CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   72 / 74

213K to 216K   out of 219.4K words

gaya wa haka?"""

"""Ke fa ki ka fara, wai kwaWayi? Ke in kwaWayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba"""

"Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta mi™awa maryam yaran, maimakon ta karSa ta ce ""Ba shakka, dole mami ta ce"

"akwai lauje cikin naWi a wannan yaran, ba zata taSa karSar su a matsayin jikokinta ba"""

"Ummi ta ce ""Noor mayar mini da ´a´ana wurin Anty""Noor na fita ummi ta ce ""Kar Allah ya sa ku karSe su a"

"matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan."

"Dama ni ban ce ta ™aunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ™i ni duk uwar ubansu Waya."

"Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na Wan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ™irjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ™alubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba."

"Zaman gidan raihan, da zazzago ´a´a yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita"""

"Maryam ta mi™e ta ce ""Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?"""

"""Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da"

"cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haWu da dai-dai ke""."

Ta fice ta bar ta a Wakin a tsaye.

"Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saSule, haka"

"na rahama cikinta, fuskarta da ™afafuwan ta duk sun ™one ´an sanda sun kama mijin nata."

Ta din ga kuka tamkar za ta zare.

"Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta mi™e ™afa ta cigaba da sabgoginta a gidanta."

"Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ™ara da wanka, ummi ta san in dai Sangaren kula da mijinta ne, to tana da"

kyau ba a magana a Sangaren kula da raihan.

"Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ™asa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taSa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa Wakin mijinta."

"(Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ™ware ba, suna bayar da magunguna daban-"

"daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku. Suna da kaya kamar haka;"

Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau

Wayyo dadi

Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino

Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini

Gumba kalla kalla da dai sauran su

A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba Ga kuma maganin slimming

Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su.

Kayan mu tested and trusted ne

Suna maraba da masu siyan Daya ko sari Suna Nan cikin garin kaduna

Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah

AMINA GACHI

07034404975

CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA

Phone no 07034404975.

"Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka,"

"dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daWin ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in."

"Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata"

"da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika Sul-Sul gwanin sha'awa."

"Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ™warya, ga ™arfi ga kuma iska hakan ya"

sanya rufin Wakin iya kwashewa.

"Dama dr. Ne ya bayar da kuWi, a gyara mata Wakin ta saka aka yi rufi ta karSe sauran kuWinta ta cinye, sai ledar Waki da ta saka."

"Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya ji™a tsohuwar ™asar da aka yi ginin Wakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ™walo mata a ka."

"Gashi itakaWai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari."

"Babu wanda yayi zaton za a ciro iya da rai, haka aka kwashe ta aka yi asibiti da ita, tamkar an ji™a kaza a ruwa, ga"

"jikinta duk ™azantar zawon wahala da tayi, kan nan kamar an suWe ™wallon giginya, duk ta zama abun tsoro."

"Su farida kuwa an kai ruwa rana, da su da mijin rahama a wurin ´an sanda, dan kuwa ´ar kwananta goma sha Waya ta mutu, kasancewar uwarsa tana da kuWi, sai kaiwa ta ke tana komowa a kan lallai sai an sake shi."

"Ana wannan ™adamin, su Alhaji Tahir suka kai kuWin auren noor, aka saka watanni tara watan da za ta kammala karatun sakandare, za a yi bikinta da Salim."

"Tun da aka saka auren nan, ummi ta dage wa noor da addu'a, tare da yi mata nasiha sosai a kan zamantakewa."

"""Noor, bani da burin rabaki da anty farida mahaifiyarki ce, kuma komai ta yi miki, mahaifiyar ki ce. Abun da nake so"

"ki sani shi ne, kar ki yadda wani ya Wauki wani abu na tsafi ya ce miki ki yi wa mijinki. Daga zarar abun ya karye, za ki ji kunya, kuma sai mushen kare ya fi ki daraja a wurinsa."

