Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 47

39K to 42K   out of 139.6K words

More · 14 Aug 2015

Autan Fazebuk

So masu gari

Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015

Shafiu Shanabash

DAME AKE ADO...?

Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015

Ibrahim Ubali

GD

Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015

Zaharaddeen Abdullahi

muna godiya sosai

Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015

Ummu Suhairat

Sae kuma muka ji shiru wae malam yaci shirwa.

Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015

Abdul Umar Katuka

Meye haka wnnan labari ba kai?

Like · React · Reply · More · 24 Feb 2016

Ibrahim Al-hassan

Naja buk din yahadu

Like · React · Reply · More · 23 Feb 2016

Usman Aliyu Taller

Nice

Like · React · Reply · More · 15 Aug 2015

View more comments&

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

DAME AKE ADO.... 4**6



ya kwanta tausayin ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zuciyarsa har baisan sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa sannan ya daga kai da sauri kamar wanda ya farka daga barci. Nana ce tsaye ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance Sorry hajiya na tafi wani dan tunani ne. Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka baiyi kama dana komai ba bayan na soyayya, ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne? Yayi yake me ya sanya tayi saurin ganoshi? Amma sai ya dake yace waya gaya miki haka? Mubar wannan chapter mu koma ta aikin daya shigo dake.

Taja kujera ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace. Yau ba aiki na shigo yi ba hira ce ta kawoni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don Allah ka gayamini ka taba soyayya Ahmad? Tambayar tazo masa a bazata cikin mamaki yace maiyasa kikayi min wannan tambayar? Ta gyara zama domin nagano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka bazan kaffara ba ban taba soyayya ba, bantaba jinta cikin jikina ba a baya dukkan rayuwata na karar da ita ne haka bantaba surkata da soyayya ba, bantaba son wani ba, hakan ne ma yasa iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman da suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aureni, sunce sai anyi da gaske zai barni nayi aure, su fa sun yarda da hakan shi ya sanya suke lallabani da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa mini nayi aure, don ance musu da sun fada ko sun matsamin zasu iya rasani daga lokacin don aljanin wai zai gudu dani. Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada, tayi ajiyar zuciya ta cigaba da magana. Ahmad babu abinda iyayena ke bukata yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna tsoron fadamin haka, nasan dukkan abinda aka gaya musu na kuma san karya ne, amma na bisu ahaka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban ma taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarar nan shine ya dawomini da rayuwata irin ta sauran mutane wadanda ke dandanar kalma da aman soyayya. Gaban Ahmad ya kama bugawa ganin irin kallon da take masa amman sai ta basar ta kauda idonta daya ciko da kwalla tace ka manta da wannan bani labarin tsohuwar budurwarka ko ita ce matarka ne? Yayi murmushi yana kallonta ta kauda kanta gefe. Yace ke da baki san amo da dandanon soyayya ba yaya kika gane ina cikin soyayya, ko kuma na tuno da tsohuwar budurwata ta da?

