CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   64 / 74

189K to 192K   out of 219.4K words

bana son ka samu matsala da mami, idan ka mayar da ni zaku cigaba da samun saSani, daga baya na dawo Maiduguri, ina gidan su mama, na yi niyyar gaya musu na kasa, ga zuciyata na ta azabtuwa da rashinka, wallahi yau ne na zo nan, saboda ba na son su mama su sani, bana son soyayyar da suke yi maka, da mutuncinka da suke gani, ya ragu a idonsu. Ban yi haka dan na Sata maka rai ba, rashin gata ne ya sanya"

"hakan faruwa. Dan Allah ka yi hauri MD na, ka yi hauri ka daina fushi da ni, na wahala da yawa Please"" ta arasa"

maganar tana fashe masa da wani marayan kuka.

"Gaba Waya sai jikinsa yayi sanyi, ya anameta a jikinsa yana shafa gashinta zuwa bayanta."

"A hankali ya ce ""Is ok sweetheart, kukan ya isa haka"" ya Wagota yana share mata hawayen fuskarta sannan ya ce ""Duk da kin neme ni da haka ba ta faru ba, amma ki ka aurace mini gaba Waya haba Salmana"""

"""To ka ce baka sake ni ba, kuma na riga na ce ka sake ni"""

"""Baki da shaida ai, dan haka ni ban sake ki ba, takardun gidan suna mota ta, amma kina ganin babu matsala abun da"

"ki ka sa na yi? Ina za su koma su zauna?"""

"Ummi ta ce ""Cewa aka yi bani da masauki a gidan, ba gidan ubana bane ba, tun da bana ubana bane ba, yanzu na"

"mijina ne, sonake a rushe gidan ma ya zama tarihi na daina ganinsa saboda na manta mummunar rayuwar da na yi a cikinsa""."

"Ya ce ""Mu bar wannan maganar for now, i so much miss you sweetheart, abinci babu daWi, ko san tunkarar gida"

"bana yi, saboda babu ke a cikinsa"""

"Ta kwaSe baki ta ce ""Ba amarya zaka yi ba? Meye na damuwa da ni"""

"""Salma kin fa san komai, kuma waye ya ce miki zan yi aure? Kema kin san ba so nake yi ba""."

"Ta harare shi ta ce ""Ni zaka yi wa daWin baki, duk wadda take ganin za ta iya kishi da mummunar mace kamar ni, bisimillah"""

"Raihan ya ce ""Innalillahi, wai ummi anya ba canza mini ke aka yi ba? Dan Allah mu bar wannan zancen i so much"

"miss you kairun nisa'i"" yayi maganar yana ara anameta."

"""Na kusa gama idda, kar ka Sata mini iddata"""

"""A'a takaba ki ke yi ba idda ba"" Nan suka shiririce, suka manta da duk wata damuwa da suka shiga a an kwanakin."

Tare da nuna wa juna tsantsar soyayya da yadda suka yi missing Win juna.

"""My"""

"""Na'am sweetheart"""

"""Meye abun yi yanzu?"""

"""A ina?"""

"""Ban gayawa kawu abun da ya faru ba, ban sani ba ko ya sani, ina ga dai wurin mama zan koma na zauna dole"""

"Raihan ya ce ""Ke a tunaninki zan bari ki sake kufce mini ne? Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zamu tafi Abuja"""

"""Amma mami fa? Kuma ga aure zaka yi, kar ka kuma samun saSani da ita"""

"""Ke ina ruwanki da aurena ne? Kin san wani abu?"""

"Ta ce ""A'a"""

"""Har cewa su Alhaji na yi, bani da lafiya ba zan iya ara aure ba, kema hauri ki ke yi da ni"" A zabure ummi ta"

"kalleshi ta ce ""Amma da wasa ka ke yi ko?"""

"""Wallahi da gaske nake"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai kai ba ka jin kunya ne?"""

"""In dai a kan ki ne bana jin kunya, a wurinki ne kawai nake da lafiya"" haka suka manta da damuwa da matsalolin da"

suke ciki.

"Washegari da sassafe, suka shirya suka tafi Abuja da shi da ummi."

Ya danawa ummi takardun gidan gagarawa ba tare da ya cigaba da takura mata a kan me za ta yi da gidan ba. Sai

dai ta ce masa ya ajiye mata.

"Raihan Win da sai da Alhaji yayi ta fama da shi a kan tafiya Abuja, amma daga baya ya ji raihan shiru, ya tafi babu ko"

sallama.

"Ummi har mamakin irin son da raihan yake yi mata take yi, kullum fatanta da Addu'arta Allah ya sa kar ya daina"

sonta.

