Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Cutarwa Complt Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 74

99K to 102K   out of 219.4K words

kasuwanci, muna shigo da kayan gini daga asashen etare, ana bamu kwangilar kayan gini, na ofisoshi, manyan ma'aikatu na gwamanti da na an kasuwa, kuma muna"

rarraba wa kamfanoni da yawa kayanmu a Nigeria da asashen mawabta.

"Ya kunna system Win gabansa, ya shiga nuna mata kayayyakin da suke sayarwa, kama daga ofofi, furnitures, kayan banWaki, da sauran kayan alfarma na awata gini."

"""angare guda, mahaifinmu babban dealer ne na shige da ficen kayan masarufi, sai dai an fi saninsa da harkar"

"kayan gine-gine, iya kano muna da shaguna sun kai goma sha biyu a wurare daban daban ban da sauran garuruwa. Mahaifinmu duk shi yake kula da ayyukan kasuwancin sa, sai ma'aikatansa wasu lokutan a cuce shi a karkatar da kuWaWen sa, babu mai taimakonsa a cikinmu sai dai ya nemo mu kashe."

"Wannan shi ne babban ofishinmu na asa, duk da ya ce zai mayar da shi Abuja, duk da haka mukan tafka asara wasu"

"lokutan, amma hakan ba ya sanya mahaifinmu shiga hakkin ma'aikatansa, idan an samu riba da yawa kuma, ya kan ara musu domin farincikin su da mu baki Waya, to kuma duk da wannan abun sai azo da son zuciya mu aa cikinsa mu din ga cutarsa duk oarin da yake yi mana?"""

"Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Raihan, na ji duk abubuwan da ka faWa, ka na da gaskiya, amma still ka yi kuskure, ba"

dan Allah ya fi sonka ya sanya ka zama shiryayye ba har Alhaji yake janka cikin al'amuransa ba.

"Yayyenka na buatar kulawarka da tausayawa, a wannan halin suna sama da kai, amma ace sai ka yarje musu yin"

"wani abu, ka yi tunanin yaya za su ji? Ka na da gaskiya, amma kamata yayi ace ka yi oarin dannewa kun rabu lafiya, abun da ka yi masa bai kyautu ba gaba Waya."

"Raihan komai lokaci ne, ina sake jaddada maka, ranar da ba sa doron duniya sai ka din ga ina ma ace, ni ba gani ba,"

"sha'awa ku ke bani, mahaifina ya rasu, mahaifiyata ban san in da take ba, bani da wa, ba ni da ani, haka nan kawai dai rayuwa nake yi. Duk da ka ce yayyenka basa ji, but they are blessing to you idan ka kallesu an uwanka ne, ban ce ka yale su su yi abun da bai kamata ba, amma gaba suke da kai, su yakamata ace a wannan position Win, amma Allah ya addara kai ne ba su ba, haba Raihan, why are you kind to me, amma brother's Win ka ka yi musu haka?"""

"Gaba Waya jikin raihan yayi sanyi ya ce ""Haka ne, na yi kuskure kuma na fahimce ki, in sha Allah zan kiyaye gaba ba zan sake ba, raina ne ya Saci sosai, kuma na yi oarin dannewa amma yayi pressing Win na"""

"""Yauwwa dan Allah ka daina, ba ka ' sanin muhimmancin wasu abubuwan a rayuwa, sai ranar da ka rasa su, wani"

"rashin idan ka yi sai ya tafi ya barka da rauni mai raWaWin da har ka koma ga Allah ba zai goge ba, kamar dai ni da na rasa babban masoyina babana, da barinsa duniya ya yi wa rayuwata giSi"" tayi maganar hawaye na kwararowa daga idonta, har jijiyar goshinta ta tashi."

"Raihan ya matsa kusa da ita ya ce ""Ummi, dan Allah ki daina koke-koken nan haka, Addu'a ita ce abun da mahaifinki"

"ya fi buatar mu yi masa""."

"Ta jinjina masa kai tana share hawayen ta, ya ce ""Ga lemo na sayo mana, na san is hardly idan kin karya, yau ba ki zo"

"mana da abinci ba"""

"""Na oshi, ba zan iya cin komai ba"""

"Cikin damuwa raihan ya ce ""Ni gaya mini menene ya saka ki kuka ma tun farko, kin ce zaki gaya mini"""

"Ta Wan yi shiru sannan ta ce ""A bar wannan zancen kawai"""

"""Ba za a bar shi ba, sai mun yi shi, ai alawari ki ka yi mini"""

"""Ai ba zaka gane ba""."