Tayi murmushi kuma fa hakane kanada gaskiya. Amma ina zaton na gano hakan ne cikin littattafan soyayya na turawa da nake karantawa ko kuma ayawon kallon fina finansu. Koma dai meye sai ka bani labarin nan yau. Yayi dariya lallai da gaske kin shiga cikin soyayya amman babu abinda zan gaya miki bayan nace miki ummi ce tsohuwar budurwata ta bugomin waya bayan ni kuma na ma,u ne ita daya. Gabanta ya fadi yanayinta ya sauya zuwa damuwa da kyar ta iya daurewa tace wacece ma,un? Ya jingina da kujera yana murmushi tamkar ta masa albishir da gidan aljanna. Yace ma,u ita ce matata, mai sona mai darajani fiye da yanda yakamata ta mini, ban hadata da kowa cikin raina da al,amuran rayuwata ba. Cikin gaggawa da rashin sanin abinda ta fada tace Har ni ma? Shirun da yayi yana kallonta ne yasa ta gano ta fadi wani abun daya jima aranta tana nuku nuku dashi. Sai ta dauke kanta daga kallonsa da sauri ta kalli gefe gabanta na faduwa dakin yayi shiru sai karar A.C da ta bugawar zuciyoyinsu. Ahmad kam addu,a yake cikin ransa Allah ya sanya abinda ta fada bashi take nufin fada ba, amma sai ya jiyo sautin muryarta ya cigaba da fadin. Maza da dama sun soni masu kudi da masu mulki da sarauta, amman bantaba kallon kowa da mutunci ba tunda bansan meye so ba, sai kwatsam watarana naci karo da wani tsageran matashi a gidan mai wanda ya tsaya cikin raina har ya karya tarihin zuciyata, tun ina yaudarar kaina da zuciyata karya takeyi bazan taba son mutum irin haka ba har daga karshe na yarda na sallama ina sonka Ahmad. Ta waigo ta kalleshi yayi mutuwar zaune. Ta cigaba da magana idonta na zubda hawaye Nasan ka jima da gano ina sonka domin na gwada maka abubuwa da dama irin na masoya amman kana basarwa nasan badon komai bane sai don ma,unka! Sai dai ina fatan zanci albarkacin ma,un ka sammin kadan daga cikin son da kakeyi mata

Like· Report·Jun 14

Nusaybarh Mustapha Ibraheem

123. Tana kaiwa nan ta mike tsam da sauri ta nufi kofar fita Ahmad yana zaune kamar an dasashi ya kasa motsawa daga inda yake yana jin kamar bashi bane ba. Ya bi nana da kallo wacce ta kama kofa zata bude har saida ta bude sannan ta kuma yin magana ba tare data waigo ba. Ahmad ka sanya aranka ba karamin abu ne zai sanya mace kamata mai cika da daraja da kyau da arziki ta fuskanci namiji kamarka ta sanar dashi tana sonshi ba. Tana fadin hakan ta fice. Ahmad ya doki tebur ya dafe kansa dake juya masa yana fadin Ya subahanallah! Lallai lokacin barina cikin wannan



So naga kuna korafi dayawa, bari na wakilci@maitama nakarasa muku.



Surayya



10 October 2015 at 11:27 · Public

Save · More

Like

React

Comment

Share

Like26

Write a comment...



·

Jamila Umar Tanko Books

thañk you sury

1 · Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Sarauta Ta

Tnx

Like · React · Reply · More · Yesterday at 23:21

Amina Abdullahi

Good

Like · React · Reply · More · 30 Nov 2018

Mubeenat Muhammad

Muna godiya

Like · React · Reply · More · 30 Nov 2018

Kamaluddeen Sulaiman

Agaida suryy

1 · Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Tahir M. Kaumi

No, pls continue this.

Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015

Abubakar Ibrahim

tnx alot

Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015

Salisu M. Mu'azu Dankado

Him

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Ibrahim M-Gani Yariman Fcbk

Tanx surry

Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015

Usman Aliyu Taller

Mungode

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

View more comments&

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

DAME AKE ADO....4**8



Haka ranar ya koma gida sukuku ba walwala har sai da ma,u ta fahimci yana cikin wani hali, bata matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tuntuni akwai matsala a ofis dinsu, don haka addu,a kawai takeyiwa mijin nata. Duk yadda taso faranta masa ta sanyashi cikin farin ciki ta kasayi dole ta barshi shi daya cikin daki don ta kula abinda yafi bukata kenan.

