CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 74

63K to 66K   out of 219.4K words

brown, ta kawo dogon hijjabi milk ta saka, ta Wauki ni™abinta ta sanya."

"Ta shashshafa turare, tafin hannunta har Waukar ido yake yi, saboda tafin hannunta fari ne ™al, kamar mata jini a jiki,"

kuma aka Wora mata jan lalle a kai.

"Ta Wauki ´ar ™aramar jakarta ta fito, Abdul ya ce ""Inyee ka ga amaren sauka"""

"Kawu yahaya ya dube ta cikin fara'a ya ce ""Congratulations dear, Ubangiji Allah ya sanyawa karatunki albarka, ya"

"™ara hasken makaranta"" ta risuna ta ce ""Amin kawu, na gode sosai da sosai"""

"Ya kalli farida da ´an matanta da suke ta sabgoginsu, kamar ba su san da zaman su a falon ba ya ce ""To mu mun tafi"

"wurin saukar"""

"""Allah ya tsare"" ta faWa a yatsune."

"Kawu yahaya yaji babu daWi, da yaransa ko mutum Waya babu wanda yayi saukar nan, idan baya nan sai sun ga dama suke zuwa makaranta, dan kuwa farida wurin koyon kwalliya ma ta sama musu, maimakon zuwa makarantar."

"Ummi gaba Waya bakinta ya™i rufuwa, kaf a ´an saukar ita ce ™arama, danma tana da jiki ne, dan ko Maryam shekara biyu ta bata, itakaWai ce mai shekaru sha shida a cikinsu, maryam na da sha takwas."

"Aka gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan aka fara raba musu alluna."

"Ana bata nata ta nufi rumfar iyaye maza, har da gudu, wurin kawu ta ™arasa ta dur™usa a gabansa tana cewa ""Kawu"

"ka ga"""

Ya karSi allon yana murmushi ya shafa kanta ya ce

"""Allah ya sanya albarka ummana"""

"""Amin kawu na gode"" tayi maganar cikin tsantsar farinciki."

"Abdul ya ce ""Rufe bakin mana"""

"Ta kalleshi ta ce ""Ta ina ka san bakina a buWe yake a cikin ni™ab""."

"""Yadda ki ke magana ne ya sa na gane"""

"Ta ce ""Bari Yaya Abdul, Alqur'ani da daWi wallahi""."

"""Wannan gaskiya ne ummana, kalli ba™in ki na waccan rumfar"" ummi ta waiwaya ta Waga kai."

"Wa zata gani? Yaya Magaji da auwwal, har da su Alhassan."

"Maimakon ta yi murna sai gabanta ya faWi, ta kasa magana, dan fatanta Allah ya sa babu Idris suka zo, dan bata"

™aunar ganinsa.

"Sunanta aka din ga kira a speaker, ta zo ta karSi kyautarta ta Waliba mai haza™a."

"A hankali ta tashi ta nufi in da ake kiranta, tafiya take cikin nutsuwa, shugaban makarantar ya ce ""˜aramar su"

"babbar su, Salma Muhammad Bashir, kun ganta nan duk ita ce ™arama a ´an sauka, amma babu Walibar da ta kai ta cin maki lokacin screening"""

"Ummi ta karSi kyaututtuka daban-daban, na haza™a, ladabi da biyayya da sauransu."

"Mamin su maryam ummi ta hango, ta tafi wurin da take, dan jan lallen da aka yi mata ma, gidan su maryam ta je,"

mamin ce ta biya.

"Mamin ta rungume ta tana faWin ""Allah yayi albarka ummi, Allah ya sanya wa karatunku albarka"""

"Ta risuna ta ce ""Amin ya Allah"""

"Sau Waya ya Waga kai ya kalleta, ya lura da yadda ko iya haWa ido da mamin ba ta yi, saboda tsananin tarbiyya da girmama manya, ya so ta Waga ni™abin ya ga ainihin fuskarta."

"Ya dubi Maryam ya ce ""Ke ba uban da aka baki? ba na ™o™arin, babu na Wa'ar"" yayi maganar yana sake gyara zaman"

face mask Win sa.

