CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   58 / 74

171K to 174K   out of 219.4K words

da ga kyau ga kwalliya. Abdul kuma babu ™wa™™waran aikin yi.

"Saura kwana uku tafiyar, Ummi da raihan suka je maiduguri ma, Mariya kamar ta haWiye ummi, suma sun yi farinciki"

"ganin ummi, raihan yayi musu alkhairi sosai da sosai."

"Suke gaya mata har a lokacin bayan bikinta, dr. Yana zuwa ya kawo musu sha tara ta arziki, tare da duba lafiyar"

Mariya.

"Hakan ba ™aramin daWi ya yi wa ummi ba, karamcin kawu yahaya ya sanya ba ta taSa mantawa da shi a cikin"

"Adduo'inta, kuma a duk lokacin da ta samu abun alkhairi take kai masa da iyalinsa."

"Jin mami ta matsa a kan maganar auren raihan, ya sanya jikin ummi yin sanyi, a baya tana ganin babu wani abu idan"

"raihan ya ce zai ™ara aure, amma a yanzu fargaba ta shige ta da tsoro."

"Dan a gabanta mami ke kiransa ta jaddada masa maganar auren, ko ma safiyyan ta kira shi wai zata gaishe shi, tana iya kokarinta wajen kar ta nuna masa wani abu na Sacin rai, dan tana ganin idan ta yi masa haka ba ta yi masa adalci ba. Ta ji gaba Waya tafiyar ma ta fita daga ranta ba ta so."

"Sai dai suna barin ™asar, ta Wan samu nutsuwa, mussman da kullum tana tare da raihan tana shan soyayya da kulawa"

kala-kala a wurin matashin mijinta.

"Sun samu zuwa wurare masu matu™ar kyau da Waukar hankali, ™ar™ashin jagorancin Waya daga manyan manajojin su"

"raihan, da suke kasuwanci tare. Shi yake kula da komai nasu kama daga masauki zuwa abincin su da sauran bu™atu."

"Ummi ba ta taSa tunanin ganinta a ko da airport ba, sai gashi ta keta hazo, ta bar ™asa Nigeria."

"Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda ba ta ga mutanen ™asar na muzanta halittarta ba, sai ma bayan shirya musu wani cin abinci da managern yayi, da iyalansa da wasu daga abokan kasuwancin su, suke cewa ba"

su taSa ganin ba™ar fata mai kyan ummi ba.

"Da aka fassara mata da turanci abun da suka ce, saboda galibi ba su iya turanci ba, mamaki abun ya bata, wai idonta"

"mai kyau da fatarta, har ta fara tunanin ko ba'a suke yi mata, suka din ga layin hotuna da ummi."

"A duk lokacin da suka fita sha™atawa, sai mutane su yi ta kallonta, har wasu su nemi su Wauki hoto da ita, suna yi"

"musu tambayoyi mussaman idan ta yi shigar hausawa, duk da ta fi saka rigunan abaya a kan kayan hausawa."

"Duk da ummi na ™o™arin kare mutuncin aurenta, da matan su kawai take gaisawa tayi hotuna, sai da kishin raihan ya"

kasa Suya.

"Sun fita baki wani ruwa da daddare shan iska, take tambayar raihan ""MD dan Allah mutanen nan da gaske suke, ko"

"zagina suke yi da suka ce ina da kyau?"""

"Ya ja hancinta ya ce ""Idan na faWa ai ba kya yarda, you are beautiful baby"""

"Ta saka hannu ta shafi fuskarta ta ce ""An ce fararen fata suna ™yamar ba™a™e, amma ni har ´an uwana ba™a™en"

"™yamata suke yi"""

"Ya kwantar da muryarsa ya ce ""Mutanen china suna da ™arancin nuna wariyar launin fata, su kuma mutanenmu son"

"zuciya ne kawai, da rashin bawa abun da muke da shi muhimmanci""."