Nana kam da kyar takai kanta gida domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainihin sashinta ba ta yanke jiki ta fadi kasa. A dai dai lokacin hajiya batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya batula ta fasa kara ta nufeta da gudu tana salati, ta kamata ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka iso kowa a rude jin kiran da hajiya batulun ke musu, ganin halin da nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma. Hajiya batulu cikin kuka take cewa kubani ruwa na yayyafa mata, daga daga cikin matan ta kwasa da gudu sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi.. Hajiya batulu ta karba saboda tsabar gigicewa ma kurzawa nana shi tayi ajikinta gaba daya. Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya batula tayi doguwar hamdala sannan ta kalli yan aikin tana cewa ku taimaka mini ku kamata mu kwantar da ita akan kujera. Suka ciccibi nana aka kwantar da ita ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake abuja. Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali hajiya batulu tace masa Alhaji nana bata da lafiya, yanzu ta fadi har da suma. Alhaji nura kwangila ya gigice yace, suma kuma me ya sameta? Ta kalli nana dake kwance akan kujera tana kallonta tace bansani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi, amma danayi mata magana sai tace babu komai..........Kinga bar bayanin nan haka zanyiwa likita waya yanzu yazo ni kuma zan hayo jirgi na taho yanzu, ki kula da ita kafin nazo. Ya kashe wayar da damuwa a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa kano.

Like· Report·Jun 14

Nusaybarh Mustapha Ibraheem

127. Hajiya batula ta isa ga nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. Sannu nana, meke damunki? Nana ta rintse ido hawaye ya zubo mata , batason tunawa amma bazata taba mantawa ba domin soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, bazata iya rayuwa ba Ahmad ba. Ganin tana hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyarta ta tace shikenan ya isa daina kukan. Mintuna goma baya sai ga likita ya iso gidan masu hidima sukayi masa jagora har cikin gidan da yake kowa ya sanshi a gidan. Hajiya batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin yauwa karaso doctor ka dubamin ita. Likitan ya isa da sauri ya sauke jakarsa da yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala kala. Cikin yan mintuna kadan ya kammala auna nana yayi mata wasu yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti.



11 October 2015 at 16:52 · Public

Save · More

Like

React

Comment

Share

Like26

Write a comment...



·

Salisu M. Mu'azu Dankado

Gud

Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015

Ummu Khadijah Ummu Adnan

Weldon

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Asabe Ali

10x

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Abubakar Ibrahim

pls continue

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Usman Aliyu Taller

Nice

Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015

Dauda Yahaya Masanawa

Madalla

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Adamu Safeeyarh

tnx

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Tahir M. Kaumi

Next pls

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Azinatu Umar

TNX

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Muhd Dawud Rano

Muna tare

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

View more comments&

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

DAME AKE ADO 4**9



daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti, Acikin mota tayiwa Alhaji nura kwangila bayanin sun wuce asibiti, alokacin shi kuma yana cikin airport hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amma ya dake. Dukkan gwaje gwajen daya kamata anyiwa nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan don haka yaja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba. Ana kiran sallahr isha,i alh nura kwangila ya iso garin, kai tsaye asibitin dr musa ya wuce har dakin da nana take ciki lokacin anyi mata wata allurar barci idonta yana rufe, hajiya kuma tanayin sallah. Alh nura ya isa gadon da nana ke kwance ya tsaya yana kallonta sai kuma ya fara lalubar wayar Dr. musa daya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa. Yana shiga Dr. musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi amma bai kula da wannan ba cewa kawai yakeyi Dr meke damun diyata me ya faru da ita? Dr. musa ya jinjina kai yace kwantar da hankalinka alh zauna na maka bayani.