"Raihan ya ce ""Zan gane, ko ta ina ne yi mini bayani, ina cin maths a aji ai"" yayi maganar yana Wan murmushi."

"Ta Wan tsura masa ido, har cikin zuciyarta take jin yardar da ta yi wa raihan, ba arama ba ce ba, saboda sosai take"

"jin sa a ranta, mutumin da yake ta oarin fuskantar matsalolin ta."

"""Ina arama mahaifina ya rasu, kakata ta karSi riona daga hannun babata, nikaWai kuma suka haifa, mama ta koma"

"garinsu, an uwanta suka yi ta zuwa a basu ni, amma kakata ta hanasu ni, aka ce mamana ta haihu Wan babu rai, ga damuwar rabamu, ta samu larurar wawalwa, amma aka hana su ni, har an uwan mama suka yi fushi, basu sake zuwa sun ce a basu ni ba."

"Abubuwa suka Wan faffaru, har kawu yahaya, ya Waukkoni daga gagarawa ya dawo da ni nan, tun da ya kawo ni, ake ta samun issues da family Win sa, Allah dai yayi sai na zauna a gidan, yanzu ma dai wata rigimar ce ta taso, matar kawuna ta ce zan bar gidan na koma auye, ni kuma bana son komawa garin nan wallahi, mamana nake son gani, wallahi ko ba ta warke ba ko bola take bi, zan bita bolar mu rayu tare da dai in koma wannan garin da ko sunansa bana son ji, Raihan aalla na kai shekaru goma sha takwas rabona da mama, kuma ban ji labarin ta rasu ba, kowa yai gaya mini sunan garinsu abun da na sani kawai a Maiduguri take."

"Ba wanda yake kulani, duk wanda na raSa sai ya tsangwameni, an ce mini mummuna, an ce mini mayya, an aibata ni, to wai ya zan yi nema? zuciyata ta kusa fara ciwo, ban ma san ina na dosa a rayuwata ba, tun a kan cinyar mama nake ganin bala'i da tashin hankali, raihan tafiya kawai nake yi amma na san zuciyata na ciwo, wawalwa ta kuma kamar na haukace nima, abubuwa suna damuna, ba wanda yake zama na gaya masa ya zan yi?"" Wata irin karkarwa ummi take yi, tana magana ba comma babu full stop, wani Soyayyen abu ne da yake cin zuciyarta da ba ta taSa zama ta faWe shi ba, once in her life, yau ta samu chance."

"Babu tsammani ta durushe a asa daga kan kujerar, tana kuka mai sautin gaske."

"Raihan bai san lokacin da ya durusa, duk da dauriya da dakiya irin ta raihan, yau da aka zo gaSar da yake jira a zo,"

"ya ji wacece ummi, ya ji sai dai zuciyarsa ta gaza Wauka, zuciyarsa ta karye, ashe da ba tausayinta yake ji ba, kallonta kawai yake yi bai san meye a unshe a zuciyarta ba, a hakan ma ba wai buWa masa rayuwar ta tayi ba."

"Shekara sha takwas, ba ta sanya mahaifiyarta a idonta ba, alhalin duk suna raye, bama ta san in da take ba."

"Ya sanya hannun sa cikin tattausan hannunta, yana murzawa a hankali amma ya kasa magana, sai saurara sautin"

"kukanta, da yake ara bugun zuciyarsa."

"Dane hannunsa tayi sosai a cikin nata, tana ara pressure kukanta."

"""Is ok salma, ya isa haka"" ta girgiza masa kai ta ce ""Allow me, idan na yi kuka ina jin saui""."

"Ya Wora hannunsa Waya a kafaWarta, amma ya kasa magana."

"Ganin kukan nata ba mai arewa bane, ya Wago fuskarta yana share mata hawayen da suke ta kwarara ya Wan tura"

"baki ya ce ""Nima kin sani kuka, ya isa haka please"" yayi maganar yana cigaba da goge mata hawayen."

