Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Cutarwa Complt Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   68 / 74

201K to 204K   out of 219.4K words

´an uwa aka yi walima a can maidugurin."

"Anty maryam ta kalli mariya ta ce ""Wai duk murnar ganin angon ce haka? Bakinki ya ™i rufuwa"""

"Ta ce ""Haba Anty Maryam, kin saka na ji kunya, kawai zan ga ummina ne, nake ta jin daWi"""

"""Kai mariya, ke sam ba ki da alkunya, ´ar fari ce fa"""

"Ta Wan rausayar da kai ta ce ""Shekarar mu nawa ba ma tare, sai in din ga jin tamkar ta koma ´ar karamarta, ´ar"

"ba™ar ´a ta mai kyau, na gyara duk wasu abubuwa marasa kyau da suka faru da rayuwar ´a ta, wallahi anty maryam haryanzu ina jin tausayin ummi, rayuwar da ta yi ya kasa zama tarihi a wurina, kuma zuwan da ta yi na ™arshen nan, kamar akwai wata damuwa da take Soyewa, fatana Allah ya sa ba wata matsalar ce a gidan auren nata ba, Allah ya sa ta daina shan wahala"" kan ta kai maganar gaba Waya hawaye ya wanke mata fuska."

"Mama ta ce ""Mariya, ba zaki daina Worawa ranki damuwar abun da ya wuce ba ko? Ga bawan Allahn nam sun zo, ai sai su zata ko son shi ne ba kya yi"""

"Sallama dr. Yayi tare da abokinsa, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa."

"Suka shiga Wakin da aka saba saukarsu, ya kalli maman ummi, ya tuna maganar Farida, ta yi shar da ita, sai dai yayi"

mamaki ganin tana kuka.

"Ya kalli mama ya ce ""Mama lafiya kuwa take kuka?"""

"Anty maryam ta ce ""Daga yin zancen ummi, ta hau kuka ta ™i ta bar abu ya wuce, kullum ta tuna rayuwar ummi sai"

"ta yi kuka, abu ya riga ya zama tarihi"""

"Mariya ta ce ""Anty Maryam, tun tana kan cinya fa, aka ™wace mini ita, kuma fa itakaWai ce da ni"""

"Mama ta ce ""To da mutuwa ta yi ya zaki yi?"""

"Da sauri ta ce ""A'a ummi ba zata mutu ba, babanta ya mutu, ™aninta ya mutu, idan ta mutu ya zan yi?"""

"Dr. Ya fuskanci jikinta haryanzu da saura, kuma tuna rayuwar ummi, ke saka jikin ya motsa mafi akasari, dan haka ya"

"ce ""Shikenan ya isa haka, ke da zaki koma kano ma, duk lokacin da ki ke so zaki ganta, ku koma kusa da juna"""

"Kamar ™aramar yarinya take goge hawayenta ta ce ""Ni sonake ta koma ´ar ™arama kamar lokacin da iya ta ™wace mini ita, in din ga goyata, idan na yi mata wanka na yi mata kwalliya, amma kawai iya ta ™wace mini ita, ga zafin"

"mutuwar mijina"""

"Ya Wan ™ura mata ido, ba a ™asa ummi ta Waukko shagwaSa ba, duk da ummi ta ninka mariya shagwaSa nesa ba kusa"

ba.

Ya kalli su Anty Maryam ya ce su Wan basu wuri.

"Bayan sun fita ya matsa gabanta ya ce ""Haba maman ummi, idan mijinki ya mutu yanzu ba gani ba""."

"Ta kalleshi ta ce ""Kai ba bashir bane, yaya yahaya ne, ba na so kai ma iya ta ce na kashe ka, wai iya ta ce ni na kashe"

"baban ummi, ya za ayi na kashe shi?"" Tayi maganar hawaye na cigaba da zuba."

"""Ki manta da maganar iya, yakamata ace memorynki, yana tuna abubuwa masu daWi, idan baby ki ke so ki yi addu'a"

"Allah ya kawo miki ™annen ummi, ki yi ta goyawa ita yanzu ummi tana da mai goyata"""

"Ta Wan yi shiru kamar wadda ta farka daga bacci ta ce ""Kai, ummi fa ta yi aure, kuma nima sai na haihu?"""