"Cike da tsiwa Maryam ta ce ""Ina ruwanka da ni? Ba a bani Win ba sai ka ™wace allon saukar ma gaba Waya, mami ki"

"rabani da shi wallahi, ai da yake ma ba gayyatarka na yi ba, waye ya ce ka zo?"""

"""Rufen baki kan na Sarar da ke a wurin nan"""

"Ummi dai murmushi kawai take yi, duk ta san yayyen Maryam, wannan ne dai bata sani ba, kuma da alama maryam"

Win ta raina shi.

"Aka tashi daga filin sauka, su yaya magaji suka nufo su, ""Ummi masha Allah, kin ga yadda ki ka girma?"" Magaji Yayi"

maganar yana kallon ta.

"Alhassan ya ce ""Ummi har kin yi sauka anya ba zu™u ba ce ba?""."

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Ai makarantar nan ba a saukar zu™u"""

"Suka rankaya zuwa gida, suna komawa gida ta tarar da Iya, sai da ta Wan ci burki, domin kuwa ba ta zaci Iyan za ta zo ba."

"Ta Soye mamakinta ta ce ""Iya sannu da zuwa, dama zaki zo?"""

"Ta harari ummi ta ce ""Eh, da ki ka ce ke ba zaki zo in da nake ba, kar na yanka ki na cinye ko?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a makaranta ce take hanani zuwa, ya gida ya kowa da kowa?""."

A ciki Iya ta amsa mata da lafiya lau.

"Dai-dai gwargwado kawu ya yi wa ummi ™o™ari, dan naman kasuwa ya sayo fal, ya bata tayi girkin da zata rarrabawa mutane da ™awayenta."

"Ita ummi ma kasancewar ba ta da ™awaye, sai ma™wabta ta babbawa, sai su Iya da suka zo."

"Sam farida ba ta bi ta kan Iya ba, ummi ce take ta Wawainiya da su, suna ta hirar makaranta da su magaji, sai dai ko"

"da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaWan."

"Kawu yahaya ya ji daWin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ´an uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuSe take ba."

"Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura,"

tun bata saba ba har suka saba da she™e ayarsu.

"Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga."

"Dan haka zance ya fasu a gari, sai faWuwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta."

"Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunWensu a garin."

"Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan Wa ya ri™e, kuma sai ya aureta."

"shiyasa Iya ta lallaSo wai kawu yahaya ya Wauke shi ya sama masa sana'a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!!"

"Iya a Wakin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin."

"Yayi ™uri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta."

"Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faWuwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce ""Amincewar"

"ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so""."

"""Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba Wan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane"

"ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi, ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauWar gora ai ciki ka sha ta!"""

Ayshercool

8081012143.

WHAT'S APP ONLY PLEASE

18

"Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshshe™ar kuka take yi, dan kuwa da ace ta"

"koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa."

"Iya cikin masifa ta ce ""To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai"

"aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ™one ™urmus, har wani zaSi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba""."

"Kawu yahaya ya ce ""Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani"

"abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni""."

"""Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za"

"a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo Win, sai a ja masa kunne"""

"Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshshe™ar kuka ya ce ""Ummana, jeki Waki abunki kin kwaso gajiyar sauka"" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi Wakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana"

"fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faWa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko ma™iyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris."

Noor ta bita Wakin tana kiran sunanta.

"Kawu ya kalli Iya ya ce ""Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba"

"Waya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci Wan wani ba, yadda ya yi wa ´ar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba."

"Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauWar gorar ba, sai ummi?"

"Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan ri™e ™ato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ™auye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi ha™uri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke Wawainiya da shi""."

"Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce ""Haka ka ce?"""

"""Ba faWa na yi dan na Sata miki rai ba, amma gaskiya ce"" Iya ta yi ™wafa ta ce ""Shikenan na tabattar da uwarka ce ba"

"zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku Waya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba""."

