Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DA ME AKE ADO Complete 1 4 Complete Hausa Novel by Aunty Fauziyya D Sulaiman

Author :  Aunty Fauziyya D Sulaiman Category :  African Stories & Novels

Chapter   21 / 47

60K to 63K   out of 139.6K words

saurin yadda da batunsa har daga fuskarta ya fahimci hakan ta hanyar yin murmushinta tana fadin 'duk abinda aka ce ALLAH magana ta kare tabbas na yadda da batunka amman taimake ni sanar da ni wannan abin dadin'

yayi dariya yana kokarin tattaro farin cikinsa su yi rabonshi tare yace 'danki dai ya sami matar aure kuma

"a wannan ranar dai za a yi ba fashi' ta kalle shi da tsananin murna da mamaki wacce ta gaza boyuwa akan fuskarta tace 'na jima ban ji labari mai dadin wannan ba, alhamdulillah don ALLAH malam wace ta"

sadaukar da kanta da farin cikinta ga ahmad haka cikin sauri?

yayi dariya 'shi lamarin ALLAH haka yake a yanzu muka rabu da dan uwana ya amince da baiwa ahmad

"auren diyarsa raliya kinga asiri ya rufu ko? gabadaya annurin fuskarta ya dauke 'yan sakwanni, takaici da jimami ya mamaye fuskarta har malam sulaiman ya fahimta cikin mamaki yace 'naga kamar bakiyi"

"farinciki da jin wannan labarin ba, wanda nayi zaton ke zai fi yiwa dadi fiye da kowa'"

"tayi yake tana fadin 'tabbas abin farin ciki ne, amman kana ganin idan muka yi wannan hadin mun yi"

adalci malam? yarinyar nan ta gama yawo a kwararo gurin bin maza har ana raderadin anyi mata ciki sun

"zubar shi kuwa ahmad yaro ne nutsattse da bai taba gauraya rayuwarsa da shedana ba, sai nake ganin kamar tafiyar ba zata zo daya ba halin zai zama gambiza'"

"'duk wannan tunanin saida nayi kafin kiyi, amma ki tuna ahmad yana da wani fenti wanda duk kyan"

"halayyarsa al'ummarmu ta hausawa basa yafiya a kansa, idan har ba raliyar ba zai jima bai sami macen aure ba tunda aka fara da haka kin san komai zai iya faruwa a gaba ko fiye da wanda ya faru a baya ma, don haka a ganina auren raliyar shine rufin asirinsa da namu, ki sani duk abinda mace take tana da rangwamen ra'ayi idan ya aure ta zai ita sauya mata ra'ayi zuwa irin wanda yakeso, ki yi kokarin sanya"

albarka kawai'

"dogon bayanin mijin nata ya ratsa ta matuka, har ya sanya ta amince da kudirin nasa, cikin sanyin murya"

"tace 'ALLAH ya sanya haka shi yafi alkhairi. ALLAH ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba amin' farin ciki ya cika malam yace 'yauwa abinda ya dace ki fada kenan umman ahmad' tayi dariya cike da jin dadi da kunya saidai acan kasan ranta ALLAH ya sani bata son wannan hadin, amman ba zata ja da ikon ALLAH"

"ba, zatayi ta addu'a watakila wata rana zata wayi gari taji tana son auren."

"acan gidan su lami rikici ne ya barke sanda mijinta ya sanar da ita abinda yake faruwa, tayi tsalle ta dire"

"tace 'wallahi wannan ba abune da zai taba yiwuwa ba, yaron shege dan mahaukaciya da ba a san asalinsa ba wanda bashi da abin ado za a baiwa diyar tawa gaskiya ban yadda ba sam' malam jibril yayi kasake yana kallonta tabbas shi ma irin ra'ayintane ra'ayinsa, saidai yana tsoro da shakkar ja da yayan nasa don haka ya tattaro dauriya ya hade fuska yace 'kinga lami wannan fa wani hukunci ne da muka"

riga muka zartar ni da dan uwana ba wai neman sbawara nazo gurinki ba'

ta kalle shi da tsananin mamaki tace 'amman mafi kowa sanin yaron nan shegene mahaumaciya ce ta

haifeshi a soron gidannan ko? sannan kuma duk inda yaje neman ba a bashi ko?

