CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   73 / 74

216K to 219K   out of 219.4K words

zan zo duba ki ba, Allah ya baki lafiya"""

"Rahama ta ri™o hannun ummi ta ce ""Ummi ba zan musa ba, idan aka ce alhakinki ne ya kamani, na san mun azabtar"

"da ke, wallahi tun da na yi aure ko amarci ban gama ci ba, na fara shan wahala har yau ban samu kwanciyar hankali a gidan aure ba. Dan Allah ki yafe mini"""

"Ummi ta shafa hannun rahama ta ce ""Na yafe miki wallahi, Allah ya yafe mana baki Waya, Allah ya baki lafiya bari na"

"je falon na ji kamar kukan aiman"" ta mi™e ta fita."

"Farida ta kalli noor ta ce ""Sannu sallalamammiya, ashe kin canza uwa ko?"""

"Noor ta ce ""Idan na yi miki laifi fa ce wa ki ke yi na nemi wata uwar, dama ke ba uwata ba ce, ki yi ta hantarata da"

"zagina, ni kuma bana jin daWi ni ki ka tsana ban san me na yi miki ba"" sai jikin Farida yayi sanyi, ta tuna maganar ummi, ba ta taSa zaton abun da tayi zai yi tasiri a zuciyar noor ba."

"Ta basar ta ce ""Da uban wa aka saka miki rana ban sani ba?"""

"""Yayan yaya raihan ne, yaya salim"""

"Kausar da ke gefe tana danna waya ta ce ""kutt wannan gandamemen mutumin, me yayi miki zafi?"""

"""Ni kar ki yi mini hassada, haka kurum in tsufa a gida, ke da ki ke kyau ma baki yi aure ba, balle ni ba zaki zigani ba"""

suka hau faWa kasancewar kwana biyu ba su haWu ba.

"Farida ta tsawatar musu, sannan ta koma kan rahama da masifar, uban me suka yi wa ummi da take neman"

yafiyarta.

"""Ashsha! Yaya ki farga kema kan lokaci ya ™ure. Kin san mun azabtar da ita, ke ki ka gaya mini halin da Iya take ciki, ni"

"dube ni wallahi hakki ne"""

"""A'a ni ban Wauki hakkin kowa ba, dan haka ba wata yafiya da zan nema, ta daWe ba ta yafe ba""."

"Ummi kuwa na komawa falo, ta tarar da inteesar tana zaune ta zuba wa yaran ido, ta saka hannu ta Wauki aiman da"

ya tashi ya fara kuka.

"Tana Waga kai ta ga ummi ta ajiye shi, tana basarwa. Ummi ta yi murmushi, ta ™arasa ta Wauke shi, ta ajiye mata shi a"

"cinyarta ta ce ""Haba Wan gidan babban mutum, mamanka ce da ba ka santa ba, ka buWe ido ka kalleta"" Inteesar ta saka hannu ta rungume shi, ta fashe da kuka."

"Ummi ta san kukan me take yi, ta dafa ta ta ce ""Haba Anty intee, Allah ya baki rai da lafiya, kar ki yi masa butulci,"

"rashin haihuwa jarabta ce, ki gode masa ki yi addu'a idan ki na da rabo, Allah ya baki naki kema. Zan taya ki Addu'a in sha Allah zaki ga Wanki, Allah ya baki rabo a satin nan, ni na yi biyu ke ki yi uku, mu tarawa kawu abokan wasa"""

"Cikin kuka ta ce ""Aurena ya mutu ummi, uwar mijina ta saka ya sakeni, wai bana haihuwa sai ci da kashi. Sun"

"wula™anta ni, sun tozarta ni, Abba ya ce babu ruwansa na ™arata na nemi wani uban. Zuciyata za ta fashe ummi, gashi tun da na dawo kausar ta mayar da ni kamar ma™iyiyarta sai raini da wula™anci ita kanta maama tayi ta hantarata, wallahi ji nake kamar na sha guba na mutu"""

"Da sauri ummi ta toshe mata baki, fuskar ummi Wauke da hawaye ta ce ""Haba anty inteesar, mutuwar aure ba kan ki aka fara ba, ba kuma yana nufin ™arshen rayuwarki bane ba. Abba kuma kun yi masa laifi yana gaya mini, kun tafka"

"kuskure da kuka daina kula shi, ko gaishe shi ku ka daina yi, dan ya auri mamana. Ku ka manta da duk Wawainiya da hidima da ya yi mana a rayuwa."

