CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 74

15K to 18K   out of 219.4K words

bayan mace ko dan ba ™ara ta kawo ba, zahiri suka gani, dan maryam ta labarta musu komai, har da yadda ake muzanta ummi, da cewar da iya tayi, wata™ila Wan ta ma baya haihuwa, saboda su kaf danginsu babu kalar ´ar, daga baya kuma ta ce ita zata ri™e ta."

"""Ai ban san mutanen kawai bane na basu ´a ta, dattakun yaron da nutsuwarsa ce ta sanya haka, ina da ya™inin zuriyata babu lalatacce, kar wanda ya kuma bi ta kan yarinyar, ku ™yale su da ita, ke kuma idan kin gama takaba,"

"Allah ya kawo miki miji nagari""."

"A Sangaren mariya ba ta ji daWin wannan goyon baya da aka yi mata ba, mussaman yadda ´an uwa suka goya masa baya, a kan yanke al™arsu da in da ummi take, ita a ganinta hakan ba masalaha ba ce, ita da ummi meye nasu a ciki."

"Babu bakin magana, haka tayi shiru sai bin su da ido, ta ™are ta shige uwar Waka, ta dur™ushe a kan gwiwoyinta, ta din ga rusa kuka, ita ma meya rage mata na bashir da za ta kalla ta ji daWi ban da ummin? Ta din ga kuka, zuciyarta"

"na wani irin zafi, ji take kamar duniya babu wani abu da ya tage mata da zai sanyata farinciki, mahaifiyarsu ta rasu, yayyenta duk sun yi aure, sai ™ananan ™annenta da matar babansu, dan ma mutuniyar kirki ce."

"Washegari da asuba, iya ta idar da sallar asuba, ummi na ™asa a du™un™une a cikin hijjabinta a ™asa, ko zani ba a"

"shimfiWa mata ba, ba wanda ya kai ta tayi fitsrai, ta saba sai mariya ta kai ta tayi fitsari, kan ta kwanta, dan haka ta yi wa iya fitsarin kwance."

"Kamar zata daki sa'anta, haka iya ta ta™ar™are ta Walawa ummi duka, a gigice ta tashi tana sosa wurin, saboda zafi."

"""Dan ubanki fitsarin kwance ki ka yi mini saboda sangarta?"" Dubawa ummi tayi ta ga fitsarin tayi, ta yi shiru ta kasa"

"magana, sai hawaye."

"""Au kuka ma ki ke yi mini, saboda sangarta da iskanci, zan yi maganinki, fita ki Webo ruwa a randa ki zo ki zuba"""

"Da sauran duhun asuba, dan haka ummi tsoro take ji, ta fito waje ta tsaya tana kuka."

"""Ba zaki wuce ba, sai na zo"" ta jiyo muryar iya. Cikin sauri ta je ta Webo ruwa, garin sauri ta koma Wakin, ta faWi"

sassanyar ruwan randar nan ya she™e mata a jiki.

"A gigice ta yi wata irin ajiyar zuciya, tana kyarma. Ta tashi da guntun ruwan a moWa, ta shiga ta zuba a wurin, kamar"

"yadda iya tayi mata umarni, ta dawo Wakin ta tsaya."

"Iya ta kalleta ta ce ""Munafuka, shi ne ki ka zuba ruwan a jikinki, sai ki cire kayan ki saka wasu, ga tsummokaranki"

"can""."

"Cikin rashin wayo, ta kwance kayan, ta saka uniform Win ta, dan ta san ranar monday ce, ta tattara kayan fitsarin, ta"

"haWa su a cikin masu kyan ta Waure, dan kuwa mama ta hanata zubar da kaya ko ina."

"Ta juya ta kalli gabas tayi salla, ba tare da tayi alwala ba, dan da ruwan Wumi take alwala da mama tana nan, dan"

"haka ta zata idan ba ruwan Wumi, ba sai ka yi alwala ba."

"Gari yayi haske, ta je gaban murhu, ta saka hannunta ta dangwalo toka, ta cuccuWa bakinta, ta kuskure ta koma"

"Wakin iya, tana jiran iya ta bata abinci."

"Aka kawo wa Iyan kunu mai zafi, amma ta kalli ummi, ya ce ta Wauki tuwon jiya ya cinye, dan ba za a zubar ba."

"Miyar karkashin ce ba ta so, dan haka ta sake jagwalgwalawa, ta ajiye ta fito tsakar gida, tayi ta kallon ™ofar Wakin su,"

"ta ™arasa ™ofar Wakin tana ™wan™wasawa, wai ko mama zata buWe, sai da ta gaji, kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaWata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita."