"Ummi ji take za ta iya Waukar kowace kasada dan ta cigaba da rayuwa da mijinta, dan sai dai ta bar gidansa ta ara"

"tabattar da Wakinta shi ne rufin asirin ta, dan sai da ta yi wa maryam Allah ya isa."

"A gidan su wani abokin raihan suka sauka, gidan babu kowa a ciki, kuma kafin su je an gyara gidan komai akwai a"

cikin gidan.

"Cikin dare suna bacci, raihan ya farka ummi na jikinsa, sai dai jikinta ya Wau zafi sosai."

"Ya haskata ya ga baccinta take yi hankali kwance, washegari da safe da ta tashi, idonta ya Wan yi wani iri."

"Ta dube shi ta ce ""Good morning"""

"""Sweetheart, wai ba ki da lafiya ne? Jiya da daddare na ji jikinki ya yi zafi?"""

"Tayi murmushi ta ce ""Duk cikin murnar ganinka ne, amma lafiyata alau"""

"Ya rungumeta a jikinsa ya ce ""Anya kuwa, idonki kamar wadda ba ta da lafiya"" wayarsa ce ta fara ringing, ya kai"

hannu ya Waga yayi sallama.

"Muryar Safiyya ya ji ta ce ""Yaya ina kwana?"""

"""Lafiya lau"""

"""Dama mami ce ta ce na kiraka, maganar kuWin party, sannan kuma kayan da zan yi fitar biki""."

"Raihan ya ce ""Ai dama auren na mami ne, dan haka ita zaki tambaya bani ba"""

"Ya katse kiran, ya kalli ummi da take ta sauke numfashi."

"""Salma ya dai?"" oarin tashi take yi daga jikinsa, ya rie ta ya ce ""Meyafaru ne?""."

"""Dan Allah idan kana sonta, kar ka yi pretending dan ka kwantar mini hankali, dan Allah ka yi aurenka""."

"""Haba ummi tun yanzu? Kin fara karaya ni ya zan yi to? Dan Allah kar ki ce zaki daina kulawa da ni, wallahi banda"

"tursasawar mami, ni babu agender ara aure a gabana, wannan Win ma da yaya aka yi ana cewa na yi ananta?"" Ummi ta yi masa shiru, dan wani irin zafi irjinta yake yi mata."

"Ya tashi zaune ya ce ""Me zan yi mana order mu karya, zan fita da wuri ne"""

Ta juya masa baya ta yi shiru.

"Sai a lokacin ta ji ashe arya take yi, da take cewa ba zata Waga masa hankali idan zai ara aure ba."

Ya lea fuskarta ya ga yadda ta haWe rai.

"Bai ce mata komai ba, ya tashi ya shiga banWaki, har ya gama shirinsa ya fita ba ta sake kula shi ba. Sai dai fitarsa ke"

"da wuya ta fashe da kuka, yayi wuri ace za ayi mata kishiya tana tsaka da karSar kulawa da soyayya daga wurin mijinta, an hanata samun cikakkiyar nutsuwa tare da shi."

"Ya dawo da takeaway, nan ma ta ce ya ci nasa ba yanzu za ta karya ba."

"Haka an kwanakin yayi ta fama da ummi, ita kanta ba ta san tana da azabar kishi har haka ba, sai yanzu dan ta fara"

zancen ita maiduguri za ta koma.

"Ta addabi kanta da zuciyarta ko abincin kirki ba ta iya ci, idan baya nan sai ta zauna ta sha kuka kamar aramar"

"yarinya, idan ya dawo babu ruwanta da shi, ko shimfiWarsu ya je, sai ransa ya Saci. Ga kiran waya da mami take babu"

aautawa a kan maganar auren sa.

"Yau da ya kai arshen ulewa da halinta, ya hau zazzaga mata bala'i. Tayi masa shiru abun da ya fi komai Sata masa"

rai.

"""Ai gara na yi auren, tun da kin gaji dani kin daina tausayi na, ina ta taki kina wahalar da ni""."

"Kai tsaye ta ce ""Da ka huta dama kana son abun ka a ranka"""

Sai da ya sake Waga kai dan ganin ko ba ummi ce ta yi maganar ba.

"Janyota yayi da arfi yana fuskantar ta, zai sake balbale ta da faWa, ya ji tana sheshshear kuka, sai kuma jikinsa yayi"

sanyi.

"""Ummi wai meye haka? Gaba Waya kin canza""."

"""Dan Allah ka bari na koma maiduguri na zauna, ka je ka yi aurenka"""

"""Ummi ni Win ne ba kya so kuma yanzu?"""