"Yayi murmushi, ganin kamar tunaninta ya dawo."

"Ya ce ""Idan ki ka cigaba da kuka, da tuna abun da ya wuce, ba zan tafi da ke ki ganta ba""."

"Haka yayi ta rarrashin ta, dama tuni su mama sun haWa mata kayanta, suka raka su har mota, suka kama hanyar"

kano.

"Gidan ummi, bayan sun gama aiki, noor ta Wauki wayar ummi ta tafi Waki tana game."

"Ummi kuma na falo tana kallo, sai ga Farida ta zo gidan, gidan da tun da ummi tayi aure, kusan shekara ba ta taSa takowa ba."

"Sai dai duk yadda ake kwatanta mata haWuwar gidan ummi, sai yanzu ta tabattar da idonta ya gane mata."

"Kamar babu komai ummi ta tashi cikin fara'a, kamar babu wani abu a ™asa tana ""Oyoyo, yau na yi babbar ba™uwa, sannu da zuwa anty"" wani irin mugun kallo take yi wa ummi, da mamakin iskanci ne ko rainin hankali ya sa take"

wannan washe mata bakin.

"""Ke saurara bana son karuwanci da iskanci, ni zaki yi wa bariki kina wani washe baki kamar bakin buhu?"""

"Ummi ta shafa bakinta, a iya saninta dai ba ta da ™aton baki, ji ta yi kamar ta yi dariya amma ta maze ta ce ""Ai"

"ba™onka annabinka anty, kuma akwai hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da yake cewa wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya girmama ba™onsa. Ki zauna bari na kawo miki ruwa""."

"""Ki yi mini shiru ko na Sarar da ke, ba ki da abun da zaki bani, ke da aka kawo mini ke cikin dauWa da ™azanta babu ko"

"suturar kirki, har ke ki ke da abin bani, dan kin auri mai kuWin da uwarsa ba ™aunarki take yi ba, auren abun kunya, auren yaro ™arami? Butulallaiya mara mutunci, wato abun da ki ka yi wa wancan ´an ™auyen shi ne nima ya biyo ta kaina, ki ka saka dr. Ya auri babarki, mahaukaciya da ba ta san ciwon kanta ba?"""

"Ummi ta ce ""A'a fa, ni ban bayar da shawarar hakan ba, dr. Ya zo mini da maganar na goyi bayansa Wari bisa Wari, ko"

"ba komai na yi ramuwar gayya, kuma ba fata ba ko aurena ne ya mutu, ko wani abu ya faru ina da wurin zuwa."

"Da ki ke i™irarin an kawo ni cikin dauWa da ™azanta, ai ba ke ki ka kula da ni ba, wan ubana ne, dan haka ke bai kamata a ji wannan gorin daga bakinki ba, ba ki isa ki yi mini gori ba a kan wannan, ko kin manta irin ri™on da ki ka yi mini?"" Ummi ta Waga rigarta, gefen cibiyarta ya Wan yi shati, ta ce ""Na san wata™ila ke kin manta, kuma an yi sa'a jikina ba ya ri™e tabo, wannan ne kawai yayi saura kuma da shi zan koma ga Allah, har azaba da wuta ku ka yi mini ke da ™anwar ki, wallahi da ramuwar gayya zan yi a kan ki, sai kin bar gidan dr. Kuma Alhamdilillah a yanzu dai Allah ya yi mini sutura da rufin asirin da ba kwa so, kuma wallahi ni Salma ina da abun da zan baki."

"Amma ba wannan ba, na zata bayan na yi aure komai zai wuce, na yafe komai ya wuce, amma na fuskanci hali zanen duste ne, ba zaki canza ba, tun bayan da ki ka yi mini korar kare da na je gida aurena ya samu matsala, dan haka mun saka ™afar wando Waya da ke, za ki ga mahaukaciya ganin idonki, yadda na ke shimfiWa mulkina ba boka ba malam a gidan mijina, sai uwata mahaukaciya ta shimfiWa na ta mulkin ba yadda ki ka iya, zaSi ya rage naki, ko ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ko kuma ki shirya yin fito na fito da ni, tsakanina da ke babu Waga ™afa, kuma ki gaya wa rahama, idan har muna raye sai Allah ya jarabceta da wuta, kamar yadda ku ka yi mini azaba da iata, dan wallahi ban yafe ba! Ko zan yafe muku komai, banda wannan"""

"Tir™ashi! Ummi ta shayar da farida ruwan mamaki, gani take kamar daga wani wurin maganar ke fitowa ba bakin"

ummi ba.

