CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 74

81K to 84K   out of 219.4K words

ce ""Mass communication"""

"""Mass communication, ai karatun masu baki ne, ke kuma kamar ba kya magana ma"""

Ita dai tayi shiru ba ta ce masa komai ba.

"Ya bata wayarsa ya ce ""Saka mini lambar ki, sai na turawa maryam, ku dinga gaisawa, zumunci abu ne mai kyau""."

"Wayar ta sa zueiya mai kyan gaske, ta saka masa lambar ta mia masa."

"Ya ce ""Masha Allah, to nima za a din ga zumuncin da ni? Tun da aninki ne ni?"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""To"""

"""To yaya ummi na gode sosai, sunana Muhammad Raihan"""

"Ta ce ""Ai na sani"""

"""Ai tuna miki na sake yi, ranar da muka haWu mun kusa yin faWa, ashe kin sanni nine ban gane ki ba"""

Tayi murmushi tana sake gyara zaman facemask Win ta.

"""Ki rage saka niabin nan da facemask, idan ba haka tayaya mutum zai gane ki, you are lucky ina da saurin gane"

"mutane ma, da mask Win na gane ki"""

"Ummi dai ba baki, dan dama can ba mai hayaniya ba ce, sai murmushi da take yi."

A bakin titi ta ce masa zata sauka.

"Ganin ya takura mata, ya sanya ya yaleta, ta buWe motar ta waiwayo ta kalle shi ta ce ""Na gode sosai"""

"""Nima na gode ki gaida gida"" yana kallonta cikin dabara ta ajiye masa ruwa da lemon da ya bata ta fice."

"Raihan ya taimaketa da ya Waukkota, ba dan haka ba, sai ta ci uwa tafiya, kafin ta hau mota, dan kuWin motarta ba"

yawa a jakar.

"Har ta shiga gida, jikinta amshin turaren raihan yake yi, kasancewar gaba Waya motar ma amshin turaren take yi."

"Yana zaune a motar ya kira lambar ummi, tana sauri zata shiga gida, wayarta ta fara ringing, ta ciro wayar ta Waga tana hello."

"Kashewa yayi jin muryarta ce, yayi saving number da brown eyes."

Ummi ta shiga gida tana fatan Allah ya sa ba wanda ya ganta ta sauka daga motar raihan.

"Bayan sallar isha'i maryam ta kira ummi a waya, tare da yi mata ciwon bakin bata nemanta."

"Sosai suka fara hira da ummi, sai dai hirar ta daina yi wa ummi daWi, lokacin da maryam ta fara yi mata zancen ita"

yaushe za ta yi aure? Ummi ta arare hirar suka yi sallama.

***

GAGARAWA

"Masifa da bala'i a gidan idris, kamar karnuka tun mawabta na shiga cikin lamarin, ana oarin sasant al'amura, abu ya gagar a gaban yaran suke faWa, suyi ta zage-zage da ashar kamar maguzawa."

"Yarinyar sa ga fari kuwa, tun da aka je da ita family house, aka yi mata gori, Hindu ta wanke afa taje har gidan tayi musu tijara da rashin mutunci."

"Babu wanda hindu take saurarawa a dangin Idris, tun daga kan Iya har sauran mutanen gidan."

"Dan haka Idris ya fara tunanin ara wani auren, ko ya samu sassaka daga masifa da bala'in hindu, gashi kamar tayi masa asiri, duk tijara da bala'in da zata yi masa ba zai iya sakinta ba."

"Hashim kuwa ya kasa samun nutsuwar samun matar aure, saboda gaba Waya hankalinsa a kan ummi yake, sai dai iya"

"tayi masa kandagarki, dan ta riga ta ce ba ta lamunce ba, dan haka ya san ko giyar wake ya sha, tun da iya ta furta ba ta so, babu mai goya masa baya."

***

"arfe kusan goma na dare, Ummi ta yi wanka tana shirin kwanciya bacci, dan washegari asabar ce, za ta je islamiyya da safe ta koyar da yara, dan haka da wuri take son kwanciya dan ta kammala aikinta da wuri ta tafi da safe."

"Kallon bauwar lambar take yi, sannan ta Waga tayi sallama."

"Ba ta Wau muryarsa ba da farko, dan haka gabanta ya faWi, ko bisa tsautsayin wrong number, wani namiji bai taSa"

kiranta ba.

"Sai da ya ce ""Yaya ummi"" sannan ta Wau muryar."

"Ta ce ""Au babban mutum, yanzu na Wau muryarka ai""."