"Ki kwantar da hankalinki, ki nemi afuwarsa nima zan taya ki ro™onsa, na san zai yafe miki. Abu na gaba kuma, ki yi ta"

"addu'a da mi™a wa Allah lamuranki, idan ki ka gama idda, ki ro™i Abba ya bar ki, ki koma karatu, ko ki fita ki koyi wata sana'ar hakan zai rage miki lokacin da ki ke spending a cikin gida da su Anty farida, amma dan Allah kar ki sake cewa zaki kashe kanki"""

"Inteesar ta kwanta a jikin ummi ta ce ""Ba ki san me nake ji ba"""

"""Na WanWani fiye da abun da ki ka WanWana, da ko ma™iyina bana fatan ya WanWana. Sai da ta kai a duniya ina jin"

"kamar nikaWai aka tsana, na sha jin nima kamar na kashe kaina, a lokacin da bani da kafaWar kashingiWa na yi kuka, noor ce kawai take tayani kuka, sai zuwan Baban su iman rayuwata, ya nuna mini ita rayuwa yadda ka Wauke ta, haka take zuwar maka. Dan Allah ki daina wannan kukan""."

"Ummi ta yi ta rarrashin inteesar, Farida ta fito tana faWin ""Ke Inteesar kukan me ki ka yi mata?"""

"Inteesar ta share hawayen ta, ta ce ""Babu abun da tayi mini, mi™o mini macen na ganta"""

"Ummi ta mi™a wa inteesar iman, ta haWa su ta rungume, tana cigaba da zubar da hawaye."

"Duk yadda farida ta bugi cikin noor, a kan ta gaya mata shirye-shiryen da ake ciki a kan aurenta, amma tayi mursisi"

tayi shiru.

"Sai da suka yi faWa, ta ce noor ba za ta bi ummi su tafi ba."

"Sai ga inteesar ta sake da ummi, tana ta bata labarin irin zaman da ta yi a gidan aurenta."

"Ummi ta ce ""Babu auren da ba shi da ™alubale"" nan ita ma ta din ga ba ta labarin irin ™alubalen da take fuskanta."

"Ummi ta din ga jaddada mata, ta nemi yafiyar dr."

Raihan ya kira wayar ummi ya ce yana waje.

"Noor ta kwashi takalmanta da gudu, ta yi waje saboda farida ta ce ba zata bar gidan ba."

"Ummi ta je ta ajiye wa rahama kuWi, suka yi waje."

"Inteesar ta raka ummi da jariran nan, kamar kar ta bawa ummi su, har ta yi wa ummi al™awarin zuwa har gida ta yi mata barka."

"Daga nan suka wuce gidan mariya, tayi murna sosai da sosai da zuwansu, aka yi sa'a dr. Yana nan, ummi ta yi masa"

maganar inteesar.

"Ya ce ""Inteesar tsakanina da su ai sai ido, ni da ban ishe su kallo ba"""

"Ummi ta ce ""Mun yi magana da ita kawu, dan Allah ka yi ha™uri, za ta baka ha™uri ma. Ta fara i™irarin shan guba ta"

"kashe kanta, dan Allah ka yi ha™uri ka ja ta a jiki dan Allah. Mun yi hira da ita sosai, ta fuskanci ™alubale sosai a gidan aure, sai dai anty farida ba ta din ga ba ta shawara ta kirki ba"""

"Ummi ta cigbaa da lallaSa shi, har ya amince."

"Noor tun da aka saka ranar aure, take wani irin jin nauyin Salim, idan ya zo duk surutun ba ta iya yi masa."

"Kausar kuma hankalinta ya tashi, noor za ta yi aure ta bar ta, duk samarin nata babu na aure sai ´an sharholiya."

"Mariya kuwa, Abdul ne zai kai ta maiduguri, ummi kuma da ita da noor, raihan ya tafi da su bauchi, daga can idan"

suka kwana biyu su tafi maiduguri.

"Hajiya Aisha ta din ga murna, dan dama raihan bai taSa kai mata ummi ba."

"Ranar da suka sauka da magariba, Hajiya Aisha ta kira wata a waya, ta ce ta shigo yau ga matar raihan su gaisa."

