CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   1 / 74

1 to 3K   out of 219.4K words

˙ūCUTARWA!

P1

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION



"*˜ir™irarren labari ne, duk abun da aka gani a ciki, yayi kamanceceniya da wani abu, na zahiri ko makamancin haka, arashi ne*"

"*Ha™™in mallakata ne, ban yarda a juya mini shi ta kowacce irin siga ba, sai da izinina"""

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH).

Gagarawa Jihar jigawa.

"Kasancewar wata ya nausa, domin kuwa watan jumada ula, ya kai kwanaki ashirin da biyar, wanda yake dai-dai da"

watan Nuwambar shekarar miladiya.

"Mislain ™arfe biyu da rabi, dare ya tsala, duhu ya mamaye ko ina, baka jin sauti ko motsin komai, sai kukan ™ananan ™wari, da sautin busassun ganyen bishiyu, da iska ke kaWawa lokaci zuwa lokaci."

"A dai-dai wannan lokacin da kusan galibi mutane ke kwasar bacci, ni kuma har a lokacin idon ta tamkar an soya,"

"babu alamar bacci a tare da idanun nata, sakamakon bushewar zuciya da raWaWi da take ji."

"Sai yau ta tabbatar da cewa, nutsuwar zuciya, da kwanciyar hankali, da ™arancin tunani, suke haWuwa su haifar da"

"daddaWan bacci, mai cike da annashuwa."

"A hankali ta tashi daga kan katifar da take kwance, na nufi tagar Wakin, ta buWeta, wani sanyi ya daki fuskarta, ta kalli"

"™aton tsakar gidan, da baka iya gane komai a cikin sa, saboda duhu."

"Ta Waga kanta, ta kalli taurari, yadda suka yi wa sararin samaniya ado, ™udura da iko na Ubangiji na ri™e da su a sama."

"Tayi ajiyar zuciya, tare da kamanta rayuwarta da wannan ba™in daren, mai cike da duhu, da ban tsoro."

"A lokacin da karin maganar bahaushe ya yi amsa amo, a tsakanin ™abilar ta hausawa, na cewa dauWar gora ciki ka sha ta, sai dai kash! Zamani ya zo mana da cigaba, ta hanyar nuna mana muhimmancin lafiyarmu."

"Duk da cigaban da aka samu, hakan bai hana a tauye ta ba, a shayar da ita dauWar gorar ta ™arfin tsiya ba, wanda hakan yake CUTARWA! Domin kuwa ya zame mata tamkar guba, domin ya zama silar sanya mata ciwon da take ta fama da shi, ta rasa maganin sa, wanda tun yana Soye, sai da ya fito yayi tsiron da mutane suke yi mata tambari da shi."

"Haka zalika, azancin hausawa na ciwon ´a mace na ´a mace ne, ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ´a mace, na ta ne ita kaWai. Wata™ila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waWanda ciwon ´a macen yake zama nasu ba."

"Duk iya ™o™arin da ta yi wurin haWiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashina fita cikin huci."

"A hankali ta furta ""Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ™alubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma"

"kuWinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na Waura aniyar fito na fito da duk waWanda suka cutar da ni. Tun da babu sani babu sabo, dole in fasa ™wan da warinsa ka iya sanadiyyar tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure WaWWake dauWar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ™ara gaba,, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa."

*****

"La'asar sakaliya, wata matashiyar mace ce da ba zata gaza shekaru sha takwas a duniya ba, zaune a ™aton tsakar"

"gida, tana ta ™o™arin tsince waken da zata daka, ta zuba a cikin miyar yau™in da take yi, cinyarta wata yarinya ce ´ar kimanin shekaru uku da rabi a duniya a kwance, ta saka babban Wan yatsanta a baki ta na sha, hannunta Waya kuma tana wasa da cibiyarta."

"Idan ka kalli yarinyar sau Waya, sai ka sake kallonta, tare da son sanin daga wace ™abilar wannan yarinyar take?."