"Noor Allah bai halicci namiji dan ya bi mace ba, mace ita ce a ™ar™ashin namiji, gwargwadon biyayyarki, gwargwadon mallakarki. Idan ki ka kwantar da kai, ki ka yi addu'a ki ka mi™a lamarinki ga Allah ki nemi aljannar ki da gaske, zaki juya namiji yadda ki ke so. Wasu abubuwan sai lokacin auren yayi zan gaya miki, babu ruwanki da Waukar shirmen ™awaye su gaya miki abun da ba zai amfane ki ba."

"Babu ke babu yi wa miji asiri noor, asiri ba ya tasiri, ko yayi na lokaci kaWan ne."

"Namiji kullum shi ne a gaba, dan haka ban da Waga masa murya, kuma ki fara yi muku addu'a samun zaman lafiya tun yanzu""."

Noor ta jinjinawa ummi kai.

"Hajiya kamar ta taka rawa, ganin a wannan karon Salim ya yadda zai yi aure. Kuma ta ji daWin zaSar noor da yayi, ko"

"ba komai ta ga misali a kan ummi, ahalin gidan dr. Suna da tarbiyya."

"Dr. Ya je gagarawa, ya duba Iya, sai dai aka tabattar masa da spinal code Win ta ya taSu, ba zata ™ara takawa ba, komai sai dai ayi mata."

Dr. Ya tsorata da yanayin da ya ga Iya a ciki sosai da sosai.

Gashi babu wata cikakkiyar kulawa ta a zo a gani.

"Bayan ya koma gida, ya tarar an dawo da rahama gidansa, a nan za ta yi jinya, da kamar ya ce bai yadda ba, kawai ya"

™yale su.

"Ummi ta na ta Alla-Alla tayi arba'in, tana son ta je ta duba rahama, kuma ta duba jikin iya."

"Sai dai shi YallaSai MD, lissafinsa kawai tayi ta koma turaka."

"Da dr. Ya gaya wa Farida batun karSar kuWin noor, bala'i ta hau bala'i ta™i nutsuwa yayi mata bayani balle ta ji waye."

"Hankalin kausar yayi mummunan tashi, jin an karSi kuWin auren noor, ita kuma ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko."

"Ummi tana jikin raihan, tana ta zuba shagwaSa, ta kalli fuskar sa tana ™o™arin tashi ta ce ""Malam cikani na tashi,"

"yarana jarirai ne, ba zaka haWa ni da ™ajaga ba ban gama warkewa ba, ka sakani konika"""

"Yayi dariya ya ce ""Ke matar so ita ce ke konika, ki yi wa duniya proving Win ke Win matar so ce ga raihan"""

"""Ni zaka yi wa wayo? Ai na riga na gama yi wa duniya proving ni Win Waya ce a zuciyar mijina"""

"""Wallahi faWi ki ™ara faWa, ni kyautar da Alhaji yayi miki ni na so yi miki ita, wata gigitacciyar kyauta nake son yi miki""."

"""Ni ba na son kowace kyauta, wuri nake son ka ™ara gyara mini a zuciyarka na mi™e ™afata"""

"Raihan ya ce ""Kin samu, ba kowa a ciki sai ke Salmana, Allah ya ™ara miki lafiya da nisan kwana, ya ™aro miki lafiya,"

"ki yi ta haifo mini ´a´a"""

"Ri™e hannunsa tayi tana dariya ta ce ""Ni zaka yi wa wayo, wai ba zuwa ka yi kana cewa ba ka da lafiya ba?"""

"Ya kwashe da dariya ya ce ""Duk cikin neman hanyar tsira ne, bani da lafiya idan har ba tare da ke nake tare ba, ni a"

"idona duk wata mace idan ba Salmana ba ba zata taSa zama Waya da ke ba. Ke daban ce a kowane fanni""."

"Kalaman jinjina da girmamawae da yake yi mata, ya sanyata jin kamar ta fi kowace mace sa'a a rayuwarta."

***

"Idris da sasassafe yana ta shirin fita zuwa karSar wani kuWi, sai faWa suke yi da hindu suna zage-zage kamar ´an tasha a kan kuWin cefane."