malam jibril kada kai yana fadin 'duk nasan da wannan amman ki tuna idan shi shegene to raliya ma tayo

"cikin shegen wanda ALLAH ya taimaka muka zubar dashi, idan kuma har ba wannan damar ba babu sauran wata dama da zamu iya katangeta ko hanata yin wani shegen, kin manta tsahon shekarunta kuma har yau babu wanda yazo da zimmar aurenta na gaskiya saidai abokan iskancinta, ni kam ina ganin wannan ce kadai damar da zamuyi amfani da ita gurin maganin matsalar raliya, kada ki manta tana da kanne mata wadanda muddin suka kara girma suka ga abinda take yi babu abinda zai hanasubin sahunfa su ma' ta kuma hasala matuka 'kawai kace min an zugoka ka tsani 'ya'yanka malam banda haka ta yaya"

zama hada darajar raliya da shege maras dangi. duk lalacewar biyu ai tafi daya wallahi'

banko kofar dakin raliya da shigowarta babu ko sallamane ya katse su daga doguwar tattaunawar da

"suke yi mai zafi. raliya ta kalle su far da idonta sai ta kada kai ta nufi cikin uwardaki ba tare da cewa kowa komai ba, malam jibril ya doka mata tsawa yana kallon agogo yana fadin 'ke raliya daga ina kike sai yanzu kika dawo gida a matsayinki na mace yanzu fa karfe sha daya da rabi nadare' raliya ta juyo a tsaye"

kerere tana kallon mahaifin nata tace 'baba daga zance nake fa'

'zancen ubanki' ya katseta da zafin rai 'duk diya tagari idan goma ta wuce ta kammala zance amman ke

"kikai wannan lokacin baki dawo gida ba, ai ta kusa yin kai ALLAH ya kusa raba yari da barawo, ki sani saura sati guda a daura aurenki na gaji da wannan mugun halin naki' ta kalli mahaifin nata a tsorace tace 'baba aure fa naji kace zaka min nan da sati guda, da wa kuma? sai da ya fara galla mata harara sannan yace 'da ahmadu na gidan nan tunda kin ki fitar da miji kin zauna kina watsewa gwara na aurar dake na"

huta da abin kunyar da kike ja mini'

"kayan dake hannunta ledoji guda biyu suka zube a kasa wanda da alama kayan dadi ne wani ya sai mata,"

"ta dafe kirji gami da kwalalo idanuwa waje tana fadin 'baba ka ji abjnda bakinka yace kuwa, ahmad na gidannan fa ko ka manta shege ne bayan yana matsayin shege mutum mugu azzalumi da baya kaunarmu, anya kuwa baba kaine kake fadin wannan kalamin da bakinka?"

mikewar da yayi a zabure ya kai mata duka ce ta katse ta daga doguwar rshin kunyar da take masa saidai

"tsallan da ta doka tayi gefe da kuma shiga tsakani da lami tayi ne ya hana duka usa ga raliya, ta koma gefe ta fasa ihu kamar wacce aka yiwa shegen duka."

"lami cikin fushi tace 'wallahi ba zaka dokar min diya akan wani shege ba, wanda tunda yazo gidannan"

"dukkan albarkar dake gidan aka dauke ta ba, tun bayan bayyanarsa agidan nan banga komai na alheriba sai bakinciki, yaron da saboda shi har saida aurena ya mutu, ka tabbatar ba ita kadai ke ja da auren ba har da nima bana kaunar wannan auren kuma in dai ina raye wallahi ba za a yi shi ba' malam jibrul yana huci ya kalleta yace 'wallahi karya kike yi ni kuma nace sai anyi shi idan kuma kin ga ba a yishi ba wallahi.saidai ko ni ko raliya wani ya mutu mu zuba ni da ke' ya juya ya fice daga dakin yana huci ransa a"

bace matuka.

raliya ta kuma sanya ihu tana fadin 'na rantse da ALLAH wallahi ko baba zai kashe ni ba zan yadda na auri

wannan shegen mutumin ba. haka kawai saida ya nemi auren wata aka gano shege ne aka hanashi

"sannan ya dawo kaina, me zanci dashi bashi da komai sai tsananin fatara da talauci da suka isheshi, mutumin da bai wuce zama dan wankin gidana ba'"

lami ta dafa kafadarta 'kwantar da hankalinki muddin ina raye babu wanda ya isa yayi miki auren dole

koda hakan yana nufin komai kuwa' da wannan ta samu ta rarrashi diyar tata har ta kwantar da

"hankalinta, suka zauna suka kama cin kayan dadin da ta shigo musu da shi, wanda ta saba kawowa kusan dul dare."

