"Musa yayi jum. Da mamaki sannan ya daure yace ""cikin ahmad kuma kamar yaya?"

"""Ko ma yaya ne zaka ji ai, amman wannan cikin nashi ne, kwanciya yayi sai yanzu kuma ALLAH ya tayar"

"dashi, dole ya amshi kayansa."

"Musa ya waro ido cikin kidimewa yace ""lami haka ta tsara miki kuma? To WALLAHI karya take yi, wannan"

"ba cikin Ahmad ba ne, kada ta sanya ku cikin karyarta da shashancinta"""

"""Sai ka hana cikin ya zama nashi. Kai tsaya na gaya maka, ko kotu zamu je WALLAHI sai ya amshi wannan"

"cikin domin na kula kai ka fi kaunar shi da mu tunda ka taso, to ko ubanka daya da shi a wannan karon kayi karya ka hana shi ansar cikin DA ya san nashi ne"""

"Ta kalli raliya ""tashi mu shiga daki don idan na biyewa wannan yaron sai ya sanya zuciyata ta buga farat"

"daya na mutu"""

"Musa ya bi su da sauri. ""Lami ki tsaya don ALLAH ki saurare ni, kada ku yi abinda zaku sanya mu shiga"

"uku"""

"Lami ta waigo a fusace. ""Idan baka ja bakinka kayi shiru ba WALLAHI zan tsine maka, zan yi maka baki"

"duniya ta juya maka baya baki daya na dak gaya maka"""

Ya tsaya turus da damuwa yana kallonta. Jikinsa yayi sanyi sabodajin abibda ta fada. Ta ci gaba da bala'i.

"""Idan ma na kara jin bakinka a cikin wannan maganar sai na saba maka WALLAHI. Wuce ciki mu je raliya kin ji ko"""

Raliya ta shige ranta yayi fes domin abinda ta tsara ya tabbata. Babu kuma wanda ya isa ya karyata ta.

***

"Su ma'u suna can basu san wainar da ake toyawa ba, sannan umma ta ki bata hadin kai akan su jajanta"

"abin, sai sabgoginta take yi."

Ma'u ta kagu mijinta ya zo ya dauketa ko sa sami damar tattauna matsalar raliyan da shi.

*

*

*

DA ME AKE ADO?

39

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Malam Sulaiman ya dawo daga sallar magriba ya nufi gida da casbaha a hannunsa yana lazimi, ya jiyo"

"kiran dan uwansa daga bayansa yana fadin ""Yaya! Yaya!!"" Malam Sulaiman ya tsaya cak gami da juyowa ya kalleshi har ya karaso inda yake ya mika masa hannu duka gaisa."

"Malam Sulaiman ne ya fara magana ""ina ka shiga ne jibril kwana biyu bana ganin ka?"

"Malam jibril ya shafa keya. ""WALLAHI yaya ina can gurin 'yan buge-bugena, daman ina son muyi wata"

"muhimmiyar magana ne da kai"""

"Malam sulaman yace ""to mu karasa wajen dakalin can sai mu zauna"" suka nufi dakalin dake kofar gidan"

suka zauna dukkansu.

"Malam Sulaiman ya kalli malam jibril yacr masa ""ina jinka jibrilu me ya faru?"" Malam jibril ya gyara"

"tsayuwa yana tunanin ta inda ya dace ya fara bayanin nasa. Can ya nisa yace ""yaya ka san raliya ta dawo gida kwana hudu da suka wuce kuwa?"""

"Malam sulaiman ya dan zabura yace ""raliya kuma?"" Yayi wata doguwar ajiyar zuciya ya kara da cewar"

"""Masha ALLAH yaushe ta dawo kenan?"

"""Yau kwananta shida"" malam jibril ya bashi amsa yana in-ina."

"""Haba jibrilu amman ka kasa sanar da ni tun randa ta dawo din. Amman babu komai tunda ka sanar da ni"

"yanzu, amman ko karo ban taba ci da ita ba tsawon wannan kwanakin da tayi din ba"""

"Malam jibrilu ya ja doguwar ajiyar zuciya. ""Yaya Ina dan fargabar yanda zan gaya maka zuwan nata ne,"

"saboda abinda ke tare da ita, wato raliya dai ta dawo da ciki tsoho, kuma..."""