"Ba™a ce sosai, mai ™iba, tana da Wan goshi, sai dai yalwataccen gashin girarta ya rage fitowar goshin nata, tana da"

"manyan idanuwa farare, sai dai ™wayar idonta brown ce, maimakon ba™a, bakinta Wan cukul, sai dai laSSanta jawur, tamkar an saka mata jambaki. Babban abun da zai baka mamaki, bai wuce yadda take da dogon gashi ba, ba™i wuluk, mai tsayin gaske, ba curkukuWaWWe irin na ba™a™en fata ba, tamkar gashin larabawa, kalba aka yi mata guda biyu, amma ta saukko har cikinta, hancinta ba shi da wani tsawon kirki, saboda kumatu ya shanye su."

"""Wai Mariya ba zaki ajiye wannan gunsumemeiyar yarinyar ki mayar da hankali ki kammala aikin nan ba. Kawai kin"

"Wauki ´a kin narka a cinya ´a ba kaWan ba ko nauyi ba kya ji? Na ga dai ba nono za ki bata ba"""

"Mariya a ranta ta ce 'Ban da abun iya, ta yaya saniya za ta gaza da ™ahonta?'"

"A zahiri kuwa cewa ta yi ""Yanzu zan kammala iya"""

"""To ki ajiyeta ta shiga cikin yara tayi wasa mana, wannan uwar matan ta zauna a cinya, kema ki haihu ki yi mata ™ani,"

"kin naWe kin ™i haihuwa, kiyi ™o™ari dai ki haifo wani, ko Allah ya sa a samu mai Wan dama-dama, wannan ´a muninta yayi yawa, Ko da yake can danginku ta kwaso wannan ba™in da muni, barebari ai haka ku ke ba™i kamar zunubin mutanen farko"""

"Mariya ta sunkuyar da kai tayi shiru, ta na jin zafin maganganun nan, amma ba yadda ta iya, haka ta ™a™alo murmushin dole, ta ce ""Hajiya iya kenan, jikar nan taki mamaki zata baki, idan ta tashi kawo miki siriki, mai mai™o za"

"ta kawo, wanda zai kai ki makka""."

"Iya ta furzar da goron bakinta ta ce ""Da wannan ba™in da munin? Maza na rububin farar mace, wa zai kwashi kayan"

"muni, ai ko wannan idon nata, ya isa hanata auruwa, ido abun tsoro kamar ragowar maita, sai ido furi-furi kamar bururrun gawayi"""

"Sake kwanciya yarinyar ta yi a jikin uwarta, tare da kawar da kanta gefe."

"Mariya ta shafa kanta ta ce ""Ummina, ki tashi in haWa abinci, kar yayyenki su dawo ban gama girki ba, ki tashi ki je ki"

"yi wasa da su Auwwalu"""

"No™e kafaWa yarinyar tayi, tana tura Wan mitsitsin bakinta, ta sake gyara zama ta mayar da hannunta baki."

"Sallamar da aka yi ne, ya sanya su haWa baki wurin amsawa."

"Sai dai ba ™aramar razana ta yi ba, da jin muryar mai sallamar, dan sai da tayi wani zillo ta tashi zaune, wani Wan"

"matashin saurayi ne, hannunsa ri™e da wata ´ar jaka."

"Iya ta ce ""Ahh, idris ka dawo?"""

"""Eh, an gama abinci ne?"""

"""Ina fa, tana nan tana la™ai-la™ai tana fama da wannan jibgegiyar yarinyar, ita ba nono za ta sha ba, sai iskanci da"

"taSara dan sangarta""."

"Ya kalli yarinyar ya ce ""Ummi, zo mu je na sai miki biscuits, ki bari anty ta gama mana girki"""

"Ma™ale hannunta tayi, tana zazzaro ´an idanunta, da tsoro ya bayyana ™arara a cikin su."

"""Ummina, dan Allah ki bi yaya idris, in kammala aikin nan"""

"Hawaye ya cika mata ido, tana kwantar da kanta a jikin mahaifiyarta."

"Ya mi™a hannu zai Wauke ta, ta fashe da kuka mai kama da na shagwaSa, amma a zahiri na tsoro ne."

"""Kai dalla ™yale mata ´ar ta, dan ta samu za a Wauke ta, ji iskancin da take, ita shagwaSar ma ba kyau take yi mata"

"ba, aba ba kyan gani kamar turotso""."

"Ta ™arfin tsiya ya saka hannu, ya Wauketa, tana ta kuka, mariya kuwa cikin kara da kawaici, ta tashi tana cewa"

"""rigimammiya sam ba kya girma""."

