Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   41 / 47

120K to 123K   out of 139.6K words

ina tunanin yanda muka rabu kamar daman ka gaji da nine abinda nayi maka ina cikin fushi da bacin rai ne Amman kaima ka biye min. Tabbas a wannan lokacin daga ni har iyayena muna cikin fushi na zuga da korafi da ake yi maka sanda muka huce kuma muka tabbatar ka guje min kamar daman ba sona kake yi ba, tunda ka tafi baka taba"

"waigowa ba, me ya sanya Ahmad?"""

"Ta fama masa wani tsohon ciwo da ya jima yana cin ransa gaba daya kamanninsa suka sauya, idanunsa"

"suka fara yin jawur, kirjinsa ya sauya bugu zuwa da karfi ya dai daure ya danne fushinsa yace ""Ummi ya"

"kamata mu bar tuna duk abinda ya wuce, mu baiwa juna wani labarin idan muna da shi ba wannan ba,"

"wannan tamkar fama gyambon da ta jima ne"""

"Tayi ajiyar zuciya gami da cewa ""haka ne amman kai ai baka da wani labari da zaka bani bayan na auren"

"ma'unka da samun cigaba a rayuwarka, sabanin ni Ahmad."

Bayan rabuwata da kai mutane da dama sun yi ta zuwa neman aurena daga karshe dai ni da iyayena

"hankalinmu ya tsaya akan Salim, wani matashi mai ji da kyau da kuruciya, babana yafi kaunar asalin Salim fiye da komai a rayuwarshi, don ya kasance JININ SARAUTA ba da jimawa ba aka yi bikina da Salim. Kamar yadda Salim ke nuna min kauna haka ya dinga nuna min ita a gidansa har tsawon wata guda kafin"

mugayen hakayensa su fara bayyana.

"Duk wani abu da ka sani na bugarwa Salim yana shan shi, ga neman matan tsiya da dan banzan yawo,"

"tun ina boye halin da nake ciki har iyayena suka fara fuskanta don na rame na fita daga hayyacina, bani da kwanciyar hankali sam ga dan banzan duka da nake sha a hannun Salim, iyayesa kuma tamkar kurame, domin sun toshe kunnuwansu daga duk wani kukana game da dansu, sai a sannan na gano"

Salim dan iyayene maras tarbiyya.

"Shekararmu biyar ina cikin wuya da tashin hankali, danmu daya. Kwatsam wata rana Salim ya dawo a"

"buge daga yin magana ya rufe ni da duka har da karaya a hannu, wannan shine ya kawo karshen aurenmu domin na gaji da azaba, iyayena ke tausaya..."""

"Tayi shiru tana maida numfashi, idonta ya cika da kwalla ta cigaba ""shekaru uku da mutuwar aurena na"

"kasa samun wanda ya dace da ni da burikana. Ahmad ka tuno Ummi da soyayyarta cikin ranka?"""

"Gaban Ahmad ya fadu, Ummi ta dawo da shi ruwa tsundum, amma ya dake yace ""Ummi ko kin manta"

"kina magana da Ahmad ne SHEGE dan gidan Asma'u mahaukaciya? To nine yanda kika san ni ba a sauya ni ba, kuma ba a siyo min uba a kasuwa ba. Me zaki yi da shege Ummi?"

"Hankalinta ya tashi ta kankame wayar tana fadin ""WALLAHI ban ga laifunka ba akan dukkan abunda zaka"

"fada, amma ka sani ko mahaifana sun yi da na sanin raba mu da suka yi, don sun gano wani maras iyayen yafi mai uwa da uba daraja da hali nagari. Ka yi hakuri Ahmad ka manta da dukkan abunda ya wuce."""

Yayi shiru bai ce mata komai ba yana ta maida numfashi har sanda muryata ta kara sauya masa tunani

"da fadin ""Ka yafe min Ahmad"""

"Yanda tayi magana ya sanyaya dukkan gabbansa, bai san sanda yace ""na yafe miki ummi."" Wani irin dadi"

"ya cikata tace""na gode Ahmad, fatan zamu dora daga inda muka baro a soyayyarmu?"