"Cikin dakiya farida ta ce ""Yaushe aka yi daren, da har gari zai waye, ki ke i™irarin shimfiWa mulki a gidan miji? Ša"

"namiji ne fa da bashi da tabbas""."

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Anty farida, ai daren yayi tsayi, ke ce ba ki farga ba, sai da garin ya waye. Duk da kina"

"i™irarin uwata ba ta da hankali, amma a hakan ta din ga yi mini nasihar, jin tsoron Allah, ri™e addu'a da biyayya a aure, idan har tsoron Allah, addu'a da yi wa miji biyayya na saka a ci ribar aure, da yardar Allah ni da uwata mun fi ™arfin masu bin ´an tsubbu, kuma zamu zauna dai-dai a gidan miji, namiji ba shi da tabbas, ya danganta da yadda ki ka Wauke shi ne, nawa yana da tabbas, haka babana dr., Ke ce baki iya tattalinsa ba ki ke ganin ´an tsubbu sun mallake miki shi, shiyasa ki ka ga bashi da tabbas""."

"Farida ta saki baki, hangal tana kallon ummi, ba ta gama mamakin ba ummi ta ce ""Yauwwa tun da bani da abun"

"baki, zaki iya tafiya, na ga kin yi mini aike noor ta koma, in dai noor ce, sai dr. Ya Wauke ta ya ba wa mamana, saboda kin raini ´ar ki da ™iyayyarki, saboda banzan dalilinki, na an saka mata sunan mahaifiyata, duk sha™uwar Wa da uwa, ta fi son babanta a kanki, cikin sau™i zan sanya ya karSe ta ya bawa mama ita, ba zan so ta tashi da rashin imani irin naki da su kausar ba, masu ba™ar zuciya ba, tayi aure tana hali irin naki ba, idan kin fita ki rufe mini ™ofar falo, kar ™uda ya shigo mini bana son ™uda"" ko jiran amsar farida ba ta jira ba, ta bar falon ta bi wata hanyar, ta tafi can bedroom Win da noor take, wadda ba ta san ma farida ta zo ba."

"˜arfe huWun yamma, dr. Ya sauka, basu tsaya ko ina ba sai gidan raihan, ta rungume ummi suka din ga murna,"

kamar sun shekara ba su ga juna ba.

"Sam farida ba ta san ranar ma maiduguri ya je ba, yana komawa gida, ta dira masa bala'i tana gaya masa abun da"

ummi ta yi mata.

"Kai tsaye ya ce ™arya take yi wa ummi, sharrinta ne kawai ummi ba zata aikata haka ba, tsabar kishi ne kawai, idam"

ma hakan ne meyasa da ba ta je gidan ummi ba sai yanzu da wannan lamarin ya zo.

"Abun duniya duk ya ishi farida, asirin tayi har ta gaji, ya shammaceta, da kan ayi ne da ta yi ya™inin asirin zai kama shi, maganar ta rushe."

"Raihan ma ba ™aramin daWin zuwan mariya ya ji ba, tayi ™alau da ita."

"Noor kuwa tun bikin ummi da suka je maiduguri, suka saba da mama, tun da dr. Ya gaya mata takwararta ce."

"Kuma aka yi sa'a ba ta manta ta ba, a ranar da daddare, sai ga Salim ya zo har da Sagir."

"Mariya ta din ga murna, duk idan tana magana wasu lokutan ta kan haWa da shirme, amma a hakan take yi musu"

"nasiha, tare da ™ara musu haske a kan rayuwa."

"Sagir ya din ga mamaki da aka ce ita ce maman ummi, ita da haskenta ma, ummi ce dai ba™a, sai dai idan tayi wani"

abun kamar ummin.

"Ta tsiro da batun cewa lallai, a kai ta su gaisa da babar raihan, da babansa sun gaisa da Alhaji, babar raihan ce ba su"

taSa haWuwa ba.