"Ya fita da ita a kafaWarsa, bai tsaya a ko ina ba, sai wani sashi na gidan, a ™ofar wani Waki da ba kowa a sashin,"

yanayin wurin zai nuna maka wurin Wakin ´an maza ne.

"Ya buWe Wakin ya shiga da ita, yana zuwa ya dungurar da ita a tsakar Wakin."

"""Rufe mini baki, ko na sha™e ki, ki mutu"" cikin sheshshe™a take ™o™arin danne kukan nata, gaba Waya ta burkice cikin"

matsanancin tashin hankali.

"Ya bankaWa gefen wata katifa, ya Waukko almakashi, ya dur™usa a gabanta ya ce ""Kin gaya wa mamanki ko?"" Ta"

"girgiza masa kai, hawaye na zuba daga idonta, ga ™o™arin haWiye kuka da take yi tamkar zata shiWe."

"""Kin faWa ko baki faWa ba?"" Ta sake girgiza masa kai cikin razani."

"""Duk ranar da ki ka faWa, sai na gutsutstsura namanki da almakashin nan, na zuba a leda na kaiwa karen namadi, ya"

"cinye ki, kuma sai na saka ki a murhun da babarki take girki, ai kin taSa ™onewa kin san zafin wuta"""

"Ba ta iya cewa komai, sai bin sa da ido, hawaye na zuba daga idonta."

"Ya ajiye almakashin, ya janyo ta, ya fara ™o™arin cire ´ar doguwar rigar jikinta."

"Sake fashewa ta yi da kuka, har da Wan ™ara sauti, aikuwa ya zare mata ido, ya sha™eta ya Waukko almakashin, ya"

"saita tsinin a ma™oshinta, jikinta na rawa ta yi gum da bakinta."

"Kamar yadda ya saba Waukkota yayi mata, haka yau ma idris yayi mata, sai da ya gama abun da Allah ya nufe shi da"

"yi, sannan ya ™yale ta, sai dai bai taSa gangancin ™etara ta ba."

"Ya cigaba da yi mata kashedi, tare da firgita ta, a kan idan ta faWa, sai ya sakata a murhu ya babbaketa."

"Ya bar ta a nan zaune, ya kintsa, sannan ya zo ya ja hannunta, da ™arfi sai da ta ji zafi, amma ba damar yin kuka, tana"

tsoron kar ya babbakata a wuta ko ya yankata da almakshi.

"A wula™ance, ya tafi da ita kanti, ya saya mata biscuit Win naira ashirin, da alewar naira biyar, ya sake fizgo hannunta"

"ya nufo gidan da ita, sai tankaWata yake yi yana masifar tayi sauri."

"""Ba zaki yi sauri ba, sai wani jagwab-jagwab ki ke, kamar tsohuwar talo-talo"" tafiyar sa da tata ba Waya ba, mussman"

"ita da ke da jiki, haka ya ja ta sai daf da zasu shiga gidan, ya sake jaddada mata, kar ta gaya wa kowa abun da yayi mata. Ya saSata a kafaWarsa ya shiga da ita gidan."

"""Anty mariya, ga rigimammiyar ´ar ki nan, uwar kuka, ta karSe mini biskit, amma har muka dawo kuka take, saboda"

"shegiyar ™yuya""."

"""Ohh, Ummi Allah ya shirya mini ke, an girma amma ke ba kya girma, kamar ba ´an mata ba"" gaba Waya ummi"

"hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai da sosai, sai dai kasancewar ita kan ta mariyar yarinya ce, shekarunta sha takwas, a zaton ta kawai rigima ce, kasancewar ummi, yarinya mai azabar ™yuya da miskilanci."

"A nan tsakar gida ta yasar da biskit Win, ta je ta rirri™e mahaifiyarta, ana daf da sallar magariba, mahaifin ummi ya"

"dawo, ya Wauke ta yana juyi da ita a tsakar gida, yana faWin ""Ummi, waye ya taSa ni ´a Waya tilo, na ga kamar kin sha kuka? Ko dai kin daketa ne?"" Yayi maganar yana kallon mariya."

