Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Cutarwa Complt Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 74

33K to 36K   out of 219.4K words

Wan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan"

"cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaWe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ™o™arin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda Wakin ya zame mata a yanzu ba™i ™irin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ™awata shi."

"Dur™usawa tayi ta fashe da kuka tana sheshshe™ar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka."

"Ummi ba ta samu fitowa daga Wakin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da"

"take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita."

"Ta yo alwala ta dawo Wakin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi."

"Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai"

"yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince."

"Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya Wan sirka,"

kuma su kumbura.

"Ta kalli kuWin da yaya Wanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar Wakin, ta ™an™ame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta."

Ba tsammani ta ga magaji a kanta.

"""Ummi"" ya kira sunanta a hankali."

"Ta Waga kai tana kallonsa. ""Kukan me ki ke yi?"""

"""Yaya magaji"""

"""Na'am ummi""."

"""Wai mamana ta haukace?"" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta."

"""Subhanallah waye ya gaya miki haka?"""

"""Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuWin"""

"Hashim ya ce ""Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ™wa™walwa aka ce"""

"""Likitan ™wa™walwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ™wa™walwa"""

"""Ba haka bane ba"""

"""To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?""."

"""Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya"""

"""Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah"" tayi maganar tana haWe hannayenta alamar magiya, tana kuka."

"Cikin matsanancin tausayinta ya ce ""Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take"

"a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taSa zuwa muka yi ba. Amma ki yi ha™uri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah"""

"""Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta'ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai"

"na hau kujerar tsiya na ci ubanka la'ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai."

"Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ™o™arin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki Sare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da Wa na, ke da ita har abada, sai ta WanWani abun da ta ™unsa mini, wannan kuWin na meye?"" Tayi maganar tana nuna kuWin da ummi ta watsar a wurin."

"Hashim ya ce ""Yayan babarta ne ya bata"""

"""Tattaro mini su ki mi™o mini"" ummi ta tarkata kuWin ta mi™a mata."

"Ta karSe ta kalli Hashim ta ce ""Zaka tashi ka fita ko sai na Sata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai"""

"Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buWe bakinsa, zai iya Wurawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya"

bar Wakin.

"""Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba"""

"Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ™o™arin aikin da Iya ta saka ta, ™asan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta."

"Kayan da yaya Wanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ™aunar duk wani abu da ya shafi Mariya."

"Duk salla sai ummi ta yi addu'ar Allah ya ji™an babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta Wauke ta."

"Tun wannan tafiya da yaya Wanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da"

"hankalinsu a kan lafiyar ´ar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sau™i ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taSin hankali."

"Ummi kuma ta cigaba da karSar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida."

"Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, Wan taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi."

BAYAN SHEKARU BIYU!.

"Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu."

"Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaWai ta san me take ji."

"Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koWe"

"sun jeme, ™afar wandon duk ta Wage ta tattare, gwiwar duk a farfashe."

"Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ™afe, ta Wau bokiti ta samo ruwan wanka, ta Wauki ledar omon da babu"

"komai a ciki, ta faWa banWaki wanka, da sosonta na buhu."

"Ta daWe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta ri™e shi bata yi ba,"

saboda azabar da take sha.

"A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaWe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take Waure kan da"

"shi, ta Waure yadda ba zai ji™e ba."

"Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-"

"robar jiki ta zaro, har da in da aka yi Winkin zare da allura a jikin phant Win, haka ta rataye shi a jikin ™ofar banWaki, sai tsami yake mara daWi."

"Ta koma gefe Waya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai"

sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu.

"Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raWaWi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har"

"™afafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ™ulle kan fitsarin ya fita."

"Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga."

"A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ™arni mai haWe da wari ya daki hancinta, ta Webo ruwan nan da sanyinsa da"

"komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ™arni mara daWi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ™ai™ayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ™urajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daWin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ™arfin ta, saboda azabar ™ai™ayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini."

Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banWakin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaWai ce take fama da wannan

"masifar da bala'in, to idan ma haka ne wa zata tambaya?"

"Da ™yar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ™arshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta"

"mayar shi jikinta a ji™en, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana Wan buWe ™afarta, saboda raWaWin da wurin yake yi mata."

"Man kaWanyarta da na'ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform Win ta, ™ungun wandon saboda rashin"

"roba, da leda take kama wani sashin ta Waure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta Waure shi da shi, ta saka."

"Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala'in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu."

"Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi ya™i karatun boko ya™i na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaWa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba."

"Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris Win nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haWu su yi masa aure."

