Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   98 / 140

291K to 294K   out of 417.8K words

hannunsa duka biyu kana ya furta.
_“Astagfirullah wa'atubu ilaik”_.

Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya juya ya kalli Zakariyya dake cewa.
“Moddibo muyi alwala muyi sallah ana kiran Sallah”.
Kai suka gyaɗa kana suka miƙe sukayi al'wala kana nufi masallaci alayi ɗaya sukayi jam'i koda suka idar da Maghriba basu dawo gida ba saida akayi Isha'i kana suka dawo.
Suna dawowa suka samu an shirya musu komai na a binci dining....


Acan falon da aka sauƙe su Khausar kuwa cikin gigita Asma'u ta shiga falon tare da faɗawa kan Ummi dake zaune cikin ficewar hayyaci take faɗin.
“Wallahi Ummi naga Yah Jameel”.
Da sauri Ummi ta zaro ido kana tace.
“Me kike faɗa Asma'u”.
Cikin zubda hawaye da rauni Asma'u ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Wallahi Ummi naga Yah Jameel tare da Yah Moddibo”.
Yanayin da take magana cikin alamun kiɗima da gigita yasa Ummi saurin janyota ta riƙe ta.
Innayi ma matsowa kanta tayi kana ta riƙe hannunta tare da cewa.
“Asma'u wanda ya rasu yana dawowa ne?”.
Kallon Innayi tayi da jiƙaƙkun idanunta kana tace.
“Innayi wallahi Yah Jameelu na gani naga Yah Jameel Wallahi na ganshi”.
Cikin fesar da numfashi Ummi tace.
“Asma'u ki nutsu mana, In dai Jameelu ne da gaske ai zai iso mu”.
Ummi kam kallonta kawai take aranta tasani cewa tabbas Jameelunta ya rasu ya barta tasan cewa babu wani Jameelu sai dai in gezo yake wa Asma'u ta.
Aunty Ruƙayya dake zaune can gefe ta miƙe ta matso gefen Asma'u ta zauna tare da riƙe hannunta tace.
“Asma'u ya za'a yi wanda ya mutu ya dawo? Shi wanda ya mutu baya dawowa ai shi mutuwa ɗayace idan mutum yayi ta yayi ta har abada”.
Cikin matsanancin kuka Asma'u ke girgiza kai kana tace.
“Wallahi Allah Aunty Ruƙayya na gansa”.
Ƙiran Sallar Maghriba da akayi ne yasa Ummi kallon Asma'u cikin tsawa ta haɗe fuska kana tace.
“Maza tashi Kije kiyi a''wala kizo kiyi Sallah”.
Da sauri tace.
“Wallahi! Wallahi!! Ummi Yah Jameel na gani, ki yarda dani”.
Cikin haɗe fuska Ummi tace.
“Zakije kiyi salla ko zaki tsaya hauka”.
Jiki asanyaye ta miƙe taje tayi al'wala kana tazo ta shimfiɗa Sallah kana tayi Sallah koda suka idar da sallar Maghriba Azkhar sukayi har aka kira Isha'i kana sukayi ...

Bayan sun idar da Isha'i Asma'u ta koma gaban Ummi ta zauna cikin muryan kuka tace.
“Wallahi Ummi Yah Jameel na gani Ummi ki yarda dani ku nemi Yah Moddibo wallahi Yah Jameel na gani fa Ummi”.
Ganin yanda ta rikice yasa Ummi sauke zazzafan ajiyar zuciya tare da kallon Innayi da tazo gabansu kana tace.
“Innayi ane momin Moddibo al'amarin Asma'u yayi yawa fa, gaba ɗaya agigice take kinga Sallar nan har aka idar da Maghriba kuka take har aka zauna Azkhar still kuka take har muka jira Isha'i kuka Asma'u keyi”.
Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi side ɗin Didi.
Tana shiga Side ɗin Didi suka sake gaisawa kana ta yiwa Didi bayanin abinda ke faruwa.
Cikin sauƙe numfashi Didi tace.
“Tabbas ai shima kanshi Aleeyu sanadin shigowar sa Masarautar nan haɗuwar sa da Dr Jameel ne”.
Cikin yanayin mamaki Innayi ta tallafe kuncinta tare da faɗin.
“Toh waye Dr Jameel ɗin?”.
Ahankali Didi ta shiga bata Labarin da Dr Jameel ya bata.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe kana tace.
“Toh dan Allah ayi min iso zuwa Side ɗin dasu Moddibo suke dan bansan inda suke ba”.
Ƴar dariya Didi tayi tare da cewa.
“Ai suna kusa daku suna ƙasa, kuna sama bari nayiwa Jakadiya magana ta rakaki”.
Nan Didi ta umarci Jakadiya kana ta yiwa Innayi jagora zuwa sashen dasu Moddibo suke...