"Malam Sulaiman ya zabura da rudani yace ""ciki fa kace jibrilu, ciki dai juna biyu na haihuwa?"

"""Ciki na haihuwa yaya, wannan ne ma dalilin da yasa na kasa sanar da kai har sai da na sami hujjar da zan"

"gaya maka, don na san hankalinka zai matukar tashi idan ka ji cikin nata shege ne, amman da yake da ubansa shi yasa na sami karfin gwiwar iya tunkararka har na sanar da kai yanzu"""

"Har lokacin bakin malam sulaiman yana bude da tsananin damuwa a fuskarsa cikin takaici yace ""aure ka"

"daura mata ban sani ba da ya sanya cikin nata ya zama mai uba ba shege ba jibrilu?"" Yanda yake"

maganar ya sanya gaban malam jibril faduwa har yaji yana shakkar fada masa abinda yayi niyyar fada din.

"Sai da malam sulaiman ya kuma cewa dashi ""kai fa nake sauraro jibrilu, kace min cikin nata yana da uba,"

ka gaya min waye uban nasa?

"Malam jibril ya gyara zama yace ""eh ka san lokacin da ta bar gidan mijinta da aurensa a kanta bai saketa"

"ba..."" Yayi dan shiru yana kallon malam sulaiman domin ya ga yanda ya dauki maganar. Sai ya ga ya"

"nutsu tsaf yana sauraronshi, don haka malam jibril din ya ci gaba da jawabinsa. ""Ko ka manta hakan ne yaya?"""

"""A'a ban manta ba, Ina sane da cewar raliya ta gudu daga gidan Ahmad ba tare da ya saketa ba. Ina jin"

"har zuwa wannan lokacin ma akwai aurensa akanta. Amma duk ba wannan ba, yanzu ina son na ji yanda ta sami ciki halattacce ne jibrilu."""

"Malam jibril ya gyara zama yana duban yayan nasa. ""Eh kafin ta bar gidan shi Ahamd din da ciki a jikinta"

"kuma shi Ahmad ma da kansa ya san da shi. To wai cikin kwanciya yayi sai wannan karon ya tashi, shi ne ta dawo gidan don a shaida ya haifar masa abinsa ta ba shi."""

Malam Sulaiman ya shiru yana sauraron malam jibrilu sai yaji kamar ya shakoshi don bakin ciki ya rufe

"shi da duka. Ya rasa dalilin da ya sanya kanin nashi ya maida kanshi kamar tababbe mara hankali idan yana sani zancen. Ya dai daure yace ""bari na tambaye ka jibrilu, tsawon watanni nawa mace take yin"

"idda idan mijinta ya sake ta? Da sauri malam jibrilu yace ""wata uku ne yaya"""

"Malam Sulaiman ya kada kai. ""Ita kuma macen da ta gudu daga gidan mijinta tsawon shekara biyu ko"

"uku ma wanne hukunci ne akanta kenan? Malam jibril yayi shiru yana juya tambayar sannan yace ""WALLAHI ban san hukuncin dake kanta ba sai dai idan malamai sun yi jawabi"""

"Malam Sulaiman yace ""to idan haka ne kaga bai kamata kai tsaye ka danganta cikin dake jikin raliya da"

"na ahmad ba, domin ba sakinta yayi ba balle tace kwanakin iddarta sun cika kuma tana tare da ciki ba"" yayi shiru yana kada kai. ""Amman dai bari nayi shiru na fara jin ta baki shi Ahmadun domin shine hakkin komai ke hannunsa ko nace wajensa. Amman idan ka shiga gidan ka gayawa raliya ta zauna cikin shiri"

"kafin Ahmad din ya karaso"""

"Malam Sulaiman ya mike tsaye yana duban dan uwan nasa ""bari na shiga daga ciki sai an jima"" ya juya ya"

shige cikin gidan ba tare DA yaji abinda dan uwan nasa zai kara fada masa ba.

"Malam jibril ya bishi da kallo gwiwarsa da jikinta gaba daya sun yi sanyi, sai ya mike a zabure kamar"

wanda aka tsikarawa allura ya nufi cikin gidan kai tsaye ko sallama babu.