"Kallon raihan take yi, da girmanta ko Abdul bai taSa kai hannu jikinta haka ba, tana da taka tsantsan da kanta, wa ma"

"ya damu da ita balle yayi yinurin kai hannunsa jikinta? Amma rarrashin nan da Raihan yake yi mata, ji take yi kamar"

Wan uwanta da suke ciki Waya ne yake yi mata.

"""Waye ya ce ke mummuna ce?"""

"Ta Wan ja numfashi ta ce ""Mutane"" tayi maganar cikin tura baki"

"Hannunsa a kan fuskarta, yana goge mata hawayen ya ce ""Kuma kin yarda?"""

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ya girgiza mata kai ya ce ""Kar ki sake sakawa kanki cewa ke mummuna ce, i understand that you are traumatized by"

"what people are saying about you, this is common among us. Ke fa malama ce ummi, kin fi kowa sanin Ubangiji gwani ne, kuma ba ya kuskure. Kin manta cikin suratul mu'iminun, aya ta goma sha huWu, bayan Allah ya yi bayanin yadda yake tsara halittar Wan Adam da kansa ya yabi kansa ya ce fatabarakallahu ahsanul kaliin? Ubangiji da ya yi ki ya yabi kansa, kuma sai ki sawa ranki cewa ba haka ba saboda surutun banza na mutane, as from today duk wanda ya ce miki mummuna, ki tabattar kin gaya masa maganar da gobe ba zai ara ba, fight for yourself ke ba mummuna ba ce""."

"""Har gorilla fa wani Wan ajinmu ya ce mini"" tayi maganar wasu hawayen na fitowa daga idonta."

"Wani abu mai zafi ya soki zuciyar raihan, banda tsabar rashin mutunci ya za a haWa mutum da biri?."

"Amma ya maze ya ce ""Sai kuma ki ka din ga kuka ko?"""

"Kamar mara wayo, ta jinjina masa kai."

"Raihan ya ce ""Meyasa baki tsinka masa mari ba"""

"Ummi ta zare ido ta ce ""Haka kurum ya dake ni, ni bana faWa"""

"""Ai shiyasa mutane suka rainaki ai, da kin guara masa mari, gaba ba zai ara ba ai"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ni ban kula shi ba, muna level 3 ma aka kore shi daga makaranta ya yi satar amsa, duk abun da"

"zan yi mutane ba za su daina ce mini mummuna ba"" tayi maganar a raunane."

"""Sun gano weak point Win ki ne, shiyasa suke amfani da hakan suna yaarki. Ki kwantar da hankalinki na san kawu ba"

"zai taSa bari ki koma auye ba, and ki ara tuntuSawa ko zaki samu wani information a kan in da mama take, zan yi iya oarina na gano miki ita""."

"Ummi ta zabura ta ce ""Dan Allah raihan da gaske?"""

"""I promise you salma, wannan kukan nake son na daina gani sai farinciki a fuskar ki"""

"""Nifa abubuwan da suke sakani kuka da yawa, ka san alfarmar da nake so ka yi mini?"""

"""Sai kin faWa""."

"""Dan Allah ka manta na taSa baka labarin nan, ban taSa yin irin wannan hirar da wani ba, kai ne mutum na farko da"

"na ji na nutsu da kai, na yi maka kuka, na rage abun da nake ji a raina, dan Allah kawai ka manta da labarin babu wani abu mai daWi na tunawa a rayuwata, amma for now ka manta da shi, na gaya maka ne saboda na yi maka alawarin gaya maka abun da ya sani kuka"""

"Idanuwanta yake bi da kallo, ya kasa amsa mata maganar, muninta kawai yake so ya gani, amma har ga Allah ya"

"kasa, kawai dai baa ce, kuma bai dai ba muni bane ba."

"""Kayi magana mana"" tayi maganar a Wan shagwaSe."

"""Zan yi, amma ba yanzu ba, mu karya ko, zuwa azahar mu yi salla sai mu je siyayyarmu ko?"""

"Ummi ta Wan Sata fuska ta ce ""Ko kawai mu canza rana, kaga yau duk sai godiyar Allah""."

"Ya jingina da jikin tebur, ya ce ""Kin sani kuka ba, marainiyar Allah, Allah ya ara kulawa da ke""."

"""Amin amma ba na ce ka manta ba""."

