CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 74

24K to 27K   out of 219.4K words

ganin tana auren mai kuWi mijinta Wan sanda ne, idan suka haWu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta."

"Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa ""Ai nan asalamiyya ke bani labari, ´ar da mariya ta baro,"

"wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ™afarta, na ce ta Wan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun Waukko yarinyar nan"""

"Mama ta ce ""Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ™i, shiyasa muka ™yalesu, ba"

"su da mutunci ko kaWan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ™yale su idan yarinyar ta girma ta nememu"""

"Jimmai ta ce ""Ashsha! To Allah ya kyauta""."

"Mama ta amsa da ""Amin"""

"Mariya ta ajiye ninkin, ta haWa kai da gwiwa ta din ga kuka."

"Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga Wakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce ""Mariya na san kin ji abun da jimmai"

"take faWa, amma ha™uri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini"" shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ™ona zuciya, tana ji a ranta ba zata taSa yafe wa Iya ba."

"An doshi shekaru huWu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta"

"gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haWa mata."

"Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina Worawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa."

"Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka Salle ™ofar Wakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karSe kuWin, wai da su zata tarawa ummi kayan Waki, Wakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi."

"Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ™asansa kuwa ya huje,"

"malaman su, sun gaji sun ™yaleta, ™afarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta."

"Jiki a sanyaye ta ™arasa in da Iya take, ta ce ""Iya laifi na yi ne?"""

"""Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ™wace, kuWina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a Wakin"""

"Gaban Ummi ya faWi, ta girgiza kai ta ce ""Wallahi iya ban Wauka ba, ki sake dubawa""."

"""Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? ˜arya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuWina kan jikinki ya gaya miki"""

"Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuWi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba."

"""Au saboda kin mayar da ni ´ar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuWina ba?"""

"Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba Waya kanta ya kulle."

"Iya ta saSa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ™arasa cikin Wakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuWin."

"Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce ""Ka tambayeta ina ta kai mini kuWi, ka yi ta dukanta, har sai ta faWa"" kan ummi ta"

"ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa ri™e da manyan reshen bishiyar darbejiya."

"Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiWa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita."

"Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ™arfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ™afa."

"""Fito mini da ita daga Waki, Sarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a Waki"" a ™asa haka ya"

"din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida."

"""Ga Wakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuWina"""

"Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a Wakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe Wakin bisa"

umarnin iya.

"Ummi ta kwanta a ™asa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ™afarsa, tamkar ba a jikinta yake"

"ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata."

"Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin Wakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su"

"Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuWi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a Waki."

"Hashim ya ji kamar ya Wora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaWon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri Waya,"

"saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare."

"""Ummi"" ya kira sunanta, ta Wago ta kalleshi ta sunkuyar da kai."

"""Da gaske kin Waukar wa iya kuWi"""

"Ta girgiza masa kai, ya ce ""Na san ba zaki Wauka ba ummi, yi ha™uri taso ki fito"""

"Ta girgiza masa kai ta ce ""Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni"

"wurin mama, wallahi zan mutu"" tayi maganar tana sheshshe™ar kuka."

"Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana i™irarin ta mutu, ""Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun"

"ya cije ki"" Da ™yar ya fito da ita daga Wakin."

Iya kuwa duk ta gama barbaWawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuWi.

"Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka."

"Tana banWaki, Hashim ya samu Iya ya ce ""Iya dan Allah meyasa ba kya ™aunar ummi ne?"""

"""Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ™aunar uwarta ne,"

"kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi"""

"""Ba wannan ba, Iya kin duba Wakin nan da kyau baki ga kuWin ba? Ummi bata taSa yi miki sata ba fa?"""

"""In ji uban wa? FaWa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon Seranya"""

"Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana Wingisa ™afarta."

"Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a"

hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.

"Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi."

"Iya ta watso mata ™ullin kayanta, ta ce sai dai ta koma Wakin itace ta cigaba da zama."

"Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba."

"Da kansa ya share wa ummi Wakin, ya samo buhu ya shimfiWa mata, ya kawo tabarma ya shimfiWa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata ha™uri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka."

"Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ™asan katifarta ya Waukko Wari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce ""Iya ba wannan kuWin ki ke nema ba?"""

"A razane ta karSa tana ™ifta masa ido, gaba Waya ta manta ina ta ajiye su."

"Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuWinta, duk wasu"

"kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi ha™uri, saboda ™arfin hali, har da Murmushin ta, tare da ™o™arin nuna bakomai."

"Da daddare ya sayo gyaWa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ™ara rarrashin ta, ya daWe yana sake kallon"

"Wakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a Wakin, kuma ba za a rasa ™wari masu cizo a ciki ba."