"Ta sake jan numfashi ta ce ""Ni fa bayan baba da mama, kai ne kawai ka ke cewa ina da kyau, sai noor gani nake duk"

"Nigeria na fi kowa muni"""

"Ya Sata fuska ya ce ""Ban hanaki faWar irin wannan maganar ba? Me ki ke nema a yanzu da Allah bai yi miki ba?"

"Ubangijin da ya yi ki yana sonki, mama na sonki nima ina sonki to me ki ke nema kuma?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""hmm MD kenan, idan aka ce ina da kyau wallahi sai in ji kamar zagina ake yi, saboda na fi"

"sabawa da jin kalmar cin mutunci """

"""Ni kuma wallahi a duniya, a yanzu dai ban sani ba ko a gaba, amma wallahi ba ki ga yadda ki ke yi mini kyau ba"

"Salma, komai naki son shi nake, wallahi duk macen da na gani, sai in ga ba ta kai ki ba. Ina kaucewa auren Safiyya ne saboda a yanzu dai na ™ara aure ba zan iya adalci ba son da nake yi miki daban ne, a ™asan zuciyata nake jin ki, bana son wani abu na rashin daWi ya raSe ki, ban san ya zan misalta miki ba ki gane ummi, kawai ni dai ki yadd ki saka a zuciyarki ina sonki, kuma wallahi ban taSa ganin muninki ba ko sau Waya. Kawai ji nake duk matar da zan aura ba zan samu biyayya da kulawar da nake samu a wurinki ba, mutane kawai suna ganinmu ne, amma ba za su gane tarin baiwa da Allah ya yi miki kala-kala ba, su muninki suke gani, ni kuma abubuwan da nake gani game da ke ba zasu lissafu ba. Ina sonki kariun nisa'i"""

"Sanyin iskar wurin, da daWin kalaman raihan, ya sanya wani irin shau™i ya kama ummi, tare da jin ta a sama, kalaman"

"na raihan suka sanya ta ji kamar a duniya babu wadda ta fita sa'ar miji. Abu kamar a mafarki ita da ake cewa ba zata auru ba, sai dai a taimaka a aureta saboda muninta, amma yau gashi Allah ya gwangwaje ta da miji na kere wa sa'a, kalaman na raihan ko ™arya yake yi mata sun yi mata daWi."

"Ta rungume shi sosai ta ce ""Allah ya barmu tare har aljanna Zaujul janna, kana cikin mutane masu muhimmancin da"

"suka haska fitila a rayuwata mai cike da ™alubale kala-kala, dan Allah kar ka daina sona, ko zaka yi aure a gaba ko ka so wata, dan Allah kar ka daina so na, ko da ka daina sona ka Soye mini dan Allah, kulawarka tayi tasiri a rayuwata idan na rasa soyayyarka da kulawarka komai nawa zai koma farko, kai kaWai ne hope Wina yanzu, an ce wataran ana gajiya da juna dan Allah kar ka gaji da ni"" ta ™arasa maganar kamar mai magiya."

"Ya saka hannayensa biyu yana shafa bayanta, yana jin yadda take kuka."

"""Soyayyar da aka gina da tubalin toka ita ke gushewa, tamu kuma da tubalin dutse muka gina ta, ni da ke har aljanna"

"babyna"" ya ™arasa maganar yana Wago fuskarta yana share mata hawaye."

"Tausayin ummi ya cigaba da mamaye masa zuciya, tare da jin zai jure kowane ™alubale ummi ta samu farinciki."

"Kwanakin su ummi takwas a ™asar, Waya daga cikin waWanda suka ci abinci tare da su ummi, ta nemi iznin ummi a"

"kan tana son Wora videonsu da suka yi ita da ummi, a YouTube, babu tunanin komai ummi ta ce mata to, saboda yadda ta san da shigarta ta mutunci a jikinta a ka yi videon."

"Sai dai kwana Waya take nunawa ummi adadin views Win da videon ya samu, ya tafi viral da yadda mutanen ™asar har"

ma da wasu suke sharhi a kan ummi.