"Yayi wani tari da bai shirya ba yace ""Nan fa daya, ai ma'u ce kadai matata a duniya insha ALLAHU."

"Farin cikinta ya gushe lokaci guda tace ""ka yiwa ma'u alkawari ko rantsuwa cewa ba zaka yi mata kishiya"

ba Ahmad?

"Ya kada kai ""ko daya ban taba yi mata wannan alkawarin ba, amman na sanyawa raina hakan, iyayen da"

"suka rike ni suka mai da ni mutum kamar kowa, suka raine ni sanda ban san kaina ba, suka bani aure sanda na rasa shi yaushe zan hada son diyarsu da na wasu matan? Ba zan iya ba koda ma'u ace azabtar da ni take ba zan iya hada ta da kowacce mace ba, balle ina cikin mazan da ke cikin sa'ar aure da iyali a duniya, don haka bana bukatar kari sai dai nayi miki addu'a Ummi ALLAH ya baki wani mijin da yafi"

"mijinki na farko alkhairi da ni kaina."""

"Amman sai ta fashe masa da kuka tana fadin ""don ALLAH kada kayi min haka Ahmad kada kace zaka"

"Rama dukkan abinda na aikata maka, ni mace ce ba zan iya dauka ba"""

"Jin Kalamanta zai iya karya masa zuciya, bayan kuma ya san ko kukan jini zata yi ba zai taba yi mata abun"

"da take bukata ba, don da ma'unsa tayi kuka gara kowacce mace a duniya tayi kukan jini idan an cire ummansa don haka da sauri yace ""kiyi hakuri Ummi sai an jima"" ya kashe wayar."

"Ya koma jikin kujera ya kwanta, tausayin Ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zucuyarsa har"

"bai san sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa ya daga kai da sauri tamkar wanda ya farka daga barci."

"Nana ce ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance ""Sorry Hajiya na tafi wani dan tunani ne"""

"""Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka bai yi kama da komai ba sai na soyayya. Ko ka tuna da"

"tsohuwar budurwarka ne?"""

*

*

*

DA ME AKE ADO?

48

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"Nana ce ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance ""Sorry Hajiya na tafi wani dan tunani ne"""

"""Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka bai yi kama da komai ba sai na soyayya. Ko ka tuna da"

"tsohuwar budurwarka ne?"""

"Yayi yake me ya sanya tayi saurin gano shi? Amman ya dake yace ""waye ya gaya miki haka? Mu bar"

"wannan maganar mu koma ta aikin da ya shigo dake"""

"Ta ja kujera ta zauna ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace ""yau ba aiki ya shigo da ni ba, hira ce ta"

"kawo ni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don ALLAH ka gaya min ka taba soyayya Ahmad?"

"Tambayar ta zo masa a bazata cikin mamaki yace ""me ya sanya kika yi min wannan tambayar?"

"Ta gyara ""domin na gano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka ba zan yi"

"kaffara ba ban taba soyayya ba, ban taba jinta cikin jikina ba a baya, dukkan rayuwata na karar da ita ne haka ban taba surkata da soyayya ba, ban taba son wani ba, hakan ne ma ya sanya iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aure ni, sun ce sai anyi da gaske zai bar ni nayi aure. Su fa sun yarda da hakan shi yawa suke lallaba ni da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa min akan nayi aure, don an fada musu da sun fada ko sun matsa min zasu iya rasa ni daga"

"lokacin, don aljanin wai zai gudu da ni ne"""

Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada. Tayi ajiyar zuciya ta cigaba

da magana

"""Ahmad babu abunda iyayena suke bukata a Yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna"

"tsoron fada min haka, na san dukkan abunda aka gaya musu na kuma san karya ne, amman na bisu a haka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarara nan, shine ya dawo min da rayuwata irin ta mutane wadanda ke dandanar kalma da aman"

"soyayya"""

"Gaban Ahmad ya kama bugawa ganin irin kallon da take yi masa, amman sai ta basar ta kau da idonta da"

"ya ciko da kwalla tace ""bani labarin tsohuwar budurwarka ko ita ce matarka ne?"