"Ummi na zaune a kan sallaya tana lazumi, ta ji muryar da ko a mafarki ba zata manta mai ita ba."

"""Ina amaryar tamu, yau Allah ya yi zamu haWu, na ji kunya ni ban je ba su gasu a garinmu"""

"Raihan da yake bawa yaransa madara ya ce ""Aikuwa dai kin ji kunya yasin, kuma na daina uwar Wakin da ke"""

"""Amma dai ka san uzurina, bama gari amma tuba nake, dolena na je Kano, Mummy ki taya ni bayar da ha™uri"""

"Hajiya Aisha ta ce ""Kun fi kusa ni babu ruwana""."

"""Anty Na'ima"" ummi ta yi maganar cikin rawar murya."

"Na'ima ta waro ido ta ce ""Ummi, ummi ke ce"" da gudu ummi ta ™arasa jikin na'ima suka rungume juna, ummi na"

"kuka"""

"Na'ima ta Wago ta ce ""Ummi, dama zan sake ganinki? Kan rasuwar mama duk lokacin da na je gagarawa sai na"

"tambayeki, ace mini ki na kano, bayan rasuwar mama na daina zuwa, ummi me ki ka zo yi nan, zan sake ganinki dama""."

"Mummy ta ce ""Ikon Allah, ai ita ce matar babban mutum"""

"Na'ima ta waro ido ta ce ""Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, ummi na san ba zaki wula™anta ba a"

"rayuwa, raihan ummi ™anwata ce, dan Allah ka ™ara ri™e mini ita da kyau, ta sha wahala a rayuwa"""

"Raihan dai ya din ga bin su da ido, da ™yar suka bar kukan. Na'ima yaron mijin Hajiya Aisha take aure, shi ne, shi ne babban yaronsa, dan shi ne babban manager, kuma lokacin da raihan ya zauna a bauchi, gidanta yake zuwa yawon"

"cin Wan wake, suna zaman mutunci sosai."

"Ummi ta fara basu labarin, gudunmawar da take iya tunawa, da Na'ima ta yi mata a gagarawa."

"Raihan ya ce ""Salma, ku daina tuna abun da ya wuce, anty na'ima in dai ummi ce, ba zan sake barin tayi kukan"

"wahalar rayuwa ba""."

"Na'ima ta ce ""Ummi ina Anty mariya?"""

"Nan ummi ta bata labarin suna tare, da yadda gagarawa ta koma."

"Ai har kusan sha biyun dare, Naima suna tare da ummi, kuma ta yi wa ummi al™awarin zuwa kano."

"Kwanansu biyu a bauchi, suka tafi Maiduguri."

"Mariya sai Soye-Soye take yi, dan kar a ga cikinta, ita kuwa ummi tuni ta gano ta."

"Gagarumin taron family aka shirya, ™aton hall na gaske, da ya haWa da manyan mutane daga sassan ™asar nan,"

"wanda suke duk ´an uwa ne, ba tare da sun san ´an uwa bane ba."

"Riahan ma yana wurin, noor ta ce ""Yaya ummi, kin ga har da larabawa a ´an uwanku""."

"Aka rarraba musu sovenir, wanda a ciki yake Wauke da littafi da ya bayar da asalin su."

"Asalin mahaifin kakan su mariya ta Sangaren uba, balaraben ™asar tunus ne. A yawon fatauci ya auri wata ´ar"

"somalia, ya taho da ita Nigeria, yawon fatauci, jin daWin zamansa a Nigeria, ya sanya ya cigaba da zamansa a Nigeria, ya auri wasu matan ya hayayyafa."

"Bayan rasuwarsa, galibi duk suka kama gabansu, ita ta somalia ta koma ™asarsu, manyan ´a´anta da suka riga suka girma a Nigeria, basu bi ta ba suka yi auratayya a Nigeria, duk suna jin turanci, larabci da wasu yarukan na Nigeria."

"A taron har da ire-iren dangin su na tunusiyya, da wasu daga cikin dangin matar nan ta somalia."

"Kuma Sangaren su ummi, suka faWo a Sangaren matar nan ta somalia."

"Ta ™aton allon majigin da yake Wakin taron, aka din ga nuna hotunansu, wanda da ka kalla ka san na da ne, sai dai da"

"aka zo kan matar nan ta somalia, duk da tsohon hoto ne mai black and white, sai da na kusa da ummi suka juyo suna kallonta."