"Cikin kuka ta girgiza kai ta ce ""Ba fa abu ne mai saui ba, wallahi ba zan iya jurewa ba, kishi zai kashe ni, ba zan iya"

"pretending ba Wan aljannata, i so much love you sweetheart, ba zan iya pretending ba, kullum zuciyata da sauri take bugawa idan na tuna zaka zama namu ni da wata, ka yi hauri ba dan in Sata maka rai nake yi ba, ban san haka kishin yake ba, na Wauka ba shi da wahala"" ta arasa tana aname hannunsa tana kuka mai ratsa zuciya."

Tausasan kalamanta sai suka sanya tausayinta ara shigarsa.

"""Na san babu saui, amma ki jure dan Allah na samu na yi wa mami biyayya ko na gama da duniya lafiya, idan ina"

"ganinki a haka zan iya bujirewa, ki daure Salmana ki yi hauri na san da ciwo"" ya din ga rarrashinta tana wata irin ajiyar zuciya, da sai da ta din ga bashi tsoro kar wani abu ya sameta."

"Cikin dare jikinta yai daWi, dama tana zazzaSinta a tsatstsaye, idan ta ci abinci tayi ta amai, ba abun da yake zama a"

"cikin ta, sai dai na yau ya tsananta, da har sai da raihan ya gane, tun tana iya zuwa banWaki yin aman har ta kasa."

"Ranga-ranga ya tafi da ita asibiti, a karon farko gwaje-gwaje suka tabattar da ciki ne da ita. Raihan kamar yayi tsalle"

dan murna. Tun da tayi Sarin nan ba ta ara yin period ba.

"Aka din ga saka mata ruwa, sai dai zazzaSi ba ya sauka, kuma ko ta ci abinci ko ba ta ci ba sai tayi amai."

"Tausayinta ya cika raihan, ga zafin laulayi ga kishi, sai da likita ya zo dubata ne ma take gaya masa ta fi wata tana"

zazzaSi a kaWan-kaWan.

"Raihan yana saka ran a sallame su, amma likita ya ce sai sun rie ta, saboda low bp, ga jininta ma yayi asa, sai an ba"

ta kulawa ta musamman.

"Kwananta biyu a asibiti, da sassafe ya dafa tea zai kai mata, ya fito daga motar sa, sai ga kiran wayar Alhaji."

Ya Waga yana gaida Alhaji sai dai yanayin muryarsa ya tabattar masa ba lafiya ba.

"""Kana ina?"""

"""Ina Abuja Alhaji lafiya?"""

"""Ban sani ba, ina ummi take?"""

"Gaban raihan ya faWi ya ce ""Tana gida?"""

"""Ni zaka yi wa arya? Ashe baka da hankali ba ka da mutunci raihan? Jiya da daddare babanta ya kirani cikin"

"damuwa ashe sakar masa a ka yi, kuma an nemi in da take an rasa, ga wani case can a familynsu ma ana ta nemanta, ka gaya mini ka sakar masa a? A baka yarinya cikin girma da mutunci amma ka wulaanta ta, yarinya mai tarbiyya da nutsuwa, bilki ce ta saka ka saketa ko?"""

"Raihan ya girgiza kai ya ce ""A'a ba ita ba ce ba""."

"""Koma waye ya saka ka, ka cuci kanka, kana ina? Kuma ina ar mutane"""

"Raihan ya ce ""Muna tare a nan Abuja"""

"""Uban me ka Wauketa ka yi mata a abujan bayan ka saketa?"""

"""Alhaji ba sakinta na yi ba, rashin fahimta ne"""

"A fusace ya ce ""Kai ka sani, baka ma da kunya, in anjima zan shigo garin Abujan, ka bani ar mutane da takardarta"

"na danawa mahaifinta ita, kai kuma tun da mutumin banza ne ka je ka arata, am so disappointed on you!."

08081012143

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut

Irik

Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha

Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

45

PAID ADVERT

"*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? an bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir Win da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin shein fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma"

"skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sano, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson arfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuSe su a kan lambar wayar su dan arin bayani 07045971194 ko 08140450950*"

45

"Raihan ya rasa ta ina zai fara kare kansa ma, haka yayi shiru Alhaji ya gama faWan ya kashe wayarsa."

"Kamar wanda aka gayawa saon mutuwa, haka ya arasa cikin asibitin, ya taimakawa ummi ta wanke baki, ya haWa"

"mata tea da dankali yana bata. Cikin Wari-Wari take ci, dan ta san arshen abun ta amayar da abun da ta ci, ga yunwa tana ji sosai."

"""MD ka ga wancan cikin ban san ma da shi ba, ban yi laulayi ba wannan kuwa sai wahala nake sha"""

"Yayi murmushi da yar ya ce ""Wancan kin ci bonus"""

"""Wai ya na ganka duk wani iri ne? Na san zaman asibiti da gajiya, ba daWi shiyasa gara ka mayar da ni maiduguri"""

"Raihan ya ce ""No, ba gajiya na yi ba, da ke da babyna kuna buatar kulawata. Ai gazawa ce in ce ki koma gida dan"

"baki da lafiya, ni zan yi abun da ya dace na kula da ku"""

"Tayi murmushi ta ce ""To aikin fa?"""