"Ya girgiza kai ya ce ""Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya Webo da zafi bakinsa, kin riga kin"

"sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaWai ne Wa a dangi ba""."

"Ba ™aramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ™iri-™iri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaSi tonuwar asirin su."

"Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaSa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da"

ita.

"Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuWin motar,"

"ya basu kuWin kashewa, suka tafi."

"Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da"

aka yi.

"Duk da kuWin da yahaya ya bawa Iya sun saka ta Wan sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya"

"Wauki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa'i kala-kala."

"Ko da suka koma gida ta sanarwa Idris da babansa cewa yahaya ya goya wa ummi baya, ya™i yadda da magabar da ta"

je masa da ita.

"Hankalin Idris ya tashi, dan kuwa baban hindu Wan bala'i ne, ya ce ba zai yadda ba, ba za a zubar da cikin jikin hindu"

"ba, sai ta haife shi, kuma sai sun karSa sun ri™e, hindu na da wani yaya da yake soja, kurtu nema a cikin sojojin, amma ya zamewa su Iya barazana, dan kuwa shi ma cewa yayi sai ya saka bomb a gidan su iya, ko ya kama Idris ya harbe shi, tun da aka taSa ™anwarsa."

"Magaji ya san duk barazana ce, babu Waya da zai faru, amma yayi shiru da bakinsa, saboda sun cancanci koma"

"menene ya same su, dan da idris bai taSa ´ar mutane ba, babu mai Waga musu hankali, kuma ya danganta hakan da alhakin ummi"

"Babu yawon da Iya ba ta yi wurin malamai ba, a kan a rufe bakin baban hindu, da ita kanta hindun da yayanta,"

"amma abu ya ci tura, dan har barzanar kai su gaban hukuma baban hindu yayi idan suka cigaba da takura masa a kan maganar cikin nan, ko kuma ya saka Wan sa ya Wauki duk matakin da ya ga dace a kan su."

***

"Tafiyar rahama daga gidan dr., Bayan an yi mata aure bata sauya zani da komai ba, daga wahalar da ummi take yi,"

"dan har undeas Win su intee ba zasu wanke ba, sai a haWa mata a kayan wanki, duk ta haWa ta wanke su."

"Sai dai tun ba aje ko ina da tafiyar rahaman ba, ta fara sintirin kawo ™ara wurin kawu yahaya, dan dama mahaifinsu"

"ya rasu, duk wani abu na jin daWi da ta sanya ran samu a gidan mijin, sai ta ga akasin haka, yana da hali ba bashi da shi ba, amma hatta shinkafa da man da za ta ci, sai ya ™ulla mata, ba yadda da zuwan ba™i gidansa ba, sai an kira shi ya bayar da iznin a zo, idan bai bayar ba kuwa babu mai zuwa."

"Kawu yahaya ya kira shi, dan a samu masalaha amma ya nuna shi tsarin gidansa ne a haka, dan haka dole a bar shi"

yayi yadda yake so.

"Haka nan kawu yahaya ya ce sai dai tayi ha™uri, yace shi tsarin gidansa ne a haka."

"Tun da shekaru goma sha shida, samari suka fara bin intee, hakan ba ™aramin farantawa farida yayi ba, tana ganin intee mai goshin arziki ce, shekara goma sha shida, samari sun fara sintiri, dan ma dr. Yana korarsu ya ce yarinyarsa"

tayi ™an™anta sai ta fara karatu idan ma auren zai yi mata.

"Lokacin da ummi ta fara period babu wanda ta gayawa, dama ta riga ta san shi tun a karatuttukansu na makarantar"

"islamiyya da na boko ana gaya musu shi, sannan an koyar da su tsabta a lokacin da mutum yake cikin jinin haili. Dan har wata ™ungiya ta je makarantar su suka wayar musu da kai, a kan jinin haila da tsafta, dan haka babu wanda ta gayawa da ya same ta."

"Ta samu kayanta da suka Wan kwana biyu, ta yayyanka Wankwalin, take amfani da shi."