"Aka kama masa hayar wani gida mai Waki biyu da kitchen da banWaki, ginin ™asa ne dai, amma an yi floor, da plastar"

™asa an shafa farar ™asa.

"Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake"

"ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren ´ar mai suna Hindu."

"Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta"

"zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka."

"Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da"

"idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara."

"Ana ta shirye shiryen biki, gida ya Wau harama, ´an uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, Wan"

"wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, Wan wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni."

"Yau kusan tun bayan azahar, yanayi ya nuna akwai matsala, duba da yadda Iya ke ta shiga tana fita ita da mahaifin su"

"magaji, kasancewar ba abun da ya shafi ummi bane, ya sanya ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta."

"Shi kansa yanayin Idirs ya nuna hankalinsa a matu™ar tashe yake, alamu suka tabattar da akwai matsala."

"Ba a tsaya da shirye-shiryen biki ba, dan magana ake ta bai fi saura kwana huWu a shiga hidimar biki ba."

"Da yamma hashim ya shigo, ya tarar ummi na cikin mutane ana ta aiki, yayi mata nuni da ta zo."

"Ta wanke hannunta ta bi shi, ya kalleta ya ce ""Ke ina naki shirin bukin, ki ke ta fama da aiki haka, ko gajiya ba kya yi?"""

"Murmushi ta yi masa, sai da fararen ha™oranta suka haska fuskarta, fi™arta da ta karye tana nan a yadda take, sai"

"´ar siriryar wushiryarta ta ce ""To yaya magaji wani shiri zan yi? Ina da atamfata sabuwa da takalmin da zan saka"""

"""Ke ba zaki yi Wan lallen da ake yi na zamani ba?"""

"Ta kalli hannunta, ta Wan rausayar da kai ta ce ""Bana so, ba zai yi mini kyau ba"""

"Ya kamo hannunta ya ce ""Jan nan da ake yi tafin hannunki fari ne masha Allah, ko kitson ma ba ayi miki ba, kin"

"cukurkuWe gashi kin Waure"""

"Yayi maganar yana kallon yadda Wankwalin kanta yake cike fam, ko ba a gaya maka ba, ka san wannan uban gashin nata ta Waure."

"""Ai ka san ni ba a iya yi mini kitso, duk sanda na cewa yayi mini kitso, sai ya ce wai bs zai iya ba kaina ba zai yi ba,"

"lalle kuma ai sai an biya Wari biyu huwaila take yi hannu da ™afa"" tayi maganar cikin yanayinta na shagwaSa da Iya take cewa sangarta."

"Ya ce ""To shikenan, da safe zan baki kuWin lallen, kitson kuma sai na yi miki"""

"Tayi dariya ta ce ""To mata ne kawai suke yi wa mata kitso ban da maza"""

"Ya ce ""Shikenan, je ki sai goben in Allah ya kaimu"""

"Cikin murna ta tafi ta cigaba da aikin, tana matu™ar son lalle, amma rabon da ayi mata, tun kan na'ima tayi aure, da"

"take yi musu, yanzu yaran na'ima biyu a gidan miji."

"Da magariba Saminu baban su Idris ya shigo hankali a tashe ya ja hannun Iya suka fita, wata duhuwa ya ja ta ya ce"

"""Iya muna cikin tashin hankali da masifa, Idris ya zubar mana da mutunci"""

"Cikin kaWuwa ta ce ""Menene? Meyafaru?"""

"""Ban da masifa da bala'i, saura ´an kwanaki a Waura maka aure, a ganka kana watsewa da wata, saboda rashin"

"mutunci"""

"Iya ta ce ""To ba mun gama wannan maganar ba? Har wurin maude mai babban carbi na je, ya yi mini aiki ya ce"

"maganar an bar ta har abada, ba zata fasu ba, ko ta fasun ne?"""

"""To yanzun nan ™anin baban yarinyar da zai aura Win, ya dawo da kuWin auren, sun ce aje a karSi kayan auren gobe"

"da safe, ba za su bawa mutumin banza ´a ba"" yayi maganar yana nuna mata kuWin."

"Iya ta dafe ™irji ta ce ""Mun shiga uku, amma mutanen nan basu da mutunci, basu san tsautsayi ba?"""

"""Koma menene ai shi ya janyo wa kansa, da bai yi ba wa zai ce yayi, ni wannan mutanen da muka tara ne, ban san ya"

"zamu yi da su ba"""

"Iya ta ce ""Ni kuma tashin hankalina, garin Allah ya waye a dawo da kayan nan, kowa ya ji abun da ya faru, da sassafe"

"ka je da kanka ka karSo kayan, ka kai mini gidan kuluwa""."