"Communication da mutanen yana bawa ummi wahala, dan su ba su iya turanci ba, ita kuma ba ta jin yarensu."

"Amma duk da haka mutane ne masu tambaya, wasu lokutan har live videos suke yi da ummi, suna yi mata"

"tambayoyi a kan mutanen Afrika, a gaya mata tambayar da turanci, ta basu amsa da turanci a fassara musu."

"Raihan sai dai ya kalle su yayi dariya, ya san suna takura ummi, dan ba son mutane take yi ba, gashi kuma kamar"

tsoronsu ma take ji.

"Sai dai ya ™yalesu ne, saboda wata™ila a dalilin haka ummi ta samu wani cigaba a rayuwarta, da zai tabattarwa da"

"duniya musamman masu nuna cewa ita mummuna ce, ba za ta yi acheiving wasu abubuwa a rayuwa ba saboda kalarta."

"Har tambayarta suke yi a kan ™abilar hausawa, da Nigeria baki Waya, duk da akwai masu tambaya cike da izgili ga"

™asar sai dai cikin hikima da dabara ta aiki ummi take basu amsa.

Sai da ummi ta fara damuwa da yadda adadin masu zuwa ganinta da hotuna da ita ke ™ara yawa kamar wata halitta

"ta daban, ga kuma kyaututtuka da ake ba ta."

"A daddafe suka yi wata Waya, fatarta ta ™ara kyau, duk da daga ita har raihan abinci ba kowane iri suke iya sakin jiki"

su ci ba.

"Ummi ta tara kyaututtuka sosai, ranar da zasu tafi ™awarta da suke video ta ba ta kyaututtuka, Wan zaman da suka yi"

"sun saba da ita, suka yi ta tambayarsu yaushe za su dawo, raihan ya ce musu sai wani lokacin."

"A jirgi ya din ga yi wa ummi mitar daga zuwa ™asar mutane ta zama cele, shi fa haushi yake ji yadda ake sakata a"

social media.

"Cikin damuwa ta ce ""Meyasa baka gaya mini ba ka so ba? Ka bari muke yi, ni bana son su ga kamar na yi musu"

"wula™anci ne"""

"Yayi murmushi ya ce ""Sweetheart, komai yana da sila, tsakani da Allah zuciyata kamar ta fashe, ana talla da matata,"

"amma sai na tuna ke ´ar jarida ce tun ainihinki ma, kuma ban san alkhairin da zaki iya samu a sanadin hakan ba, ina fatan ko iya haka a ranki zaki ji cewa ke ta mussman ce, kalli dubban mutanen da ke bibiyar live Win da ku ke yi, ba kuma wai dan kina wani abu na musamman ba, kalarki da irin halittarki da mutanenmu suke kushewa, su ita ta ja hankalinsu"""

"Tayi shiru ba ta ce komai ba, ta cigaba da wasa da yatsun raihan da ke hannunta."

"Ko da suka dawo ya hanata gaya wa kowa sun dawo, ya ce sai sun gama hutawa. Ita kuwa ba ta zauna hutun ba,"

saboda ganin yadda gidan yayi mata ™ura da yawa.

"""Dan Allah ki zauna ki huta, aikin nan yayi miki yawa, ki yi da kaWan-kaWan, an ce a samo miki ´ar aiki kin ce ba kya so""."

"Ta ce ""Bana son in ga wurin da datti ne, dan Allah ka yi ha™uri"" haka ya ™yaleta ta yi ta share-sharenta."

"Sai da suka kwana biyu da dawowa, ya je gida, ya gaida su mami. Alhaji ya din ga mitar meyasa bai zo da ummi ba."

"Raihan ya ce ""Ta gaji ne sosai, ba ta saba doguwar tafiya ba, kamar ma dai ba ta jin daWi shiyasa na baro ta a gida""."