"shi kam ahmad bawan ALLAH bai san wainar da ake toyawa ba, yana can shagonsa cikin tsananin bakin"

"ciki saidai daga baya zuciyarshi ta bashi shawara sanar da ALLAH halin dayake ciki domin shine kadai zai kawo masa mafita, don haka ya fito kofar shagon nashi cikin dare ya daura alwala ya koma ya fara sallah."

*

*

*

haka ake so malam ahmad saboda na tare da ALLAH baya tabewa.

DA ME AKE ADO?

16

Aunty Fauziyya D Sulaiman

(Matar Bello Q for Q)

Typing

ALBISHIR NOVELS

Whatsapp number 08163840712

Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu.

"washe gari da safe ya shigo cikin kananan kaya da kayan aikinsa na gidan man cikin jaka goye a bayansa,"

"don tun daga daren jiya yayiwa kansa alkawarin mantawa da komai, zai fuskanci rayuwar da take"

"gabansa ya kyautatawa iyayensa da 'yan uwansa, sannan zai yi kokarin tara kudi ya koma karatunsa n digiri na biyu, domin yanzu ilimi ne zai zame masa gata abin kima da debe kewa."

"kamar yadda suka saba samarin gidan kowa da kofinsa na koko da robar kosai, don haka kai tsaye kicin"

"ya wuce ya ya fara dauko koko da kosan sannan ya wuce dakin ummansa, a rumfa ya same ta kamar"

"yanda ya saka ran ganinta, ya sami guri ya zauna ya tankwashe kafafu ya ajiye koko da kosan ya kalleta yana fadin 'umma ina kwana? ta kalle shi da kulawa cike da fara'a tace lafiya lau ahmad an tashi lafiya?"

'lafiya umma' ya bata amsa sannan ya fara cin abincinsa suna hira. daga yanayinsa ta kula kamar yayi

"kokarin kauda duk wata damuwa dake ransa, hakan kuma ya faranta ranta matuka, sai da ya kammala"

shan koko da kosan ne sannan ta dube shida kulawa tana fadin 'ka hadu da babanka a masallaci kuwa? ya girgiza kai 'bamu hadu ba ALLAH dai ya sanya lafiya?

umma tayi dan jim kamar ba zata sake magana ba sannan ta nisa tace 'malam ya yanke shawarar hadaka

"aure da raliya nan da sati guda za a kammala komai, hatta sadakinka ya bayar da kayan da aka kawo daga gidan su ummi' ya daga kai a firgice da sauri yana fadin 'umma kinji abinda kika ce kuwa kamar raliya naji kin ambata' umma tace 'eh ita na ambata ina son kayi hakuri, kaji ka ki ji, ka gani kuma ka ki"

"gani, dukkan abinda ALLAH ya tsarawa bawansa shine daidai, ya amsa da biyayya'"

da zai iya abinda tafi dacewa da shi a wannan lokacin sakin kuka ne amman sai ya tsinci kansa yana

murmushi domin yayi alkawarin ba zai kuma batawa ummansa rai ba yace 'na gode umma ALLAH ya sanya hakan shine zai zame mana alkhairi baki daya' daga haka ya mike yana fadin 'umma bari na wuce gurin aiki kada na makara'

"ta bishi da kallo da tsananin tausayi, tabbas tasan bai yi murna da wannan hadin ba amman tsananin da"

"yake musu ya sanya bai musa ba, ta hango shi ya nufi kofa da sauri tace 'a dawo.lafiya ALLAH ya tsare'"

"ya amsa da amin ya fice. kai tsaye kofar gida ya wuce gurin babur dinsa ya fara kokarin tashinsa, kamar"

"ance ya daga kansa sai yayi ido hudu da raliya ta rike kugut tana murguda baki, suna hada ido tayi tsaki ta kau da kai tana taunar cingam kas-kas kamar wata kilaki, yayi tsaki yana kallonta, wannan ce matarsa.wai ita zai aura, ya sha mafarki ya auri mace 'yar asali 'yar dangi mai tarbiyya da nagarta, ya ganta tana yiwa 'ya'yansa rawa da wasa tana koya musu karatun addini ashe duk soki burutsune irin na"

mafarki raliya ce matarsa.