"Gaban raihan ya faWi, amma ya basar ya ce zai kaita su gaisa."

"Su Salim sun daWe sosai, duk da a zahiri bayan mama, noor ce ta ri™e shi, dan chatting suke a wayar ummi ba ta sani"

"ba, idan suka gama sai ta goge."

"Ummi ta yi iya ™o™arinta, ta mantar da mariya, batun haWuwa da babar raihan."

"Allah ya taimaki Iya, ba ta samu mumunan rauni ba, sai dai ta fasa kai, fuskarta duk ta ™uje, sannan ta targaWe"

"™ashin ™afarta, da hannunta, gashi kuma kanta sai da aka yi mata Winki, kan ayi Winkin nan kuwa sai da aka sauke gashin kan gaba Waya, ga bakinta ya kumbura saboda wahala."

"Da ™yar suka yi karo-karon haWa kuWin magani, likita ya rubuta hoton ™wa™walwa, saboda kai da take ta kuka da shi,"

"amma babu kuWin yi, maganin ma ba duka suka saya ba."

"Suna tsaka da wannan gaganiyar, ana ™o™arin kiran dr. Suka samu labarin yayi aure, ya auri mariya."

"Gaba Waya sai suka manta da halin da iya take ciki, suka shiga salallami."

"Iya na daga kwance ta tuna yadda tun bayan ya gano in da mariya take, ya ce zai aureta, amma ta ce ba ta lamunta"

"ba, tun da ya ri™e ummi shikenan, ba zai sake kwasota ya kawo musu dangi ba, saboda a cewarta mariya annoba ce, mugun abun ta ne ya sanya ta haukace."

"Su ummi suna airport, tare da dr., Ta wani Sangaren ransa a Sace, saboda tijarar da ya sha a wurin farida daren jiya,"

"da ya ce yau zai koma uganda, tare da babar ummi."

"Har da zaginsa ta ™are masa cin mutunci, abubuwa da dama yana duba yaransu ne ya sanya yake Waga mata ™afa, kuma tun ainihi, shi mutum ne mai sanyi ba shi da hayaniya, shiyasa take yi masa duk abun da ta ga dama."

"Suna airport sun rako su dr. Mariya sai kalle-kalle take yi, da alama a tsorace take."

"Sai ga wayar kawu Sagir, dr. Ya Waga tare da amsa masa sallamar."

"""Yanzu yahaya tsakaninmu da kai abun har ya kai haka? Muna ´an uwanka amma sai dai mu ji a gari ka yi aure?"

"Abokanka sun fi mu kenan?"""

"Dr. Ya ce ""Ba abun Waga hankali bane ba, abun ne ya zo ba shiri, na ga akwai bu™atar tun ina raye ya zamana ummi"

"tana da madogara ko bayan raina, dan yadda ba a kula da ita bayan ran mahaifinta ba, bayan raina ma ba za ta sauya zani ba, dan na san kun san wadda na aura, kuma da na neme ku, ba zaku bari ba, da kaina zan zo har gida na yi muku bayanu"""

"""Aishikenan, ni ba ma wannan ba, ka ganmu fa a asibiti da iya"""

"""Subhanallah me ya same ta?"""

"""Wallahi dai tsautsayi ne, Auwwalu ne ya sha ta gaya masa ™arya, ta yi masa faWan rashin sana'a sai bacci, ya din ga tamaula da ita, saura ™iris ya jefa ta a rijiya. Yanzu dai gamu a asibiti, magunguna an sayi wasu, wasu kuma ba a saya"

"ba, ga hoton kai an rubuta shi ma ba kuWin"""

"Dr. Ya ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga illar rashin mayar da hankali a kan tarbiyyar yara da iliminsu ko? Ina Auwwalun yake?"""

"""Ya gudu ba a san in da yake ba""."

"""To ka ga ni yanzu ina filin jirgin sama, zan koma makaranta, zan turawa Abdul kuWi ya zo ya dubata ya baku, Ubangiji Allah ya sauwwa™e"""

"""Amin, amma dan Allah yayi sauri ana bu™atar kuWin"""

"Dr. Ya ce ""Sai ya tura muku, idan ya so daga baya sai ya zo ya dubata"""

"Kawu Sagir ya ce ""To hakan ma yayi, bari na ga Idris yana da lambar banki, sai a turo ya saka kuWin, an gode"" bayan"

"dr. Ya gama wayar suka din ga jajantawa, mariya kuwa ko Allah ya kyauta ba ta ce ba."