"""Allah sarki, with time za ta saba ne in sha Allah"" ya samu kyakkyawar karSa daga Hajiya da Alhaji banda mami, da"

ke masa abu kamar agola ba Wanta ba.

"Ganin shirun yayi yawa ya sanya ya mi™e zai tafi, da mamaki mami take kallonsa kamar yanayin ko in kular da take yi"

masa baya damunsa balle ya saduda.

"""Ya maganar mu?"""

"Ya Wan yi turus ya ce ""Wace maganar?"""

"Ta ce ""Tambayata ma ka ke yi?"""

"""Mami ki dubi girman Allah ki yi ha™uri, wallahi ni bana son yarinyar nan, ummi ba ta yi mini laifin komai ba,"

"watanmu shida fa da aure har kuma sai na ™ara aure, da ™anan shekaruna in tara mata"""

"""Raihan ni ka ke gayawa ba ka son safiyya? Kuma da ka ji maganata tun farko ai da haka ba ta faru ba, kuma wallahi"

"ka cigaba da bujire mini sai na kashe auren nan a kwanakin nan dan bana ™aunar yarinyar nan""."

"""Mami, dan Allah ki taimaki rayuwata, ki ka rabani da ummi, ba zaki iya sama mini matar da zata maye mini gurbinta"

ba!.

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

40

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

AYSHERCOOL

08081012143

"MASU BU˜ATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ŠINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH."

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

41

"Galala mami ta buWe baki tana kallon raihan, ba ta taSa zaton wannan kalaman daga bakinsa ba ko a mafarki, ta rasa"

"wace amsar ma yakamata ta bashi, ganin ba ta da abun cewa ya sanya jiki a sanyaye ya fice, zuciyarsa na wani irin zafi."

"Har ya nufi motarsa ya ji an ri™e hannunsa, ya waiwaya ya ga Salim."

"Ya gyara nutsuwarsa cikin girmamawa ya ce ""Yaya ina wuni?"""

"""Meyafaru ne?"""

"Raihan ya kalleshi ya ce ""A ina?"""

"""Dambe ka yi ne? Ba ka ga yadda ka ke gumi ba, idonka ma yayi ja?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Bakomai, dama mun dawo ne na zo gida mu gaisa ban zaci ma kana nan ba"""

"Salim ya kama hannun raihan ya wuce da shi Wakinsa, Sagir na kwance a falo yana kallon tv suka shigo, sallamar su"

kawai ya amsa ya cigaba da abun da yake yi.

"Ya zaunar da raihan a kan kujera, shima ya mayar da hankali a kan kallon ba tare da ya cewa raihan Win komai ba."

"Sun shafe a ™alla mintuna talatin a haka, sannan Salim ya numfasa ya kalli raihan ya ce ""Are you ok now?"""

"Ya jinjina masa kai ya ce ""Yes, na gode sosai"""

"Salim ya sake tattara nutsuwar sa a kan raihan ya ce ""Me yake faruwa? Kar ka Soye mini"" raihan ya yi shiru yana yi"

"wa Salim kallon mamaki, dan sam ba mai shiga abun da bai shafe shi ba ne ba."

"Kamar ya san me raihan yake tunani a kai ya ce ""Na san zaka yi mamakin tambayarka da nake yi, na samu labarin"

"matsin lambar da ake yi maka a kan ™ara aure a wurin Hajiya, kuma daga dawowarka ba zai yiwu ace har wani abun Sacin rai ya faru da za ka shiga cikin tashin hankali ba, in dai ba a kan maganar ba ne ba."

"Ka san meyasa na titsuyeka nake tambayar ka?"""

Raihan ya girgiza masa kai alamar a'a.

"""Al™awarin da muka Waukko wa mahaifiyarta da ni da kai, Allah ya sani ina tausayin baiwar Allah nan sosai, kuma kai"

"ka bani labarin irin wahalar da take sha a rayuwa, idan har ka rabu da ita, ka yi wa mahaifiyarka biyayya haka ake son Wa na gari amma ka sa a ranka ko da ranka ko bayan ranka sai wani ya auri ´ar ka ya saketa!."