"Ya shafa sumar sa ya ce ""Kema dai kin faWa ne kawai, tashi in nuna miki aikin da zan kai wa Alhaji na gama"""

"Ta mie suka koma kan kujera, yadda ya rarraba bayar da zakka, da kujerun umara da na hajji da zasu bayar, da arin da za a yi a Wan bawa ma'aikatan na riba da sauransu."

"Ummi a ranta ta jinjina dukiya tana nan a in da take, kuma yadda raihan ke gudanar da lamarinsa, ba zaka ce Wan"

"mai kuWi ne haka ba, Maryam ce ma dai uwar jin kai, da jin ita wata ce."

"Sai da suka yi sallar azahar, sannan suka nufi tafiya, a mota take tambayarsa ina za su je, ya ce mata zata gani."

"Ya ja Wan guntun tsaki ya ce haararinsa a rie yake, zai fara koya mata mota, ya gaji da aikin direba ba a biyansa."

"""Ai ba ni na Wauke ka aikin ba, kai ka Wauki kanka, amma ba faWuwa ka yi ba ka ke ciwon haarari?"""

"""Ina fa, coach Wina ne na gym, ya sakani Waga wani arfe, haararina ya amsa""."

"Ta kalleshi ta ce ""Wai sai ka ji wa kanka ciwo tukuna, meye na zuwa gym kai ba iba ba?"""

"Ya rausyar da kai ya ce ""Waye ya ce dan a rame ake motsa jiki, bari na nuna miki arfen da na Waga a Instagram"" ya buWe mata wayarsa ya bata."

"Suna tafe tana mitar arfen yayi girma, daga bisani ta cigaba da yi masa taSe-taSe a wayar."

"Suka shiga go slow, yana jiran a basu hannu, ya Wan lea wayar, ya ga ta nutsu, kallon dogwayen riguna kawai take yi"

"tana liking Win su, da takalma da jakunkuna."

"Ya Wan yi murmushi, aka basu hannu suka tafi."

"Katafaren kantin saye da sayarwa, suka shiga, ummi kamar ar auye, sai kalle-kalle take yi."

"""Ta ina zamu fara?"""

"Ummi ta ce ""Ko ta ina ne ma""."

"Sannu a hankali suke zagayawa, suka fara zuwa wurin turarruka, ya saka hannu ya Wauki wani, ya jefa a cikin trolley."

"Ummi ta waro ido ta ce ""Raihan, dubu sha takwas fa aka rubuta, ka manta kuWin dubu sha biyar ne?"" Ya kashe mata ido Waya ya cigaba da Waukar kaya."

"Tayi ta magana, amma yayi mata shiru, suka je wurin kayan kwalliya ya kalleta ya ce ""Me ki ke so a nan?"""

"""To ai kuWin sun are"""

"""Ke ina ruwanki ne, Wauki abun da ki ke so kawai"""

"Comb ta Wauka sai ribbon da coacoa butter, dan man yana burgeta ta ce sun isa."

"""Wai ke ba kya kwalliya ne, ga su hoda da kayan mata"""

"""Ni bana wata kwalliya"" ta bashi amsa tana Wan kalle-kalle."

"Ya Waukko Waya wayar ta sa, yana dube-dube, ya Waukko wasu mayuka ya koma kan mayukan gyaran gashi, suma ya"

Wauka.

"""Wannan me zaka yi da su?""."

"""Budurwata zan saiwa lefe zan fara tarawa""."

"Ummi ta yi dariya ta ce ""Riga malam masallaci, za ta kwashi kayan shiririta"""

"""Ni ne ma shiriritar ko? Son kowa in wanda ya rasa da ni Win nan, Wan kyakkyawan matashi mai gemu, kin san maza"

"masu gemu muna da tsada""."

"""Ai mami ta ce mai ka shafa ya fito"""

"""Wallahi ban shafa mai ba, girma na yi gemu ya fito"""

"""Muyi sauri kar na makara komawa gida"""

"Ita dai ummi ta zuba wa sarautar Allah ido, ta san dai abubuwan da raihan ya Wauka, sun fi arfin kuWinta nesa ba kusa ba."

"A wurin biyan kuWi aka yi billing Win sa kuWi masu yawa, ya basu ATM suka cire."