"Ya kalli ummi ya ce ""In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaWe ko"

"ina, ki tabattar babu wani abu a Wakin kan ki kwanta""."

"""To yaya na gode"" ya jinjina mata kai ya fice."

"Iya tana kallonsa daga tagar Wakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ™ular da ita, dan haka"

"tayi ™wafa, tare da aniyar Waukar mataki a kansa."

"Sai dai can ™asan ranta, ta ji babu daWi ganin kuWin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a Waki"

"kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har Waki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta."

"""Kin karya ne zaki tafi makaranta?"""

"Ummi ta ce ""A'a"""

"""Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama"" ummi ta Wan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haWe rai idan"

ta je karSar kunun.

"Ummi ta ce ""Na san idan na je ya ™are"""

"Iya ta bankaWa Wan tofinta, ta ciro naira Wari, ta ajiye wa ummi ta ce ""Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci"""

"Ummi ta kalli kuWin, tana wani irin murmushi da ita kaWai ta san ma'anarsa, ta mi™e tsaye idonta fal hawaye ta ce ""Ki"

"bar shi iya, idan na dawo na ci abincin"" tayi waje."

"Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye."

"""³ar ™an™anuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki"" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya."

"Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ™arasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuWin jarrabawar da ™yar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo"

"ta, take ta yi mata tambayoyi da ™yar ta gaya mata batun kuWin jarrabawar."

***

"Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaWa ya raya, amma ta™i tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke."

"Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huWu kenan rabonta da aure."

"Kuma shekarun nan huWu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba."

"Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ™ara tsananta kaWaice kanta, ga rashin barcci da ya sar™afe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci."

"Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta"

"kasa, ta din ga burgima a ™asa tana wayyo kanta."

"Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan"

"magani, idan ta sha Win ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata ri™e kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai."

"˜arshe aka tura su ganin likitan ™wa™walwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ´an uwanta, jin an tura su"

Sangaren likitan ™wa™walwa.

"Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a"

"kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba Waya."

"Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani Wan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da"

"hawaye, yana matu™ar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya ha™uri, ko sau Waya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta."

"Yaya magaji ya ce ""Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta"

"mu dawo"""

"Maryam ta ce ""A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daWi ne,"

"dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya"""

"Yaya magaji ya ce ""Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ™alau ba, amma zan jarraba zuwa"

"na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai."

"""Zata shekara goma zuwa sha Waya fa yanzu, ai ta zama budurwa"""

"Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi."

"Ummi ta daina zuwa Wakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da"

buhhunan hatsi take kwana.

"Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta Wurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai."

"Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ™ishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a"

"™ofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ™arasa ™ofar gidan."

"Shi ma ™uri yayi da ido, yana kallonta, ta ™arasa ta dur™usa ta ce masa ""Ina wuni?"""

"Jiki a sanyaye ya amsa ya ce ""Ummi kin gane ni?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"""To waye ni?"""

"Maimakon ta bashi amsa sai ta ce ""Ina mama?"""

"""Haryanzu baki manta da ita ba?"""

"Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce ""Da ita ku ka zo?"""

"""A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ™i yarda"""

"Kawu Ilyasu ya wani haWa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce ""Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida"""

"˜afafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya Waukarta ba"""

"""Ba zaki tashi ba?"" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya dan™a mata"

"kuWi, yana ri™e da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce ""Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ´ar Wan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ™afafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faWa, Allah zai zama gatan marainiya"""

"""Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka""."

"""Wai ba zan sake ganinta ba?"""

"""Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki"""

"Rirri™e hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita."

"Da ™arfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida."

"Tana kuka suka ™arasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana Waga murya tana cewa ""Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini Wa suna bibiyata saboda"

"´ar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaWan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karSi ´ar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ™ara tuburata, yadda ta rabani da Wa na babu ita babu sukunin duniya!!""."

"Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai "

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

arewabooks ayshercool7724

Watpad ayshercool7724

Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

P7

"A guje mama ta koma tsakar gida, tana ™walawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi."

"Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo ma™wabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti."

"Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ™afar ummi, ya ™arasa"

"da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi."

"Wani irin ba™in ciki ya turnu™e masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke"

"iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar Wan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba."

"Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa"

"dukan tsiya, sannan ya Waukko ummi ya shiga da ita gida."

"Gaban iya ne ya faWi ganin yadda ya shigo da ummi, ta mi™e tana faWin lafiya?."

"""Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"""

"""Saboda iskanci, me tayi masa?"""

"""Oho masa"""

"""Kema uban waye ya ce ki fita?"" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye."

"Ya ce ""Dan Allah iya ki yi ha™uri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaSi"""

"Ya karkaWe mata ™asar nan, ya samu ruwa ya din

9 / 74