"""Ke daga ina?"" Malamar da take ajin su ta tambaye ta."

"""Gida"" ta faWa a ta™aice."

"""Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?"""

"Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce ""Mama ce bata nan, ba ta dawo ba"""

"""To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda"

"zata aikatau ba makaranta ba"" ´an ajin suka kwashe da dariya."

"""Silent"" malamar ta tsawatar tana kallon ™afar ummi, da kamar an ciro ta daga ha™a rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ™asan farin hijjabinta, tana goge hawaye."

"""Wuce ki je ki zauna"""

"Ta nufi wurin zamanta, can wuri Waya, ta cigaba da sheshshe™ar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ™asa²"

"yana cewa ""Ba™ar tukunya, yau an shafeta da toka"""

"Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa"

tana nemanta.

"Ummi kuwa da ™yar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu'a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke Wora girki, shi"

"ma babu komai a wurin, ta kalli ™ofar Wakin su, Wakin dai a rufe."

"Šakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba."

"Bacci ya Wauke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, ""Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta"

"yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya."

"""Makaranta na je"""

"""Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?"" Ummi ta girgiza kai."

"""Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai Waga mini hankali ba, balle ke"" ummi dai tayi shiru ba ta ce"

komai ba.

"Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci."

"Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na'ima, ta zo tafiya da ita, Naima ´ar Wakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ™wace ummi. Ta"

"tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye."

"""Iya na zo tafiya da ummi makaranta"""

"""Gata nan, sai kun dawo"" iya tayi maganar tana nuna ummi a wula™ance."

"Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga ji™a™™un kaya a ciki."

"Ta ce ""Ummi, na ji kayan ki a ji™e?"""

"""Fitsarin kwance na yi ban sani ba"""

"""To ki daina haWa su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu"""

"Ummi ta saka mata kuka ta ce ""Yaushe mama zata dawo?"""

"""Ki yi ha™uri, nima ban sani ba, amma za ta dawo"" ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta."

"Kwana Waya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ™afa, ta koma gagarawa, ta Waukko ´ar ta, duk sallar da tayi,"

"bata iya addu'ar komai, sai ro™on Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta."

"A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana Wauke da"

"juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki."

"Da suka koma gida, aka din ga yi mata faWa, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun"

nan.

"Watanni huWu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma"

"tafi samun sau™i da sassauci, a lokacin da mariya tana nan."

"Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ™yar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform Win nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi ta™i yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta."

"Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata"

Sarnar mai.

"Wanki kuwa, sai idan na'ima za ta yi nata, sannan ya ta haWa da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa,"

sai dai tayi ta yawo cikin dauWa.

"A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin"

"zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta ha™ura."

"Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta Wauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka"

"mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta ji™a jikinta da ruwa buta Waya."

"Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken"

"nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ™oshi da wanda iya take bata."

"Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuSe"

"ummi, ta ce ya zane mata ita."

"Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya Wauke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya"

ce idan ta sayo ta kai masa Wakin su.

"Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raSe-raSe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciSis da ummi a soro ta ce ""Ummi, tun Wazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara,"

"amma shi ne baki taho ba""."

"""Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa Wakin su""."

"""Šakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki"

"kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa Wakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki"" ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karSi omon ta ce ""Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma"""

"Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci."

"Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa Wakinsa a"

samarin gidan.

"Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala'i."

"""Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?"""

"Naima ta ce ""kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara"""

"""Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini sa™ona?"""

"""Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka"

"Wakin ka"" nan da nan bala'i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya."

"Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris."

"Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuSe tana kuka."

"Naima ta ce ""Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza"

"kawai"" iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima."

"Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya sha™o ummi tare da lu™a mata wata irin ashar. ˜ara tayi"

tana kakari.

"""Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai"

"na kashe ki"" ya jefar da ita a wurin, ta ri™e wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata."

"Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga Waki, tana ™o™arin fita, mama wadda take matar"

"babansu, ta ri™e ta, ta ce ""Mariya lafiya ina zaki?"""

"""Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ™ofar gida fa"""

"""Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?"""

"""Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji"""

"Mama ta ce ""Iya kuma, nice fa mariya"""

"Mariya ta yi ™uri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba Waya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata."