"Sallama aka yi a waje ya fita, ya tarar da ´ansanda a tsaye, ba su yi wata-wata ba suka cafke shi suka tafi da shi. Babu wanda ya san in da yake, dan babu wanda ya san kama shi."

"Sai da aka je wurin ´an sanda, wai ana tuhumarsa da yi wa wata yarinya fyaWe, an tsinci yarinyar a hanyar"

"makarantar islamiyyar su, an yi mata fyaWe an kasheta, wai shi ake zargi saboda hanyar wucewarsa ce, kuma an san halinsa na biye-biye yaran mutane."

"Farida na tsaka da jinyar rahama, Wakin da take ™onuwa sai wari take yi, duk da yadda ake kula da ita sosai."

"Inteesar ta shigo falon gidan, fuska duk a kumbure, idanunta sun yi jawur."

"""Ke inteesar lafiya meyafaru?"" Ta mi™a wa farida takarda, tana kuka ta ce ""Hajiyar sa ta saka ya sakeni, wai sun gaji da ciyar da ni sai dai na yi kashi babu haihuwa, alhalin Wanta ne silar komai!"""

"*Ina baku ha™uri, na san ina laifi rashin posting, ayyuka da bukukuwa ne suka yi yawa, ayi ha™uri dan Allah ina"

godiya da kulawa jama'ata ko in ce na ummi *

Ayshercool

08081012143

CUTARWA!

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

50

"Jikin farida na tsuma, ta karSi takardar ta duba, ga saki nan rangaWa-rangaWa guda biyu."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu Waya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai ba™in hali. Šaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa"

"hawa-hawa"" ta kira wayar dr. Amma bai Waga ba."

"Ta dungurar da wayar ta ce ""Ai na sani, ba zai Waga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida""."

"Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce ""™amshin abincin kawai"

"ya sa na ji na ™oshi"" tayi murmushi ta ce ""Ka dai fara ci tukuna"""

"Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce ""Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi"

"aure ba ta iya girki ba"""

"""Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor Wina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta"

"koya"""

"Dr. Ya ce ""Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daWi"""

"""Son kai, saboda ´ar ka ce ko?"" Yayi dariya yana kashe mata ido Waya."

"""Yauwwa ga wayarka, an kira ban Waga ba"""

"Ba tare da ya karSa ba ya ce ""Ki na tsoron kar ki Waga ki ji budurwa ta ce ko?"""

"Tayi dariya ta ce ""Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana bu™atar wani"

"abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta"" ya Wan ™ura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta ri™e mata ummi, daga baya ta ha™ura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta."

"Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ™afa ya lumshe idonsa."

"Ta ce ""Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri"""

"""A'a"" ya faWa a ta™aice."

Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa.

"Ya Wago haSarta ya ce ""Kin yi fushi ne?"""

"""A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?"""

"Ya ce ""A'a sai kin faWa"""

"""Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da ala™a,"

"ba tare da mun san mu ´an uwa ba ne, dan Allah baban ummi"""

"Ya Wan yi murmushi ya ce ""Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina"

"da juna biyu kar ki wahala"""

"""Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a"" yanayin yadda ta kwantar"

"da kai take lallaSa shi ya sanya shi jin daWi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. SaSanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani."

"""Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah"""

FaWaWa murmushinta ta yi tana yi masa godiya.

"Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su."

"Sai dai ta fara da yi masa ™orafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta mi™a masa takardar da inteesar ta zo da ita."

"Ya karSa ya karanta, sannan ya kalleta ya ce ""Na gani, me zan ce?"""

"""Kamar yaya me zaka ce? Ba zaka kira shi ba a kan abun da ya aikata, ya wulakanta ´ar ka"""

"Dr. Ya ce ""³ar ki dai, ki nema mata wani uban da zai tsaya mata, ni da ban isheku kallo ba ke da su, ai na yi zaton"

"wani uban ki ka canza musu, kuma ba wani abu da zan kira mijinta na ce masa, tun da ya riga ya saketa, in dai irin halin da ki ke yi, ta je tana yi dole a korota, yayi ha™uri ma. Idan baki ri™e tawa ´ar bazawara karo biyu ba, ga zaurawa biyu nan har da ™arin budurwa Allah ya haWa miki, kuma dolenki ki ri™e"" ya fice ya bar mata gidan."