"""Shima duk zan iya"""

"""an Aljannana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya barmu tare har aljanna"""

"Ya amsa mata da Amin, asan zuciyarsa yana fargabar hukuncin Alhaji, dan daga ji ya Wau zafi sosai."

"Yadda ta gama cin dankalin nan, sai da ta amayar da shi gaba Waya, abun har tsoro yake bawa raihan, duk ta rame saboda laulayi."

"Yana nan zaune tare da ita, har ta samu bacci, bayan wasu awanni ta din ga jin hayaniya kamar a mafarki. Ta buWe idonta, ta ga Alhaji a Wakin tare da Salim, ga raihan a gefe ransa a haWe sai kuma likita a tsaye da file."

"A hankali ta tashi zaune, tana mamakin zuwansu ta ce ""Alhaji sannu da zuwa"""

"Ya dubi Ummi ya ce ""Sannu ya jikin? Dan Allah kalli yadda duk ta bi ta are ta rame, meke damunta ne? Ko kuma"

"duk tsiyataku da rashin mutuncinka ne ya sanya ta rame"" Yayi maganar yana kallon raihan."

"Likita ya ce ""Ahh ba wani abun damuwa bane, laulayi ne na mata, ba ta iya cin komai shiyasa muka ajiyeta mu ke ta"

"saka mata ruwa"""

"Alhaji ya ce ""Ka rubuta mata sallama, gida kano zamu tafi, za a cigaba da kula da ita a can"""

"Ya mayar da idonsa kan ummi ya ce ""Banda abunki ummi, gani menene amfanina? Ko dr. Ba ya nan wani abu ya"

"haWaku sai ki zo ki gaya mini, ni a ta ce ke ba sirika ba, kawai sai ki biye masa ki tafi wani wurin ace ba a san ma in da ki ke ba? Kuma dan baka da kunya ka lallaSa ka mayar da ita ka taho da ita nan ba wanda ya sani, hankalin mahaifinta na can a tashe bai san ina take ba, ka bani kunya"" daga ummi har raihan aka rasa mai magana, ummi ba ta taSa zaton Alhaji ya iya faWa haka ba, saboda kullum fuskarsa cikin murmushi yake."

"Haka aka sallami ummi, suka nufo kano, raihan ya sha faWa a wurin Alhaji,kuma yayi shiru bai ce komai ba ummi gaba Waya ta ji babu daWi."

"Asibiti suka zarce da ummi, aka cigaba da ba ta kulawa ta musamman, saboda suna tafe a hanya ma tana amai."

"Alhaji ya kira dr. A waya ya sanar masa ya gano ummi, tana tare da raihan a maiduguri."

"Dr. Ya ce ya haWa shi da ummin a waya, Alhaji ya ce masa ba ta da lafiya, ba za ta iya amsa waya ba."

"Dr. Ya ce a cikin satin zai shigo Nigeria, dan hakan yayi dai-dai da lokacin zuwansa hutu. Ya karSi kwatancen asibitin,"

"ya kira Abdul a waya, ya ce su je asibiti da shi da noor, su duba masa jikin ummi."

"Ko da suka je, sai da Abdul ya yi wa raihan orafin, meyasa bai gaya masa ba ya ga ummi."

"Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda Salim da noor suke yi wa juna murmushi ba, kamar sun"

saba. Kuma a iya sanin ummi ba shi da fara'a ko kaWan.

Noor ta arasa gaban gadon ummi ta na yi mata sannu.

"""Yaya ummi shi ne ki ka tafi aka neme ki aka rasa ko? To an gagarawa ne suka samo wani abokin Abba, suka saka ya"

"kira musu shi, aka gaya masa abun da ki ka yi, ya bi ba'asi ban san dai me suka ce masa ba, ya kira waya yana faWa ya cewa yaya Abdul ya je gidanki ya duba masa ke dama ba ya samunki a waya, aikuwa dai ya gaya masa gaskiya, amma fa mun sha faWa saura ke idan ya dawo dan ransa ya Saci"""

"Salim ya ce ""Ba ki ga bata da lafiya bane?"""

"Ta ce ""Au, haka ne fa, zumuWi nake na ganta, ba ka san yadda na shiga tashin hankali ba da aka ce ta Sata""."

"Yayi murmushi ya ce ""I see"""

"Alhaji ya ce ""Ai daga ita har shi, sun yi laifi, kuma ba zan matsa

64 / 74