CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 74

135K to 138K   out of 219.4K words

WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

"Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon."

"Raihan ™ararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar"

"falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murWa mata."

"Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuSe."

"""Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya"

"goWai-goWai da kai sai ka auri yarinyar da Wan ka ya ce yana so?"""

"Alhaji Tahir ya ce ""In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza"

"abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ™ara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya"" ya ™arasa maganar tare da Waukar wayarsa ya fita."

"Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya."

"Rakiya na Wagawa mami ta fashe da kuka, ""Anty rakiya na shiga uku na lalace"""

"""Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?"""

"""Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haWo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini"

"mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa"""

"Anty Rakiya ta ce ""Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a"

"matsayin sirika"""

"""Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana Waya yake yi ko ta yi maka daWi, ko kuma"

"akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?"""

"Anty Rakiya ta ce ""TaS, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi"

"™arfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa"""

"Mami cikin takaici ta ce ""Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba"

"zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karSo kuWin auren nan, shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ™i aure ya lalace yaya zan yi?"""

"Anty Rakiya ta ce ""Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya"""

"""Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?"""

"""To ki koma ki samu babansa ki lallaSa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan """

"Mami tayi ajiyar zuciya ta ce ""Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima"" ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki,"

ita ba mai asma ba.

***

"Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce ""Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Idan sayar da ni Win ma ka yi ai na saidu kawu"""

"Yayi murmushi ya ce ""Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar"

"nan"""

"""To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta"""

"Ya amsa mata da ""amin"""

"Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi,"

har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?.

"Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tu™insa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci."

"Ta tuno lokacin da ya Waukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin ri™onta da yayi"

"A ranta ta ce ""Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai"

"da zuriyarka""."

"Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita."

"""Mamana tashi mun zo"" a hankali ummi ta motsa tare da buWe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa"

"komai ba, sai bin wurin da kallo."

"˜ofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya Wan daddana ya kara a kunnensa ya ce ""Gamu mun zo"""

Wani matashin saurayi ya le™o ya dur™usa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga.

"Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Al™ur'ani"

bugun warshi a gabansa.

"Dattijon ya mi™e tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta Waga ni™abin fuskarta ba, sai dai ta"

"shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa."

"Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa."

"Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina"

kallonta.

"Dr. Ya ce ""Ina mutuniyar kuwa?"""

"""Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya Wan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a Wora"

"muku girki, ai bamu san zaku zo ba"""

"Dr. Ya ce ""Ai al™awarin da na Wauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo""."

"Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banWaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiWa tana hutawa,"

saboda gajiyar da tayi.

"Ummi ta Wan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya"

"kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a Wora sanwa."

"Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam."

"Dr. Ya ce ""Malam ba ka ganni da ba™uwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba"""

"Malam yayi murmushi ya ce ""Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai Wakinka"

"ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da ni™abi"""

"Dr. Yayi murmushi ya ce ""Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?"""

"Ummi ta ce ""Na sanshi amma na manta a ina?"""

"""To ki cire ni™abin ko zai gane ki"""

"Ummi ta jinjina kai tana ™o™arin cirewa, aka yi sallama."

"Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ™irjinta ya buga da ™arfin gaske, ta ji tamkar"

"numfashin ta zai bar ™irjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa."

"Malam ya ce ""Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi ba™i tafiyayyu daga kano"""

"Ta ce ""Baban ummi ne?"""

"Malam ya ce ""Eh shi ne, tun da shikaWai ki ka sani a kanon ba"""

"Shigowa suka yi tare, tana ri™e da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur."

"Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda"

"™irjinta ke lugude. Gaba Waya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta ni™abinta."

"Ta mi™a hannu a hankali ta Waga ni™abin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai,"

kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar.

"A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taSa ummi sai"

hawaye da ya fara zuba daga idonta.

"Mama ta mi™a hannu tana faWin ""Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya"""

"Mariya ta buge hannun maman da ™arfi, ta ru™un™ume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta."

"Ta mi™a hannu ta warware mayafinta, ta lulluSe da ummi da shi, ta Waukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka."

"Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin ´ar sa."

"Ya zura hannu a aljihunsa ya Waukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya Wan lami."