"dogon tsakin da ta kuma jane ya sanyashi hanzarin tada babur dinsa ya haye ya bar gurin da sauri, domin"

"kallon fuskarta yana cigaba da zafafa zuciyarsa, bai kuma san me take shirin fadi ba, domin ya kula akwai magana maras amfani da izgili a bakinta, yaja babur din ya wuce da sauri amman duk da haka saida ya jiyo sautin muryarta tana fadin 'aikin banza wai wannan matsiyacinza a aura mini, wada ke yawo akan babur irin na acaba wallahi an cuce ni' bai bar zuciyarsa ta tsaya yin fashin baki kan maganarta ba ya fara"

tasbihi yana ci gaba da tukinsa.

"yana gurin aikinsa yana ta dura mai cikin motoci da babura, amman zuciyarsa ta kasa mantawa da abin,"

"can ya hango wata yarinya mai sai da goro a gefen gidan man tana ta wasan banza da wani saurayi, ya kura mata ido yana kallo yanda suka taba kama raliya da saurayinta shekarun baya ya fado masa. raliya tasan maza tun tana shekarun kuruciya, shin ta yaya zai iya gamsar da ita, ta yaya kuma zata iya tarbiyyantar da 'ya'yansu, mutumin da bai san waye shi ba ta yaya zai iya sanar da wani kansa, idanuwansa suka kada suka yi jawur can zuciyarsa ta kara zafi, lokacin da wani tunani ya kuma fado"

masa.

"duk rashin tarbiyyar raliya tafi shi tunda tana da asali, iyayanta sunyi kokarin ganin sun haifeta ta hanyar"

"halak, shi kuwa fa? idan har raliya zata yadda ta aure shi ta zauna da shi a matsayinsa na shege shi me zai hana ya kasa hakurin zama da ita da rashin tarbiyyarta, ita za a iya gyarata ta koma mai tarbiyya, shi kuwa har abada ba za a iya sanyawa ko kuma asake nasabarsa ba, shi ne dan mahaukaciya asma'u shege"

mara uba.

"hawaye ya fara zubowa daga idonsa yayi nisa a duniyar tunani, mutumin dayake zubawa mai ya kwala"

"masa kira da karfi 'kai malam kana kula kuwa, na dubu daya nace ka zuba amman dubi yadda ka zuba na dubu daya harda dari uku'"

"da sauri ya kashe dan bututun dayake dura man ya zare shi, mutumin yaci gaba da masifa 'wallahi kai"

asara ta shafa domin ni na dubu daya nace kuma ita kenan garen' ya dagawa mutumin hannu yana fadin 'don ALLAH ya isa malam bani dubu dayan ka wuce'

"mutumin ya mika masa dubu daya ya shige motarsa ya tada ta, shi kuma ya cigaba da zubawa mutane,"

"amman ya san wannan dari ukun sai manaja ya zare ta cikin albashinsa domin komai a lissafe yake, ko man naira daya ya bata kai zaka biya hakan ya sanya suke takatsantsan kwarai da gaske,duk da wasu abokan aikin nasa sukan cuci mutane ma su murde lita din, su dinga rage man idan kace a baka na dari sai a zuba maka na casa'in da biyar a makale sauran na biyar din, idan aka tara sai kaga mutum a rana ya tashi da mai na kusan dubu uku, ya cire kudin ya sanya a aljihunsa, shi kam ya san haka haramun ne shi ya sanya ma baya yi, kuma abindake bashi mamaki bai wuce da sanin manaja ba wani lokacin ma shike kara iza su yin haka, yana kokarin cin halak dinsa ne. amman wani lokaci kudinsa yana shiga lissafi domin akan samu karyewar lita, don haka kusan duk wata sai an cire asarar da aka samu daga albashinsa baya damuwa domin yace da ya cuta gwara a cuce shi, wannan ya sanya yake ganin haske a cikin sana'ar tashi sabanin abokan aikinsa da kullum suke cin haram din kuma basa ci gaba sai shegen cin bashin tsiya da"

"roko, ranar dai saita ALLAH."