"Haka zalika idan ka auri wannan yarinyar ka zalunci ummi, ko ita wadda zaka aura Win, shi ma ka shirya kare kanka a gaban Allah"""

"Gaba Waya raihan ya sake rikicewa ya ce ""Wallahi yaya na rasa yadda zan yi, ina son ummi muna zaune lafiya tana"

"kyautata mini, me zai saka na saketa ko ace sai na yi wani auren? Ni ba na son safiyya a matsayin matar aure, kuma bana son saSa wa mami"""

"Salim ya kaWa ™afa ya ce ""Am sorry to say, iyayenmu mata wasu lokutan na da gajeren tunani, iyayenmu da suke"

"aure fa, ba daga sama suka faWo ba, su ma ´a´an wasu ne. Anyway Allah ya kyauta, na kira ka ne dama dan na yi maka tuni a kan amanar da ka Waukko, kayi ™o™arin gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka, ba tare da wani ya cutu ba""."

"Raihan ya jinjina kai ya ce ""Na gode sosai yaya da tunatarwa, zan yi iya ™o™arina in sha Allah"" yayi musu sallama ya fice."

"Sagir ya bi bayansa da kallo, yana wani tunani a ransa na kowa da irin jarrabawar sa, shi da yake mai biyayya babarsa"

"ta saka shi a gaba, su da suke sai a hankali su suka saka tasu uwar a gaba, kuma ya san su ta su uwar ba za ta taSa yi musu haka ba, amma tabbas da shi ne a matsayin raihan, ba wanda ya isa ya tursasa shi yin abun da ba ya so."

"Mami kuwa hankalinta ya gama tashi, tare da tabattar wa da kanta, ummi da danginta sun haWu sun mallake mata"

"Wa, dama ance irin su ba sa zaman aure haka sai sun yi asiri."

"Cikin rashin dabara, ta kira yayarta da ke yi mata ba™i jagoranci, ta zayyane mata komai, aikuwa ta ™ara zigata a kan"

"ko dai ta raba raihan da ummi, ko kuma maganar Hajiya ta zama gaskiya, Wan so ya auri matar so!."

"Raihan ya koma gida, yana ta sa™e-sa™e, amma tunda ya ci ya ™oshi, suka shiga soyayyarsu da ummi sai ya manta, ta"

hau bashi labarin aikin da ta sha na gyara gidan jikinta sai ciwo yake.

"Ya yamutsa fuska ya ce ""Ki daina gaya mini kin wahalar mini da kanki, tun da dai ba kya jin magana""."

"Tayi murmushi ta ce ""Zaujul janna, wata alfarma nake nema dan Allah"""

"Ya ce ""Yau Allah ya yi kenan, tun kan mu tafi nake ganin alamar akwai magana a bakinki, kin ™i faWa ne kawai. Ina"

"jinki"""

"Ta Wan yi jimm tana jujjuya maganar sannan ta ce ""Dan Allah idan ban takura maka ba, dan Allah so nake idan da"

"Wan space a taimaka a Wauki yaya Abdul aiki dan Allah, amma idan babu shikenan bakomai"""

"Kawai ya zuba mata ido, dama wannan maganar take ta yi wa kwana-kwana."

"Ya maze ya ce ""Ki rubuta a rubuce ki kai mini office"" hararsa tayi ta ce ""zaka sake kenan ko?"""

"Yayi dariya ya ce ""Ashe baki manta ba?"""

"""Ya za ayi na manta, waccan ranar sai da na yi kuka"""

"""Koma me na yi miki ai ke ki ka janyo, handsome guy kamar ni, a wanke hannu a taSa Wan kyakykyawa da ni, wai ki"

"ka rufe ido ba zaki aureni ba,

58 / 74