"Inteesar ta Wora hannu a ka ta din ga rusa kuka, can gefe ma rahama kuka take yi, dan an saki mijinta, ya ™wace mata"

"sauran yaran, bayan aiko mata da tata takardar sakinta."

"Farida ta koma kamar mahaukaciya, ta rasa in da zata saka ranta."

"Kwanan ummi arba'in da biyar, ita da raihan da noor suka tafi yawon arba'in, a motar da Alhaji ya bata."

"Suka fara da zuwa gidansu raihan, da suka je gwiwa a ™asa ummi ta dur™usa ta din ga yi wa Alhaji godiyar mota da"

ya bata.

"Yara sun cika hannu, sun ™ara kyau sosai, babu yadda za ayi ace yaran hausawa ne a yadda."

"Alhaji ya ce ""Su wannan larabawan ba su fara dariya ba ne? Ko ni Win ne ba su gane ba"" yayi maganar yana yi musu"

wasa.

"Har wurin mami suka je, sai dai Nihal ce kawai ta Wauki yaran, tana hangen yaran abun ka da jini, zuciyarta na son"

"Waukarsu, amma sharrin zuciya da ™iyayyar ummi ta saka ta share su."

"Ana ta shirin bikin Nihal, saboda an kusa kawo kayan lefe, da an kawo kuma ba za a saka da yawa ba, za ayi bikin."

"Daga nan kuma ta ce su tafi can gidan farida, daga nan ma ta duba jikin rahama, tun da an ce a gidan take jinya."

"Raihan ya ajiye su, ya ce awa uku ya basu, zai dawo ya Wauke su, su tafi gidan mama."

"A falo suka tarar da inteesar, kamar aljana ta rame, hasken nan babu shi, duk ta fita hayyacinta."

"Ummi ta zauna tana faWin ""Anty intee kwana da yawa, ya ki ke ya gida?"""

"""Lafiya lau"" ta amsa jiki a sanyaye, tana ™arewa ummi kallo, da shigowarsu kawai ™amshin kabbasar kayanta, ta"

"gauraye Wakin. Wata irin dan™areriyar lafaya ce a jikinta mai tsada, hannunta yatsu uku duk gold ne, haka kunnenta, har da chain na gwal a ™afarta. Kai ba sai an gaya maka ba ka san ummi a hutu take."

"Noor ta ce ""Anty intee baki da lafiya ne? Duk kin rame"" inteesar ta girgiza kai."

"""Ina su Antyn su ke da rahama?"" Da hannu kawai ta nuna musu Waki."

"Ummi ta kwantar da iman, a kan kujera noor ta ajiye aiman suka shiga Wakin da sallama."

"Šakin sai warin gyambo yake, sai Wan zani aka yafawa rahama, duk ta ™one."

"A gigice ummi ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Anty rahama sannu ya jiki"" rahama ta sunkuyar da kai sannan"

ta amsa.

"Ta kalli farida ta ce ""Anty ina wuni, ya mai jiki?""."

"""Dalla rufe mini baki, kin zo munafunci ki ga a wani hali nake ciki, ko na haukace na fara bin bola kamar babarki, to"

ina nan daram. Dangin maita bakin da ki ka yi mata ya kama ta.

"Jiki a sanyaye ta ce ""Astagfirullah, ™addara ce daga Allah, kuma ke ki ka hasala ni, Sacin rai ya sanya na yi wannan"

"furucin. Sannu Anty rahama, yadda Allah ya jarabce ki da wuta a duniya, Allah ya haramta mata namanki a lahira, Allah ya baki lafiya da akwai wani abu a raina ba

72 / 74