"Yayi murmushi yana kallonta ta kau da kanta gefe. Yace ""ke da Bali san amo da dandanon soyayya ba ya"

kika gane ina cikin soyayya? Ko kuma na tuno da tsohuwar budurwata ta da?

"Tayi murmushi ""kuma fa haka ne kana da gaskiya, amman ina zaton na gano hakan ne cikin littattafan"

"soyayya na turawa da nake karantawa, ko kuma a yawan kallon fina-finansu. Ko ma dai meye sai ka bani labari nan yau"""

"Yayi dariya ""lallai da gaske kin shiga cikin soyayya, amman babu abunda zan iya gaya miki bayan na ce"

"miki Ummi ce tsohuwar budurwata ta bugo min waya bayan ni kuma na ma'u ne ita daya"""

"Gabanta ya fadi yanayinta ya sauya zuwa damuwa dakyar ta iya daurewa tace ""wacece ma'un?"

"Ya jingina da kujera yana murmushi tamkar tayi masa albishir da gidan aljanna. Yace ""ma'u itace matata,"

"mai sona, mai daraja ni fiye da yadda ya kamata a min, ban hada ta da kowa ba cikin raina da al'amuran rayuwata ba"""

"Cikin gaggawa da rashin sanin abinda ta fada tace ""Har ni ma?"""

Shirun da yayi yana kallonta ne ya sanya ta gano ta fadi wani abu ne da ya jima a ranta tana nuku-nuku

da shi.

Sai ta dauke kanta daga kallonsa da sauri ta kalli gefe gabanta na faduwa. Dakin yayi shiru sai karar AC

da ta bugawar zuciyoyinsu.

"Ahmad kam addu'a yake a ransa ALLAH ya sanya abunda ta fada ba shi take nufin fada ba, amma sai ya"

"jiyo sautin muryarya na cigaba da fadin ""maza da dama sun so ni, masu kudi da masu mulki da sarauta, amman ban taba kallon kowa da mutunci ba tunda ban san meye SO ba, sai kwatsam wata rana na ci karo da wani tsageran matashi a gidan mai wanda ya tsaya cikin raina har ya karya tarihin zuciyata, tun ina yaudarar kaina da cewa zuciyata karya take yi ba zan taba son mutum irin haka ba har daga baya na"

"sallama na yarda ina son ka Ahmad"""

Ta waigo ta kalle shi yayi mutuwar zaune.

Ta cigaba da magana idonta yana zub da hawaye.

"""Na san ka jima da gano ina sonka domin na gwada maka abubuwa da dama irin na masoya amman"

"kana basarwa na san ba don komai bane sai don ma'unka. Sai dai ina fatan zan ci albarkacin ma'un ka sammin kadan daga cikin son da kake yi mata"""

Tana kaiwa nan ta mike tsam da sauri ta nufi kofar fita. Ahmad yana zaune kamar an dasa shi ya kasa

motsawa daga inda yake yana jin kamar ba shi bane ba.

"Yabi Nana da kallo wacce ta kama kofar zata bude, har sai da ta bude sannan ta kuma yin magana ba"

tare da ta waigo ba.

"""Ahmad ka sanya a ranka cewa ba karamin abu bane zai sanya mace kamata mai cika da daraja da kyau"

"da arziki ta fuskanci namiji kamarka ta sanar dashi tana son shi ba"" tana fadin haka ta fice."

"Ahmad ya doki tebur ya dafe kansa dake juya masa yana fadin ""Ya Subhanallah! Lallai lokacin barina"

"cikin wannan daular ya kusa"""

"Ya koma ya zauna ya dafe kai, ya ma rasa me ya kamata yayi. Kiran wayar ma'u ya cika kunnuwansa"

amman ya kasa daga wayar.

*

*

*

Rayuwa kenan Ahmad wacce ke cike da kalubale mabambanta. Fatan ALLAH ya ba mu ikon cinye dukkan

jarrabobinmu Ameen

DA ME AKE ADO?