"Idan kuma Allah ya sa dr. Ya bata kuWi, babu abun da take fara saya sai pad, tana iya ha™ura da kowace irin bu™ata ce da ita, ta sai pad Win da za ta yi amfani da ita da kuma farin muski."

"Sintirin samari zuwa wurin intee, ta din ga wani iyayi tana yau™i, ya sanya aka fara yi wa ummi gori da habaici,"

"domin kuwa babu wanda ya taSa zuwa ™ofar gidan ya ce yana sallama da ita, ko a hanya ma babu wanda ya taSa biyota ya ce ya na so."

"Su yi ta yi wa ummi wula™anci, wai farar mace Alkyabbar mata, ba™ar mace bolar maza."

"Kodayake bolar akwai wadda ake iya recycling, wata ta riga ta zama waste gaba Waya bata da mamora."

"Ko sai sun ga ummi su fara wankan ba™i asarar ruwa, ko yayi ma kamar bai yi ba, blaki kalar dauWa, su din ga yi suna tuntsura dariya."

"Ummi kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da sabgoginta, duk da a ™asan zuciyarta kalaman na su na tasiri a"

"cikin zuciyarta, tana jin babu daWin cin mutuncin halittar ta da suke yi."

"Haka Maryam ma, kasancewar ta kyakykyawa, kullum ba ta da aiki sai bawa ummi labarin saurayinta kaza yayi mata"

"kaza, ko ya bata abu kaza."

"Ba maryam kawai ba, ´an ajinsu ba su da aiki, sai hirar samari, ita kuwa da ta san ba ta da kowa, ta rungumi litattafanta yadda yakamata."

"Idan suka so yin dariya kuwa, sai su yi ta zungurar ummi, suna tambayarta wai ita waye nata saurayin, ta gaya musu"

"fari ne ko ba™i, dogo ko siriri."

"Kawai sai tayi murmushi ta yi musu shiru, ta™i kula su."

"Maryam ce ta fara bata shawara ""Ummi, yakamata ko Wan mayukan nan na zamani ki Wan din ga shafawa, ko kema"

"kya yi haske, maza ba sa son ba™ar mace, ummi kin yi duhu da yawa, duk kwatancen ba™in da za ayi a makarantar nan da ke ake yi, idan ki ka shafa mai ki ka Wan yi haske, ko yaya zaki samu saurayi, ko zaki ji daWi duk mu yi aure mu bar ki? Ni fa mami ta ce ina candy aure za ayi mini, na cigaba da karatu a gidan mijina, amma ke kullum kin ™i wayewa, ga uban hijjaban da ki ke sawa, ba kya kwalliya kamar mu, bayan hijjabi har da wani uban ni™ab, to waye zai ce yana son ki, kalli ranar da muka je barkar gidan su Saratu, kowa yayi kwalliya amma ummi ke kin zunduma over size hijjab fisabilillahi. Ranar da babu school, ki zo gidanmu akwai wata mai mayukan gyaran jiki, muje ta haWa miki mai sai na biya"""

"Ummi shiru tayi tana ™o™arin haWiye wani abu mai Wacin gaske, da yake yi mata kai komo tsakanin ma™ogwaronta da"

"™irjinta, wannan shawara maryam take bata ko ci mata fuska."

"""Ina magana kin yi mini shiru"" Maryam ta yi maganar a Wan hasale, dan daga abun da maryam ta tsana a halin ummi"

bai wuce miskilanci da shariya ba.

"Wanda ba wai miskilancin bane kawai, tana gudun shiga harkar mutane, kar tayi wani abun da za aci mata mutunci."

"Ummi ta Wago ta kalli maryam, hawaye har ya zagaye cikin fararen idanuwanta, ta Wan juya brown Win ™wayar idonta"

"ta ce ""Maryam, I won't bleach my skin, ko a so ni a haka, ko a ™yale ni, banbancin fari da ba™i a wurin Allah, wanda yafi tsoronsa mu ´an adam mune muke Worawa kanmu""."

"Cikin ™uluwa maryam ta ce ""Au dan na baki shawara ina nema miki mafita, shine ki

22 / 74