"Gaba Waya ummi ta manta da damuwar da ta baro a gida, jin zuciyarta take fes, yau ta faWi abun da yake ci mata"

"zuciya tsawon shekaru, kuma ta samu ta yi kuka, an saurareta."

"""Raihan"" ya Wago ya kalleta ""Na gode sosai da lokacinka, Allah ya saka da alkhairi, ya ja kwanan Alhaji da mami"""

"Ya ce ""Da kuma Hajiya"" tayi murmushi ta ce ""Amin, kuma dan Allah da ka je gida, ka yi hauri ka danne zuciyarka, ka"

"bawa yaya Sagir hauri dan Allah"""

"""Zan yi in sha Allah"""

"""Allah ya yi maka albarka"""

"Kasa amsa mata yayi sai murmushi, asan zuciyarsa na hango masa ita tana kuka Wazu."

"Suka isa bayan layin su ummi, ta buWe motar ta sauka har ta fara tafiya ya ce ""Ke wannan alkunyar taki tayi yawa,"

"maimakon ki ce ""Malam bani kayana, ko kin bar mini dubu sha biyar Win taki?"" Ta waiwayo ta jinjina masa kai alamar eh."

"Ya fito daga motar, ya Waukko kayan yabi bayanta, ta tsaya cak ta waiwayo ta ce ""Ina zaka ne?"""

"""Gidan zan biki na kai miki kayan"""

"A rikice ta ce ""A'a dan Allah"""

"""To karSi kayanki"""

"""To ya zan yi da su, idan aka tambayeni...."

"""Ki ce da salarynki ki ka saya, ba wasu kaya ne masu yawa ba fa, ya kamo hannunta ya dana mata ledar ya ce ""Zan"

"je gida na cika alawarin da na yi miki"" ya juya ya koma motarsa ya tafi."

"Cikin mamki ummi take kallon kayan, wai duk wannan nata ne? Amma uban kuWin da raihan ya kashe, dubu Wari da"

"sha takwas, kayan mai turare da ciye-ciye."

"Cikin matsananciyar fargaba ta shiga gidan, kasancewar Wakinta ne a farko, ba ya cikin main safe contain na gidan, shiyasa ba sa sanin shige da ficenta."

"Ta kalli agogo ta san noor tana makarantar islamiyya, da ta kirata ta gani."

"Tayi alwala ta yi sallar la'asar, ta zauna ta din ga kallon kayan, wannan mayuka masu uban tsada, ita za ta shafa a"

fatarta.

"Wai har da hoda, to ita mai za ta shafawa hoda ma? Ta Wau turaren tana shaar amshinsa mai sanyi da daWin gaske. Ga roll on, kusan kala huWu, wanda kullum cikin dabaru take na haWa alumun, ko ta jia gishiri bayan yi wanka ta shafe jikinta, saboda kar ta yi wari."

"Wata envelope ta gani a cikin kayan, wadda ba ta san da ita ba, ta Wauka ta buWe taga kuWi a ciki sai takarda."

"""Assalamu alaikum, brown eyes, this is your first salary, given to you 15th April, spend it well, ga additional na 15k"

"making 30k, ki lallaSa na ji daWi na kuma gode da shopping, Allah ya ara arziki ummita. Raihan"" galala take bin takardar da kallo, Raihan ya mayar da ita sakarya ma."

"Wurin Alhaji ya fara zuwa, ya tarar da mami, da kuma Hajiya tare da Alhajin."

"Cikin damuwa mami ta ce ""Raihan sannu da zuwa, ba abun da ya sameka dai ko?"""

"Ya ce ""A ina?"""

"""An ce mini Sagir yaje har office, ya yi yinurin dukanka, na kira wayarka baka Wauka ba, na zo in ji ba'asi""."

"Raihan ya haWe rai ya ce ""In ji wani munafukin ne ya faWa?""."

"Alhaji ya ce ""Bai yi maka komai ba dai ko?"""

"""To aini Alhaji ban gane yayi mini wani abu ba?"""

"Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faWin ""Wallahi dole ka Wau mataki Alhaji, kar a"

"kassara mini Wa a cuceni"""

"Cikin dakiya Hajiya ta mie ta ce ""Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinurin dukansa?"" Yayi shiru yana"

kallon Hajiyan.

"Alhaji ya ce ""Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba,

34 / 74