"Ya fada gidan yayi wuri-wuri da ido bai ga kowa ba a tsakar gidan, sai ya jiyo muryarsu cikin daki, sai ya"

juya da sauri ya fada dakin kai tsaye.

Suna zaune suna sake-sakensu na banza suka ganshi ya shigo dakan kamar an jefo shi. Gaba dayansu

"suka dago kai suka kalle cike da mamaki da fargaba. Lami ta far karfin halin yin magana ""malam lafiya ma shigo babu KO sallama? Amina tayi tsayi gami da murguda baki tana fadin ""ni WALLAHI tsoro ma ya"

"bani"""

"""Tsoron ubanki ja'ira"" cikin fushi malam jibril ya katse amina. Ya kai mata duka ta kauce da sauri ta boye"

"a bayan lami tana haki. Malam jibril ya ci gaba DA bala'i. ""Banda iskanci da raini ace na shigo ana mini tsaki har da murguda baki, kin koyawa yara rashin tarbiyya, dubeki suna jera kafada dake babu kunya ko"

"takaici a zuciyarki sam"""

"Lami ta daga masa hannu da sauri cikin bacin rai. ""Don ALLAH malam ka rabu da ni haka naji da abindake"

"damuna. Don tayi maka tsaki ai ba zai zama laifi ba tubda kai ma baka cika hukuncin UBANGIJI ba na yin sallama da zaka shigo mana, ni WALLAHI tayi mini daidai."""

"""Ai dole tayi miki daidai tunda halin tsiya ya cikata, amman ta cigaba da hi watarana zan karyata gaba"

"daya sai naga abinda za kiyi"""

"Ya mai da dubansa ga raliya dake kallonsa ranta a bace. ""Ke kuma gurinki na zo, ina son ki kara gaya min"

gaskiyar abin dake cikinki na waye don ALLAH idan kika mai dani karamin mutum sai ranki ya baci fiye da yanda kike tsammani kin ji na gaya miki ko?

"Raliya ta zunburo baki gaba ranta a bace tace ""ni fa gaskiya ba fada, cikinsa ne idan kuma ya musa na"

"yarda mu sanya Al-Qur'ani ayi rantsuwa, wanda yayi wa wani karya a tsakaninmu ALLAH ya kona shi tun a duniya"""

Malam jibril ya yi shiru yana kada kai alamar ya yarda da abinda tace. To shikenan sai ki zauna cikin shiri

"don yanzu Ahmadun zai shigo"""

"Lami tayi kwafa ""WALLAHI gwara ya shigo ayita ta kare. Don ina ji ina gani ba zan yarda anuna bambanci"

"tsakanin cikin dake jikin diyata da cikin dake jikin diyarsu ba. Domin shi ma da ne kuma na halak. Dukkan abibda aka yi mata sai an yiwa raliya an biyata dukkan ciyarwar da tayi wa kanta da cikinsa, duk sai an"

"biya ta komai WALLAHI"""

Malam jibril bai kara kulata ba ya juya ya fice daga dakin da sauri ya barsu a nan suna ta surutunsu.

"Amina sai cika baki take yi tana fadin ""banza a banza, ma'un ma ga kuma irin burgar da zata kuma yi mana, don har wani takama da iya yi take yi min wai ita gata mai aure da ciki. Ta manta mijin yayata ta aura kuma saura. WALLAHI banda lami ta hana ni da sai na ci ubanta da cikin nata baki daya, amman"

"daga yau girman kai ya kare, domin mai guri yazo mai tabarma kuma ya nade"""

"Lami ta amsa da fadin ""lallai kam haka wannan batun yake domin dole raliya ta koma dakinta ko ana so"

"ko ba a so."" Ta dawo da kallonta kan raliya dake kallonsu tace ""kina jina ko. Idan muka isa gurinsu ki dage akan kina son komawa dakinki domin kuwa daman kayanki ne dole ta bar miki gidanki, dole ta bar"

"miki mijinki, tunda daman auren cin amana ne aka yi. Munafikan banza Munafikan wofi"""

Raliya tana kallonsu kawai tana ta addu'a acikin zuviyarta akan ALLAH ya sanya Ahmad ya amince har ya

"amshi cikin nata ma kafin aje ga amsar gidan ko mijin nata. Wayarta ta fara ringing da sauri ta kalli

34 / 47