"Ummi har da hawayen murna, ganin mama tare da dr. Za su keta hazo tare, ko ba komai tana sanyawa mama ran"

samun kulawa daga dr. Kasancewarsa jajirtaccen mutum.

"A ranta ta ce ""So so ne, amma son kai ya fi, in sha Allah a kujerun hajji da umaran da Alhaji yake rabawa sai kun"

"samu, ko ban je ba ku je a tare hakan nan, ku yi mini Addu'a."

"Bayan jirginsu ya Waga, suka koma gida."

"A cikin jirgin ™an™ame dr. Ta yi, saboda gani take kamar za su faWo daga cikin jirgin."

"Dariya ya din ga yi mata, ganin yadda take a rikice gaba Waya, hakan ya bashi damar rungumeta a jikinsa, sai wani"

irin daddaWan ™amshi take yi.

"A hankali take tambayar sa ""Baban ummi ba zamu faWo ba kuwa? Tsoro nake ji sosai"""

"""In sha Allah ba zamu faWo ba, lafiya zamu sauka""."

"Dr. Dubu hamsin ya turawa Abdul, ya ce masa ya tura wa su iya idan sun turo account number, shima ya ™ara dubu talatin ya tura musu dubu tamanin."

"Ummi bayan sun koma gida, raihan ne ya sakata a gaba, yana mammatsa mata jikinta a hankali cikin tsantsar"

"soyayya da kulawa yake ce mata ""Am sorry sweetheart, kwanan nan am very busy, kamar bana kula da ke sosai, kuma na san kina bu™atata"""

"Tayi murmushi ta ce ""Saboda jin daWi yayi mini yawa ko? A cikin mata hamsin nawa ne suke samun kulawar da nake samu, idan suna da juna biyu, kana iya yinka aiki ne yayi maka yawa""."

"Ya numfasa ya ce ""Duk da haka dai, wallahi ummi wasu lokutan kaina kamar ya fashe, ina jinjinawa Alhaji yayi"

"™o™ari, kin ga yakamata ace Yaya salim yana cikin system Win nan, tun da bamu muka tara dukiyar ba, mu kula mu tattalata ta haSaka, ga branch Win mu na Abuja, ina ga a watan da zaki haihu za a buWe shi, ban san ma ya zan yi ba, wa za a mayar can Abujan, atleast yakamata ace da wani daga cikin mu"""

"Ummi ta ce ""Mhmm ka lura zuwan yaya Salim gidan nan ya ™aru sosai?"""

"Ya jinjina kai ya ce ""Magana ce kawai ban yi ba"""

"""Anya nan gaba magana ba zata taso tsakanin sa da noor ba, sha™uwarsu ta yi yawa"""

"Cikin murna raihan ya ce ""Wallahi sam ban kula ba, tun da ya ce ke ™anwarsa ce na zata saboda ke ne, yana cigaba"

"da bibiyata ne kar na yi miki wani abu. Amma kina ganin dr. Zai bashi ita? Kamar yayi mata tsufa kuma ga yanayin sa"""

"Ummi ta ce 'Aikuwa yaya Salim ya shiryu, a kan lokacin da na san shi, ba abun da zai hana ya bashi ita, nima haka"

"aka yi mini surtu da na aureka, in dai suna son juna ba shikenan ba"""

"Ya jinjina kai ya ce ""To Allah ya tabattar mana da alkhairi, Kairun nisa'i, wannan cikin naki kamar ya fi ™arfin"

"watanninsa, kafin mu koma awo, sai mu je ayi miki scanic kawai mu tafi da shi"""

"Ummi ta shafa cikin ta ce ""Nima na gani, kamar girman yayi yawa a wata biyar, amma sai a sake hoton"""

"Sun jima suna hirarsu cikin nishadi, har ta nemi izininsa a kan zuwa duba Iya, an kai ruwa rana kan ya amince, ta ce"

idan Abdul zai tafi sai ta bishi

68 / 74