"Kamarta Waya da matar, sai dai shi mutumin, brown Win gashi ne da shi, haka zalika yaron hannun raihan aiman"

kamarsa Waya sak da mutumin.

"Raihan ya ce ""Allahu Akbar, sweetheart ashe can ki ka tafi ™arshen dangi, ki ka kwaso mana kamannin larabawa. Su Aiman ma haka"""

"Ummi na zaune ta ga an fara zagayeta ana kallonta, sai larabci ake yi mata a ka."

"Aka kamo hannun ummi, aka fita da ita kan stage, tare da sake nuna hoton matar nan, a ™alla kakarta ta huWu"

kamanninta ta Waukko.

"Sai da mariya ta yi kukan daWi, mussman idan ta tuna yadda aka din ga wula™anta mata ´a, da i™irarin cewa ba ´ar"

su ba ce ba.

"Galibin wanda suka zo taron daga somalia, duk brown eyes ne da su, irin na ummi."

"Sai taro da kallo ya koma kan ummi, aka din ga Waukar hotunanta, duk yadda raihan yake kaffa-kaffa da yaran nan da"

"matarsa, haka ya zuba ido yau, dan sosai yaran suke kama da wannan mutumin na tunusiyya."

"Gaba Waya taro ya koma kan ummi, aka din ga basu kyaututtuka da ita da yaran, aka ce har gidanta za a bayar da"

"wakilci, aje a ga in da take zaune, kuma za a bata mu™ami a shugabancin jagorancin haWa kai da tattaro kan sauran iyalan."

"Ba ummi ba har raihan da mariya sai da aka gabatar da su a wurin, aka gabatar da shi a matsayin MD na Tahir and"

son's.

Ummi ta ga manyan mutanen da ba ta taSa tunanin ganinsu ba.

"A matu™ar gajiye ummi suka koma gida, da a ranar raihan ya ce su koma kano, amma gajiyar da suka yi sai da suka"

bari su kwana.

"Labari har a gidajen jaridu da radiyo, aka haWa hotunan ummi da na matar mai suna Alina, da kuma su Aiman da"

"balaraben tunus, yadda yara suka Waukko kamanin kakansu na biyar."

"KuWi kuwa ummi ta same su, Alhaji Tahir suna kano ya kira raihan, yana gaya masa suna gida suka ga taron su ummi."

"Ummi dai a satin sai da ta zama cele, ko ina zancenta ake yi."

"Kamar yadda ummi ta bu™ata, dr. Ya yafewa inteesar kuma ya ce ta cire tunanin tsohon mijinta daga ranta, ta gama"

"idda, zai yi ™o™arin ganin ta koma makaranta."

"Raihan da kansa ya je gidan su, ya samu mami ya ce ""Mami, ina fatan zuciyarki ta wanke daga zargin da ki ke yi, na"

"cewar su aiman ba yarana bane ba"""

"""Na ji, ni matarka ce ba na ™auna, kuma ba zan taSa ™aunarta ba"""

"Ya ce ""Na sani, ita ma ta gaya mini na daina wahalar da kaina ba zaki taSa ™aunarta ba, amma ina ro™on kar hakan ya shafi yarana""."

Tayi masa banza ba ta kula shi ba.

"Na'ima sai da ta zo Kano, gidan ummi, har wurin mama suka je."

Mariya ta ji daWin haWuwa da Na'ima sosai da sosai.

"An kawo lefen nihal, sai dai wasu abubuwan duk babu, tun da kuWi ya bata ta haWa abun ta da kanta, ya zo ya Wauka"

ya kai gidansu aka kawo.

"Sai dai babarsa da yayyensa duk suka ciccire wasu abubuwan, ita kuwa ta ce masa ko dai a dawo da abubuwan da"

"aka cire, ko kuma ta fasa."

"Ya je gida yana masifa, uwar sa ta ce idan ba sa so, ya je ya karSo kayan, tun da ba ´ar gold ba ce ba."

"Aka din ga kai ruwa rana, Mami ta ce su zo su kwashi tsiyarsu."

"Alhaji ya ce ba za a mayar da shi ™aramin mutum ba, neman auren ´ar sa a hannunsa yake ba hannunta ba, dan haka ba za a mayar da lefen ba, shi zai sayi abun da babu a saka."