"""Ke, Alhajinmu ne fa kawai yake faWar sunan da ki ka faWa, sai Hajiya, waye ya gaya miki wannan sunan?""."

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""A bakin maryam na ji, kuma ai sunanka babbane, ba a faWarsa anyhow"""

"""To sai ki ce Raihan ai"""

"""To shikenan, ya mami da su Hajiya?""."

"""Suna lafiya, ta kira ki kuwa?"""

"""Eh mun yi waya da ita, ka kyauta ai""."

"Ya ce ""To Allah ya haWamu a ladan baki Waya"""

"Ta amsa da ""Amin ya haiyyu ya aiyyum"""

"""Ya aikin?"""

"""Aiki Alhamdilillah"""

"Ya ce ""Masha Allah, kiranki nayi na kwashi gaisuwa kawai, tun da mun yarda mu yi zumunci, tun da maryam ba ta"

"nan, sai mu mu din ga yin zumuncin. Dama bani da abokai na yi awa, awar yayata ta zama awata""."

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""Mace da namiji ba sa awance ai, anina ne kai""."

"Yana daga kwance ya tashi zaune ya ce ""To shikenan, muje a haka yaya ummi"""

"Tayi murmushi ta ce ""Sai da safe""."

"Ya ce ""Allah ya tashemu lafiya yaya, sweet dreams""."

"Ummi ta ajiye wayar tana cigaba da murmushi. Ta bi wayar da kallo, anne suna da daWi, ta so ta rungumi su intee"

"kamar anneta, amma suka nuna mata ba haka ba, shima Abdul alaarsu farida ta saka musu ido, da ta gansu tare sai zagi da cin mutunci."

"angaren Raihan ma, wayarsa ya bi da kallo, yana kallon lambar ummi da ya sakawa brown eyes, sanyin halinta ya"

"burgeshi, abun da mami ta gaya masa game da ita, ya sanya masa tausayinta, dan haka yake jin ko na ananin lokaci ne, zai shiga rayuwarta ya fahimci ta ina zai taimaketa, kuma zai yi mata addu'ar samun miji nagari mai aunarta."

"A rayuwarsa ummi ce mace ta farko da ya ji yana son shiga rayuwarta, idan ba iyayensa ba sai an uwansa mata, ba"

"ruwansa da shiga harkar kowacce yarinya, duk da suna yi masa shishshigi, saboda Raihan kyakykyawa ne kamar maryam, kamar sa Waya da mahaifinsu."

"Washegari tana makarantar islamiyya, tana fama da Walibai, kusan arfe goma da rabi, ta sake ganin kiran Raihan."

"""Ina kwana yaya"""

"""Lafiya alau, ka tashi lafiya?"""

"""Lafiya alau, ya nake jin hayaniya kina ina ne?""."

"""Na je islamiyya, ne ina tare da Walibai"" ."

"Ya ce ""Ok, ashe sayyada ce, mu yi waya idan kun tashi, dama kira na yi idan kina lafiya"""

"Ta ce ""To godiya nake, Allah yayi albarka"""

"Yayi murmushi ya ce ""Dan Allah ki saki muryarki ki daina iyayi"""

"Dariya ce ta kamata, ta ce ""Ka cuci iyayi kuwa"""

"""Am serious, na yi recording wayar nan, zan tura miki ta what's app ki ji yadda ki ke magana, sai anjima take care"""

yayi maganar a hankali.

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P23

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur

Gab Gab

Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha

Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

23

"Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faWar Raihan rigiamamme ne."

A Sangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi.

"Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banWaki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita."

"Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka."

"Ya buWe foodflask, ya tarar da doya ce da wai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai."

"Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye Sangaren mahaifinsu ya wuce."

"Yana zaune yana shan tea, gefen sa aton tray ne, Wauke da kayan marmari yana kallon labarai."

"Ya Waga kai ya kalli raihan ya ce ""Dama kana gidan nan?"""

"Raihan ya arasa kusa da shi ya risuna ya ce ""Barka da safiya"""

"""Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?"""

"Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin."

"Ya ce ""Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ara fresh sosai"""

"Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce ""Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi,"

"haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci""."

"Cikin kulawa raihan ya ce ""Ka yi hauri, ka daina damun kanka, kai ka ce uruciya ce take damunsu, za su daina""."

"""Zuwa yaushe kenan? Idan uruciya ce kai meyasa ba ka yi?"""

"Raihan ya ce ""Haka ne, amma dai kayi hauri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka Wauka"

jarabta ce daga Allah.

"Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al'umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni'imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai""."

"Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce ""Madalla"

"da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu'a"""

"Raihan ya ce ""Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu'a in sha Allah zai zama"

"labari"""

"Alhaji Tahir ya ce ""Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya"

"oarin ta a kan tarbiyya""."

"""Haba Alhaji, kar ka Worawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaWan""."

"""Haka ne, ina son na roeka wata alfarma ne""."

"Raihan ya gyara zamansa ya ce ""To Alhaji, Allah ya bani ikon yi""."

"Ya ce ""Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da"

"wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran asashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba"""

"Raihan ya Wan yi shiru yana nazari, ""Ya dai na ji ka yi shiru?"""

"Raihan ya Wago ya ce ""Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi""."

"Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa ""Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai"""

"Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haWa shi da shi, dan aiki ne"

ba arami ba.

"Ya shanye shayin, ya mie tsaye ya ce ""Bari na arasa wurin Hajiya mu gaisa"""

"""To shikenan babu laifi"""

"A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a'a ba ne ba, amma wannan aikin kamar"

"yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba."

"""Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?"""

"Ya zauna yana faWin ""Eh, ina Wan jin yunwa ma, me ku ka yi?""."

"""Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a Wumama mini na sha da tea"""

"""To ni ma zan ci tuwon"""

"Ta ce ""To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai Wan karen daWi"""

"Yayi murmushi ya ce ""Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?"""

"Ta Wan rausayar da kai ta ce ""Ba su tashi ba""."

"Ya jinjina kai sannan ya ce ""Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? awar maryam?"""

"Ta ce ""Eh, ya aka yi?""."

"""Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?"""

"Hajiya ta Wan yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce ""Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?""."

"""Ba wani abu bane ba, mami ta fara faWa mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like"

"she's not socially ok"""

"""To ai kaga awar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuar hauri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce Waya daga ciki ya rasu, yayan babanta"

"yake rionta, matarsa take maltreating Win ta, gaskiya i don't know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haWa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai"""

"""Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?"""

"""A'a sai ka faWa""."

"""Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaanci suna makaranta,"

"gidansu an yi maltreating Win ta, makaranta yara sun yi maltreating Win ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daWi ba wallahi Hajiya"""

"Hajiya ta ce ""Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani""."

"Cikin damuwa ya ce ""Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi"

"idan na tuna abun da maryam ke faWa a kan ta, gaba Waya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?"""

"""Babu kam"""

"""Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?"""

"""Me zai hana? Idan har da Sangaren da zaka iya supporting Win ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan"""

"Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce ""Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su"

"yaya salim, da Waya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta"""

"Cikin damuwa ta ce ""To ya zan yi, sun i karatu, sun i kasuwa sai shirme, sai addu'a kawai"""

"""Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu'a"""

"Hajiya ta Wora hannunta kan na Raihan ta ce ""Addu'a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku"""

Ya amsa da Amin.

"Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita."

"Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba."

"Dr. Yan gari, yana ta oari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata"

"sake aurar da a ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar."

"Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga"

ware kanta ita kaWai a Waki.

"Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a asa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaWaicin a Wakinta."

"Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi."

"Abdul ya ce ""Noor, dan girman Allah ki zauna wuri Waya ki yi karatun nan a nutse""."

Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa.

"""Ke dan ubanki ki nutsu"" Kausar tayi mata tsawa."

"Noor ta ce ""Babanmu Waya"""

"Dr. Ya ce ""Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi."

"Farida ta ce ""Duk ta bi ta ishi mutane da karaWin tsiya""."

"Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce ""Dr."""

"Ya ce ""Na'am shalelena, yau kuma a dr. Na nake"""

"""Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan""."

"Yayi dariya ya ce ""Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya""."

"Ta gyara zama ta ce ""To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na"""

"""Tana sonki mana""."

"""Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu"""

"Ashar Win da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana"

"murguWa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can arshen falon ta ce ""Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya"""

"Farida ta dafe kai ta ce ""Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaWai aka yi wa tiyata a Wakin nan ba ayi mini"

"musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba Waya a ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba"

"laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata"

"wulaanta ni""."

"Tsam ummi ta mie, dan ta san arshe faWan kanta zai dawo."

"Ta tarar da noor a Wakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiWa."

"""Mama"" ta kirata kamar yadda take kiranta."

Noor ta Wago ta kalleta.

"""Meyasa ba kya jin magana ne?"""

"""Me nayi?"" Tayi maganar cikin tura baki."

"""Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?"""

"Noor ta ce ""Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina""."

"Ummi ta ce ""To ai ke Win ce ba kya ji mama"""

"""Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa

28 / 74