Alh nura kwangila kamar bazai zauna ba amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likitan. Dr. musa ya zauna ya dakko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon alhaji nura wanda ya kagu yaji abinda zaice. Dr. musa ya fara bayani. Da farko na fara yiwa nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau........... Nanar me zai sanya jininta hawa kuma? Alh nura kwangila ya tambaya a gigice. Dr. musa yace wannan shine abinda ke bani mamaki. Sannan yanayin bugun zuciyarta ya sauya yana dudu fiye da yanda ka,idarsa take wannan dalilin ya sanya nace mu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje gwajen, ga mamaki na sai naga zuciyarta ta dan sami matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga musamman lokacin da ta fadi, Allah ya taimaka anyi gaggawar kawota asibiti da wani mummunan abu ya faru da ita. Hankalin alh nura kwangila ya kuma tashi yace. Abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa har akusa rasa rayuwarta? Kwantar da hankalinka alh, wannan ba wata matsala bace insha Allahu komai zai zama dai dai zata dawo dai dai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri. Alh nura kwangila ya gyada kai yana fadin, na gode Dr. bari naje wajen mahaifiyarta. Ya tsare hajiya batula da tambayoyi, abinda ta fada masa yana can kafin yazo shi ta kara fada masa yanzu ma, dole dai su bari diyar tasu ta sami lafiya. Washe gari tunda safe Ahmad ya sami labarin abinda ya faru, hankalinsa yayi matukar tashi, don haka da wuri ya wuce asibitin ya tadda mutane anyi dandazo kama daga kan yan fadanci zuwa dangin hajiya batula dana alhajin, amma ba,a barin kowa ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifan nata ka juya ka tafi. Shima Ahmad din sun gaisa sai dai bai samu ganin hajiya batula ba tana ciki da yake dakin irin na masu kudine har da wani katon falo. Nana tana barci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad. Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da alh nura kwangila. Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyar ta da ke zaune a kusa da ita tayi tagumi cikin sanyin murya tace mummy ba Ahmad ne yazo ba? Hajiya batula tace bansani ba ko kinason ganinsa ne? ta gyada kai alamar eh da sauri hajiya batula ta mike ta nufi falon. Alh nura ya kalleta da sauri ganin ta fito arude yace yaya dai lafiya hajiya? Cikin karewa mutanen wajen kallo tace nana ce tace taji kamar muryar Ahmad wai. Ba wai bane shine yanzun nan ya fita bari na kirashi idon tana son ganinsa ne. Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad bugu daya ya daga har ya tayar da motarsa, amma yace masa ya dawo maza maza nana nason ganinsa. Gaban Ahmad ya fadi yaji kamar kada ya koma din, amma bazai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita daga motar ya nufi dakin gabansa na faduwa yana ta addu,a a cikin ransa. Kai tsaye Alh nura ya shige dashi cikin dakin da nana ke kwance , mutanen dake zaune agurin suka dinga mamakin irin matsayin da Ahmad yake dashi a gurin Alh nura kwangila din daya samu shiga gurin nana. Nana ta kurawa kofar dakin ido dai dai lokacin da Ahmad ya shigo sukayi ido hudu, tayi doguwar ajiyar zuciya murmushi ya bayyana akan fuskarta. Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace sannu hajiya nana, yaya jikin? Tayi murmushi da sauki nagode da kazo dubani ka kula da komai kafin na koma. Azahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi don kamfani da gaske sai dai kasan zuciyarta tayi hakane don ta ganshi kawai. Alhaji nura kwangila da hajiya batula suka kalli juna da mamakin abinda tace.



Surayya



11 October 2015 at 18:02 · Public

Save · More

Like

React

Comment

Share

Like26

Write a comment...



·

Son Guy Bin Abdallah

Ana ahaka

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Salisu M. Mu'azu Dankado

Him

Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015

Son Guy Bin Abdallah

Ana haja

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Tahir M. Kaumi

Next pls.

Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015

Amirah Muh'd

Tnx

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Umar Dahiru

Tnx Alot

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Ummu Khadijah Ummu Adnan

Tnxxx

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Ahmad Sabo

Good. Sury

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Azinatu Umar

TNX

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

Firdaus Feedy Paradise

Dan Allah aci gaba

Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015

View more comments&

Free Mode See Photos

Facebook logo

Go To Home

Jamila Umar Tanko Books

DAME AKE ADO....4**10



Ahmad yayi tsaye kamar bazai tafi ba sai da ya dan jima sannan ya musu sallama ya wuce idonsa ya ciko da kwalla saboda ganin

14 / 47