***

"ana ci gaba da shirye-shiryen biki gwanin sha'awa, duk da bangaren amarya da ango basa so, hajiya"

"amina ma da ta ji labarin hadin ta damu amman tana ganin hakan shi ne mafita daman tace sai saura sati guda zata ba da tata gudummawar, don haka ta bada babbar gudummawa domin bayan tazo tayi masa"

nasiha ta dauki mukullin gida sukutum ta bashi tace ya zauna har muddin rayuwarsa ta mallaka masa.

"dadi ya cika shi tamkar ya rungumeta, da yasan zata bashi gida ai da bai kama haya har yayi gyara ba,"

"amman babu komai zai bada haya a bashi kudinsa, ya kalleta da farin ciki, da me zai sakawa wadannan mutane irin wannan soyayya.da suke nuna masa tabbas koda shi shege ne yana cikin mutane masu sa'a"

"da ALLAH ke son su, ya dinga godiya umma da abba na taya shi. hajiya tace babu komai ai duk yiwa kaine,"

a take anan ta mika masa takardun gidan sannan tace su tafi shi da auwal ko sani da ita ta nuna musu gidan.

"anyi sa'a sani yana nan don haka tare suka dunguma a unguwar rijiyar lemo gidan yake, bai kuma shiga"

"ciki da yawa ba. abinda yafi burge shi bai wuce kusa da yayi da gidan mansu ba, domin gidan man nasu a"

"kofar ruwa yake. hakan yana nufin ba zai dinga shan wahalar zuwa wajen aiki ba, gida ne mai daki biyu sai shago a gaban gidan da kicin da bandaki ginin talaka dai ya isheshi rayuwa."

"ya dinga kallon gidan da farin ciki, inama ace shi da ummi ne zasu rayu a wannan gida, yanayin tsarin"

"gidan yafi dacewa da zaman masoya domin duk kankantarshi a gyare yake tsaf, duk dakunan an sanya tiles ga fenti ya sha har da su fanka, babu wani abu da zai yiwa gidan."

"sai yaji son ummi ya dawo dal aransa, inama da ita zai zauna awannan gida, yayi saurin kau da wannan"

"tunanin, domin yasan ba abune mai yiwu ba, maganar hajiya amina ta dawo da shi hayyacinsa."

ta kalle shi da farinciki tace 'dana ahmad tun ranar da ka cika shekara guda a duniya na fara tunanin

"wacce kyauta ya dace na baka ta cikarka shekara guda a duniya, sai naga siyan filine kawai ya dace nayi don haka idan ka duba jikin takardar mallakar filin zaka ga da sunanka ma aka siye ta' ya kalli takardar da yana murmushi ga daga kai ya kalleta yana fadin 'anty gashi nan kam, to da ban rayu ba fa? ya karasa"

maganar yana dariya.

"ta kai masa duka tana fadin 'ka ci gidanku, ai kullum nayi sallah sai na gayawa UBANGIJI ya raya mini kai"

har naga aurenka gashi kuwa ya nuna min. dukkan yabo ya tabbata ga ALLAH'

"ya dinga kallonta cike da farin ciki, wadannan mutane suna sonsa matuka, koda bai ga mahaifuyarshi"

"mahaukaciya ba yaga wadanda suka ganta masu sonsa da kaunarsa, ALLAH dai ya saka musu da alkhairi."

"ana ci gaba da gudanar da sha'anin biki abba duk ya raba IV ga dangi da abokansa, abin mamaki har"

"sanarwa ya sanya a gidan radiyo, itama umma ta dauki dukkanin burinta ta sanya akan bikin nan, hakan ne ya sanya ya danne zuciyarsa da damuwar ake gudanar da komai cikin farinciki dum da ba hakan ne a kasan ranshi ba. abinda ya bashi mamaki da tsoro ya kuma sanya raliya fita daga ranshi bai wuce rashin"

mutuncin da tayi masa a soron gidan ba.

"ya dawo daga aiki a wahalce domin yau aikin dare yayi sai yara da rabi suka tashi, ya sako kansa soro yaci"

"karo da ita, sai shi ya janye jinye jikinsa ya bata rai

21 / 47