Innayi na shiga ta samu Zakariyya Dr Jameel Ibraahim suna Kan dining yayin da ta haɗu da Moddibo gab bakin ƙofa da alamun zai tafi wajensu ne, dan ya duba halin da Asma'u ta tafi.
Yana ganin Innayi sai yayi saurin komawa baya.
Innayi kuwa tana ganinsa tayi murmushi.
Shi kam hannunta ya riƙe suka ƙarasa cikin falon kana suka zauna kan kujera suna zama kan kujera yace.
“Innayi nayi kewarki”
Cikin jin daɗin ganinsa ta gyara zama tare da faɗin.
“Nima nayi kewarka, amman dama ai nasan cikin danginka za taho nasan ka dawo cikin ƴan uwanka muhallinka”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Innayi wani irin tarin abubuwa kikayi ta ɓoye min a iya tsawon rayuwata?”.
Numfashi ta fesar da cewa.
“Sai ahankali yanzu dai farko waye Asma'u ta gani ta koma tana ihu tana ce mana Jameel ne”.
Kai ya jinjina tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Gashi can Innayi juya ki kallesa baiyi miki kama da Jameel ba?”.
Da ƙarfi Innayi ta tashi kana ta buga hannunta akan ƙirjinta cikin tsananin ruɗu tace.
“Kamar yaya kama?,Aliyu kace min Jameel dai Ashe gaskiyan Asma'u Jameelu ta gani”.
Ta ida Maganar tare da juyawa ta nufi dining area cikin sassarfa.

Tana zuwa ta kamo hannun Dr Jameel tare da riƙewa tace.
“Jameelu”
Kallonta yayi tare da yin murmushi shima kansa yanda suke zuzuta tsananin kamansa da Jameelu ya fara bashi tsoro da mamaki.
Innayi kuwa batare data jira komai ba ta kama hannunsa tana ja.
Shi kuwa Dr Jameel tsintar kansa da bin bayanta yayi.
Shima Moddibo cikin sauri yabi bayansu yana cewa.
“Innayi ba Jameelu bane wallahi tsananin kama ne”.
Ina tuni Innayi ta fice batare data sauraresa ba ta fara haurawa step ɗin tana cewa.
“Ummin Jameel”.
Zakariyya da Ibraahim ma na biye dasu suna shiga Falon da Ummu ke zaune Innayi na cigaba da cewa.
“Ummin Jameel Wallahi gaskiyar Asma'u ne Jameelun kine”.
Akuma dai-dai lokacin Ummi ta juya da sauri idanunta suka sauƙa akan Fuskar dake tsananin kama da Jameelunta komai na Jameelunta a fili.
cikin wata raunatacciyar murya tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.
Sai kuma ta koma ta faɗa kan kujera idanunta na zubda hawaye shar-shar-shar.
Itama Asma'u cikin sauri ta riƙe hannun Ummi tare da faɗin.
“Ummi ba kin gani ba na faɗa miki Yah Jameel ne”.
Sai kuma ta saki hannun Ummi ta koma ta riƙe hannun Dr Jameel na dama Innayi kuma na riƙe da hannunsa na hagu suka zo gaban Ummi suka durƙusa sai shima ya tsinci kansa da durƙusawa agabanta, haka nan yaji kima da martaban matar sun cika masa idanu.
Da sauri Moddibo ya ƙarasa shiga wa falon tare da zama gefen Ummi wacce ke kan 3sitter kana cikin raunin murya yace.
“Ummi”.
Cikin zubda hawaye ta juya ta kallesa cikin rauni ya cigaba da cewa.
“Ummi ki kalli duk komai na Jameel ne muryansa, Tafiyarsa, Gangar jikinsa, Har fa asakin da Jameel keyi shi yake yi amma wallahi Ummi ba Jameelunki bane kamannin ne yayi yawa Wallahi!³ Ummi ba Jameelunki bane”.
Juyawa Ummi tayi ta kallesa cikin jinjina masa take cigaba da gyaɗa kanta jikinta yana bata ba Jameelu bane domin jikinta ba amsheshi a matsayin Jameel ba wannan bawai ɗan ta bane agabanta amma zuciyarta taƙi yarda.
Kai ta girgiza still hawaye na bin fuskarta ta juya ta kalli Dr Jameel da yake durƙushe agabanta.
Ganin yanda take zubar da hawaye yasa shima yake zubar da hawaye.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh meyesa ka kuma?”.
Ahankali ya ɗago kai ya kalleta cikin tarin tausayinta da kuma rauni yace.
“Saboda kukan da naga kunayi shiyasani kuka, nasan ko waye Jameel awajenku mutum ne mai daraja, mai kima wanda shine jigo acikin rayuwarku”.
Kallonsa kawai Ummi keyi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta sabida yadda muryasa ma sai ta Jameel ɗinta.