49

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing Dan Almajiri

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

Duk kwanakin da suka biyo bayan wadannan cike suke da rudani da tashin hankali ga Ahmad. Matarshi

"ta kasa gano kanshi, da farko hankalinta ya tashi, domin tayi zaton matsalar Ummi ce, sai dai sanda yace mata ta taya shi addu'a wani abu mai girma ke faruwa a ofis dinsu da yake shirin raba shi da aikinsa, sai"

tunaninta ya bar can ya koma kan dalilin da zai sanya a kori mijinta daga aiki.

"Shi ma wannan tunanin bata bashi dama ba addu'a tafi yawa a cikin ranta, domin wannan aikin shine"

rufin asirinsu da shine rayuwarsu da ta yaransu ta sauya baki daki.

Makarantu da kayan da suke sanyawa da jin dadin da iyayenta da 'yan uwanta ke ciki kadai ya isa ta rike

amfanin aikin cikin ranta da kuma yiwa mijinta addu'a akan ALLAH ya daidaita ko ma menene ya cigaba da aikinsa.

Janye hankalin ta daga kan tuhumarsa da takeyi ya taimaka masa kwarai da gaske gurin sauwake masa

"irin tarin matsalolin dake kanshi, domin bata damu da wayarshi ba balle bincikar wayarshi ba da ta ci karo da sakonnin Ummi kala-kala wanda da sun shigo yake gogesu."

"Nana kam bata yi masa sako, sannan ta daina shiga ofis dinsa, sai dai su hadu a hanya ko gurin meeting,"

wannan zuru din da tayi masa shi yake damun sa.

"Game da Ummi kam yayi banza da komai nata har ta fara yin fushi, amma lamarin Nana kam yana daure"

"masa kai kwarai da gaske, ya rasa gane me take nufi da shi. Nata haukan bai kwantar masa da hankali ba sai ma kara tsorata shi da yake yi."

***

"Yau yayi yamma gurin kammala ayyukansa, don har kusan magriba yana ofis, daidai lokacin da ya"

kammala ya fara kokarin tattara kayansa aka turo kofa aka shigo da sauri ya dago kansa ya kallo kofar ofis din.

"Nana ce ta shigo ta dan tsaya bakin kofa tana kallonsa tsawon lokaci, sai kuma ta kada kai ta fara"

karasowa kusa da shi.

Gaba daya jikinsa ya sankame kamar jini bai zagayawa cikin jijiyoyin jikinsa. Cikin ransa addu'a yake yi

ALLAH ya sanya ba waccan maganar zata yi masa ba.

Ta karasa ta ja kujera ta zauna tana murmushi tana kallonsa yayi tsumu-tsumu kamar an tsamo shi daga

cikin ruwa.

"""Da alama baka yi farin ciki da ganina ba ko? """

"Yayi yake cikin borin kunya yace ""waye ya gaya miki haka?"""

"Yanayinka ne ya sanar da ni"" ta bashi amsa a takaice. Bata barshi yayi magana ba ta cigaba da magana"

"""ka kasa gaya min amsar tambayar da nayi maka, na kula ma kamar mun fara wasan 'yar buya da kai, da ka gan ni ma sai ka dinga boyewa kamar baka son ganina. Ahmad na san baka sona..."""

"Cikin sauri yace ""me ya sanya kika ce haka Nana?"

"""Ba ni nace ba yanayinka ne ya nuna haka, ka taba jin wanda ke son abu an kawo masa tallan abun ya"

"kau da kai? Da ace da gaske kana sona ba zaka bari na bar nan ba tare da ka gaya min kana sona ba"""

Tayi shiru idonta ya ciko da kwalla.

"""Wai ace kamar ni mace mai mutunci da daraja na zo ina rokon namiji ya soni, hakan abin kunya ne"

"kwarai da gaske a gare ni"""

"Ahmad ya kada kai ""ba abun kunya bane ba, ko baki ji labarin Sayyada Kadija macen da tafi kowcce mace"

"daraja a duniya, ita ce ta sanar da Manzon ALLAH (SAW) tana son shi ba. Ina ganin wannan ba sabon abu bane tunda ya samo asali daga babban tushe"""

"Tayi murmushi da jin dadin abin da yace ""idan haka ne me ya sanya kake yunkurin watsa kasa cikin idona?"