"""Ni kuma Iya? Ni zan je Waukko kayan?"""

"""To kar ka je tsaya asirinmu ya tonu, sai ka ji daWi, santolo kawai""."

"""To Shikenan zan je in sha Allah """

"""Kai ka ga idan da hali, ka tafi yanzu cikin daren nan, ka tafi da babur ba wanda ya ji balle ya gani"""

"""To bari sahu ya ™ara Waukewa, amma Iya yaya zamu yi da wannan mutanen, ta yaya zamu ce musu an fasa auren nan?"""

"Iya ta ce ""Nima shi nake tunani, dama ga akuyarsa tayi kuka a dangi, dan ma ana tsoro na ne, ya sanya ba a magana,"

"amma jeka na san abun yi """

"""Meye abun yin to?"""

"""Ka tafi na ce, idan ka dawo sai ka ji"" ya jinjina mata kai ya tafi."

"Šakin samarin ta shiga, neman Idris, amma ba ta tarar da shi ba, dan haka ta juya ta tafi."

"A daren saminu yayi yadda Iya ta ce, ya je ya karSo kayan a daren."

"Sosai Saminu, ya din ga yi wa idiris faWa, a kan tashin hankalin da ya sanya su a ciki."

"Washegari kamar yadda Hashim ya yi wa ummi al™awari, ya bata kuWi ta je aka yi mata lalle."

"A ™ofar gida ta gan shi ya karSo kayan guga, tun daga nesa take Waga masa hannu ta ce ""Yaya ka ga lalle na?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Inyee an sha kyau, lalle yayi kyau, ki yi sauri ki shiga gida, Iya ta fara faWa ana nemanki"""

"Cikin faWuwar gaba ummi, ta ce ""Bari na yi sauri"" ta yi cikin gida da gudu."

"Cikin damuwa Saminu ya kalli Iya ya ce ""Iya kina ganin babu matsala, ba fa son yarinyar nan yake yi ba, kuma"

"shekarar ta goma sha uku ne kawai"""

"""To yaya ka ke son mu yi? Asirinmu da nasa ya tonu, idan ba haka ba kawo wata mafitar"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Ba ni da wata mafitar""."

"""To na yanke hukunci, ya auri ummi dan mutuncinmu ba zai zube ba, a sakamu a bakin duniya da wannan iskancin"

"da yayi ba kamar Wan taure"""

Ayshercool

8081012143.

*CUTARWA*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS (FREE BATCH)*

"Mafaka gidan ™amshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ´an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daWi da ™amshi."

"Mafaka gidan ™amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

P10

"Saminu ya numfasa ya ce ""To shikenan, Allah ya sanya alkhairi"""

"Iya ta ce ""Yauwwa ka turo mini shi, ko kuma ya jira ni a Wakinsu, zan same shi"""

"""To shikenan, bari na je na nemo shi"""

"Hashim kuwa dariya yake yi wa ummi, yana cewa ta tafi a hankali, saboda yadda ta kwasa da gudu cikin tsoro."

"Da Iya tayi karo, iya ta kalleta ta ce ""Daga ina ki ke?"""

"A tsorace ta ce ""Dan Allah kiyi ha™uri, huwaila ce ba ta yi mini lallen da wuri ba"""

"""Yenyenyen da an yi magana, dan Allah ki yi ha™uri, ki wuce ki nemi wuri ki zauna kar ki sake fita"". Ummi ta ce ""to"" dan ba ta yi zaton Iya ba zata yi mata tijara ba."

"Iya duk ta bi ´a´anta da ta haifa da na ri™onta, ta sanar musu da halin da ake ciki."

"Ilyas ya ce ""Amma Iya naga yarinya ce ™arama sosai, girman jiki ne kawai ba zata iya jure Wawainiyar aure ba"""

"""Yarinya kuma? Ni ma shekarata sha uku aka yi mini aure, uwarta ba sha huWu aka auro ta ba? Da ta shiga"

"bulunbu™ui za ta yi, yaran yanzu da sun san komai, to idan ba haka ba ya zamu yi?"""

"Sagir ya ce ""To ai Iya ba a shirya ba, da wani kayan Wakin za ta tare?"""

"""Wani shirin za ayi? A sayo mata katifa a gidan dillalai, tsohuwa ba sabuwa ba, mai biyar mai goma ku yi karo-karo,"

"ku haWa a saya mata

12 / 74