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

"Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce ""Ki yi ha™uri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya Wauke ni na ga ummi"""

"Mama ta ce ""Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa"""

"Mariya ta amsa da ""To"""

"""Ki din ga yi mata addu'a, Allah zai tsare miki ita"" gyaWa mata kai kawai ta yi, ta koma Waki."

"Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin sha™ar da ta sha."

"Iya ta ritsuta a Waki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na'ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai,"

tana tsoron kar ta dake ta.

"Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daWi, ta yi wanka, ta sanya cukurkuWaWWun uniform Win ta, dan ma an yi sa'a a wanke suke, dama na'ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi."

"Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta Wau kofinta, ta je sashin sa'adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta."

"Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji."

"""Baki tafi makarantar ba ne?"" Ta jinjina masa kai."

"Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki."

"""Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?"" Ta jinjina masa kai."

"Ya karSi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya mi™a mata kunun cikin kofi."

"Har ™asa ta tsuguna ta karSa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji."

"Ta shanye ya karSi kofin, ya bata naira ashirin, ta karSa ta ce ""An gode"""

"""Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki"" ta ce ""To"""

"Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ™oshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaWi."

"Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ™azanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta."

"Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala."

"Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buWe jakarta da yanzu a ba™ar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace,"

"fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama Wan mitsitsi da ™yar take iya ri™e shi ta yi rubutu."

"Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna."

"Ya dubi malamarsu ya ce ""Malama, yara biyar zaki zaSo mini masu ™o™ari, zamu tafi da su gidan talabijin, za ayi wani"

"shiri da su, a haska su"""

"Malamar ta ce ""Ok sir, yanzu kuwa"""

"Ta tashi ta kira yara uku, ta huWu ta kira sunan Salma Muhammad Bashir."

"Wani irin farinciki ya kama ummi, saboda malamarsu ta zaSeta a cikin wanda za a tafi da su gidan talabijin na"

"jigawa, tana ta murna za ta ganta a talabijin, dan duk da rashin kulawar nan, ummi tana da matu™ar ™o™ari, in dai aka yi darasi a gabanta, to ta Wauke."

"""Ke!ke tsaya"" headmaster ya dakatar da ita a tsakiyar aji."

"""Wannan kuma ina zata?"""

"Malama ta ce ""Sir, yarinyar na da ™o™ari fa, ita ce take first position"""

"""A hakan, wannan yarinyar da ya take karatun,? Ba ita ake kora ba ba ta biyan kuWin PTA, da yaya take iya karatun"""

"Ta ce ""A haka, ita take ta Waya?"""

"""Kai canza wata dan Allah, haba wannan tayi muni da yawa, wannan ko an saka mata camera ai ba za a ganeta ba,"

"ba™i ™irin da ita haka, ji uniform Win ta fa, tubarkallah ni wannan tayi ba™i samo wata mai Wan kyan gani, ke koma ki zauna ba za a tafi da ke ba, ji kayan jikinta kamar ´ar ci rani"""

"Tuntsirewa da dariya da yaran suka yi,hakan ya bawa hawayen idonta ™warin gwiwar zubowa, ta tafi lungun aji ta zauna, tana share hawayen."

"Tana gani aka zaSi wata daban, bayan malamar ta fita, suka Wora da yi mata dariya da tsokanar ta, har da masu ja mata hijjabi, suna ™azama ba ta wanka ba ta wanki, wa™ar da aka saba yi mata a assembly idan an zo duban tsabta,"

"har misali ake yi da ita, na ™azamai."

"Ana tashi ta fita daga aji, ta nufi gida har da gudunta, dan kar ma ´an ajinsu su taso, su tireta a hanya, ta ™arasa tana ta numfarfashi."

"Sai da ta Wan huta sannan ta shiga sashin su da sallama, muryar iya ta fara jiyo wa tana hayaniya, da muryar baba saminu, ba ta san dai faWan me suke yi ba, ta kutsa kai ta shiga."

"Wan mahaifiyarta ta gani, a zaune suna ta jayayya da su iya."

"Hayaniyar da suke yi, ba ita ce ta dame ta ba, murnar ta Allah ya sa da mama suka dawo."

"Bai lura da ummi ba, sai da ta ri™e hannunsa, ya waiwayo ya kalleta ta ce ""Ina maman take?"" Yayi ™uri da ido yana kallon ummi, sai ka ce ba ´ar mutane ba."

"Yadda mariya ke ™al™aleta, take kula da ita, amma ya ganta kamar an janyota daga ramin ™asa."

"Ya ce ""Baki gaishe ni ba"" ta tsuguna ™asa ta ce

6 / 74