"Hajiya kuwa suna ta shirin bikin Salim, Sangaren ummi ma, ita da mariya ke ta shirin bikin noor, farida ta zama ´ar"

kallo.

"Rahama ta warke, sai dai ga zawarci, ga inteesar ga kausar duk a gabanta."

"Ummi da ta je ta ga Iya, ta tsorata. Gaba Waya kamaninta sun sauya, jikinta har saSa yake yi saboda tsabar kwanciya, ba a Waga ta a gyara mata jikinta. Ga Wakinta duk ya rushe, ga kuma abun da aka ce Idris yayi, ´ar sa nana ma ta"

"gudu, babu wanda ya san in da take."

"Watan ´an biyu shida, mariya ta haifi Wanta namiji, murna a wurin dr. Ba a magana, aka saka masa sunan baban"

ummi.

"Ummi na ta shirin auren ™anwa, kuma ´ar da ta raina, sai haWeta ta take yi da kayan gyaran jiki kala-kala, tare da yi mata nasiha da addu'a."

"Noor da sassafe bayan raihan ya fita, ta samu ummi ta ce ""Yaya ummi, kin san meyafaru?"""

"""A'a"""

"""Muna waya da shi da asubar nan, yake gaya mini wai yayar raihan, jiya da daddare ta dawo gida"""

"Ummi ta ce ""Maybe zuwa ta yi ganin gida"""

"Noor ta ce ""Akwai magana, gaya mini ne ba zai yi ba, ba ganin gida ta zo ba, ban tambaye shi ba ya fara gaya mini,"

"bai kai ™arshen labarin ba ya wani maze ya canza labarin. Ni ya fara bani tsoro ma"""

"Ummi ta ce ""Tafi can, ba wani tsoro kar ki yadda mijinki ya baki tsoro, abokin rayuwa ne, kuma aure tausasawa ce a"

"ciki. Nima fa kan na yi aure sai da ya fara bani tsoro, yadda ya canza mini, amma daga baya komai normal"""

"Sai dai da azahar bayan raihan ya dawo, yake gaya wa ummi cewar, Maryam ta kama mijinta da wata a gidanta, tayi"

"magana ya kamata yayi mata dukan tsiya, jikinta duk jini ta Waukko mota ta taho gida."

Ummi kuwa ta jajanta ta ce Allah ya kyauta.

"An kai ruwa rana sosai da sosai, maryam ta ce ba zata koma gidansa ba, ta daWe tana zarginsa ba ta tabattar ba, sai da ta kama shi red handed."

"Ana tsaka da case Win maryam, aka yi auren nihal, sai dai a yanayin yadda aka yi bikin, zaka san iyayen mijin ba su da"

kirki.

"Aka jinkirta buWe kamfanin su raihan na Abuja, sai an yi auren Salim."

"Alhaji ya yanke raihan ya koma Abuja, Salim ya ri™e Kano."

"Raihan ya ji daWin hakan, saboda Ummi ta samu chance na reapplying aikin gidan jaridar, da suka taSa gayyatar ta ya"

hana.

"Lokaci-lokaci inteesar na zuwa gidan ummi, ummi kamar babu abun da ya faru, haka za su yi hira su ci abinci, ta"

kawo alkhairi ta yi mata.

"Ta kan yi amfani da damar, wurin nemawa farida afuwar ummi."

"Ba yadda ´an gagarawa ba su yi da ummi ba, da dr. Akan su taimakawa Idris, a fitar da shi sharri aka yi masa, ummi ta ce babu ruwanta. Dr. Ya ce kar wanda ya sake kiran ummi, ya ce tayi masa wani abu, ba zaman kanta take yi ba, a"

™ar™ashin wani take.

"Tun ana ™o™ari a kan case Win nasa, har aka Satar da file Win shari'arsa."

"Ummi da za ta bar kano, gaba Waya furniture's Winta, raihan ya canza mata."

"Ta Wauki nata ta bawa mama, na mariya kuma masu kyau, ta bawa matar yaya magaji."

"Bikin noor ne kawai ya zaunar da ita, aka yi gagarumin biki, aka din ga taya Hajiya murna, an samu Salim yayi aure."

"Duk irin tarin miskilancinsa, da rashin son wargi, sai da yaba wa noor, dan

73 / 74