"""A'a wallahi, ™yuya ce kawai, ba zata yi wasa a cikin yara ba, ta ma™al™aleni, dan idris ya Wauke ta take kuka""."

"""Ki daina ™yuyar nan dan Allah, na zo miki da alewa daga kasuwa, da yalo ai kina ci ko?""."

"But iya ta fito daga Wakin ta, ""Balarabe wannan ´ar ka sunkuta ka ke shillawa sama, sai ™irjinka yayi ciwo tukuna ko?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Iya guda nawa ummin take"""

"""Ajiyeta dan Allah, duk a haka ku ke sangarta ta, tayi ta taSara tana iskanci, ´a sai ka ce teba"" cikin jin nauyin mahaifiyar sa, ya ajiye ummi, yana murmushin ya™e."

"""Ina alewa da yalon da na ji ka ce ka zo da su? Bani nan a rabawa sauran yaran gidan, ai ba ita kaWai ce ´a ba, nan"

"idirs yanzu ya fita da ita ya kaso mata uban kuWi, amma kai sai ka zo da abu ka hana sauran yaran? Saboda ka haifi gwal?"""

"""A'a Inna, ina sayo da su suma, gani na yi ita ce ™arama, kuma yau kasuwar sai godiyar Allah, tun da ba ranar kasuwa"

"ba ce ba, Wan kaWan ne na zo da su ba yawa"" yayi maganar yana nuna mata ´ar ledar hannunsa."

"Ta ™araso ta fizge ledar ""To tun da ba ciniki, sai ´ar taka ta ha™ura, kai dai balarabe kamar a kan ka, aka yi wahayin"

"talauci, kullum kasuwa ba cigaba, kana kallon yadda ´an uwanka suke ™o™ari kowa da abun arzikin sa, kai kuwa ba ka ajiye komai ba, sai son mace da wannan mummunar yarinyar, daWi aure ba zaka zage ka nemi arziki ba"" shiru yayi ya sunkuyar da kansa, dan ba shi da abun cewa."

"Mariya kuwa ta mayar da hankali wurin kwashe tuwo, roba-roba."

"Malam Hashimu dodo, shi ne mijin iya, gidansu babban gida ne, da aka yi ittifa™in babu gidan da ya kai su yawa."

"Da yayi aure ya ja nasa Sangaren a cikin gidan su. Kasancewar gidan babba ne sosai, dan kusan duk garin babu mai girman gidan."

"Kowa ya san su, saboda galibi ´an gidan manoma ne, sai masu taSa kasuwanci, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado."

"A hankali wasu suka din ga samun rufin asiri, suna watsewa daga gidan, malam hashimu yana sake shigar da wasu sassan nasa sashin."

"Daga baya ya auri iya, bayan matarsa ta ladan noma wato salamatu. Malam Hashimu mutum ne mai hidimtawa iyali, a lokacin boko ba ta yawaita ba, sai karatun allo, dan haka da shi da ´an uwansa suna da ilimin soro."

"Bayan wani lokaci, salamtu ta mutu, ta bar yaranta huWu, biyu mata biyu maza, iya ta cigaba da ri™on su, da nata"

´a´an.

"Sai dai iya macece me shegen son abun duniya, tamkar ta yi ™wace, ga ta da iya fuska biyu, a waje ta nuna ta Allah"

"ce, amma na cikin gidan, su suka san gashin da suke sha."

"Ba ´a´an da aka bar mata ba, har facalolinta, da suke cikin gidan iya na azabtar da su, gwargwadon abun hannunka, da abun da ka ke bata, gwargwadon mutuncinka a idonta."

"Aka aurar da ´a´an salamatu mata, Wayan kuma Yahaya, ya ce shi karatun boko yake so. Iya tayi ta sukar abun,"

amma malam Hashimu da suke kira da baba ya bashi goyon ba.

"˜aninsa kuma Ilyas, yana zaune a nan ™auye, amma yana taSa kasuwanci, nan da nan ya fara tara kuWi, yayi wuf yayi"

"aurensa, shima ya tare a cikin gidan."

"Yaran iya su biyar, biyu mata Shafa da zaliha, uku maza, Sagir, Saminu, sai Bashir wato balarabe. Duk wanda yake da"

"kuWi shi ne nata, hatta a jikokinta bambanci take nunawa muraran, sagir ne babba shine baban Idris da kuma Hashim suna ce masa magaji, saboda sunan malam ne da shi."