Ka san ba karamar matsala bace zata sanya na iya fitowa nace maka ina son ka Ahmad. Wallahi mutanen

"dake sona ba zasu kirgu ba, amman ni kai ALLAH ya dora min son ka... Ka ce wani abu Ahmad ko naji dadi a raina, kada ka yaudare ni amman ka gaya min gaskiya"""

"Yayi shiru kansa akasa tsawon lokaci, ta kasa dauke idonta daga kansa. Sai da ya jima sannan ya dago ya"

"kalle ta yace ""Nana WALLAHI tun ranar da naji sunanki ASMA'U sonki da kaunarki suka shiga raina, amman bayan kin furta min kina sona sai naji tausayinki ya dami zuciyata, idan nace miki bana sonki nayi karya, sai dai ba irin son da kike bukata bane, wato ba soyayyar aure ba, ina miki so irin na 'yan"

uwantaka.

"Nana ba zan boye miki komai ba, Ma'u ce kadai matata har abada har karshen rayuwata. Wannan wani"

"alkawari ne da na daukarwa kaina da rayuwata. Kiyi hakuri Nana"""

"Idonta ya fara zubar da hawayen da ya taru, ta kada kai tana zubar da majina tace ""ba zan matsa maka"

"ka soni ba, Sai dai ka sani daga yau har na koma ga ALLAH ba zan taba son wani da namiji ba bayan kai, ba kuma zan auri kowa ba, zan cigaba da rayuwa da bakin aljanin da kowa ke zaton ya aureni"""

Ta mike tsaye tana goge idonta.

"""Na gode... Ahmad... Na gode!"" Ta nufi kofa da sauri idonta yana zub da hawaye."

"Ya mike da sauri yana kiran sunanta amman bata kula shi ba, bata ma tsaya ta saurari abinda zai ce ba ta"

fita ta banko masa kofar ofis din.

"Ahmad ya koma ya zauna da damuwa ya dafe kansa zuciyarsa na tafasa, dama zai iya taimakonsa kamar"

"yadda ta taimake shi da yayi, amman ba zai iya ba, ba zai taba hada son wata 'ya mace da ma'u a cikin ransa ba."

"Haka ya koma gida a ranar sukuku babu walwala har sai da ma'u ta fahimci yana cikin wani hali, bata"

"matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tun tuni akwai matsala a ofis dinsa, don haka addu'a kawai take yiwa mijin nata."

"Duk yanda ta so ta faranta masa ta sanyashi farin ciki ta kasa, dole ta barshi shi daya cikin daki, don ta"

kula abinda yafi bukata kenan.

***

"Nana kam dakyar ta iya kai kanta gida, domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta"

"nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainahin sashinta ba jiri ya dauketa ta yanke jiki ta fadi kasa."

A daidai lokacin Hajiya Batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya Batula ta fasa kara ta

"nufeta da gudu tana salati, ta kamota ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana"

kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka karaso kowa a rude jin kiran da Hajiya Batulan take musu. Ganin halin da Nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma.

"Hajiya Batula cikin kuka take cewa ""ku bani ruwa na yayyafa mata"""

"Daya daga cikin matan ta kwasa da gudu, sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi."

Hajiya Batula ta karba saboda tsabar gigicewa ma zubawa Nana tayi a jikinta gaba daya.

Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya Batula tayi doguwar hamdala

"sannan ta kalli 'yan aikin tana cewa ""ku taimaka min ku kamata mu kwantar da ita akan kujera"""

"Suka ciccibci Nana aka kwantar da ita, ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake"

Abuja.

"Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali Hajiya Batula tace masa ""Alhaji Nana bata da lafiya, yanzu ta"

"fadi har da suma"""

"Alhaji

41 / 47