CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 74

138K to 141K   out of 219.4K words

mutane ne, idan muka ce a ™ara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara"""

"Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano."

"Ummi taga gata da ™auna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa"

"ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faWan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen."

"Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai Waga mata hankali ba."

***

"A ka yi bikon raihan da ™yar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake ""ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne""."

"Hajiya ta ce ""Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka"""

"Raihan ya ce ""Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai"

"sake faruwa ba"""

"Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya"

tarar da sabon Sacin rai.

"A bedroom Win ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya dur™usa ya ce ""Mami barka da gida"""

"Maimakon ta amsa sai ta ™ure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa."

"""Ai gara in ™are maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har"

"ubanka? In haifi Wa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ™aunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ™ara ta ta kira ni ta ci mini mutunci"""

"""Wallahi mami ba ™ararki na kai ba"""

"""Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan"

"gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu Wari biyar Win ta isa komai da komai"""

"Cikin damuwa raihan ke ™o™arin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata Waki."

"Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ™aunarta"

"amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu Wari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa."

"Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata"

banza ya ™yale ta.

"Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daWi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daWewa ba."

"Ummi a gabanta aka fara haWa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ™asa ana"

tsuma su.

"Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure."

"Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba."

"Mami ta ™ara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son"

"wula™anta Wan Adam irin na raihan, ™arshe sai da yayi blocking Win ta, dan ta daina damunsa da kira."

"Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta"

kusa dawowa.

***

"Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma Waukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ™waya biyu da ta je da su, sai da aka Winka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haWa kayan gyaran jiki masu haWe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi."

"Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haWa"

mata.

"Mariya ta kalli dr. Ta ce ""Ka yi mini al™awarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba"""

"""To ai zaka dawo da ita ko?"""

"""In sha Allah"""

"""To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka"""

"""In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai"""

"Ta kalli ummi ta ce ""Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ™yuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga"

"dukanki kin ji ko?"""

"Ummi ta ri™e hannunta ta ce ""To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?"""

"Ta Wan yi jimm sannan ta ce ""Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke"

"ba"""

Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daWi.

Da ™yar suka rabu suka nufo hanyar Kano.

"Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta."

"Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo."

"Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta"

san matsala ce ta kawota gida.

"Ummi ta koma Wakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta."

"Noor ta ce ""Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka"

"dawo ko?"""

"Ummi ta ce ""Ban sani ba"""

"Suka din ga dariya, noor ta ce ""In gaya miki, Inteesar mijinta ya Wauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba"""

"""To waye ya tambaye ki?"""

Noor tayi shiru tana ™ifta idanu.

"Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna."

Haka nan ta samu kanta da yin shirin haWuwa da shi.

"Ta Wauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karSe ba tare da godiya ba."

"Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta Waura Wankwali, abu ya gagara saboda ba ta"

"saba ba, ™arshe noor ce ta Waura mata da ™yar, shima gashin ya ™i rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka Waura Wan kwalin."

"Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta"

"ce ""Anya in fita a haka kuwa?"""

"""Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma"""

"Da ™yar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ™arasa in da yake."

"""Oyoyo sweetheart, long time"""

"Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe."

"""Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Tana lafiya ™alau"""

"""Kin bata labarina kuwa?"""

"Ummi ta ce ""Idan na yi mata babu lallai ta gane ma"""

"Ya ce ""Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai"""

"""Ka gama yajin?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Ke ma haka zaki ce?"""

"Ummi ta ce ""To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?"" Yayi dariya ya ce ""Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da"

"sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna"" ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta."

"Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta."

"Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma"

shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta

"Cikin gadara ta ce ""Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki Wora ba,"" tayi"

maganar cike da son wula™anta ummi a gaban raihan.

"Raihan ya ce ""Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana bu™atar hutu, tun da yau ta dawo daga"

"tafiya, kuma ina bu™atar yin magana da ita"""

"Zare ido ummi tayi ta ce ""Na shiga uku, raihan"""

"""Shhh"" ya Wora yatsansa a kan lips Win sa yana zare mata ido."

"Ya sake kallon kausar ya ce ""Ki koma ki ce ba za ta yi ba"""

Ayshercool

8081012143.

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

34

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE

AYSHERCOOL 08081012143

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

"Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon."

"Raihan ™ararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar"

"falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murWa mata."

"Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuSe."

"""Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya"

"goWai-goWai da kai sai ka auri yarinyar da Wan ka ya ce yana so?"""

"Alhaji Tahir ya ce ""In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza"

"abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ™ara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya"" ya ™arasa maganar tare da Waukar wayarsa ya fita."

"Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya."

"Rakiya na Wagawa mami ta fashe da kuka, ""Anty rakiya na shiga uku na lalace"""

"""Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?"""

"""Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haWo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini"

"mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa"""

"Anty Rakiya ta ce ""Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a"

"matsayin sirika"""

"""Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana Waya yake yi ko ta yi maka daWi, ko kuma"

"akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?"""

"Anty Rakiya ta ce ""TaS, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi"

"™arfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa"""

"Mami cikin takaici ta ce ""Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba"

"zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karSo kuWin auren nan, shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ™i aure ya lalace yaya zan yi?"""

"Anty Rakiya ta ce ""Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya"""

"""Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?"""

"""To ki koma ki samu babansa ki lallaSa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan """

"Mami tayi ajiyar zuciya ta ce ""Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima"" ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki,"

ita ba mai asma ba.

***

"Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce ""Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Idan sayar da ni Win ma ka yi ai na saidu kawu"""

"Yayi murmushi ya ce ""Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar"

"nan"""

"""To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta"""

"Ya amsa mata da ""amin"""

"Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi,"

har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?.

"Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tu™insa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci."

"Ta tuno lokacin da ya Waukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin ri™onta da yayi"

"A ranta ta ce ""Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai"

"da zuriyarka""."

"Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita."

"""Mamana tashi mun zo"" a hankali ummi ta motsa tare da buWe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa"

"komai ba, sai bin wurin da kallo."

"˜ofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya Wan daddana ya kara a kunnensa ya ce ""Gamu mun zo"""

Wani matashin saurayi ya le™o ya dur™usa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga.

"Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Al™ur'ani"

bugun warshi a gabansa.

"Dattijon ya mi™e tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta Waga ni™abin fuskarta ba, sai dai ta"

"shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa."

"Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa."

"Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina"

kallonta.

"Dr. Ya ce ""Ina mutuniyar kuwa?"""

"""Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya Wan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a Wora"

"muku girki, ai bamu san zaku zo ba"""

"Dr. Ya ce ""Ai al™awarin da na Wauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo""."

"Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banWaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiWa tana hutawa,"

saboda gajiyar da tayi.

"Ummi ta Wan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a Wora sanwa."

"Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam."

"Dr. Ya ce ""Malam ba ka ganni da ba™uwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba"""

"Malam yayi murmushi ya ce ""Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai Wakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da ni™abi"""

"Dr. Yayi murmushi ya ce ""Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?"""

"Ummi ta ce ""Na sanshi amma na manta a ina?"""

"""To ki cire ni™abin ko zai gane ki"""

"Ummi ta jinjina kai tana ™o™arin cirewa, aka yi sallama."

"Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ™irjinta ya buga da ™arfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ™irjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa."

"Malam ya ce ""Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi ba™i tafiyayyu daga kano"""

"Ta ce ""Baban ummi ne?"""

"Malam ya ce ""Eh shi ne, tun da shikaWai ki ka sani a kanon ba"""

"Shigowa suka yi tare, tana ri™e da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur."

"Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda"

"™irjinta ke lugude. Gaba

47 / 74