Shi kuwa Dr Jameel kuwa cikin rauni da zubda hawaye ya cigaba da faɗin.
“Na fahimci kuna jin ƙuna na rashinsa amma Ummi nayi miki al'ƙawari in dai kin amince kun bani dama in sha Allah zan maye muku gurbinsa”....



*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.


By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH

48

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

Ummi kuwa cikin sanyi jiki da raunin zuciya take kallonsa sam, jikinta bai faɗa mata cewa wannan ɗan ta bane, amma zuciyarta yaƙi amincewa da hakan.
Juyawa tayi ta kalli Asma'u da hawaye ke cigaba da zuba daga idanunta, kai ta girgiza kana ta maida idanunta kan Moddibo dake cewa.
“Wallahi Ummi wannan ba Jameel ɗinki bane. Nima kaina na gamsu da komai nashi na *J* ne amma ɗabi'unsa ba irin na *J* bane sam sun bambanta tako wacce siga ta hali da ɗabi'a”.
A hankali Dr Jameel dake durƙushe gaban Ummi ya kalli Modibbo tare da rausayar da ƙwayar idanunta acikin nasa alamar kada ka zubar min da mutuncina agaban idonta.

Numfashi Moddibo ya fesar fahimtar kallon Dr Jameel ɗin yamasa shi yasa yayi shiru...
Innayi, Asiya, Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara da duk suke tsaye daga gefe suna kallon ikon Allah da Al'ajabi na tsanananin kamannin Dr Jameel da marigayi M Jameel.
Zama Ummi ta gyara tare da jan dogon numfashi kana ta sauƙe cikin sanyi tace.
“Shikenan na gamsu Moddibo, na yarda da kai saboda sanin kai nane, baka taɓa yimin ƙarya ba, kuma koda wasa kake min baka min ƙarya aciki, dan haka na yarda na gamsu wannan ba Jameeluna bane”.
Ta ƙare mgnar tare da lumshe idanunta hawaye masu zafin gaske suka zubo kana ta cigaba da faɗin.
“Amma wannan kamanni da yawa yake.
Kuma Alhamdulillah na godewa Allah daya da wannan Rahma da yayi min na nuna min mai kamannin Fuskar Jameeluna har muryarsa irin na Jameeluna da komai nashi fa”.

Dr Jameel kuwa cikin yanayin buɗe war ido, da kuma gskyar zuciyarsa ya kalli Ummi duk da kuwa yana cikin rauni da tausayinsu, a hankali ya fesar da numfashi tare da maida idanunsa kan Asma'u kana Yace.
“Ummi”.
Da sauri Ummi ta ware idanunta dake cike taf da hawaye jin ya kirata da Ummi.
Sake langwaɓar da kansa yayi idanunsa na kan Ummi ya cigaba da faɗin.
“Ummi da zan samu a bani Asma'u in Aura wlh ina so.
Kinga shikenan sai na zame miki ɗanki Jameel In maye maki gurbin shi”.
Ware idanu Ummi tayi tarexa kallonsa cikin mmkin mgnar shi da tazo mata a bazata, sai kuma taji murmushi ya suɓuce mata batare da tace komai ba ta miƙe ta shiga bedroom..

Asmau kuwa, wani irin fitinennen sanyi kalamashi suka sakar mata, so take ta yunƙu ta mike a guje ta bar wurin amman ta gaza hanan, sabida yadda gaba ɗaya guiwowinta suka sake.

Aunty Hajara, Aunty Ruƙayya, Asiya atare suka saki murmushi kana suka miƙe cike da gamsuwan cewa ba Jameel bane kawai dai kamanni ne, domin da Jameel ne bazai ce zai Auri Asma'u ba wannan kalmar kaɗai ta gamsar dasu cewa ba Jameel bane, domin idan M. Jameel ne babu ta yanda za'a yi yace zai Auri ƴar uwarsa ƙanwarsa da suka kasance uwa ɗaya kana suka sha nono ɗaya, da wannan
gamsassun hujjoji suka bi bayan Ummi zuwa bedroom.
Innayi kam murmushi tayi cike da gamsuwa cewa lalle wannan ba M Jameel bane kamanni ne kawai, fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi ta kalli Dr Jameel tare da faɗin.
“Toh an baka”.
Saurin kallonta Moddibo yayi babu walwala atare dashi yace.
“Kece me bada Asma'u koni ne mai bada ita?”.
Still Innayi na murmushi tace.
“Kaine Mai bada ita amma kaima ai ina da iko akan ka”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh kina da iko akaina Innayi, amma ai shi

98 / 140

Chapters