"Akwai tarin ´a´a da jikoki a gidan, bayan rasuwar iya ita ke tafiyar da gidan, saboda azabar faWanta da iya masifa, hatta ´an uwan malam tsoron ta suke ji, abun da ta dama shi ake sha."

"Saboda balarabe ba shi da kuWi, wato baban ummi, duk gidan shi ne samunsa ba mai yawa ba, dan dako yake yi a kasuwa da ´an buge-buge dan haka samun nasa galibi sai damina idan yayi noma, hakan ya sanya duk wata"

"Wawainiyar gidan ta wahala, iya ta sa matarsa mariya ce ke yi, wadda asalinta ´ar Maiduguri ce babarbariya ce, sun zo garin biki suka haWu, har Allah ya sa suka yi aure."

"Tun da mariya tayi haihuwa Waya ta haifi, yarinyarta aka saka mata sunan mahaifiyarta, wanda yayi dai-dai da sunan"

"uwar gidan malam, wato Salma ba ta sake haihuwa ba, tsawon shekaru uku kenan, iya ta Worawa yarinyar nan Ummi"

"™ahon zu™a, da ba'a da cin mutunci, wai ta haifi wata halitta daban, da babu irinta a danginsu."

"Ba ita ba har yaran gidan, da sauran mutanen gidan, na yawan kushe halittar ummi, tare da tsokanarta, gashi ayi ta"

"tankata, saboda ba™inta, da kuma ™ibar ta, ga kuma kalar idonta, sai dai kuma mutane na mamakin irin gashin kanta, dam idan mariya na gyara mata kai, ruf gashi yake rufe mata fuska, tamkar na larabawa."

"Allah ya albarkaci gidan malam Hashimu, da yawan yara maza a jikokinsa da ´a´ansa, mata sam ba su da yawa,"

kuma da sun tasa ake aurar da su.

"Dan haka kusan ummi, ita kaWai ce yarinya mace ™arama a cikinsu, sai dai hakan ya zame mata babbar barazana ga"

rayuwarta!!!

08081012143

*CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724

Arewabooks ayshercool7724 YouTube Cool hausa novels What's app 08081012143

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

P2

"Yawan kyara da hantara, haWi da kushe halittar ummi, ya sanya ta zama yarinya mara karsashi ko a cikin sa'aninta."

"Dan wasu har i™rari suke ko mayya ce, saboda launin ™wayar idonta da ta sha banban da ta sauran mutane."

"Wasu lokutan mariya duk sha'anin da za ayi na taron mutane, ta kan iya ha™ura da zuwa saboda ummi, ba ta son"

mutane.

"Abubuwan da wasu daga samarin gidan suke yi mata ne, ya sanya ta sake tsorata da lamarin mutane, ta fara ganin"

"tamkar ita ta ta duniyar daban take, dan idris ne kawai yake amfani da ita wurin biyan bu™atar sa ba."

"Mariya bata taSa fuskanta ba, wasu lokutan har tsoron nuna wa ummi kulawa take yi, a gaban iya, saboda yanzu zata hau masifa da faWa, wai tana nuna wa ´ar fari soyayya saboda ba ta da kunya. Ko yaya ummi ta Wan sake a cikin yara, sai su fara cin zalinta, ko su din ga jan dogon gashin ta, ko jan kumatunta da suke tamkar doughnut ya ji yeast, ko yi mata dariya da ihun ba™ar tukunya mai ™yalli."

"Takurar yara ya takureta a gida, a gidan ma iya sashinsu, shi ma fitowa tsakar gida idan ba tare da mamanta ba, ba ta"

fitowa saboda hantarar da kyarar da iya take yi mata.

"Haka rayuwar gidansu ummi ta cigaba da garawa, iya kullum tana cikin haba-haba da ´a´a da jikokinta, masu kawo"

mata abun duniya.

"Yayin da ta tattara cin kashinta, a kan balarabe da iyalin sa, tamkar ba ita ta haife shi ba."

"Ummi ta Wan ™ara tasawa, kusan kullum sai ta tambayi

1 / 74