CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 74

102K to 105K   out of 219.4K words

zo ka yi mini bayanin"

"meyafaru?"""

"Cikin fusata hajiya ta rio rigar Sagir ta ce ""Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban"

"mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daWi ko?"""

"Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce ""Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku Wauki zafi a kan abun da ba a"

"gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi hauri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating Win sa, dan Allah ka yi hauri yaya Sagir"" wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya rieta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi."

"""Jarrabawa ce mai buatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka"" raihan ya faWa da sigar rarrashi."

"Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaSawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaWarta ya ja ta suka bar falon"

yana rarrashinta.

"""Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta wace mini Wa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba."

"Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba Waya, haka ta haura ta ajiye ta tafi"

kitchen dan yin sanwar dare.

"Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buata, domin kuwa barin gidan za ta"

yi.

"A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu."

"Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar"

isha'i.

"Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taSa yi ba."

"Raihan yana maale da Hajiya, dan tun Wazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta."

"""Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daWe ina"

nazarinsa kafin yanke shi.

"Daga yanzu Raihan zai rie office Wina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring Win ayyukan"

"sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko Waukar ma'aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka rio Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son's Limited."

"Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaWa guWa tana faWin ""araminsu"

"babbansu, ka ga Wan aramin sauro mai hana giwa bacci"""

"Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce ""Allah ya tayaka rio babana, Allah ya tsare mana kai"""

"Raihan kuwa miewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daWi ko kaWan Allah ya gani baya so, kuma ya udirci a watse ya samu Alhaji."

Ayshercool

0808012143

What's app only please

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P27

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daWi da amshi."

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki

Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

27

"Mami har ta yinura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya,"

ko zata ga damuwa ko Sacin rai a fuskarta.

"Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan Win, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai"

"Salim ya Sata fuska ya kalli Alhaji ya ce ""Yanzu idan muna buatar wani abun sai mun je wannan yaron anin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai"""

"Sagir ya ce ""Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in"

"sake neman wani abu a wurinsa wallahi"""

"""Sagir...."

"""Shhhh"" ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su."

"Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba Waya ransa babu daWi, saboda sam bai yi farinciki da wannan al'amarin ba."

"Har kusan sha Wayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a"

daren dole zai dawo ya neme shi.

"Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse."

"Alhaji bai Wago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce ""Alhaji"""

"""Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daWinka zaka fara bujure mini"""

"Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce ""Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi"

"kaima ka san na yi ananta da wannan al'amarin, kuma nine arami kar yayyena su ji babu daWi a kan hakan"""

"""Raihan"""

"""Na'am""."

"""Ba lokaci Waya kuma kai tsaye na yi assigning Win ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu'a, kuma na jarrabaka ta kowane Sangare, kai Win ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake Waukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka"

"ba ma? Wani a waje bare ka ke so na Waukko na dana masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace"""

"Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce ""Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?"""

"Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa,"

da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar.

"Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi ""Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala"

"mana, kar ka watsa mini asa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buata i will assist you like a ghost"" yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi."

"""Alhaji ka Waureni da jijiyoyin jikina, kana faWar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku""."

"Yayi dariya ya ce ""Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending Wan uwanka, ka dawo ka"

"bashi hauri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata""."

"Raihan ya jinjina kai ya ce ""Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce""."

"Alhaji ya sake dubansa ya ce ""Wace ummi kuma?"""

"""Baka santa ba, awata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataila kaina ya daina ciwon""."

"""To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulWarmu da ma'aikata, da gabatar da kai"

"a matsayin sabon MD""."

"""Alhaji rion warya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?"""

"""Tashi ka tafi sai da safe"" kamar soko raihan ya tashi ya bar Wakin ya nufi Wakinsa."

"Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya Waga."

"""araso sashina ina son ganinka"" ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi."

"Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, ""Mami, baki yi bacci ba?"""

"""Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido Waya. Uban me"

"ka je ka cewa Alhaji?""."

"Kai tsaye raihan ya ce ""Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muamin nan""."

"""Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya waci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?"""

"Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haiance ta din ga yi masa faWa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban"

"abun da ya bashi mamaki, irin huWubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya."

"Ta kafa wa Hajiya ahon zua, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haWe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an"

"yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaWai ne a an Wakinsu suke shiri"

"da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba."

"Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta Soye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara"

"shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi Waukar hankalinta."

"Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya Wagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana"

sake kiran wayarsa farida ta shigo Wakin.

"Gabanta ne ya Wan faWi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta yallin man da ta shafa, ga amshi da Wakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar"

da kai tana danna waya.

"""Ke!"" Ta daka mata tsawa, ummi ta Wago da sauri, ta ja hijjabi ta saka."

"""Dalla ki tashi ki wuce ki Wora mana abincin dare"" kallonta ummi take da mamaki, Wazu taje tayi girkin ta koreta ta ce"

"ba ta buata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi."

"Da ""To"" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen."

"Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an i ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta WanWana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai"

male-male a kai.

"Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta uduri aniyar"

"untata mata, kausar ta yi girki ya i ciyuwa."

"A daren ta tua tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma Waki."

"Missed calls Win raihan ta tarar, da message ""Call me when you are available"""

"Ba Sata lokaci ta kira shi, ya Waga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce ""Ka kyauta raihan""."

"""Da na yi me?"""

"""Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka i Waga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi arfin kuWina, kuma ka dawo mini da kuWina har da ari, kafi arfin"

"abun hannuna ko?"""

"""A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban""."

"""Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karSi kuWin nan and am serious"""

"Ya gyara kwanciyarsa ya ce ""Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ara mini damuwa"""

"Sai kuma ta nutsu ""Wace irin damuwa kuma?"""

"""Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki"""

"Ummi ta ce ""Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini"""

"""A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo"""

"""To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?""."

"""In sha Allah, sai da safe"" suka yi sallama, ta gyara shimfiWarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, amshin"

da yake tashi a jikinta sai nishaWi take yi.

***

"""Anty Rakiya, ai in gaya miki da yar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faWi wannan sanarwar da yar na yi barci saboda murna, shi Wan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so"""

"Rakiya ta ce ""Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar"

"aan can gaba ta kai ki Bilki""."

"Mami ta ce ""Can gaba ma, kuma oari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na"

"are masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruWin kuWi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riewa"""

"Yaya rakiya ta ce ""Ke bilki"""

"""Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan"

"kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuWi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma"""

"""Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haWa shi da Safiyya, ayi ar gida kawai"""

"Mami ta ce ""Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuSe shi da zancen idan har ya"

"amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ara sanya ma'aikatan su girmama shi"""

"Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ara ziga mami, da yadda za ta Sullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da"

"kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haWa shi da Safiyya, dan arafafa zumunci."

***

"urii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya."

"""Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, arshe na"

"rufta kuma kin zo kina dariya"""

"""To ai kai Win ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD"" hararta yayi yana kallon wayarsa."

"""Attention"" tayi maganar tana kallon sa."

"Ya juyo yana kallonta shi ma ""Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka"

"ne"" ya haWa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido."

"Ummi ta ce ""Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan"

"manta da shi ba, ina fatan Allah ya haWa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane."

"Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuWi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka rie gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka asantar da kowa, yayyenka annenka ma'aikatanka da duk wani na arshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah."

"Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaWe-kaWen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun i."

"Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinurin"

"mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka"

"da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka rio Muhammad Raihan"""

"Jikinsa gaba Waya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake Waure shi da jijiyoyin jikinsa."

"""Ummi wallahi an scared, ba zan iya

35 / 74