"""Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaSi ne a jikinki?"" Tayi"

maganar tana Wora hannu a goshin ummi.

"Wasu irin jijiyoyi suka WaWWaga a goshin ummi, wani irin ri™o take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata"

ni'ima.

"Sun fi mintuna talatin a haka, sun ™i sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taSa mata ita."

"Dr. Yayi gyaran murya ya ce ""Yau na cika al™awari ko?"""

"Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce ""Wallahi ba zan taSa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta"

"™wace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata Wa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita"""

"Ta Wago ummi tana goge mata hawaye ta ce ""Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya"

"ba, na san ba ta sonki ba ta ™aunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya Wan lami ya™i dagewa ya karSo mini ´a ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaWai ce me ´a, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana"""

"Ummi ta ™ura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta"

"girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ™wa™walwa."

"Ta mi™a hannu ta Waukko ledar pure water, ta buWeta ta saka wa ummi a baki tana faWin ""Na san ™ishirwa ki ke ji"

"ummi, sha ruwa kin ji"""

"Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta,"

"amma hakan bai hanata gane ´ar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haWu ba."

"Dr. Yayi gyaran murya ya ce ""Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka"

"haWu, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi."

"Ummi ban ™i sada ki da mahaifiyarki dan ba™anta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haWuwarku ba za ta yi daWi ba, idan ku ka haWu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ™i zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka mi™a masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaSi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba."

"Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ™afafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki"" yayi maganar a sanyaye."

"""Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a"

"gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya Wan lami ka ™i dagewa ka karSo mini ummina"""

"Dr. Ya ce ""Haba maman ummi, ki yi ha™uri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi ha™uri dan Allah"" yayi maganar"

yana haWa hannayensa.

"""Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya"

"Wan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ™wace mini ita dan ta wula™anta ni"""

"Dr. Ya ce ""Ba gani a gabanki kina kallona ba?"""

"""Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau"" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne."

"Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu"

"shar da ita, gashi gaba Waya ba sa kama, sai kaWan, kamar ya da ™anwa ba uwa da ´a ba."

"Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta Soye ummi a"

"bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a Wauketa a mayar da ita wurin Iya."

"Ummi ta ga ™auna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space"

"take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa."

***

"Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaWa ™afa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a"

waya.

"Falon ta shigo cikin takunta na ™asaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce ""Kai, babanka ya kasa samunka a"

"waya, yana ta ´ar murya a lallaSoka ka koma fa"""

"Raihan ya gyara zamansa ya ce ""Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce ta™i tsayawa ta fuskance"

"ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, ta™i fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata"""

"""Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu"

"ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ´ancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?"""

"Raihan ya ce ""Abun kuma har da gori?"""

"""Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata"""

"Yayi murmushi ya ce ""Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daWi sai na matata"""

"""Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak"

"yarinyar nan, haka zaku yi ta faWa da babarka"""

"Raihan ya mi™e ya ce ""Ni kaina na sani, ina ™o™arin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki"

"sosai"""

"Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage Win, ba a saka"

"pressure wurin cewa lallai sai an tan™wara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren."

"Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluSe ummin, sannan ta"

rungumeta.

"Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan."

"Aikuwa a take ya Waga ya ce ""Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru"""

"Ummi ta ce ""Albishirinka"""

"""Goro fari ™al"""

"""Na haWu da mama"""

"Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce ""Wace maman?"""

"""Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ™i zama na yi karatu ya sanya ya Soye"

"mini"""

"Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce ""Congratulations to both of us"

"ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah"""

"Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin"

"rabuwa da suka yi, da irin so da ™aunar da maman nata ta nuna mata."

"Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ™ara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da"

"maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa."

"A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi."

"Yaya maryam ta ce ""Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za"

"a zo a Wauketa a tausaya mana dan Allah"""

"Dr. Ya ce ""Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daWin zama"

"da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huWu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku"""

"Anty maryam ta yashe baki tana faWin ""Masha Allah, Alhamdilillah"""

Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka.

"""To amma, akwai Wan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata"""

"Dr. Ya ce ""Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake"""

"Yaya Wan lami ya ce ""Amma ba za a ™ara mana ko wata Waya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma"""

"""A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan

46 / 74